Showing 60001 words to 63000 words out of 124441 words

Chapter 21 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

kansa Abba koda ya ji, hakan ya yi mishi daɗi sosai. Ya ce a karo na biyu ma ya ɗaukewa Malam nauyin kayan ɗakinta.

Cikin hukuncin Allah ranar da ta kama Laraba aka kawo kuɗin Sadiya har dubu ɗari da hamsin kuma aka tsaida aure bayan babbar sallah da kwanaki. Mutane da yawa sun taya ta murna. Anti Hafsatu da Safiyya har gida suka zo da wasu cikin matan yayyunsu. Hajara kuwa washegari ta iso gidan. Fuska a sake ta taya Inna murna, Sadiya ta gaishe ta. Ta amsa a ciki-ciki tana jin wani irin tsanarta na mata yawo. Yarinya kamar aljana kullum ba ta sauyawa sai ma kyawun da ta ke ƙara zubawa. Kirarin da wata a danginsu ta taɓa yi wa Sadiya har gobe yana yawo a kanta kuma yana mata zafi, ita ta ma rasa dalilin da yasa ta kasa mantawa.

'Ka ganta kamar wata ɗawisu. Ke dai kin fita zakkah a yaran Malam Sa'adu. Matar manya, farar mace alkyabbar mata.'

Wannan abu ya yi mata tsaye a rai kuma abin haushin duk sadda ta gan ta sai kirarin can ya faɗo nata. Daƙyar ta saita fuskarta ta tattara ta bar gidan don ba za ta iya wuni har Malam ya zo ba. Ta dai yi ƙarfin halin haɗa Husna da Sadiya a waya ta mata fatan alkhairi. Hajara ta ƙara nunawa Sadiya ta yi hakuri ta dawo zumunci da ƴar uwarta, dama matar mutun ai kabarinsa. Ita dai Sadiya ta amsa da toh, a duniyarta ba ta ji har abada za ta amince wai Anti Hajara da zuciya ɗaya take ƙaunarta. Ta sani zallar makirci ne.

Bayan tafiyarta ne Inna ta ke yiwa Sadiya faɗa kan rashin sakin jiki da ta kasa yi ga Hajara.

"Ƴar uwarki ce, tunda yanzun tana kokari wajen nuna tana so a yi zumuncin, ke ma ki manta da komai ku zauna lafiya."

Sadiya da mamaki ta dubi Innarta.

"Wannan saurin yarda haka Inna? Anya ba ki yi gaggawa ba? Anti Hajara fa, matar da ta dube ni gaba da gaba ta furta min kalmar tsana tun yarinta. Matar da akan kunnena ta furta ba amin ba sadda Abba ya yi kyakkyawar addu'a ga rayuwata. Inna don Allah kar ki gasƙata matar nan."

Inna murmushi ta ɗan yi.

"Kyakkyawan zato yana da kyau a addininmu. Babu amfanin zargi kan abin da bawa ba shi da haƙiƙanin masaniya a kai. Allah ne kaɗai masanin abin da ke cikin zuƙatanmu. Koda yanzun da biyu take yi mu yi mata fatan ya juye ya zama na gaskiya."

Sadiya dai ta ja bakinta ta yi shiru, ta sani zuciyar Inna ba irin nata ba ne. Irin zuƙatan salihan bayin Allah ne da suke da saurin yarda da kuma saurin yafiya da haƙuri. Wannan yasa ta dawo da magiyar da ta fara yi ga Inna tun kafin zuwan Hajara akan ta ziyarci Gombe kafin aurensu. Inna ta miƙe ta kama hanyar shiga ɗakinta tana ba ta amsa.

"Mun gama wannan batun ai Mamana, na ce ki tambayi mahaifinki. Idan ya amince sai ki bi Dada ku je tunda za ta je bayan sallar, sai ku dawo kafin auren."

Sadiya ta ɗan tura baki, ta sani sarai Malam ba zai yarda ba cewa zai yi a bari har a kammala biki. Ita kuwa tana son ta je garin ta ga danginsu da ba ta sani ba don ko wancan lokacin aurenta su ma can Gomben suna biki bai fi mutum biyu ne suka zo ba cikin tsoffin sai ko maza ƴaƴan ƙanne. Haka suka juya da jimamin sauyin Amaryar da aka samu. Ba ta da tabbacin kuma Inna ta gayyace su wannan na biyun.

