Showing 24001 words to 27000 words out of 124441 words
kafin ta dauki wayarta da ta suɓuce ta faɗi a dandaryar tayils din ɗakin nurses din nasu ta fice waje. Wuri ta samu ta zauna tana cika da batsewa, har wani gumi ke karyo mata tsabar tashin hankalin wannan aure na Hajara da aka ɗora. Ta yi ƙwafa gami da girgiza kai. A ranta take faɗin,
'Lokaci ya yi, lokacin da zan fasa ƙwai a gidan su Hajara ya zo. Kowa sai ya shaƙi warinsa.'
Daga haka ta yi wata shu'umar dariya. Ta rantse yanda ta kasa aure a duniya dalilin munanan ɗabi'unta da ake bankaɗawa manema auren a unguwarsu, haka ma Hajara ba za ta yi zaman aure da daɗi ba. Wataƙila ma rufa-rufa ta yi wa wanda ta aura ɗin, amma tana da tabbacin idan ta tona asiri, to fa komai zai faru. Ba ta da lambar kowa a dangin Hajara idan ka cire ta Safiyya da kuma Malam.
Ta Malam ta samu ne sanadiyyar wani lokaci da Hajara ba ta da wayar hannu kuma aka yi sa'a ba ta koma gida lokacin da ya dace ba, hankalin Malam ya tashi. Dalili kenan da ya tako har asibitin, inda Allah ya taimaki Hajara sannan ko fita ba ta fara ba, iskancin nata bai yi ƙarfi ba a sannan. Hankalinsa ya kwanta jin cewa mai karɓar mata na dare wato Nusaiba ita ce ba ta shigo da wuri ba, a dole ta jira kuma kasancewar za ta kawo mata wani saƙo. Sanadin kenan da Malam suka yi musanyar lamba da Nusaibar da zummar duk sadda hakan ya ƙara faruwa zai neme ta.
Wani murmushi ta yi, ta miƙe hankalinta kwance ta ƙarasa aikinta na ranar, lokacin tashinta yana yi ta fice ba ta ƙara yarda ta amsa tarin tambayoyin da Maman Boy ke jifanta da su ba don ita zancen Hajarar ta yi aure ma ba sonsa take ba. Ji take wani malolon abu na tokare mata ƙirji duk sadda aka shiga batun.
***
Inna ta yi shiru ta kasa magana, Malam da shirunta ya nemi tarwatsa kirjinsa ya kasa haƙuri ya ce.
"Mairamu, kin ji abin da na faɗa?"
Murmushi ta yi, murmushin dake ɓoye da maganganu masu yawa da cin rai a ƙirjinta.
"Na ji Malam, Allah ya sanya alheri ya zaunar da su lafiya."
Ya amsa da amin cike da jin nauyin rashin kyautatawar da ya yi na ƙin sanar da ita. Amma ya zai yi da alƙawarin da ya riga ya ɗaukarwa Hajarar?
"Ki yi hakuri Mairamu, ki na da haƙuri. Ki ƙara kan wanda na sanki da shi, ba don na goyi bayan yara ne ya sanya ni shiru ba. A'a, da auren da..."
"Haba Malam, na yi maka ƙorafi ne? Ai ban ce maka komai ba. Har a raina na ji ma Hajara daɗin wannan auren. Kuma dama ai ba komai ke buƙatar bayyana shi ba. Duk abin da ya faru, hakan ne daidai. Kar ka damu. Burinmi ta yi aure, kuma Allah ya karɓi addu'armu. To sai mu yi fata da addu'ar nema musu zaman lafiya."
Malam ya numfasa, ya sani dole ranta zai sosu, ba shi da abin ƙarawa a kai tunda ya san wace ce Mairamu. Daga wannan ɗin da ta furta, to fa ba lallai ta ƙara koda kalma guda ba. A haka suka yi sallama bayan ya sanar da ita batun kawo lefe a goben. Nan ma da toh ta bi sa, ba ta buƙatar tanadin komai ga masu kawowar tunda tana da tabbacin yanda aka yi auren ba ta sani ba, shi ma kai lefen babban gidan ne za su yi ruwa da tsakin karɓa.
"An ɗaura auren Anti Hajara kuma? Ko dai yana nufin za'a ɗaura?"
Sadiya ta tambayi Innarta fuskarta dauke da maɗaukakin mamaki.
