Showing 87001 words to 90000 words out of 124441 words

Chapter 30 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

haɗa idanu da Sadiya, kirjinta ko ban da harbawa ba abin da ya ke yi, tun yaushe Sadiya ta sani? Tun yaushe ta fahimci asiri ne ya ci Huzaif? Ko kuma dai sanadin hirar ce duk ta ji komai? Ta kasa kwakkwarar magana, sai ita ma Sadiya ba ta ce mata uffan ba ta juya ta kwanta. A hankali ta kwanta ringingine bayan ta kashe hasken fitilar wayarta, hawaye ta shiga fitarwa mai cike da nadama da tsantsar dana sani. Tabbas son zuciya ɓacinta, wataƙila ma da ta yi haƙuri tunda dai akwai rabo tsakani ƙila a ruwan sanyi za ta samu soyayyar Huzaif har ta kai su ga aure. Yanzu ga shi nan sanadinsa ta yi shirka, abin kuma ya zo ya saki Huzaif ya dawo daga rakiyarta. Wannan daren haka ta yi ta juyi sai wuraren Asubahi bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da ita. Daƙyar ta iya miƙewa ta yi sallar ta koma, tana gani Sadiya ta yi zaman yin addu'o'i amma ta sani baccin da ke idanunta ba zai bar ta zama ba.

***
Nudrat ke duban wani bidiyo a wayarta tana kyalkyale dariya, Sadiya kuwa waya ta kammala yi da Hamma sai faman zabga murmushi ta ke. Can ta dubi Nudrat.

"Wai ke ba kya gajiya da shiga shafin wannan Joker ɗin a tiktok?"

Nudrat wacce daƙyar ta saita kanta daga dariyar da take yi ta dube ta.

"Ke kanki ai idan ki ka kalli comedies dinsa ba kya iya riƙe taki dariyar."

Ɗan guntun tsaki Sadiya ta ja har a sannan murmushi ne saman fuskarta ta ce.

"Madam just fall in love, wannan duk shirme ne. A soyayya ce za ka yi kuka, za ka yi dariya, za kuma ka koyi darussan rayuwa."

Nudrat ta saki baki tana kallonta kafin ta tsaida bidiyon da ta ke kallo.

"Allah ko Mrs Abdul? Ah lallai, yarinyar ta kamu da yawa. Yau huɗubar ma ba na maida hankali ga karatu ba ne, a kan so ya faɗa."

Dariya Sadiya ta yi tana ɗan runtse idanunta.

"Gaskiya dai na faɗa maki."

"Na ji, amma ke ma ki bi a hankali. Na kula ki na da zurfafawa a so, ki rage. Don Allah ki rage. Zurfafa abu ba shi da daɗi, ya na haifar da damuwa."

Sadiya ta jinjina kai, dagaske Nudrat ta ke, komai idan ya yi yawa ba shi da kyau. Damuwa ce kamar yadda ta faɗa ɗin. To amma ya za ta yi? Zuciyarta ce a haka, ba ta iya son abu ba. Idan ta na so ba ta iya saita kanta, amma ya ci ace ta koyi darasi a kan na baya. Ko babu rabuwa, akwai mutuwa. Ita ganau ce ba jiyau ba. Duk da haka ta ji tana son sanin dalilin Nudrat na faɗin haka.

"Amma meyasa ki ka ce haka?"

Taɓe baki Nudrat ta yi tana girgiza kai. Har ga Allah ba ta hango irin wannan soyayyar da Sadiya ke yi ga Hammanta ba a ɓangaren yayan nata. Ta san eh yana son Sadiya amma kuma bai gama mance Fareeda ba. Ta taɓa kama sa ma yana waya da ita yana cewa ita ta jefa shi a condition din da yake, ba ta bar sa da kowane option ba face na ya nemi wata kawai. Wannan abu ya yi wa Nudrat zafi, sai ta ji kamar ma ba son Sadiya yake ba kawai dai don babu yadda zai yi ne ya dauke ta matsayin second choice dinsa tunda bai samu ta farko ba.

"No ba fa wani abu bane. Kawai duba da labaran soyayyarki na baya da ki ka ban. Na karance ki, kina da zurfafawa a so."