Kiran wayarta ne ya sa ta watsar da batun zuwa Gombe ganin Suraj ne. Ɗaki ta shige suka sha hirarsu kafin daga bisani su yi sallama. Tana ajiye wayar ta ga saƙo ya shigo, ba ta da masaniyar lambar ko na waye, amma kuma tana karantawa ta fahimci Husna ce.

'Hello yar uwata. Wannan ne lambar wayata. Don Allah ki adana a wayarki. Love you. Husna Sa'ad.'

Ta yi murmushi, ai ita dagaske ta maida komai ba komi ba, da haka ba ta kasance ba ai ba za ta san da Suraj ba. Kai tsaye ta adana lambar ta aikamata da amsar "Ok.

***
"Zai yiwu a tsaida auren ta hanya ɗaya."

Hajara ta zuba wa ƙasurgumin bokan idanu. Jira take kawai ya faɗi hanyar ita kuma a shirye take ta bi. Ba ta ji kuma ko ɗarr ba da buƙatarta da ya nuna. Ta yarda ta kuma amince ta haɗa jiki da shi duk ƙazantarsa kuwa matuƙar komai zai tafi daidai.

Sai da Hajara ta shafe awanni uku a gidan Boka sannan ta fito ta tuƙa mota zuwa gidanta. A hanya ta tsaya kusan sau biyu yana kwara amai a gefen titi sannan ta tayar ta wuce. Tana ƙarasawa a gaggauce ta shige ɗakinta ta faɗa wanka. Ba ita ta fito ba sai da ta ji daidai, zama ta yi da ɗaure ƙirji tana maida numfashi sannan ta tunano zancen da Boka ya yi na ba ta tabbacin fasa auren Sadiya da Suraj a ranar da zai kasance na shafa fatiha.

Dariya sosai ta shiga ƙyaƙyatawa gami da yin ƙwafa. Idanun Inna kawai take haskowa a ranar.

"Baƙar munafuka, sai kin yi kukan jini akan Sadiya. Yanzu aka fara wasan. A ranar aurenku wannan ɗin ma zai fasa mu ga ta tsiya."

Ta furta a fili cike da annashuwa kafin ta miƙe don sanya sutura a jikinta ran nan fari sol.

***
A kwana a tashi ba wuya cikin hukuncin Allah, babbar sallah ta zo. Ana gobe sallah gaba ɗaya gidan kowannensu ɗauke da azumin arfah. Ita kuwa Sadiya jikinta gaba ɗaya a ranar wani irin sanyi ta ji ya yi ta kuma rasa dalili. Tun wayewar garin ranar take jin kasala da faɗuwar gaba. Ta kuma saka a rai ƙila ciwon cikin da Suraj yace mata ke damunsa ne sila. Inna ce ƙarfin ayyukan gidan a ranar, ba ta san meke damun ɗiyarta ba amma sanin da ta yi sam ba ta da ƙi wuyar aiki ya sanya ta yi mata uzuri.

Dab da shan ruwa tana zaune tana karatun Alkur'ani ta ji shigowar Malam. Inna da ke zaune gefe ta miƙe ta shiga falonsa. Ta tsaida karatun ta ɗaga hannu ta yi addu'o'i masu tarin yawa ta shafa. Daidai sadda ta ji muryar Malam yana faɗin
"Inna lillahi wa inna ilaihir raaji'un! Ya rasu? Yanzun nan?"

Sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Ta yi saurin dafewa, waye ya rasu? Tunaninta ya ba ta kodai ɗan yayan Malam ɗin ne da aka ce yana asibiti kwanaki biyu yana jinyar ciwon hanta ne ya rasu. Sai da wayarta ta yi ƙara ta duba ta ga sunan Zahra na yawo ta ɗaga a gaggauce amma kuma ta kasa cewa uffan. Cikin muryar kuka Zahra ke faɗin.

"Sadiya kin ji rasuwar Suraj ɗinki ko? Wai tun yamma ya rasu a ɗakinsa ba a sani ba sai ..."

Ba ta bari ta ƙarasa jin ta ba ta yi wurgi da wayar ta miƙe tana salati cikin ɗaga murya. Kai da ka ji ka san a gigice take.
"Ciwon cikin ne ashe dai shi ne ajalin Suraj, ya azumci dukkan azumin ranakun nan, na Arfah dai Allah bai nufa zai yi shi ba. Babu abin da zan ce sai Allah ya ba shi aljanna maɗaukakiya don iyakar biyayya Surajo ya yi min."

