Showing 102001 words to 105000 words out of 124441 words
gayya ta ke takun ma, to wa za ta burge a bainar jama'a haka? Ya yi wa kansa tambayar da babu amsa. Dagaske dai ya rasa me zai kushe a abin da ya kalla, jikinsa kuma ya ba shi ita ce Sadiya Sa'ad Shagari.
"Barkanku da asuba. An tashi lafiya?"
Muryar Anti Hafsatu kenan, nan su Lamiɗo suka gaishe ta. Maina ma ya ɗan dube ta kafin a tausashe ya ce.
"Barka da asuba."
Anti Hafsatu dake murmushi tana dubansa ta amsa, ita sai yanzu ta ƙara hango tsananin dacewar da ma'auratan suka yi. Ita kyau shi kyau, tana fata yadda halayen Sadiya suke da kyau, ya kasance shi ma haka. Tabbas da Sadiya ta gama dacewa duniya sai kuma lahira idan ta yi rayuwar aure mai kyau. Sai ta shiga addu'a a ranta akan Allah ya haɗa kawunansu.
Sadiya ta zaune gefen Antin bayan ta gaishe su kanta har a sannan a ƙasa, su Lamiɗo suka amsa, Maina babu wanda ya kula da ya amsa din ko a'a don ba jimawa da zaman aka kira su zasu wuce.
Gaba ɗaya suka miƙe suka ɗunguma ciki, ita dai ta riƙe hannun Antinta gam! Ita kuwa Anti Hafsatu kasancewar ba yau ne farkon hawanta ba tun da sun taɓa sauke farali tare da Maigidanta, a nutse take tsaf.
Allah ya karɓi addu'arta mazauninta guda da na Antinta. Hakan ya ɗan kwantar da hankalinta.
Ƙasa da awa ɗaya suka sauka a tashar jirgin sama na garin Gombe. Sai da suka fito daga jirgi ta gan shi, ta ga fuskarsa. Ta ga kuma yanayin shigar da ke jikinsa irin na gidajen sarakai. Riga da wando ne ruwan makuba sun sha surfani. Sumarsa kwance luf, kyakkyawa na bugawa a jarida. Ga tsayi ga kuma faɗaɗɗan ƙirji, giant da shi masha Allah. Sai ta ji gabanta ya faɗi, za ta rantse shi ne Maina. Ta raina kanta, ta ga kamar ba ajinta ba ne ta ko'ina. Sai ma da ta ga yanda ma'aikatan wurin ke ta gaishe shi a ladabce. Suna fita farfajiya wurin parking na motoci, ta ga uban dogarai sun nufo shi ana zubewa da kwasar gaisuwa. Kallon da ta yi mishi wannan karon sai ta ga ya yi mata mugun kwarjini ita kanta, ta kauda kai tana damƙe hannun Anti Hafsatu wacce ba za ta kirga adadin damƙar da Sadiya ta kai mata ba. Nan da nan ta ga wasu manyan motoci baƙaƙe wuluk masu kuma baƙaƙen gilasai sun ci burki a gabansu. Na tsakiyar aka buɗewa Maina ya shiga, su ma a ka buɗe musu na baya suka faɗa, daga yanayin kirarin ma ta san labarin aurensu ya isa ga masarautar.
"Anti tsoro nake ji, ƙirjina sai bugu yake."
Ta faɗi a hankali kamar mai raɗa, Anti Hafsatu ta ce.
"Addu'a, ki yi addu'a Sadiya."
Nan kuwa ta shiga karantowa a zuciyarta har suka shiga ginin Masarautar.
Tsayuwar motocin, ta ga bayi maza da mata an wani jeru an cika har da ma mutanen gidan maza da mata da jikoki domin tarbarsu. Koda dai mafi yawansu so suke su ga wace ce Amaryar Maina. Ciki kuwa har da cousin sisters waɗanda ke mutuwar so da ƙaunarsa kai ka ce dama a gidan wasunsu suka kwana.
Ba Sadiya ba, hatta da Anti Hafsatu sai da jikinta ya yi sanyi musamman da Maina ya fita bayin suka shiga zubewa suna kwasar gaisuwa. Bai kuma jira ba ya yi gaba ba tare da kula masu bushe-bushe da zuba kirari ba. A gefe ga mata na faman guɗa. Haka ta kama hannun Sadiya suka fito bayan dogari ya buɗe musu murfin motar.
