Showing 51001 words to 54000 words out of 124441 words
danne komai ta bi Husna amma fa ba da niyyar taɓa ko kwandala a kuɗin Hajara ba. Komai na Hajara ya ƙara sire mata a rai, gaba ɗaya ta tsane ta. Tsanar da ba ta san adadinsa ba. Ta kula ba ƙaramin cutar da rayuwar ƙanwarta take ba ta hanyar sangarta ta da komai na jin daɗin rayuwa wanda gaba daya na lokaci ƙalilan ne tunda ba ta san gidan da za ta faɗa ba. Ga wani raini da Husna ke yi ga ƴan aikin gidan, daga Maigadi har mai wanki da ma Atine ba ta ragawa kowa, ba ta duba yawan shekarunsu haka take gasa musu magana ko ta ja musu tsaki. Hakan ba ƙaramin ƙonawa Sadiya rai yake ba. Ta kuma yi magana amma ta ga alamar ta yi nisa ba ta jin kira, ta sani ba za ta iya sanar da Innarsu ba, ba ta son tayar da hankalinta. Sai dai kawai ta yanke za ta cigaba da bin ta da addu'a. Wannan kaɗai ne mafita a yanzun.
Tana tsaye jikin mota tana jiran Husna ta fito daga shagon don ƙin shiga ta yi, ita kuwa Husna ta ce sai ta faɗawa Malam, dole ya sa Sadiyar ta ce ta yi gaba tana nan tafe. A zahiri ba ta da niyyar shiga, ta ja tsaki ya fi a ƙirga amma kuma a ƙarshe dole ta sauya shawara ta shiga. Babban shago ne sosai, ta gama zagayenta a ƙasan babu Husna don haka ta kama hanyar bene ta soma takawa. Sai da ta kai hawa na uku inda kayayyakin sutura na mata yake sannan ta hango ta. Ta dage sai siyayyarta take jibga hankali kwance.
"Wai ba ki gama ba?"
Ta juyo ta dube ta.
"Yanzu ma na fara, ke nake zaɓarwa English Wears."
Ta ɗaure fuska tamau.
"Bana so Husna, koda kin siya za ki yi asararsu ne."
Husna ta saki baki kawai tans kallonta. Sadiya kuwa ta gyaɗa mata kai shaidar dagaske take. Dole ta haƙura ta cigaba da siyayyarta, ta yarda dagaske Sadiya ba ta don komai don har suka koma ƙasa wurin kayan maƙulashe nan ma ko tsinke ba ta nuna tana ra'ayi ba. Anan ne ma dole ta ɗaukar mata wasu kayayyakin tanɗe-tanɗen. Aka kammala ta ba da Atm card dinta ta biya suka fito Sadiya na ƙara jinjina wayewar kai irin na Husna. Don akawun na banki ita ma ta mallake shi, amma kuma ba ta taɓa wani amfanin da shi ba. Ba ta mancewa Yayansu Baba Habu ne ya kawo form din suka ciccike kuma suka je aka yi komai suka buɗe akawun a Ja'iz bank. Hatta da shagon da ta shigo ita duk a ɗarare ta ke komai ban da Husna wacce ta saba sosai kanta tsaye take gudanar da sha'aninta.
Daga nan kuwa babu inda suka nufa sai gidansu, sun sani Inna sai washegari za ta dawo don haka gidan gaba ɗaya ya yi ƙura. Sadiya ce ƙarfin gyara ko'ina da wankewa.
Falon Malam gaba ɗaya a hargitse, ita ce ta gyara komai ta shige ɗakinsa nan ma ta gyara ta wanke bayinsa. Kafin Malam ya dawo gidan ta yi musu girkin dare. Ya kuwa ji dadi sosai ya dinga sanya musu albarka don shi a nasa zaton har Husna aka yi aikin.
Washegari kuwa sai ga Inna da tsakar rana sun dawo, sosai Sadiya ta shiga murna, ko babu komai kaɗaicin da ya yi wa zuciyarta yawa dangane da Huzaif zai ragu.
"Me ya ramar da ke haka?" Tambayar da Inna ta soma jifanta da shi kenan. Ta yi dariyar yaƙe.
"Inna rama dai? To sai dai yanayin jarrabawa."