"Ki bar mamaki Mamana. Hajara an ɗaura aure. Yar uwarki ce, ki yi mata fatan alheri."
Daga haka Inna ta fice zuwa ɗakinta ta bar Sadiya tsaye baki kuma a buɗe. Dawowarta daga makaranta kenan ko jakarta dake rataye a kafaɗarta guda ba ta sauke ba ballantana a kai ga cire ƙaramin hijabin makaranta da ma takalmi. Au dama shiyasa Husna ta tattare a babban gida? Dama ƙusƙus din da Husna ke yi a waya kenan idan ta shigo ta waske ta katse kiran? Husna ta yi girman da za ta san abu ta kasa sanar da mahaifiyarta? Anya akwai daidai a tafiyar nan ta rayuwar ƙanwarta? Anya Malam da yayyunta sun kyautawa Innarta?
Hawaye take fitarwa masu zafi, jikinta tsabar ɓacin rai har rawa yake yi, daƙyar ta iya jan ƙafafunta da suke neman kasa ɗaukarta ta faɗa ɗakinsu. Nan ma sai da ta yi kuka mai yawa ba don komai ba sai na tausayin Innarta kafin ta miƙe jin Inna na kiran sunanta da tambayar ko ta yi sallah ne ya sa a dole ta share fuskarta ta na amsa murua a dusashe "A'a." Shi ne kawai abin da ta iya furtawa. Ta kula ko a muryar Innar babu alamar abin ya dame ta. Sallamar Anti Hafsatu ne ya katse tunaninta, sai ta ji kamar ma a masu laifin har da Anti Hafsatun idan ka cire Mahaifinsu da ta ji hatta da shi ɗin haushinsu take ji. Kasa fita ta yi bayan ta sauya kaya, duk yanda ta so ta watsa ruwa saboda ƙaiƙayin da jikinta ke yi idan ta cire kayan makaranta amma ɓacin rai bai bar ta ba. Ƙarshe ma tana jin shigar Inna da Anti Hafsatu ɗaki ta zura hijabinta ta fice a gidan zuwa na su Zahra. Ta san dai faɗa ne za ta sha a wurin Innar ta yanda ta fita a gidan ba da izninta ba. Amma da dai ta zauna ta bi Anti Hafsatu da kallon ba ta kyauta musu ba, gwara ta fice a gidan.
Ita kuwa Anti Hafsatu kuka sosai take yi a gaban Inna, ta rantse ta kuma kan cewa ba ta san da batun auren ba. Inna ta yi murmushi, ko Zakari ma ya kira ta daga Daura, ya kuma ba ta hakurin abin da Malam suka aikata mata. Inna ta girgiza mata kai.
"Haba Hafsatu, mene ne na kukan? Ni fa tunda har Hajara ta yi aure, wannan farin cikin ya tafiyar da kaso mai yawa da damuwar ɓoyon da aka yimin ya haifa min a zuciya. Babban burinmu bai wuce mu ga ta yi aure ba, kuma sai ga shi nan Allah ya karɓi roƙonmu. Don Allah ki daina kukan nan. Ba su kyauta maki ba tabbas matsayinki na babbar yayarsu mace, amma kar ki duba hakan. Ko me suka yi ai da sanin Malam suka aikata shi, don haka ki yi haƙuri, kuma ki saka a rai ba komai ba ne hakan. Kar na kuma ji kin ce ba za ki saka hannu a hidimar bikin ba, yar uwarki ce. Kuma kin fada ta je har gidanki bayan an daura ta sanar da ke da kuma dalilin ƙin faɗamaki a farko, to ki yi hakuri, ta ci albarkacin cewa ita din yar uwarki ce da ku ka fito ciki ɗaya. Ke ce matsayin Uwa a wajenta, don Allah ki shiga a yi komai da ke. Idan har na isa da ke."
Anti Hafsatu dake jan majina wanda ya taru sanadiyyar kukan da ta ci tun ma kafin ta ƙaraso gidan, daƙyar ma ta iya tuƙo kanta a motar.
"Kin isa da ni Inna, wallahi kin kai maƙura wajen isa. Duk umarnin da ki ka ba ni matsayinki ta Uwa a gare ni ba zan watsa maki ƙasa a ido ba. Ina ƙara neman gafararki bisa abin da ya riga ya afku."