Kalamin da suka fito daga bakin mahaifiyar Suraj su ne suka ƙara raunana zuƙatan mutanen dake zaune a tsakar gidan ciki kuwa har da Sadiya wacce ta kwantar da kai jikin Safiyya tana kuka. Ranar sallah ta zo musu a hagunce. Gaba ɗaya ahalin gidansu idan ka ɗauke Hajara da Husna babu wanda bai shigo gidan su Suraj gaisuwa ba. Malam da Abba da ma wasu cikin dattawan iyayensu tare aka yi jana'iza da su.

Sai yamma suka bar gidan kowa na jajantawa Sadiya gami da yi mata addu'ar samun madadin Suraj. Ta nemi ɗokin sallar da take yi ta rasa, tsoron Allah na ƙara ratsa ta. Wato ɗan adam ba a bakin komai yake ba, kwanakin biyu da suka wuce hatta da wayewar garin ranar suna maƙale da juna a waya. Tana tunano maganarsu ta ƙarshe inda yake ce mata.

'Ina sonki Sadiya, inama zan iya buɗe maki ƙirjina ki ga yadda ƙaunarki ta cika min shi. Amma ba komai, ke dai ki taya ni addu'a, Allah ya tashi kafaɗuna. Ya nuna mana auren nan.'

Kafin ta yi magana ya ƙara faɗin.

'Honeyna zan kira ki idan an sha ruwa, daƙyar nake wayar nan. Na bar ki lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu.'

Wannan ita ce ƙarshen kalaman da suka shiga tsakaninsu, ko saƙo na addu'a da magiyar ya koma asibiti da ta aikamasa tana da tabbacin bai karanta ba.

Hawaye masu zafi suka kwaranyo mata, ta sa hannu ta ɗauke su. Da ido kawai take bin yaran yayyunta da suka zo musu barka da sallah. Wasanninsu suke sha bayan kammala cin abinci. Ji take inama ta dawo su, ba su san wata aba soyayya ko ɗacinta ba. Rayuwar ma ba su gama tantance meke cikinta ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta mike riƙe da kayayyakinsu da Inna ta saka su cirewa saboda zafin gari kuma kar su ɓata.

Tana shiga ɗaki babu jimawa ta ji ihun yaran na yi wa Husna da Hajara oyoyo. Hajara faɗi take.

"Kai ku bi min Momina a hankali mana kar ku kayar da ita."

Sadiya ta yi juyi saman gado ta ɗauke sabbin hawayenta. Ta ji sadda Inna ke musu maraba har da gaisawar da suka yi. Husna ce ta soma tambayarta, ko sakanni ba ta ƙara ba ta faɗo ɗakin. Tun faruwar wancan al'amarin, sai yanzun ne suka yi ido huɗu da juna. Sadiya ta yi mata ƙuri da idanu, cikin da aka ce tana da shi bai kai ga nunawa amma kuma ta yi ƙiba, fatarnan ta murje ta yi fes da ita.

'Duk abin da ba rabonka ba ne, ba ka taɓa samunsa. Ba ki faɗa min ba, amma kin sani, ba a rasa masu tsegumi a sha'ani na aure. Ki saka a ranki dama rabon ƙanwarki ne wancan ɗin. Ni Suraj ni ne nan mijinki da yardar Allah.'

Ta tuno wasu shuɗaɗɗun kalaman Suraj, sai ta tsinci kanta da murmushi lokaci guda kuma hawayenta ya zubo. Husna ta rungumeta ta saka kuka zuciyarta ɗaya, dagaske ta ji mutuwar saurayin ƴar uwarta. Tana ƙaunar Sadiya, sanadin Huzaif ne ya sa ta juyamata baya. Amma kuma ta yi murna jin cewa ita ma ta mance da Huzaif ɗin ta samu Suraj. Mutuwar Suraj ɗin ta jefa Husna cikin hali na tausayin ƴar uwarta.

"To kuma ke haka ake yi? Maimakon ki taushe ta, sai ki zube ku yi ta kuka? Ya isa haka don Allah."

