Showing 75001 words to 78000 words out of 124441 words
ta ɗauki ƙara. Ya kai hannu ya ɗauko ta don har tana kokarin shigewa cikin kujerar dalilin danneta da ya yi wurin kwanciya. Ganin Nene ya sa shi miƙewa don ya san shirun da ta ji bai fito ya yi karin safe ne ba dalili, koda ya amsa kuwa hakan ne, cigiyarsa ta ke. Ya ba ta uzurin bacci ne ya ɗan mishi nauyi amma yana tafe. Da haka ya katse kiran.
Koda ya fito falon Nene ya iske Nudrat na sauri-sauri za ta fice makaranta, kamar ya ce ta jira su fita tare ya sauke ta amma kuma yana kwaɓar zuciyarsa da ta ke ta kokarin manna mishi wacce bai san komai dangane da ita ba.
'Idan da amana, har akwai wacce za ka kalla da sunan So bayan Fareedarka?'
Wannan tunasarwar ya fito daga wani sashi na zuciyarsa, haushin kansa ya kama shi har da jan istigfari kai ka ce wani saɓon ya tafka.
***
Ranar Litinin da ya kasance na zuwa makaranta ga Sadiya, sai ta wayi gari da zazzaɓi da matsanancin ciwon kai. Ga test zazzafa da suke da shi, tun a wajen karin safe take ta dauriya gudun kada Inna ta ce ba za ta fita ba sai dai tana kammala shan shayi da wainar ƙwai ta maido su gaba ɗaya. Malam da kansa ya kai ta asibiti sai daga baya da ya kasance har da su ƙarin ruwa ne ya ce Inna ta shirya ta zo.
Nudrat kuwa tun tana kiran layin Sadiya yana ringing ba a ɗaga ba har ta haƙura ganin Malami ya shigo. Koda ta fito ma duk ta yi wuri-wuri da idanu, ita tana ji a jikinta cewa ba fa lafiya ce ta hana Sadiya zuwa ba. Abokan karatunsu ma na ta tambayar ina Triple S kamar yadda sunan ya bi ta sakamakon yawan kiranta da shi da Nudrat ke yi. Ranar ce ta yi takaicin rashin amsar lambar Inna, duk gaishe ta da take yi sai dai su gaisa a wayar Sadiyar.
Bayan ta fito a lakca ta biyu cikin ikon Allah tana ƙara kiran Sadiya ta ji an ɗaga a wannan karon, muryar Inna ta ji, bayan sun gaisa ta ke shaida mata an kwantar da Sadiya. Sosai Nudrat ta ji zancen ya buge ta. Dama tun rabuwarsu ran juma'a ta ce kanta na sarawa, duk kuma a zatonta na ɗan lokaci ƙanƙani ne da zarar ta sha magani shikenan. Ashe da sauran rina a kaba.
Suna ajiye waya sai ga kiran Hammanta ya shigo. Da sauri ta ɗaga gami da amsa sallamarsa.
"Ki na makaranta ko kin tafi? Gani nan dab da wurinku. Ko Sule ya zo?"
Girgiza kai ta yi kamar yana gabanta, murya irin ta mai shirin ɓarkewa da kuka ta ce.
"Hamma ni ko ban gama ba tafiya zan yi. Triple ba lafiya tana kwance a asibiti."
Ta ji ƙarar jan burkin motarsa har sai da ta razana.
"Hamma! Mene ne!" Ta faɗi a hargitse, can kuma ta ji ya amsa.
"No, babu komai. Ki fito bakin gate ina jiranki na kai ki dubiya."
Daga haka ta ji ya katse kiran, ba ta tsaya wani dogon tunani ba ta yi wa wasu ƴan ajinsu biyu dake gefenta sallama ta miƙe da sauri ta kama hanya. Kusan a tare suka iso kofar makarantar, yana tsayawa tana ƙarasowa waje, gaban motar kawai ta bude ta shiga. Shi ma sunan asibitin ya tambaye ta kai tsaye, sai a sannan ta tuna ba ta ma tsaya tambayar Inna ba don haka ta ƙara kiranta. Daga haka ya fisgi mota, Nudrat duk ta damu tana ta ba shi labarin ai dama tun ran Juma'a ta ce mata tana ciwon kai.