Inna ta bi ta da hakane kawai, ta sani wataƙila gidan Hajarar ce ta yi rayuwa a ƙuntace tunda babu shaƙuwa ko na sakanni tsakaninsu.
***
Tun tana ƙirgen kwanaki, har suka soma zana jarrabawarsu ta Neco babu wani yunƙurin kira ko magana daga Huzaif. Zuwa sannan duk dauriyarts ta kasa, ta yi mishi magana har da kiran whatsapp amma bai ko bi ta kai ba.
"Kin takura min Sadiya, don Allah ki bar ni ina fama da karatu ne. Ke ba ki san ki nemi mutum a gaisa ba sai kin gama wulaƙanta shi ko? To ni ma ai ina da abin yi. Ba a kanki zan zauna na ƙare rayuwata ba. Ki taimaka ki ba ni lokaci kar ki yi sanadin da zan ɗauki matakin da ba zai mana daɗi ba Hajjaju."
Wannan shi ne amsar da ta samu sadda ta takura mishi da magana a whatsapp. Kalmar Hajjaju ta yi mugun baƙanta ranta, ta ji ciwon kalamansa. Ta sha kuka sosai. Haka ta daurewa zuciyarta ta kashe wayar gaba ɗaya ta cilla cikin sif ta cigaba da harkokinta da karfin hali.
Zahra ke zaune tana kwaɓin lalle za ta yiwa wata Amarya, ita kuwa Sadiya ta yi shiru kawai ta zubawa lallen idanu amma sam hankalinta na ga tunanin Huzaif. Duk yadda ta so tattara komai ta watsat hakan ya faskara, sau da dama murmushinsa, daɗaɗan kalamansa kai har ma da yanayi na ɗaukar gayunsa sukan hana ta sakat, ta sani tana kaunarsa ba na wasa ba. Sauyin da ya ke zuwar mata da shi, sauyi ne irin wanda ba za ta iya jurewa ba. Satinsu ɗaya da soma jarrabawar Neco amma gaba ɗaya ta kasa saita kanta ta maido walwalarta yadda ya kamata. A gaban Inna kawai dauriya take yi duk da ta sani daga yanayin kulawar da Inna ke ƙara ba ta, ta fahimci tana da wata damuwar da ba ta fito ta bayyana mata shi ba.
"Sadiya! Ke!"
Muryar Zahra ta tsinta kamar daga sama ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zaman hijabinta gami da kauda kai daga kallon Zahrar da take sakamakon hawayen da suka cicciko mata sai ta waske da faɗin.
"Ke bari na koma gida kafin Inna ta ji shirun ya yi yawa."
Zahra ta riƙo gefen hijabinta wanda ya sa dole ta fasa miƙewar amma kuma hawayen sun zubo.
"Meyasa Sadiya? Meyasa za ki takurawa rayuwarki ki hana kanki sukuni a dalilin ɗa namiji? Wallahi na tsani na ga kina zubar da hawayenki akan Huzaif. Ban ce bai cancanta ba, amma kuma duk wanda ya nuna kai ba ka da muhimmanci a rayuwarsa, kai ma ka fita hanyarsa gaba ɗaya ka hutarwa ranka. Don Allah Sadiya, ina haɗa ki da girman Allah ki yi ƙoƙarin rage damuwarnan. Kuma na yi alƙawarin zan ji ta bakin Huzaif, zan mishi magana. Da yardar Allah komai zai wuce."
Sadiya ta share fuskarta tana murmushin da bai kai zuci ba.
"Kin san ban taɓa son wani ɗa namiji ba Zahra, ban iya soyayyar ba, akan Yaya Huzaif na koya. Amma kuma yanzu ya ke wulaƙanta ni. Hum. Kar ma ki ɓata bakinki wajen yi mishi magana. To me za'a ce masa?"
"Mu ke da abin cewa kuwa Sadiya. Bari na gama yi wa yarinyarnan ƙunshi zan shigo gidan ki ban lambarsa. In sha Allahu yau ba za ki kwana da damuwarsa ba."
"Uhum." Shi ne kawai furucin da Sadiya ta yi sannan ta miƙe tana mata sallama. Ta gifta ƴanmatan biyu dake zaman jiran a yi musu ƙunshi ta fice.