Suka maida duba ga mai maganar, Hajara ce tsaye, ta sha adonta na wani arnen leshi da zai haura dubu sittin. Fuskarta ta sha kwalliya kai kace ba gaisuwar mutuwa ne ya kawo ta gidan ba. Sadda labarin rasuwar ya same ta ta hanyar Yaya Hashimu sai da ta kusan sakin dariya. Labari ne na bazata don ba ta tsammaci hakan ba. Ta gama tsara aikin rabuwarsu, sai ga mai gaba ɗaya ya afku, wato mutuwa. Ta tsinewa Bokanta a ranar ya fi a ƙirga saboda haɗa jiki da ta yi da shi ga aikin a sauƙaƙe Allah ya ɗauki ran bawansa.

Sadiya ta kauda kai ga barin kallon Antinta tana goge fuskarta. Gaishe ta ma a yau ta kasa, ko ba a faɗa ba ta san Anti Hajara ba wani jin mutuwar Suraj za ta yi ba. Dama ba ta sa a kai ba. Kullum fatanta Allah ya tsallakar da Husna daga makirci irin na Antin tasu.

"Sannu Sadiya. Allah ya ji kan Suraj. Har ina cewa Alhaji zan ɗauki nauyin kai ku Umarah? Ashe ma mutuwa zai yi."

Sadiya ta dube ta dakyau, kalaman ƙarshe sun mata zafi. Sai kawai ta sauke kanta tana wasa da yatsunta. Ai mutuwa tana kan kowane bawa, lokaci kowa ke jira. Inda Suraj ɗinta ya je, dole dukkansu a wayi gari watarana sun je. Husna ta dinga tambayarta ko dama can yana ciwon cikin ko kuwa na lokaci ne, ta amsa mata kawai zuwa ya yi. Hajara kuwa chatting ɗinta take yi tana sheƙa dariya ƙarshe ma ta bar gidan wai tana sauri ana jiranta suna da walima na tsoffin ɗalibai na makarantar koyon jinya da ta yi.

Husna kuwa sai wuraren ƙarfe takwas Huzaif ya zo suka tafi. A lokacin ne Sadiya suka hadu ta gaishe shi ba yabo ba fallasa shi kuwa da rawar murya ya yi mata gaisuwa ta amsa ta yi godiya duk don idanun Malam da mutanen dake gidan don har a sannan wasu cikin yaran ba su tafi ba, kwana zasu yi. Hatta da su Meenat su Radeeya da Lubna da Anti Amarya sai da suka zo mata gaisuwa. Mamin Huzaif ita ma daga baya ta zo. Zahra kuwa tun a ran farko dama da ita aka je gidan su Suraj. Ta kara dawowa har gida daga baya suka ƙara jajantawa junansu.

***
An ɗauki tsawon lokaci kafin Sadiya ta cire damuwar rashin Suraj, ta sani koda ace za ta manta ba komai ba, wasu abubuwan sai a hankali. Watanni biyu da yin sallah kiran Malam ya risƙi daga Sadiya dake zaune a ɗakinta tana gugar kayanta a dalilin wutar da aka kawo. Ta kashe dutsen gugar ta bi bayan Inna ƙirjinta na ɗan bugu da sauri-sauri. Ba ta san dalilin wannan kira ba, amma tana ji a jikinta mai muhimmanci ne.

Sallama ɗauke a leɓɓanta ta shiga cikin falon bayan Malam ya amsa. Durƙusawa ta yi gefe guda shi kuwa kallonta yake ɗauke da murmushi yana ƙara yaba nutsuwar ɗiyartasa, ya kuma gasƙata amininsa da ya ce ta bambanta da ƴan uwanta a fagen hankali da nutsuwa.

"Yau na zo maki da albishir mai daɗi, kuma ina fatan za ki yi murna da ji."

Sadiya ta ɗago kai tana duban Malam da har a sannan murmushi ne saman fuskarsa. Sai ta ji hankalinta ya kwanta. Kafin ta ce wani abu ya ɗora.

"Ni da Abbanki mun yi magana, ko kuma ince ya nema maki alfarmar a kyale ki ki cigaba da karatunki. Ya ce da zarar an soma shirin zana Jamb za ki yi in sha Allahu. Sai ki shiga shiri."

Ta ji kamar a mafarki, lallai wannan albishir ne mai girma da ta jima tana fatan ya kasance. Kawai sai ta faɗaɗa fara'arta, a gefe kuma hawayen farin ciki.