Nan fa aka zubo musu idanu kamar a cinye su. Duk dai kushen masu kushe sun kasa hangen ta inda za su raina Sadiya, asalima Abayar dake jikinta mai tsadar gaske ce tsarabar Abba da ya je Saudiya ya kawo mata duk don a sanyaya ranta bayan auren Huzaif da Husna.
Ita ma haka bayin nan suka hau gaisuwa da ladabi, suka bi bayan Hindu da ke musu jagora.
"Wai! An ji mai."
Karaf maganar ya shiga kunnen Sadiya da ta zo gifta wata, ba ta ɗaga idanu ta kalle su ba amma ta ji wata na ba da amsa da "Ƙaryarki Najma, wannan ya fi karfin mai."
Har sai da ta ji tana tuntuɓe ga uban kirarin da ake zuba mata ita mamaki ma take yadda har sunanta da na mahaifi da kakanta ya iso gare su, wato Sadiya Sa'ad Shagari.
Murmushi ne kwance saman fuskar Haj Saratu tun shigowar Hindu tare da su Sadiya sai ko mutanen gida da suka mara musu baya. Ba don bauɗaɗɗen halayya da kafiya irin na Fulani Kausar ba, acewarta ita ba ta ga abin tada hankali a auren mace kamar wannan ba da Maina. Yarinya son kowa.
Sadiya da Anti Hafsatu suka russuna a ladabce kamar yanda suka ga Hindu ta yi suka gaishe ta.
"Barka da zuwa masarautar Gombe, Gimbiya Sadiya. Muna maki maraba, Allah ya sanya albarka a zamantakewarku."
"Ameen Mai Babban Ɗaki. Bangon sukari kowa ya jingina da ke sai ya lasa, Uwa ga Babban Yarima. Baya goya marayu, giwar Mai Martaba!"
Wannan kirarin na fitowa daga wata baiwa dattijuwa da ke tsaye, sai kuma ta rangaɗa guɗa. Wasu a wurin na taɓe baki wasu na harararta a faƙaice yayin da wasu ke murmushi cikin jin daɗin wannan kirari don masu jin dadin ma sun fi akasinsa yawa. Domin duk wanda ke tare da Haj Saratu, ya sani ba ta da baƙin ciki, ga kyauta. Hakanan ta dauki duka yaran Mai Martaba tamkar nata sai ko waɗanda suka kasa biyayya gareta, waɗanda iyayensu ke hure musu kunne. Ta kuma ja girmanta yadda ta kamata dalili kenan da ba kowa ke iya kawo mata wargi ba sai ko su Fulani Kausar wacce ke tunƙahon ita ma jinin sarautar ce gaba da baya kamarta, ba ta isa ta juya ta ba. Don ma shakkar Mai Martaba ya sa wani abin takan bar wa cikinta.
"A kai su masauki su huta su ci abinci."
Iznin da ta ba Hindu kenan, nan bisa cika umarni ta miƙe, su ma suka bi bayanta. A nan dai sashen Haj Saratun ne aka kai su wani ƙaton ɗaki mai ciki da falo. An gyara shi tas, ba ka jin komai sai ƙamshin turarukan wuta. Sun iske hatta da kayayyakinsu an kawo. Nan Hindu ta musu sallama ta ba su wuri su ɗan huta.
Bayan fitarta Sadiya ta zube saman kujera tana sauke ajiyar zuciya, sai a yanzu ta shaƙi iskar ƴanci. Anti Hafsatu da jikinta ya gama la'asar da mutanen gidan duk da haka yadda Sadiyar ta yi wani zuru-zuru ya sanya ta darawa.
"Sadiya, mene haka? Faɗuwar gaba fa ba naki ba ne. Aiki ne ja ki ke da shi nan gaba. Ki daure ki yakice wannan tsoron da ke saman fuskarki, sai kin zama jarumar gaske ina faɗamaki."
Sadiya ta gyaɗa kai. Ƙuryar ɗakin ma wani tafkeke ne ba kamar nata da ta saba rayuwa a ciki ba, can ƙarshe ka ke ganin gadon. Wanka ta faɗa bisa umarnin Anti Hafsatu don gaskiya da ace na ita ce to kwanciya za ta yi ta huta ko za ta nutsu gaɓɓanta su bar rawar da suke yi. Tana fitowa ta tarar har Antinta ta fiddo mata wata sabuwar atamfarta glitters irin manyan ƴan dubu talatin da ɗoriya wanda Malam a aljihunsa ya dauka ya bayar aka siya mata don fitar biki sai dai kuskuren da tela ya yi yasa ba ta sanya ba sai yanzun.