Tana shiga gidansu ta tarar Inna na sallar Azahar sai kawai ta faɗa ɗakinsu da sallama. Husna ta iske riƙe da waya tana ƙyaƙyata dariya ga dukkan alamu chatting take yi. Tana ganinta ta miƙe zaune fuskarta ɗauke da ƴar damuwa har Sadiya ta cire hijabinta tana ƙoƙarin ninkewa.
"Sis, anya kuwa? Wai kodai na ƙara yi wa Yaya Huzaif magana ne? Ni na tsani ganinki cikin damuwarnan."
Sadiya ta dube ta, tuni Husna ta fara hawaye. Sai ta ji haushin kanta ya kama ta ma. Don me za ta dinga sanya masoyanta kuka har haka?
"Ba fa damuwarsa ba ne, kawai raina ne babu daɗi yau."
Husna ta share hawayenta ta sauke ajiyar zuciya.
"Har na ji sanyi. Dama za ki ban dama ai da na sami Abba na mishi..."
"A'a, bana so. Mu bar zancen kafin ma Inna ta tsinkaya."
Daga haka ta mike ta fice a ɗakin, Husna kuwa ta bi ta da kallo tana mata gwalo kafin ta toshe bakinta sakamakon dariyar da ta kama ta. Hauka take yi za ta bari sulhu ya shiga tsakanin Huzaif da Sadiya? Ko na farkon ma da ta ce mata ta yi masa zancen yace baya son maganar ƙarya ce kawai ta mata don kada ta yi tunanin ba ta yi ba. Yanzun ma da shi suke hira, koyaushe cikin ba ta labarin ƙasar Indiya yake yi. Ita ma haka za ta yi ta labarin gida da abin da ke faruwa amma koda wasa ba ta taɓa sanyo mishi batun Sadiya ba, shi ma kuma haka. Wannan ne yake ƙara yi mata daɗi.
***
Bayan Watanni Biyar...
Abubuwa da yawa sun fara masu daɗi da akasinsa, marasa daɗin kusan gaba ɗaya kan Sadiya ya ƙare a gidan, kamar dai abin arziƙi, Huzaif ya dawo da kula ta bayan sulhun da Anti Hafsatu ta yi musu. Ita ɗin ma a zuwan da Sadiya ta yi ne gidanta hutu bayan ta yi Candy ya sa ta fahimci akwai matsala tsakaninsu. Da kanta ta yi kiransa a waya ta whatsapp suka yi doguwar magana. Ta kula dai kamar kame-kame ne zantukansa marasa dalili, ƙarshe ta saka Sadiya ba shi haƙuri, shi ma ya ba ta.
Rayuwar ta ɗan koma musu daidai amma fa ba ta bar fuskantar matsala daga wurinsa ba. Sai ta yi magana ya ƙi kula ta, kuma a gefe sai ta ji Husna na faɗin ai ba su jima da yin magana da shi ba. Wannan kan yi mata ciwo matuƙar gaske. Ba don tana ji a jikinta cewa Husna ba za ta taɓa ba da fuskar su yi soyayya da Huzaif ba da ta ce kodai soyayyar suke yi.
A haka har suka ci waɗannan watannin, lokacin yaye Huzaif ya yi, Abba da Mami suka shirya suka tafi. A bakin Meenat take ji ai tuni Yayyunsa mata Radeeya da Lubna sun soma haɗa lefe don a lokacin da aka saka na biki ya kasance Huzaif na dawowa za'a ɗaura aure.
Sosai Anti Hafsatu ke zuwa gidan tana kawo wa Sadiya kayayyaki na gyara hakanan Safiyya ita ma tana nata kokarin. Inna dai kallonsu kawai take yi abin na burge ta yadda yan uwan ke ji da Sadiya a yanzun. Husna gaba ɗaya zaman gidan ya fice mata a rai, damuwa sosai take shiga. Ranar da Yaya Lubna da Radeeya suka zo gidan har suka dauki awon undies ɗin Sadiya wuni ta yi kuka wannan ne dalilin da ya jawo ta tattara ta koma gidan Hajara bayan Hajarar ta kira Malam ta yi ƙaryar rashin lafiya.