"To mene abin kuka? Ai abin murna ne. Allah ya yi maki albarka, ya sa ki fara a sa'a." Malam ya furta ta amsa da amin. Inna ma murmushin take yi don hakan ya mata daɗi. Aure lokaci ne, za ta iya zaman shekaru ma idan Allah bai nufe ta da yin sa ba, to fa sai haƙuri.

Babu abin da Sadiya ke hangowa sai cikar burinta na zama likita. Babban fatanta hakan ya kasance. Wunin ranar da ka kalli fuskarta ka san tana cikin farin ciki.

***
Kwanaki suka yi ta shuɗewa zuwa satittika, watanni, har aka ci wata biyar da rasuwar Suraj. Sadiya ta yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi, ta duƙufa karatun jarrabawar Jamb da za ta zana. A sannan sun yi walimar haddar Alkur'ani mai girma. Ya kasance makarantar islamiyyar ya koma mata iyakar Asabar da Lahadi kawai inda take zuwa karatun litattafan addini. Hakan ya sa ta kara samun lokaci sosai ta tattara hankalinta wuri guda.

Ranar da zasu zana Malam ne da kansa ya kaita a sabuwar Honda da ya sauya. Da kansa kuma ya ɗauko ta suka dawo gida. Ta san dai ta yi iyakar ƙokarinta, sauran za ta bi da addu'a.
Allah ma ji roƙon bawansa, sai ga sakamakon Sadiya ya yi kyau har ta wuce cutoff marks da B.u.k suka buƙata na karantar medicine. Daɗi da murnar da ta yi ba a cewa komai, Abba har kyautar sabuwar laptop ya aikomata, shi kuma Malam ya yi mata alƙawarin sauya mata waya idan ta ci jarrabawar shiga B.u.k. Duka wannan budurin da ake yi yayyunta mata dayake sun kwana biyu ba su leƙo gidan ba babu wacce ke da labari. Har lokacin zana post utme ya yi Sadiya ta je ta zana ba su sani ba.

***
Kwanan watan da ya yi daidai da na fitowar sakamakonsu kuwa, ranar ta kasance na kwanaki biyar da haihuwar Anti Safiyya. Gida ta dawo wanka, Inna ke ba ta kulawa kamar ɗiyar ta haifa a cikinta. Ranar ce kuma Hajara ta zo ganin jariri da sha tara na arziƙi. Aka yi sa'a ita ma Anti Hafsatu ta zo gidan. Sadiya ta gaishe su amma fa hankali da nutsuwarta yana ga Yayanta Zakari, so take yi ya shigo ta ji ko sunanta ya fito ko a'a.

"Wai Sadiya lafiya kuwa? Na ganki duk a firgice."

Fadin Anti Hafsatu tana kallonta. Hakan ya sa Hajara da Safiyya su ma suka kalle ta. Murmushin yaƙe ta yi.

"Lah Anti babu komai fa."

Safiyya ta na dariya ta ce.

"Matsoraciya, wai fa duk fargabar result ne ya sa ta yi shiru."

"Result kuma? Wane irin result?" Muryar Hajara ya karaɗe ɗakin. Sam ba ta da masaniyar komai. Kafin wani ya ba ta amsa sai ga Zakari ya yi sallama, suka amsa ya ƙaraso. Sadiya ta miƙe don dama wayar tana hannunsa ya fita ne ya dawo. Farko fuskarsa ta nuna jimami, ya dube ta, gaba ɗaya sai ta ji ta karaya ƙafafunta ma suna neman kasa ɗaukarta. Sai ta ji ya fashe da dariya gami da faɗin.

"Congratulations Dr Sadiya! Sun ba ki gurbin da ki ke so na Medicine."

Ai sai ta gigice don murna amma fa cikin gigitar ba ta fasa hamdala ba har ta mance da wata halitta da a baya take mugun shakka a wajen, wato Hajara.

Daidai sadda Inna ta shigo aikuwa ta ƙarasa da gudu ta rungume ta tana kukan farin ciki.

"Lafiya?" Inna ta nemi ba'asi, nan Zakari ke shaida mata sadda Anti Hafsatu ke tambayar ko yaushe duk aka yi haka basu sani ba. A bakin Safiyya da ta ɗan yi kwanaki uku a gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login