Showing 33001 words to 36000 words out of 158722 words
Chapter 12 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
din,Umma tace to ga matarsa ma tazo ta kawo kararsa,Naila tace ki fada mata na saketa saki uku Umma ta kwashe kayanta na saketa,tana jinki ma ai na sa a handsfree,Naila tace yawwa ai da Allah yasa Ina Nan da tuni na kashe auren Yaya, Umma tace wai baya biya mata hakkinta,Naila tace ai da nasan gidan yari zanje da kafin na tafi zan bawa Yaya magani na kwantar da Hallare wanwar a kasa bata sake motsi sai ya sake aure na tashe ta,Umma dariya ta kamata da kunya sosai amma bata yi dariya ba kunya ta hanata dariya ga suruka na Ji ga Naila yarta,share zancen tayi tace idan ya shugo zai kira,Naila tace to a gaida su Aslam da Hidaya Yar bakin ciki da Zarah,sannan a cewa Darling ya kirani,Umma tace to sai munzo ziyara.
Naila tace ko baku zo ba ma I can survive, Allah Yana kula da halittarsa, tururuwa ma Allah na kula da a barsa bare Dan Adam, Tausayin Naila ya kama Umma sosai harda kwalla ta datse wayar da sauri tasan magana Naila ta fada mata da suka ki zuwa mata.
Hanan tuni tayi waje ta fice ta tafi gidansu tana kuka tace Mohsin da iyayensa ne suka ci mutuncinta, Mamanta tayi mata nasiha aka maidata gidan Mijin,Mohsin baya gidan bai san ma ta koma ba,Yana dawowa daga wajen aiki ya ganta a gidan tana girki,ransa a bace yace yanda kika tafi ki tattara ki koma gidan naku ai Umma ta kirani a waya ta fada min karata kika Kai musu sannan kika wuce gidanku sai ki koma gidan naku Kuma karki sake ki daukar min 'yata,Wani takaici ya kama Hanan tace ai dai muna da gidan ko,sabo da kaje gidanku an zugaka shine zaka dawo ka raina min hankali dadin abin dai ubana Yana da gida,Mohsin yace kije dai ku kwana da yara su tsula miki fitsarin kwance a jikinki,lokacin da nake zuwa zance gidanku in kika fito mayafinki zarnin fitsari yake ko kina tunanin ban gane ba to hanci na ya jiye min shuru nake miki kawai Ina dauke kaina gefe,Hanan zuciyarta har suya take sabo da bacin Rai,bedroom ta shige ta dakko mayafinta ta saka tana tsaki tace gidan naku ai ba fin namu yayi ba,ubana na ma yafi naku,naku sai yanda tsohuwa tayi da shi,ta juya zata tafi ya fisgota yace me kika ce? taji tsoro amma duk da haka tace na fada gwara ubana...ai kuwa Mohsin ya hau jibgarta tana ihu har makwafta sai da suka shugo,da kyar aka lallaba Mohsin ya kyaleta amma mayya Hanan ta San ta kan Mohsin,sai tace bazan tafi ba ai nayi wanki gashi Nan a Saman igiya yanzu zan kwashe zan tafi.
Mutane kowa ya watse sai wata dattijuwa Mohsin yana cewa Baba sakinta zanyi,Tsohuwar tana cewa kayiwa Allah Dan girman Allah ko Dan darajar yarku karka saketa,bazan zauna da ita ba Baba,Baba tace karka ce haka Dan nan,Hanan ta koma bedroom ta cire kayanta ta fito da daura kirji ta shiga toilet ta fito ta sake komawa,ta fito karo na uku ta shiga kitchen sai ta sauke zaninta a iya kugunta ba bra ba riga daga samanta sintir sai kayan uban nonuwa suna ragaje ragaje ta fito a haka ta wuce su tana girgiza ta shige Palo ta sake fito tana girgiza kirji tana cewa duk abinda mutum yake ji nima Ina ji,Baba tsohuwa tana ta dariya a ranta tasan iskancin Hanan tasan dalilinta,Mohsin sai kace tsohon maye duk Inda Hanan tayi sai kallo Yana mika wuya Yana Cewa Baba zan sake ta fa? Iya tace a'a kayi hakuri,Hanan ta fito tana waka ahayee dawo dawayya....tana girgiza....Mohsin yace to Baba ance rayuwa sai da hakuri musamman ga ma'aurata ko? Baba tasan batun tace ae yi hakuri kaji,yace to na hakura yanzu tunda dai nima na zageta shike nan 1-1 idan ta sake sai ta bar gidan nan,Baba tace ae Hakan yayi ayi hakuri ya wuce ,yace sabo da ke Baba Ina ganin mutuncinki na hakura,Baba ta bar gida tana ta dariya.