"Anti don Allah kada ki bari na rasa Yaya Huzaif. Na rantse mutuwa zan yi. Yanzu fa sosai muka shaƙu da shi, ya ce min ba ya kaunar Yaya Sadiya, ya dauke ni abokiyar shawararsa."
Husna ke zancen a mugun firgice sa'ilin da ta ke zaune gefen Hajara tana kuka tamkar ranta zai fice. Hajara ta shiga rarrashinta gami kafin ta ce.
"Kar ki sake ki sanya damuwa a ranki. Na faɗa maki Huzaif ba zai taɓa auren Sadiya ba. Ke ce matarsa. Yanzu dai ki zuba idanu ki bari ya dawo. Komai da zai faru za ki ganewa kanki. Za kuma ki sha mamaki kin ji ko? Ke ko biki kika ga an soma kar ki sake ki tashi hankalinki. Ni na san me na taka."
Husna dai ta ji ne kawai ba don ta gasƙata ta ba, ta yaya za ta fasa damuwa alhalin ga shi nan komai na ta tafiya cikin tsari?
Ita kuwa Hajara hankalinta kwance kasancewar ta yi imani kwarai da abin da Bokanta ya ce. Aiki ne ba na wasa ba zai soma tasiri a kan Huzaif duk ranar da ya sa ƙafafunsa a ƙasar nan. Komai zai juye masa ya ji nan duniya babu wacce yake so da aure kamar Husnarta. Wannan ne ya sa ta ji nutsuwa sosai.
***
Ana gobe za'a kawo lefe su Abba suka dawo amma babu Huzaif wanda ya tsaya ƙarasa wasu abubuwa da ya shafi makarantarsu. A bakin Malam ne Sadiya ta ji cikin satin bikin nasu ne zai iso wato ana gobe ɗaurin aure. Ita dai gabanta kawai faduwa yake yi, Abba na dawowa gari da kwana uku aka kawo lefe na gani na faɗa can babban gida kamar yanda Malam ya tsara. Jerin akwatuna har saiti biyu ɗauke da tsadaddun kayayyaki. Husna kasa zuwa wurin ta yi, Hajara kuwa duk da ta san da shirinta sai da ta ji kamar ta yi hauka ganin tarin dukiyar da aka zuba da sunan mallakin Sadiya. Ta ƙara cin alwashi a rai ko za ta yi yawo tsirara auren Sadiya ba zai taɓa faruwa ba a duniyar nan dai.
Sadiya kuwa duk da ramar da ta yi amma fa ta yi kyau sosai irin na gyaran Amare. Fatarta har wani sheƙi yake yi. Ɓangaren su Inna ma haka suke ta yi mata shirin da ya dace. Zahra wacce tuni ta riga Sadiya aure amma komai ake yi da ita don Mijinta ya san irin shaƙuwarta da Sadiya wannan ne dalilin da bai hana ta taka nata rawar ba.
Babbar damuwar Sadiya lokacin bai wuce na shafe sati uku da ta yi babu wata magana tsakaninta da Huzaif ba, koda ta yi ba ya amsawa. A baya yakan amsa da ok, yes, no da sauransu, amma ban da yanzu. Tunaninta wane irin aure za ta yi babu kulawar miji?
Ranar Litinin ma ƙunshi Zahra ke rangaɗa mata na bikin da za'a fara ran Laraba amma kuma hawaye take fitarwa. Faɗi take yi
"Ta ya ya Zahra? Ta ya ya za'a ce zamu yi aure haka kamar irin na dolen nan? Meyasa Yaya Huzaif zai aure ni idan ya bar sona? Meke faruwa ne wai?"
Zahra ta dakata da ƙulle ledar da ta saka a ƙafar da ta zanawa lalle ta yi tana jin ita ma nata idanuwan na ciccikowa da hawaye, don haka a raunane ta ce.
"Ya zan maki Sadiya? Ya ki ke so a yi? Na ce maki mu sanar da manya don su san halin da ake ciki kin ce kina gudun faɗan Malam kar ya ga kamar ke ce bakya so. To don Allah idan ba su ji ba ta yaya za'a magance wannan matsala?"
Sadiya ta haɗiyi miyau tana sanya bayan hannunta ta share hawayen dake saman fuskarta dalilin tafukan hannun rufe suke da leda wanda Zahra ta ɗaure bayan ta kammala zanen ƙunshi.