Inna ta share ƙwallarta, wannan ƙauna da Hafsatu ke nuna mata ba ta jin za ta mance da ita har abada.
"Na gode Hafsatu. Allah ya ƙara wa rayuwarki albarka. Ni dama ban riƙe su a raina ba. Komai ya wuce. Allah ya sa a yi lafiya a kammala."
Anti Hafsatu ta amsa da amin.
"Sadiya! Ko ba ta dawo ba?" Cewar Hafsatu tana maido idanunta kan Inna. Ita kaɗai ta tambaya don dama Husna ta tare Hajara ta je da ita can gidanta.
Inna ta girgiza kai.
"Ta dawo, amma kuma na ga sadda ta fice a gidan ta tagar ɗaki. Ina kyautata zaton gidan su Zahra'u ta tafi."
Ajiyar zuciya Hafsatu ta saki, ta kula Sadiya fushi take da ita kenan. A baya matukar ta zo gidan to fa duk abin da take yi tana sakinsa ne ta tarbe ta da fara'a.
Aikuwa miƙewa ta yi tace sai ta shiga ta kira ta. Duk yanda Sadiya ta kai ga kaucewa haɗuwarsu sai da Hafsatun ta jawo ta suka komo gidan, ita ma nan ta jaddada mata rashin saninta kan batun daga ita har Zakari, sosai Sadiya ta fahimce ta har ta ji kunyar yanda Antin ke faman ba ta haƙuri. Zuciyarta ta yi wasai.
***
Washegari aka kawo lefen Hajara akwati har saiti uku, nan fa babban gida ya ruɗe. Kowa ya na faɗin dama ai jinkirin alheri ne. Lokacin Hajara da Husna suna can wani katafaren shago na gyaran Amare ana mata gyara jiki, a waya Safiyya ta yi musu bidiyon kayan duk suka ruɗe, Hajara kanta ya ƙara fasuwa sosai. Husna kuwa kwadayi da burinta a kan auren mai kuɗi na ƙaruwa don ta kula komai sai da kuɗi yake samuwa cikin sauƙi a rayuwa.
Gwaggo Saratu ta rasa ina ta saka ina ta ajiye tsabar farin ciki da daɗi.
Inna Mairamu ta je karɓar lefe wanda sam Sadiya ba ta so hakan ba don har kuka ta saka na takaici.
"Mamana ina yi wa Hajara kallon da nake maki, na ɗauke ta tamkar ɗiyar da na haifa a cikina. Wannan abu da ya faru, haka dama tsarin yake, zai farun babu yanda muka iya. Babu komai, watarana sai labari, zan je, zan shiga na haɗa idanu da Saratu na taya su murna da addu'a."
Wannan ne amsar da Innar ta ba Sadiya. Aikuwa dai ta sha habaici da baƙaƙen maganganu wanda duk iyakar dauriyarta sai da zuciyarta ta karye. Da wannan ƙaton raunin da aka haifar a zuciyarta ta bar gidan ta koma nata.
***
Sati na zagayowa aka fara biki, an yi kamu a nan cikin babban gida kafin a tattara a koma gidan Malam inda ta nan Hajara ke so a miƙa ta ɗakin aurenta. Ranar ne kuma masu kai kaya suka je aka dawo ana zuba uban santi na girma da tsaruwar gidan don a cewarsu har da wajen wanka. Wato swimming pool.
Hajara na ta faman dariyar tsokanar da wata abokiyar wasansu Baba Suwaiba ke mata wai ita ce ya dace ta auri Alh Nuhu ba ita ba, a gefe kuma wata babarbariya da ta zo gidan takanas tana reramata kitso don ba ta son zama babu kitson tunda tana da gashi mai tsawo da cika, wanda gadon gidansu ne. Kusan kaf dinsu sai kalilan, su na da gashi mai yawa da kuma laushi. A ranar ne kuma za'a fita yinin bikin da aka kamawa ƙaton hall kuma mai tsada.
Ƙarar wayarta ce ta sa Husna da suke tare a ɗakin ta miƙa mata tana ambaton sunan mai kiran, 'Nussy'.
Hajara ta karɓa da sauri ta ɗaga gami da karawa a kunne tana dariya.
"Mutuniyar, ke ma na maki surprise ko?"
A bangaren Nusaiba ita ma dariyar ta yi ta amsa da fadin.