"Su Safiyya sun taho fa. Husna wai Hajara ta ce ta bari su taho gobe ta jirgi."
Ambaton Hajara da Antin ta yi sai da Sadiya ta ji ƙirjinta ya ɗan faɗi, ta tuna maganar da Zahra ta faɗamata da sunan ƙawayen Hajara ke faɗi. A fili kuma ta yi musu fatan isowa lafiya daga nan ta hau shiri. Ita ma Anti Hafsatu wankan ta faɗa ta yi. Cakarewa ta yi cikin nata Voyel din mai tsada don kaf kayanta ba ta ɗauko wanda ta ke da tabbaci za'a raina ajinsu ba. Hakan yasa da kanta ta yi wa Sadiya zaɓin kayayyakin da ya kamata ta ɗauko.
"Kin ga abin da na kula wannan ita ce Uwargidan Mai Martaba daga yanayin kirarin da ake mata da ma sunan da ake kiranta da shi, Mai Babban Ɗaki. Kuma kamar dai ba ta da matsala. Sadiya dole sai kin nutsu kin karanci dabi'ar kowa a gidan nan kafin ki saki jikinki da su. Wasu zasu raɓe ki ba don Allah ba, wasu kuwa zuciya ɗaya za su so su mu'amalance ki. Ke dai ki girmama duk wand ya girmeki musamman idan ya riƙe girmansa. Dama ban sanki da rashin kunya ba, in sha Allahu ki ka riƙi addu'a komai zai zo maki da sauƙi. Don Allah Sadiya ki rufe idanu ki ba masu jiran ƙiris a auren nan kunya. Ki wanke zuciyarki ki rungumi zaɓin da Allah ya yi maki. Baiwa ce ba kaɗan ba a daidai sadda wani bai aureki ba, Allah ya kawo maki madadi da ya fi wancan komai na rayuwa. Gina sonki a zuciyarsa ba abu ne mai wahala ba a gurinki mace. Ke dai ki zama mai biyayya da kyautata tsakaninku. Wataran za ki ɗaga hannu ki godewa Allah da ni'imar da ya yi maki na auren Maina. Ina jin wannan a jikina."
Anti Hafsatu ta ƙarashe tana mai murmushi, ita ma Sadiyar ta ɗan murmusa. Ba ta san irin adadin ƙaunarta da Antin ba, mace mai sonta da Innarta. Takan mance ma ba Uba suka haɗa ba, ji ta ke kamar ciki guda suka fito da ita.
"Nagode Anti. Allah ya bar mu tare."
Ta amsa da amin. Daga haka suka fito falon kamar kuwa jiran fitowarsu ake sai ga sallama bayan an kwankwasa ƙofar. Amsawa suka yi, Hindu ce tare da wasu bayi ɗauke da manyan fulas na abinci, haka aka dinga jera musu, bayan sun kwashi gaisuwa. Hatta da lemuka da ruwa sai da aka ajiye. Bayan fitarsu ne kuma suka ci kaɗan a cikin wanda za su iya don wani ma ko taɓawa ba su yi ba. Ba jimawa kuwa sai ga Hindu da ɗaya a cikinsu riƙe da wani ƙaton bowl da aka yayyanka kayan marmari. Ganin sun kammala ya sa ta ba da umarnin a fara kwashe kayan, sai da aka kammala ita ma ta musu sallama ta fita Anti Hafsatu na ƙara furta godiya.
Can kuma suna nan aka ƙara sallama, wannan karon ba muryar Hindu ba ce, suka amsa, wata mace ce da za ta girmi Anti Hafsatu tare da wata baiwa wacce kalar kayan da ke jikinta ne irin na bayin da suka zo ɗazun ya sa su fahintar ɗaya ce a cikinsu, ita kuma riƙe take da ƴar jaka.
Matar doguwa ce mai jiki kaɗan. Ta ci ado kamar mai zuwa gidan biki. Fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso ta zaune tana kallon Sadiya. Ganin haka Sadiya ta yi gaggawar saukowa tana kokarin russunaws ta gaishe ta duk da ba ta san ta ba amma suna tsantsar kamanni da Maina.