"Ayya, Allah ya ba ta lafiya." Shi ne abin da ya faɗi kawai amma kuma a ƙasan ransa gaba ɗaya ji yake ya damu ainun. Tun ganin da ya yi mata a yanzun sati kenan tunaninta bai bar shi ba musamman da kwanakin nan ya ke cike da damuwar Fareeda da ta sauya masa kaɗan. Ba ta ɗaga wayarsa a sadda zai kira hakanan ba kasafai ta ke amsa mishi a chat ba. Sai yake jin kamar ta fi ƙarfinsa, kamar dagaske ne sadda wani abokinsa ya taɓa ce mishi Fareeda ba za ta tanƙwaru ba idan sun yi aure saboda wayewarta ta yi yawa amma sonta da ya rufe mishi idanu ya sa bai taɓa gasƙatawa ba sai yanzun da ya ke jin cewa Sadiya za ta iya yi mishi biyayya da ma soyayyar da bai samu ba a ɓangaren Fareeda.
Haka ya dinga saƙe-saƙensa a zuci, bai ko kula surutan Nudrat ba, yana ji har waya ta yi da Nene ta sanar da ita ba sai Sule ya koma ɗaukarta ba, tana tare da Hamma. Ita kanta Nenen ta jajanta da ta ji batun rashin lafiyar.
***
A raunane ta ke duban Nos din da ke riƙe da sirinji da ta zuƙo ruwan allura za ta yi mata a jijiyar hannu. Turo bakinta ta yi duk ta firgice har kwalla ta gama cicciko mata ta dubi Anti Hafsatu da Inna.
"Don Allah Anti ki ce kar a yi min. Allah kuwa na ji ƙwarin jikina."
Salallami Anti Hafsatu ta yi, wannan ne karo na biyu da Nos din ta yi yunƙurin yi mata allurar, na farko na kuka ta saki tana mammatse jiki ita wai ba za'a yi mata ba.
"Yau na ga abin da ya fi ƙarfina ni Hafsa, ke yanzu ki na matsayin ɗalibar medicine amma ki na tsoron allura? Wato sai dai ki koyi yadda za ki yi wa wasu ke ba za'a yi maki ba ko? Eh shakka babu da aiki a gabanki. Sadiya tun muna shaidar juna ki nutsu a yi maki idan kuwa ba haka ba na sa mazan da ke wajen nan su rirriƙe ki."
Inna da takaici ma ya ishe ta ta kasa magana, Nos din kuwa tun abin na Sadiya na ba ta dariya har ta soma ba ta haushi. Wayar Sadiyar ce ta yi ƙara, ganin Nudrat ce Inna ta ɗaga, lambar ɗakin ta tambaya don haka sai kawai Inna ta fita ta leƙa don ta taho da ita dama takaicin Sadiyar ya gama kai ta bango ji take kamar ta kai mata bugu. Ganin Nudrat da wani matashin bafulatani ya sa ta ɗan saki fuska, Hamma ya russuna ya gaishe ta ta amsa tana tambayar mutan gida. Nudrat kuwa tuni ta nufi ɗakin da ƙawarta ke ciki. Inna ce ta yi wa Hamma iso zuwa ciki. Ganinsu ya sa Sadiya shiga taitayinta babu ma kamar Hamma ɗin da koyaushe ke mata yawo a zuciya da gangar jiki. Kwarjini da kunya suka addabe ta, daƙyar ta iya buɗe baki ta gaida shi don har a sannan akwai zazzabi jikinta da ciwon kai da ya ƙi saurara mata.
Anti Hafsatu ke ba Nudrat labarin wai allurar jijiya za'a yi amma ta ƙi tsayuwa ita kuwa me za ta yi ba dariya ba.
"Our doctor to be, ke ce mai tsoron Injection?"
Sadiya ƙasa-ƙasa ta wurga mata harara saboda kunyar da ta ba ta a gaban Hamma.
"Wa ya faɗamaki tsoro nake ji? Yi min."