"Hajjo kenan. Na kuwa ga surprise da ki ka ba ni. Amma kuma ni ma na aikomaki da wani surprise din. Ki na iya duba whatsapp dinki." Daga haka ta katse kiran.
Jin haka ya sa Hajara fiddo idanu kaɗan. Tuni mai mata kitso ta saki kanta ganin ta ƙi tsayawa gudun kar ya ƙi yin kyau. A fili ta ce.
"To Nussy ko ke ma auren ne ya zo?"
Duk a zatonta ko katin gayyatar biki za ta gani, sai dai ganin hoto ɗaya da ya buɗe ya sa ta saurin miƙewa ba tare da ta kula kowa ba ta fito ta faɗa falon Malam don babu kowa a ciki.
Ita ce dai, ita ke tsaye da wani saurayi wanda ke riƙe da ƙugunta, yayinda ita kuma ta zuro harshe shi kuma ya kama da nashi bakin aka ɗau hoton. Ba ma wannan kaɗai ba, wani tana tsaye a club cikin shigar rashin mutunci, wani kuwa bidiyo ne mai kyau tana rangaji bayan ta kwantar da dukkannin jikinta a saman kirjin wani matashin saurayi. Akwai wanda ma suna zaune a dakin saukar baƙi na Zuma Hotel.
Jin muryar Husna ya sa a gigice ta saka wayar a key.
"Anti meyafaru?" Ba ita kadai ta shigo ba, har da Safiyya wacce ta biyo ta. Ta yi kokarin saita fuskarta da murmushin yaƙe ta amsa.
"Babu komai. Ina zuwa."
Daga haka ta koma ɗakin zaure wanda yake mallakin samarin gidan kafin su yi aure. Ta ci sa'a sai yara kawai suna ta wasa da fararen kujerun da aka yi amfani da su a jiya ranar kamu. Wayarta dake ƙara ta ɗaga, kafin ta ce komai Nusaiba ta soma magana.
"Na tabbata surprise dina ya fi naki girma ko? Kar ki damu, wannan ba ke kaɗai na turawa ba, yanzu haka Malam yana can hankalinsa a tashe. Kayya, ina fatan ma kar damuwa ta sanya shi faɗuwa."
Cikin muryar kuka da tashin hankali Hajara ta zube warwas a ƙasa har yaran da suke cike a falon Anti Kubra suna kallon maimaicin shirin Dadin Kowa suka dube ta. Wannan karon ba ta ko damu da wanzuwar kowa a wurin ba ta ce.
"Allah ya isa tsakanina da ke Nusaiba! Ashe dama ba ki da mutunci? Cin amanar da za ki yi min kenan?"
Dariya sosai Nusaiba ta saki.
"Ba ki da lokaci Hajjo, ko kaɗan ba ki da lokacin kuka yanzu. Ki tseratar da mutuncinki daga jin kunyar duniya ki nemi Malam kafin ya kai ga buɗe saƙona. Idan kunne ya ji..."
Ai ba ta bari ta ƙarasa ba ta fito a guje ta koma ɗaki har tana tunkuɗe matar ɗan uwan Malam mai suna Anti Kubra dake shirin tafiya kwalliya.
"Lafiya?" Haka kowa ke faɗi, tana shirin fita a ɗakin ba tare da ta amsawa kowa ba sai ga Malam ya leƙo ta falonsa yana tambayar wata da ta fi kusa da ƙofar falonsa Inna Mairamu.
Hajara na ganinsa ta nufe shi, koda ta ƙarasa ya dube ta ganin duk ta ruɗe.
"Autar Mama, lafiya? Meyafaru?"
"Shi ne tambayar da muke ta yi mata, ta shiga ta fita tana gudu tamkar wacce aka jefa."
Faɗin wata daga cikin facalolin Inna Mairamu kenan. Hajara kuwa ganin yanayin Malam ya tabbatar mata da cewa bai buɗo saƙon Nusaiba ba, ta yi wa kanta faɗa ta saita fuskarta sai kuma ta wayance da fashewa da kuka. Ganin haka Malam ya kama hannunta ya ja zuwa falonsa, babu wanda ya bi bayansa. Nan aka hau taraddadi da tsoron meke afkuwa. Gwaggo Saratu faɗi take.