Sauke ajiyar zuciya Sadiya ta yi.

"Hakane. Zan rage."

Murmushi Nudrat ta yi. Ba jimawa kuma lokacin ɗaukar lakcarsu ya yi suka miƙe zuwa aji.

***
Da wani irin mugun firgici Husna ke ƙara haska ƙasan gadonta.

"Na shiga uku!" Ta ce a fili ganin dagaske babu layun da suke wurin. Dama ai da niyyar ta cire su ta zo, amma kuma suka ce ɗauke mu idan kin gani.
Ta rasa wa za ta kira? Sadiya da suka zo tare da Habiba ƙanwar Zahra suka yi mata gyaran gidan, ko kuwa Huzaif da ta bari a gidan?

Girgiza kai ta yi kirjinta na dukan tara-tara ga kuma Sadik da ke faman tsala ihun kuka yana son abincinsa. Ƙarar tsayuwar motar Huzaif da ta ji a farfajiyar gidan ne ya sa ta yi saurin gyara shimfiɗar da ta bankaɗa sannan ta nufi ɗan gadon jariran da Anti Hajara ta siya musu ta sa hannu ta dauki Sadik ta fito falon tana jijjiga shi. Daidai lokacin Huzaif ya murɗa ƙofar ya shigo da sallama ɗauke a leɓɓansa. Ta amsa gami da mishi sannu da zuwa.

"Kukan me ya ke yi? Ki ba shi mama ya sha."

Bai kula sannu da zuwanta ba, hankalinsa ya tafi ga ɗansa. Husna ta haɗiyi miyau, irin wannan kallon tsanar da ya ke jifanta da shi ne ta tsana. Ba ta ga ko alama yana wani rawar ƙafa ko marmarinta ba, alhalin a baya ko unguwa ta fita ta dawo ya dinga rawar ƙafa da jiki kenan yana sumbatun ya yi kewarta. Haka ta zauna ta shiga shayar da Sadik, shi kuwa ɗakinsa ya nufa bayan ya ajiye mata leda saman teburin dake tsakar falon, ya yi ciki da wata ledar a hannunsa ba tare da ya ƙara uffan ba. Ta dawo da dubanta ga ledar da ke ajiye, irin nasa ne mai tambarin Alheri Suya a jiki.

Tun tana zuba idanun ganin ya fito har dai ta yanke shawarar bin bayansa. Aka ce cikin jego, damuwar da take ciki bai hana ta jin yunwa ba, ta kuwa juye suyar a faranti, ta ɗauko lemun roba mai sanyi da kofuna biyu sai ruwa ta dawo tsakiyar falon ta ajiye saman teburin. Duk da ta gan shi da wata ledar ba za ta ƙi yi masa tayin wannan ba, don ba haka suka saba ba. Sun saba da ci da sha tare. Duk da kirjinta da ke dukan tara-tara sakamakon shakkarsa da ta ke yi a yanzu, hakan bai sa ta yi karambanin ƙarasawa ga ƙofar ɗakin ta murɗa ba, ji ta yi gam a rufe. Ta hau ƙwanƙwasawa a hankali. Kamar ba za'a buɗe ba can kuma ta ji ana cire muƙullin a hankali sannan aka buɗe ƙofar. Kallon juna suka yi tsakar idanu, ta sunkuyar da kai sakamakon hararar da ya ke watsa mata.

"Wani abu aka yi?"

"Um um, dama abinci ne nace ka fito mu ci."

"Naki ne, ga nawa nan zan ci a ɗaki."

Nan da nan ta dube shi tuni hawaye sun wanke fuskarta. Kauda kai daga dubanta ya yi yana wani ƙara tamke fuska. Shi wallahi ta takura masa, ba ya buƙatar ko haɗa idanu da ita. Ga mamakinsa gani ya yi ta kai gwuiwoyinta ƙasa ta durƙusa cikin muryar kuka har da shessheƙa ta ce.

"Don Allah ka yafe min idan wani laifin na maka Dear. Na gaji, zuciyata na shirin bugawa, na kasa sabo da fushinka. Ka taimaka ka faɗa min laifina zan gyara na maka alƙawari."