Ta faɗi cikin dakiya tana miƙawa Nos ɗin hannunta. Kamar kuwa da wasa ta daure har a ka kammala, ita kuwa ta sani kwarjinin Hamma da ke wurin ne ya jawo haka. Haka kawai ta ji ba ta son bayar da kanta a gabansa. A na kammalawa kuwa ta kwanta ta ja ɗankwali ta rufe fuskarta. Nudrat ta janye.
"Malama ki buɗe ki shaƙi iska. Wai, jikin nata zafi fa."
Ta ƙarashe da hakan sanadin hannunta da ta kai goshin Sadiya, zafi rau.
"Yanzu da sauƙi ai ba kamar ɗazu ba ma." Cewar Inna.
Hamma ya ɗan dubi Sadiya, idanunta a lumshe, fuskar nan ta ƙara ɗanyancewa ta yi fes, kauna da tausayinta suka ƙara mamayarsa, ya ji gwara ya tafi, barin asibitin zai fi zame mishi alkhairi a kan ya zauna zuciyarsa na mishi saƙe-saƙe a kanta. Sallama ya yi musu bayan ya yi mata addu'ar samun lafiya. Nudrat ita ma haka ta bar asibitin kamar ta zauna ta taya su jinyarta ba dai don ranta ya so ba.
Ita kuwa Sadiya tana jin fitarsu wasu ruwan hawaye suka zubo mata, ga zafin ciwo, ga zafin ƙaunar Hamma da ke nuƙurƙusarta. Za ta rantse ba ta da masaniyar sadda son ya yi mata dirar mikiya. Abu kamar almara, a kwanaki bakwai kacal? Soyayyar abin da ba za ta taɓa samu ba na neman gallabar rayuwarta haka nan? Ta tuna, kwakwalwarta ta yi mata tuni ya fi a ƙirga kan batu na kuɗin auren Hamma da za'a kai nan kusa. Toh kuma ai zance ya ƙare, ita har a lissafinta ma gani take yau, gobe ko jibi mai afkuwa zai iya afkuwa.
'Fareeda.' Ta tuno sunan matashiyar da ta gani a hoto a wayar Nudrat da ta nuna mata yau kwanaki huɗu kenan, kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa ƴar gayu ga gogewa, ita ce wacce Hamma zai aura a faɗin Nudrat. Ta ji haushin Nudrat karo na farko a lokacin, to mene ne nata a ciki? Meyasa za ta nuna mata hotonta? Ina ruwan biri da gada?
A sannan ne ta ƙara fahimtar cewa lallai dagaske ta faɗa tarkon son maso wani wanda Hausawa suka ce ƙoshin wahala ne. A nata tunani da tsinkayen ma ta ji fargabar a binciken Likita ya sanar da iyayenta cewa tana dauke da hawan jini, sai kuma akasin haka, ashe Malaria ce ta taso mata lokaci guda.
"Ai ta samu bacci ma. Inna ki je gida mana ni sai na zauna da ita kafin ki dawo ko?"
Muryar Anti Hafsatu sama-sama ya shiga dodon kunnuwan Sadiya. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara runtse idanunta, kanta sarawa ya ke yi ga bakinta kamar ta sha maɗaci. Tana jin sadda Inna ta fice, a haka har bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta.
***
Baccin AbdulMajid ragagge ne a wannan dare, son sanin halin da Sadiya ke ciki ya fi komai tsayawa a ransa. Ranar ce kuna ta farko da bai nemi ko yi wa Fareeda magana a chat ba har wayewar gari.
Koda ya ga Nene ta yi shirin zuwa dubiyar Sadiya har da girkin da Nudrat ta yi mata ya ji dadi don ya sani shi ne ke kai Nene unguwa muddin dai ba wani babban uzurin ne ya taso ba. Baffa na gida sai saƙon gaisuwa da ya ce Nudrat ta miƙa masa ga Triple ɗinta don hatta shi ma ya na shan labarai kala-kala kan Triple.
Sun iske Inna da Malam sai ko Safiyya da su Yaya Hashim da suka zo dubiya. Ranar ce ta kasance ta farko da Inna ta saka Nene a idanu, suka gaisa fuskokin kowannensu a sake. Sadiya a sannan ita ma ta ji kwarin jikinta don tun asuba ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa sai ko hula da ta rufe gashinta da shi.