"Na rantse idan har Mairamu ce ta yi wani ƙullin na zautar min da ɗiya sai na ga bayanta! Ba zan ƙyale ba idan Hajara ba ta shiga gidan aurenta ba wannan karon!"
Karaf a kunnen Sadiya wacce shigowarta kenan daga gidan su Zahra'u. Baƙin lalle aka zizara mata a hannu ba don ta so ba sai saboda Inna da ta ce ta je a yi ɗin kar a ce wani abu. Gudun ɓacin ran Innar ta yi iyaka baƙin. Ta dubi Gwaggo Saratu dakyau sai kuma ta haɗiye zafafan kalaman da ta yi niyyar yi don ba tarbiyyar da Inna ta ba ta kenan ba. Ba ta kula kowa ba ta nufi ɗakin Inna. Nan ta tarar da Dada tana faman yi wa yaranta mata faɗa don Rukayya ta dage sai ta fita ta rama wa Inna. Innar ma cewa ta yi babu ruwanta.
"Haka za'a cigaba da faɗamaki ki na kyale su Adda Mairamu? To na rantse duk sadda waccan banzar dumɓarun ta ƙara faɗamaki baƙar magana a gabana sai na gwabje bakin ƴar banza!"
Cewar Ruƙayya kenan wacce ta fi Fatima da Murjanatu ɗaukar zafi. Ita Fatima kawai hawaye take fitarwa don rauni ne da ita sosai. Dada ta taushe su sosai ta ce a bar zancen. Daƙyar Rukayya ta nemi wuri ta zauna. Sadiya dama jikinta duka ya yi la'asar hawayen ma sun ƙi fita.
"Ita kuma waccan shashashar bari ta zo ta same ni tunda ba ta san zafin Uwa ba." Ruƙayyar ce dai ta ƙara faɗi, tana nufin Husna don gaba ɗaya haushi take ba ta.
***
Duk iyakar binciken Hajara a wayar Malam ba ta ci karo da saƙon Nusaiba ba, hankalinta ya yi mugun kwanciya sai dai ba duka ba, ta sani tunda Nusaiba ta furta za ta yi, to fa akwai alamun aikatawar. Ta samu ta toshe tashin hankalinta da cewa Malam ai ji take kamar za'a ce Alh Nuhu ya sake ta shi ne take jin firgici ta ruɗe. Haka ya dinga yi mata wa'azi don dagaske ya yarda da abin da tace ɗin. Sai da ya shiga ɗakinsa ne ta yi nasarar ɗaukar wayarsa.
"Me kike so?"
Saƙon da ta tsinci kanta da turawa Nusaiba kenan.
"Miliyan ɗaya." Ta maido mata martani. Hajara ta numfasa, har lokacin dai Malam bai kai ga fitowa a ɗaki ba. Dama karshen sati irin yau Asabar, ba ya zuwa kasuwa wani lokacin yakan huta a gida, ko kuma ya je can babban gida.
A take Nusaiba ta turo lambar akawun, ga mamakinta kuwa a take Hajara ta aikamata kudin. Ta bi ta da saƙo.
"Kar ki kara Nusaiba, kar ki ƙara yi min barazana tunda na sallameki."
Daga haka ta samu nutsuwar zuciya sosai, ta kashe wayarta ta kuma dauki wayar Malam ta lalubo lambar Nusaiba ta rufe daga kira da ma kan whatsapp yanda ba za ta same shi.
Sai dai kuma ba anan gizo ke saƙar ba!!
©Rufaida Umar
https://chat.whatsapp.com/FQc8pWPPMQe2IE1dUoteD1
*Hajjaju kindade kina Neman inda Zaki dinga sarin kayayyaki domin kisiyar kisamu riba?😄😃... Sha kurumin ki yar uwa Maza kishiga wannan group din Mai albarka domin samun kaya masu inganci d kuma rahusa*💃💃💃
*Muna kawo kaya daga china, Lagos d kuma sauran wurare. Muna saida bags, shoes, jewery, kayan yara, sleeping dress da kuma sauransu. Kayayya kinmu a gida suke d kinsiya xa'a Miki delivery sharp sharp*🥰💃
SANNNAN GA MASU SON FARA BUSINESS BASUDA JARI ZAKU IYA REPOSTING KAYANMU KU DORA RIBARKU AKAI WATO DROPSHIPPING😍 muyi ma