Da sauri ta riƙo ta miƙar gami da zaunar da ita gefenta a lokacin da ta ke amsa gaisuwar Anti Hafsatu tana ƙara wa da tambayar ya gajiyar hanya.
"Alhamdulillah, gajiya ta bi lafiya."
"Masha Allah. Suna na Saudatu, ɗaya daga cikin Yayyun Maina."
Dama ko ba ta faɗa ba sun ɗauki haske, kamannin sak kawai dai ita ɗin tana da ɗan duhun fata. Daga haka Gimbiya ta waiga ta dubi Baiwar da ke durƙushe kanta a ƙasa ta ce.
"Fauziyya."
Sunanta kawai ta kira yarinyar ta fahimta don haka a ladabce cike da ladabi ta matso ta buɗe jakar ta fiddo gidan wata sarƙa ta ajiye, ta ƙara fiddo wata alkyabba fara ƙal mai adon zare kalar golden ita ma. Gidan sarƙar ta fara miƙawa Gimbiya Saudatu. Ita kuwa ta taimakawa Sadiya da cire fashion mai tsada da ta sanya sannan ta taimaka mata da saka wani arnen gwal mai daukar idanu. Anti Hafsatu sai ta rasa ma me za ta ce, ƙasan ranta wani irin farin ciki da hamdala kawai take ga Allah na wannan sauyin da Sadiya ta samu. Daga zuwansu ko awa ɗaya ba su kai ga cikewa a garin ba har rayuwar Sadiya ya fara sauyawa?
Gimbiya Saudatu kuwa ta ƙara kallon Sadiya wacce har a ƙasan ranta ta ji dadi da ta gan ta a haka, tabbas idan an cire nasabar da mahaifiyarsu ke ta faɗan wai ba a duba jinin sarauta an aura wa autan nata ba sai bare, toh kuwa ba ta ga makusa a tattare da ita ba. Ita kam ta yi mata kuma tana fatan halayyarta ma ya kasance irin fuskarta. Wato mai kyau. Sosai ta ga sarƙar ta karɓe ta sannan ta miƙe tsaye riƙe da hannun Sadiyar, da sauri Fauziyya ta ɗauki alkyabbar ta da ke wani irin ƙamshi mai daɗi ta miƙa mata. Nan ma mayafin da ta yi Sadiya ta lulluɓa ta cire ta ajiye ta sanya mata alkyabbar.
'Allahu Akbar! Masha Allahu la kuwwata illa billah.' Faɗin Anti Hafsatu a zuciya har da wasu ƙwalla ta ji sun cicciko mata a idanu ganin wani irin kwarjini da haiba a fuskar Sadiya wacce ita kanta jikinta ya yi sanyi ga kuma nauyin da bakinta ya yi ta ma rasa me za ta ce.
"Kin yi kyau sosai ƙanwata. Allah ya sa kin shigo gidan nan a sa'a. Ki saki jikinki, a hankali za ki san mu don ba laifi yawa ne da mu. Komai a sannu za ki fahimta kin ji ko?"
Ta gyaɗa kai a ɗan kunyace, Anti Hafsatu ta amsa addu'ar da amin.
"Ku na iya biyo ni muje, Mai babban ɗaki tana jira."
Suka amsa da toh suna masu bin bayanta. Ita kuwa Sadiya ta ji duk ta takura, daga zuwa an ƙaƙaba mata alƙyabba? Allah dai ya sa ba haka za ta dinga yawo a gidan ba. Ƙila ma iyakar na yau ne. Haka ta dinga saƙe-saƙenta, can wani ɓangare na zuciyarta na tunanin ko ina Angon nata ya shige? Amma kuma tana ta kokarin basarwa don a ganinta me ma zai dame ta da tunaninsa?
Haj Saratu ta amsa gaisuwar Sadiya ita ma ta yaba yanda ta yi kyau. Nan kuma ta umarci Gimbiya Saudatu da yi musu jagora zuwa sassan Fulani Kausar da ma sauran matan Sarki Abdallah Tafida don ta gaishe su.