Malam cike da zolaya yake duban Nudrat ya ce.
"Ɗiyata amma dai ba za ki yi fashin makaranta ba saboda ƙawarki babu lafiya ko?"
Nudrat ta yi dariya.
"Aa, dama yau babu lectures fa. Koda na shiga sai dai mu yi group discussion saboda Lecturer din mu ba zai shigo ba."
"Toh Allah ya kara taimakawa."
Aka amsa da amin.
Nene ta ɗan zauna don ita ce ma ta taimakawa Inna ta sanya Sadiya cin abinci sosai wai bakinta babu dadi. Hamma dama tun fitar da su Yaya Hashim zasu yi shi ma ya fita ya koma wurin mota, hankalinsa ya kwanta da ganin jikin da sauki.
Zuwan Abba dubiyar Sadiya ne ya sa Nene miƙewa don dama tana dab da tashi, sallama ta yi wa Inna da Safiyya da suke faman hira kamar an saba tun can. Babu ma kamar ita da Innar da suka gane su duka biyun daga gari ɗaya suka fito, wato Gombe.
Har waje Inna da Safiyya suka yi mata rakiya aka bar Nudrat zaune gefen Sadiya tana ba ta labarin sun yi test.
"Kai kin fa rame." Nudrat ta furta, ita kuwa ta yi murmushin yaƙe idanunta suka ɗan cicciko da ruwan ƙwalla. Duk sadda za ta ga Hamman Nudrat din sai ta ji kamar ya fama mata gyambon ciwon sonsa da ba ta shiryawa ba, hakanan ta ji ta tsinci kanta a ciki dumu-dumu.
A can farfajiyar asibitin kuwa, Hajara da Husna ce suka iso dubiyar Sadiya. A dole Hajara ta zo gudun kar ta ɓatawa Husna rai tunda ita ta kira tana mata magiyar ta biyo su je tare Huzaif ba ya kusa. Ta ja tsaki ya fi cikin kwando, ta kuma yi wa Sadiya fatan mutuwa ya fi sau a ƙirga daga wayewar garin ranar Talata din zuwa yanzun.
"Ai ba ma sai na kira waya ba, ga Anti Safiyya can da Inna."
Hajara ta kai duba ga inda Husna ke nuna mata, tsaye suke kusa da wata yar dattijuwa da ta yi tsaf cikin kyakkyawar sutura. A gefenta kuma wani matashi ne fari ƙal kamarta yana riƙe da murfin mota yana jira matar ta shiga shaidar tafiya za su yi ne sun fito. Tunanin Hajara da Husna bai wuce su waye su din ba musamman ita Hajara da ta yi musu ƙuri da idanu.
Suka ƙarasa daidai sadda Nene ta shige motar Hamma ya rufe murfin. Inna da Safiyya suka ɗan ja baya don su ba su wuri motar ta fita sa'ilin da Hamma ya shiga mazauninsa ya tayar da mota.
"Ah, Husna, Hajara yanzu ku ke tafe? Sannunku."
Maganar Inna ta sa Hajara dauke kai ga kallon su Nene ta maido hankaki ga Inna. Nan ta gaishe ta a cikin ranta tana ji kamar ta ɗauke ta da mari don ita fa muddin za ta ga Inna fes da ita a kullum to ranta na susa ne. Ga shi dai ba wasu suturu masu tsada ne da Innar ba, amma akwai tsafta da yawan ƙunshi. Koyaushe za ka gan ta tsaf da ita.
Inna ta amsa gaisuwarta da ta Husna, nan ma aka gaisa da Safiyya daga nan suka ɗunguma zuwa ciki.
"Mahaifiyar ƙawar Sadiya ce ta makaranta, Nudrat Mustafa. Tana ma ciki za ki gan ta."