Huzaif ya sauke ajiyar zuciya, jikinsa ya ɗan yi sanyi. Ko babu alaƙa ta aure tsakaninsu, ita ɗin jinin Malam Sa'ad ce, ta kuma fi ƙarfin wulaƙanci koda kuwa giyar wake ya sha. Ballantana a hayyacinsa ya ke. Bai san me zai yi ba ne, ya kasa controlling kansa da ma damuwar dake cin zuciyarsa. Har yanzu tunani yake akan dalilin da ya kai shi ga cin mutuncin Sadiya a baya har ya tsallake ta ya auri Husna.

"Ki tashi, ba ki yi min komai ba. Tashi don Allah."

Ya faɗi a tausashe, ba musu ta miƙe kuwa.

"Ki je ki ci abinci, ni ma zan watsa ruwa ne zan fito na ci a falon."

Ta amsa da toh. Ko babu komai ta ɗan ji sanyi a ranta. Huzaif ya bi ta da kallo, ya rasa ita zai tausayawa ko kuwa dai shi ɗin da ya wayi gari ba ya jin ko ɗigon zarra na sonta, so irin na aure.

Husna murnarta ya koma ciki sa'ilin da a wajen kwanciya ya yi mata kai da ƙafa, bai kuma nuna alamar koda wasa ya na wani son kasancewa da ita a daren ba. Haka ta dinga sharar hawaye, ƙarshe bacci ya yi awon gaba da ita.

***
Bayan Watanni Biyu..

Hajara wacce laulayi mai zafi ya sako a gaba irin wanda ko ruwa ta sha sai ya dawo, shi ya hana ta maida hankali sosai dangane da al'amarin Sadiya, koda dai ma a yanzun tun daga samun cikinta ta ƙara gasƙata zancen Bokan nata, ta yi amanna ba ya ƙarya, duk abin da ya ce zai faru to shi ke gudana a rayuwarta (Wa'iyazubillah). Tana ji a jikinta kamar yanda ya ce hangen dala ba shiga birni ba, to hakan ce za ta faru ga Sadiya.

Wannan ne ya sa ta ƙara nutsuwa musamman ma da duniya sabuwa ta ƙara buɗewa mijinta bayan jam'iyyarsu sun haye matakin nasara a zaɓe. A gefe guda ga tarairaya da kulawa da yake ba ta, amma ba ta lokacinsa ba sai ta asusunsa. Duk abin da za ta ce tana so, komai tsadarsa to fa za ta ga ya mallaka mata. Ta kuma kula yanzu saboda cikinta sun fara ƴar tsama da Haj Nuriyya uwargidansa. Har baƙaƙen magana ta yarfa mata da ta zo duba jikinta wai Allah dai ya sa ɗan Alhajin ne saboda kamar shi ɗin juya ne, tunda da yana haihuwar a fara gani a kanta mana.

Hajara ta firgita amma ta yi na ƴan duniya ta dake ba ta nuna mata razanarta a fili ba. Ita ma ta yi mata na ƴan duniya ta maida mata amsa daidai da ita wanda ya so zame musu faɗa, sai da ƙawar Haj Nuriyya da suka zo tare ta shiga tsakani ganin Hajarar ta fama laluben waya za ta sanar da Mijinsu wai za'a sheganta masa ɗa.

***
Ɓangaren Sadiya ko, ban da shirye-shiryen biki a yanzun babu abin da suke yi. A sannan ma sun yi hudun satika uku na kammala semester. Biki bai fi sati uku ya yi saura ba. Hafsatu da Safiyya sai ko Adda Ruƙayya da Baba Habu sun je sun ga gidan Sadiya. Haka suka dawo suna ta santi da koɗawa. A waya suka shiga nunawa Inna tana kauda kai saboda jin nauyi.  Anti Hafsatu ta dara

"Oh, Inna an fa bar yayin wannan kunyar."

"Ai Mairama har yanzu fillanci bai sake ta ba. Amma kuma ban ga laifinta ba." Cewar Adda Ruƙayya kenan kasancewar kusan sa'anni suke ita da Inna ko ma ta girme ta da kaɗan.