Falon na Haj Saratu a cike da mata, haka aka dinga bin Sadiya da kallo ga gefe ta ɗazun ba cigaba da zuba mata kirari. Ita dai tana rungume jikin Gimbiya Saudatu jefa ƙafafunta kawai ta ke. Haka har suka iso wani ɓangare jama'a na biye da su a baya. Falon shi ma yana da girma kamar na Haj Saratu, ga kuma ɗakuna a can ciki. Iya tsari ya tsaru don ba ma za ka iya tantance wanda ya fi kayan alatu da na Fulani Kausar da na Haj Saratu ba.
Tana hakimce a saman kujera ta yi wani irin zama na ƙasaita. A gefenta zaune can ɓari na daban wasu ƴanmata ne su biyu sai ko wata babbar mace ita ma dake bin su da kallo. Anti Hafsatu ta kalle Fulani Kausar dakyau, ko kaɗan ba ta ga kamarta da Maina ba, ta dai gane uta ce mahaifiyarsa a kirarin mai zuba kirari dake ta yi babu ko gajiyawa. Fuskarta kawai ya fallasa sirrin zuciyarta don babu ko ɗigon walwala a samansa.
Gimbiya Saudatu duk ba ta ji dadin yanayin dake saman fuskar Umman tasu ba, ai ko don masu ɗaukar bidiyo ta daure ta yi murmushi koda kuwa bai kai zuci ba amma ta kasa. A wulaƙance ta amsa gaisuwar Sadiya tana cin magani. Daƙyar ta iya faɗin.
"Allah ya yi albarka." Mutane aka hau amsawa da amin.
Haka aka zagaya da Sadiya har sauran ɗakuna biyu na matan Mai Martaba. Daga nan kuma bisa jagorancin Jakadiya da aka kai ta wajen Mai Martaba. Babu wanda ya shiga, hatta da Gimbiya Saudatu duka tsayawa suka yi. Ita ɗin yake son yin magana da ita sai ko Maina da ke zaune tun ma kafin ta shigo. A ladabce Sadiya ta miƙa gaisuwa, ya amsa mata.
"Alhamdulillah. Muna maki murna da shigowa wannan masarauta mai albarka. Ba ma yi maki kallon suruka, ke ɗiya ce a wurinmu. Za kuma mu riƙe amanarki, dukkan wani abu da kile buƙata, ki sanar da mu za mu yi ƙoƙarin ganin an maki matuƙar bai saɓawa addini da al'adunmu ba."
Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha da kuma yin alƙawari ga Sadiya zai ɗauki mataki mai tsauri a kan ɗansa muddin ya kama shi da zaluntarta ko yaya. Haka nan ya jaddadawa Maina ya ji tsoron Allah, ya kuma kiyaye yin abin da zai ɓata ransu. A ƙarshe ya sanya musu albarka ya kuma yi musu addu'a.
Nan ta miƙe fuskarta da hawaye ta fito ta bar shi da Maina. Ji take kamar ba ita ba, wai ita ce da wannan matsayin da muƙami. Ita ake ta girmamawa, ta shiga roƙon Allah a rai kada hakan ya haifar mata da girman kai, ya sa ta zama mai tausayin na ƙasa da ita kamar yadda ta ke tun farko.
***
"Za ki zauna a nan ne har zuwa nan da kwanaki uku da za'a kammala gyaran sashenki a kuma yi bikin miƙa ki zuwa can."
Ta tuno kalaman Haj Saratu sadda ta ke ninke alƙyabbar, ita kuwa Anti Hafsatu na faman kallon sarƙar da take mayarwa cikin gidansa.
"Anti."
Sadiya ta furta, ta ɗago ta kalle ta tana murmushi.
"Na'am Gimbiyar Maina."
Sadiya ta nanata sunan a ƙasan rai, wai Gimbiyar Maina. Sai ta girgiza jai ta zauna gefen gadon.
"Anti zan iya rayuwa a gidan nan?"
'Yar dariya Anti Hafsatu ta yi.
"Za ki iya, babu abin da zai cinye ki. Kar fa ki manta kina da Allah, toh akwai wani abu da ya gagare sa?"
"A'a. Amma ba ki kula kamar wacce aka ce mahaifiyarsa ba ce..nufina kallon da na ga ta yi min. Ban sani ba ko don a fakaice na kalle ta, ko ban gani da kyau ba ne."
Ajiyar zuciya Anti Hafsatu ta yi.
"Wannan kar ya dame ki, ki kyautata mata zato. Ba