Amsar da Hajara ta ji Safiyya na ba Husna me tambayar ko su waye suka fita yanzun kenan. Ta tuna Nos Nudrat abokiyar aikinta a baya, wato dai duk inda mai sunan nan za ta ɓullo, ba mai kaunarta ba ce. A can din ma ai Nos Nudrat ba abinda ta ke yi gare ta face takura da saka mata idanu a sha'aninta sadda ta ke yawon shanawarta. Yanzun ma ga wata Nudrat din ta fito a ɓangaren wacce ta tsana. Ita kaɗai ta ke so ta fi kowa mu'amalantar masu hannu da shuni cikin yan uwanta, ita kaɗai ta ke son ta yi zarra duk inda za ta shiga a dinga batunta. Amma Sadiya ta ko'ina ta na shigar mata hanci da ƙudundune. Har suka ƙarasa ɗakin ban da tsinuwa ga Sadiya babu abin da ta ke yi a zuciya.
Duk yadda ta kai ga hasaso yanda za ta ga Nudrat din, sai ta ga ashe ta fi haka wayewa da ma tsari. Ga shi dai abaya ce a jikinta, amma hatta da zoben da ke yatsarta na gwal ne. Tashin ƙamshi ta ke yi mai sanyi, sadda suka shiga ma waya take yi tana ta yarfa turanci kai ka ce jikar sarauniyar Ingila ce. Hajara ta ja guntun tsaki a ranta tana hura hanci don a ganinta tsabar son a sani ne da iyayi.
Daƙyar ta cije ta ƙaƙalo yaƙe a saman fuskarta sadda ta amsa gaisuwar da Sadiya ke jifanta da shi.
"Ya jikin? Sannu." Haka ta furta don har zuciyarta ba za ta iya addu'ar Allah ya ba ta lafiya ba koda wasa.
Sadiya ita ma kauda kai ta yi ta mayar kan Husna wacce cikinta ke ƙara fitowa ga hancinta da suka ƙara buɗewa. Duk da yanayin da ta ke ciki bai hana ta darawa kaɗan ba.
"Wai haka ki ka koma? Allah Sarki. Allah ya raba lafiya."
Husna ta ɗan turo baki sadda Safiyya ita ma ke taya Sadiya darawa.
"Kin riga ni furtawa a fili Sadiya. Ki ga yarinya gaba ɗaya ta fashe kamar mai shan yis. Kai ciki masu gari, Allah dai ya sauke ki lafiya Auta."
A shagwaɓe Husna ta dubi Hajara.
"Antina ki na jin su ko? Muni na yi ne?"
"Ko ɗaya, ko kin yi ma sanadin ciki ne da zarar kin haihu za ki dawo daidai."
Nudrat da ta gama amsa wayar fuskarta a sake ta gaishe su. Ta kara da fadin.
"Kun shigo ina waya ne. Amm wannan ce Sis Husna ko?"
Ta nuna Husna lokaci guda tana kallon Sadiya. Murmushi saman fuskar Sadiya ta gyaɗa mata kai. Ita ma Husna murmushin ta yi mata, Hajara kuwa wani kallon banza ta ke jifan Nudrat din da shi kafin ta kauda kai.
Ita sai ta ji zaman ma asibitin duk ya gundure ta, gwara ta wuce gida don ita ma bayan Magriba tana da ganin likitan mata (Gynea Doctor). Sallama ta yi musu ta miƙe, Husna kuwa cewa ta yi ba yanzun za ta tafi ba, Hajara ko a jikinta don a yau ita ma Husnar haushinta take ji don ba ta ga dalilin da za ta saki jiki da Nudrat su yi ta kwasar hira ba.
Sai yamma lis Huzaif ya zo daukarta. Ya shigo yana sunne kai ya gaisa da Inna don Safiyya tuni ta bi Hajara ta rage mata hanya. Sadiya ta gaishe shi kamar babu wani abu da ya taɓa gitta wa tsakaninsu don har ga Allah ba ta jin komai a kansa ya amsa ya yi mata ya jiki. Bai jima ba suka wuce. Nudrat ma daidai lokacin Hammanta ya kira a waya cewa yana harabar asibitin. Ta ɗan ji mamaki don ba ta dauka kuma shi zai dawo ɗaukarta ba, amma da ta yi la'akari cewa lokacin tashinsa daga aiki ya yi sai ta ba kanta amsa ƙila shiyasa ya biyo tafiya da ita gida. Ta yi wa su Inna sallama da Sadiya sannan ta fice da kwanukansu bisa umarnin Inna don tun da rana ta wanke su a can