Shigowar Sadiya gidan daga shagon ɗinki ya sa suka dube ta. Safiyya ta riƙe hanci ta hau guɗa, ita dai ta fiddo idanu waje ma ta soma tunani a ƙasan rai ko yau aka kawo lefen madadin jibin da suka ce?  Sai da ta ji wai duk na taya ta murnar samun muhalli tsararre ne ta ji kunya ta rufe ta.

Dama Nudrat ta fesa mata wai gidan ya yi kyau, ta kula sosai suke kashe kuɗi a bikin nan don hatta lefenta ta samu labari a bakin Nudrat  din wai a Dubai a ka haɗo da yawa a cikin wasu kayayyakin. Sauran kuwa a nan wata yar uwarsu ke haɗawa. An tambayi dai awon undies dinta ta aikawa Nudrat.

"Ke waɗannan ba su ɗauki auren nan naki da wasa ba. Wannan ba uwar miji ba ce Sadiya, Uwa ce. Tana kaunarki."

Abin da Safiyya ta ce da Sadiya kenan sadda Anti Hafsatu  ta ce wai Nene za ta turo mai gyara ta musamman daga Gombe, ƴar Sudan ce amma kuma mazauniyar Gomben,  da za ta zo takanas don Sadiyar ta yi mata gyararrakin aure. 

Murmushi Sadiya kawai ta yi ba ta ce uffan ba sai Adda Ruƙayya ce ta cafe.

"Ke dai bari, don ma fa wai a Kano ne, wani abin na san ba za su gudanar da shi irin yanda suke yi ga al'adarsu ba na aure a Gombe. Su kin ga buɗar kai ma na musamman ne, biki sosai akwai gudanarwa bayan an kai Amarya. Abin sai wanda ya gani."

Ita dai Sadiya ba ta ce uffan ba. Abu ɗaya ta sani, dagaske Nene tana kaunarta, tana kuma murna da farin cikin kasancewarta wacce Hamma zai aura. Fatanta dai komai ya tafi lafiya, ita ma ta nuna wa Nene ƙaunar irin ta ƴa da uwa bayan aurensu da Hamma.

Saƙo ne ya shigo wayarta, ta ɗauka tana dubawa. Hamma ke samar da ita zai shigo anjima da dare. Har wata ajiyar zuciya ta sauke na jin dadin hakan. Zuwa yanzu ta gama fahimtar cewa Hamma har yanzu bai gama mance tsohuwar budurwarsa gaba daya ba, ta gane dole sai tana hakuri da wasu halayyar nasa tunda tana sonsa. Tana ji a jikinta idan sun yi auren za ta iya sauya shi a hankali.  Damuwarta ɗaya, ita din tana son ta ga a na ba ta muhimmanci, ta saba ko Huzaif da Suraj a baya, kusan kullum sai sun gaisa an sha hira. Amma shi Hamma ba ta sani ba ko ita kaɗai yake yi wa hakan ko kuwa ɗabi'arsa ce. Bai cika kira ba, za su shafe tsawon kwana guda bai kira ta ko sun yi magana ba. Idan ta taɓa shi daga baya zai ba ta uzurin abubuwa ne suke mishi yawa amma tana ransa.

Ko yanzu da ya ce mata zai zo da ta lissafa rabon da ya zo gidansu an fi sati biyu. Shi dai ba irin na baya ba ne, amma kuma komai ya yi ta rasa dalili ba ta ganin laifinsa sosai. Ita har haushin kanta take ji da irin wannan makahon so da ta ke masa. Amma hakan bai makantar da ita wajen addu'ar zaɓin Allah ba. Idan alherinta ne Allah ya tabbatar da shi matsayin mijinta.

"Ke wai tunanin me ki ke yi haka kin bar mu da canki-canka?"

Maganar Adda Ruƙayya ce ta katse ta. Sai a sannan ta gane zurfin da ta yi a duniyar tunani. Dubansu take cike da rashin fahimta don har ga Allah ba ta ma san me aka ce ba ake ta canki-cankar a kai.

"Kin tabbatar dagaske mazan ne za su kawo lefen ba mata ba dai ko?"

Sadiya ta gyaɗa kanta kawai a kunyace ba tare da ta dubi fuskokinsu ba.

"To ai shikenan, Allah ya kaimu, abin kun ga zai zo da sauƙi." Cewar Adda Ruƙayya karo na biyu.