"Ba zan iya ba, dagaske laifina za'a gani tunda shi bai fito ya nuna ba ya son auren ba, zan ɓata zumunci. Shirun ya fi alheri."
Zahra ita ma ta share nata hawayen.
"Ba ki fasa addu'ar da na ba ki ba ko?"
Sadiya jinjina kai tana jan majina. Zahra ta ce.
"To ki sa a ranki da yardar Allah komai zai daidaita. Allah zai maki zaɓi. Sadiya ba za ki taɓa auren wanda zai wulaƙantaki ba. In sha Allahu komai zai wuce ya daidaita tsakaninku. Kin ji? Ki bar kukan nan kada Husna ta dawo ta ganki itama ta rikice."
Sadiya ta ƙara gyaɗa kai tana share fuskarta sosai.
Husna dake laɓe a zauren gidan Zahra tana jin su ta yi murmushi da ƙwafa.
'Ai ba za ki taɓa auren Yaya Huzaif ba Anti Sadiya. Za kuma ki gani.'
Ta furta a ƙasan ranta tana gyara zaman ledar lemo mai sanyi da ta karɓo musu a shago. Daga nan ta yi sallama ta shiga ciki. Ba ta nuna musu ta ji komai ba. Ana kammala yi wa Sadiya ƙunshi ita ma ta miƙa nata hannun.
"Ni dai a yi min irin na Anti don Allah." Abin da ta ce kenan. Zahra ta harare ta.
"Ba ki da wayo amma, ta ya ya za'a yi maki ƙunshi irin na Amarya? Sannu kin ji ko."
Husna ta ɗaure fuska ta dubi Sadiya.
"Sis don Allah a yi min irin naki. Mene ne a ciki?"
Sadiya ta yi murmushi. Ita ta taya Husna roƙon Zahra akan ta yi mata babu komai. Zahra ta rantse ba za ta yi ba, wannan ya sa Husna ɗaukar zafi ta ce ta fasa ƙunshin za ta je a yi mata a wani wurin. Zahra kuwa tace sai dai a yi hakan. Ƙarshe ma tana gama cin abincinta ta fice a gidan ta bar su da zummar za ta neman gidan ƙunshi.
"Ai kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan kwano." Shi ne abin da ta ce a ƙarshe sannan ta sa kai ta tafi. Sadiya cikin takaici ta dubi Zahra.
"Ke dai akwai rigima wani zubin, mene ne ciki don ta yi irin ƙunshina?"
Zahra ta ja tsaki.
"Bana son hauka fa, kin taɓa ganin inda aka yi wa wata irin ƙunshin Amarya kuma ƴan gida ɗaya? To na rantse ba zai yiwu ba. Idan har ni zan yi mata ta jima ba ta yi fushin ba. Mahaukaciya kawai, sai ta je can ta ƙarata."
Ita dai Sadiya girgiza kai ta yi kawai, Zahra da Husna ai sun saba tamkar wasu saƙo da saƙo. Kamar dai jininsu ne bai haɗu ba sam.
Sai Magriba ta bar gidan Zahra don har baƙin ƙunshi ta zana mata mai ɗan karen kyau. Ita kaɗai ta koma gida madadin farko da suka fita tare da Husna. Har aka yi isha'i Husna ba ta dawo ba sai wuraren takwas na dare. Lallen da ta yi har ya fi na Sadiya kyau, kowa ya gani sai ya yaba kuma ace inama a ƙafar Sadiya yake tunda ita ce Amaryar. Ita kuwa Sadiya ko a jikinta don ba wannan ne matsalarta ba. Lamarin Huzaif ya shafe komai.
Ranar kamu take jin batun dawowar Huzaif a daren. Meenat da ta zo gidan kwana ta yi ta zolayarta wai sai ta bar ƙunci tunda dai Angon ya iso gari. Madadin ma hakan ya yi mata daɗi, ba ta ji komai ba face faɗuwar gaba.
"Ki tashi ki je falon Abba wai Yaya Huzaif ke son ganinki."
Abin da Husna ta ce kenan kafin ta juya ta fice a ɗakin ta bar ƴanmatan dake ciki da yin guɗa a kunnuwan Sadiya. Ita kuwa sai ta ji ƙirjinta na cigaba da lugude tamkar an ce