Nan kuma aka shiga hira inda Adda ke ba su labarin yadda ake gudanar da al'adun biki a Gombe, ita a ƙarshe ma miƙewa ta yi ta nufi ɗaki cike da zumudi ta buɗe sif din kayanta tana son gano wanda Hamma bai taɓa gani a jikinta ba.

***
Misalin ƙarfe bakwai da mintoci kuwa sai ga shi ya iso. Sai da ta jira suka gaisa da Malam sannan ta shiga falon bayan fitarsa. Sallama ce ɗauke a bakinta, Hamma ya amsa yana dubanta.

Shigar ta mishi kyau, riga da siket ne na wani yadi ruwan makuba sai mayafi da ta ɗora fari. Idan ya ce Sadiya ba mai kyau ba ce to ya yaudara zuciyarsa, amma kuma Fareeda fa? Ba iyakar kyawunta yake so ba ya sani, ba kuma surarta ke fisgarsa kawai ba. A'a, wani irin so ne da ba zai misalta shi ba, irin son da duk abin da ki ka yi ba kya laifi a wurina, irin son da komai nata ado ne a wurinsa.

"Barka da dare. Fatan ka wuni lafiya?"

Muryar Sadiya ta maido shi hayyacinsa, ya sauke ajiyar zuciya. Ita kuwa a ɓangarenta kunya sosai ta ji na irin yanda ya ke bin ta da kallo tun shigowarta falon har ta kai ga neman wuri ta zauna. Zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito don jin daɗi, daga yanayin murmushin da ke saman fuskarsa yayin da ya ƙura mata na mujiya, ta fahimci kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Wato dai ta yi kyau ne fiye ma da yadda ta ke zato, a cewarta.

"Barka dai My Triple. Fatan kina lafiya. Ya hutu? Ya kuma shirin biki?"

"Uhum, lafiya."

"Masha Allah. Ki..."

Bai kai ga ƙarasawa ba wayarsa ta shiga ƙara, ya ciro ta a aljihun gaban rigarsa ya na mai duba sunan kafin ya kalli Sadiya.

"Ina zuwa please. Bari na amsa wannan wayar."

Ta amsa da toh, tana kallo ya miƙe ya fita, can kuma ya dawo. Sai ta kula kamar fara'arsa ta fi ta baya.

"Sorry na zaunar da ke."

"Bakomai."

Hirarsu ma ta zama kamar dai ya rasa me zai ce. Sai ya shiga tambayar ko akwai abin da bai yi ba a gidan a gyara? Ta amsa da a'a, ba ma su yi zancen gidan da kowa ba. Nan ya ƙara sanar mata da batun kawo lefe a gobe. A ƙarshe kuma ya yi mata sallama ya tafi.

Sadiya jikinta a sanyaye ta koma cikin gidan. Tunanin da ta ke yi shikenan? Mintuna goma kacal, har ya tafi? A jimawar da suka yi ba su haɗu ba har ya ƙoshi da hirar?

Haka ta dinga tunani ƙarshe kuma duk ta ture ta yi masa uzurin wataƙila shirye-shirye ne ya ke hana shi kataɓus.

***
Hajara tun tsayuwarta a gaban gidan nasu take cike da zullumi, lefen Sadiya za'a kawo yau? Kuma shi ta zo kallo? Abin kamar a mafarki. To wai ya yake? Wane irin suturu aka zuba? Zai doke na ta a haɗuwa da tsari ko kuwa dai a'a? Mairama za ta zuba ruwa a ƙasa ta sha da wurwuri haka kenan? Ashe ba za ta ƙunshi baƙin cikin ganin Sadiya ta tsofe a gabanta babu aure kamar yadda ta ke muradi ba?

'Na ce maki komai da ki ke gani gaibu ne, wannan yarinya har abada ba za ta auru yanzu ba. Ke mu zuba ni da ke, idan ta auri yaron nan ki zo na maida maki dukkan abin da ki ke mallaka min. Ni ma kuma ki maido min nawa.'

Abin da Boka ya ce mata kenan a jiya da ta shiga wurinsa bagatatan hankali a tashe bayan ta amsa wayar Anti Hafsatu mai shaida mata kawo lefen Sadiya da za'a yi a babban gida. Ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login