Hanan kuwa Kwata kwata yini tayi tana zagade a gidan tana wake wake taki saka riga a haka tayi wanka ta saka Dan skert ba ko riga ba bra ta sake fitowa kamar karuwa,a Palo ta zauna tana girgiza tana wake wake,Mohsin Yana ta kallonta kamar maye hankalinsa ya gama tashi matuka,Amal dama tana gidan su Hanan,Tashi Hanan tayi tana murguda duwawu tana tafiya ta shige daki ta fito daga ita sai pant ta zauna suna facing juna da Mohsin ta baje kafafu tana tauna chewgum tace zama daram,Mohsin a nutse yace dama ai kece kika jawo ni ai bance karki zauna daram ba,idan aka yi hakuri duniyar nawa take eyeee, rayuwa dole sai anyi hakuri da juna ki daina taba min iyaye wallahi akan iyaye na ba abinda bazan yi ba,Hanan tace ni ai ka zagi nawa taya bazan rama ba daga na nemi hakkina sai kuyi min taron dangi, Mohsin yanzu Kam dama a matse yake yace indai akan pleasure stick ne ake wannan tashin hankali gata nan,ai ita ba bakuwar zafi bace,Hanan taji dadi ya sakko tace to yanzu naji zance nima ka yafe min mu tafi Downstairs, yace sai kinje kin bawa Umma hakuri,tace zanje ai ba komai,yace to suka yi cikin bedroom.
Sharhi please fans
Book 1
Free page
Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger
+22790795939
AsmaBaffa
[12/6/2023, 5:18 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
21-25
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE
GARE KI❤️
AIDA MAMAN TASNIM
PAGE NAKU NE
Hauwa S Zaria
Binta Umar Abbale
Ashanty
MASU AUDIO BAN YARDA A JUYA MIN NOVEL BA,BADA IZINI NA BA.
*_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_*
*_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_*
*_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_*
*_dama wadanda zasu ganki ahanya?_*
*_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_*
*_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_*
*_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_*
```ARZUQLANA GALLERY```
*_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_*
```Laces
Atampha
Shadda
Abayas
Materials
Gyale
Takalma
Jaka
Kayan Kitchen
Bangles n jewelries```
*And many more*
```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO```
*_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_*
*_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_*
*_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_*
*_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_*
https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ
Mohsin tsoro yake yi kar ya saki matarsa yazo Kuma sha'awa tayi Masa yawa ba Inda zai rage zafi tunda ya Saba da mace shi yasa, bayan sun Sha love sunyi wanka Mohsin cikin yard dinsa milk ya cakare Yana shining ya fito tare da Hawa lifan din Ya nufi gidan Umma.
Yana yin sallama a gidan ya samu Umma a kitchen tana Jin shuguwarsa ta fashe da kuka harda hawaye sosai,duk su Hidaya sai da Umma ta basu mamaki Hira sukeyi amma daga Jin sallamar Mohsin ta fashe da kuka.
Mohsin ne ya karasa Inda take a kitchen ya leka ya samu tana kuka,hankalinsa ya tashi yace Umma lafiya? Umma tana shesheka tace zagin da Hanan ta yi min wallahi bazan yafe mata ba,yarinya tazo har gida ta ci min mutunci Kuma su Hidaya basu iya rama min ba Wanda nasan da Naila na Nan ba a isa anyi min haka ba, in haifi Dana azo a fini Iko da shi wulakanci har kaina,ga zafin haihuwa da nakuda sannan nazo na hadu da zafin suruka,ni a haihuwarka ma ban Sha wahalar nakuda ba amma wlh abinda Hanan take min yafi zafin nakudarka zafi.
Mohsin yace kiyi hakuri Umma zata zo ta Baki hakuri,da masifa Umma tace ka dauki mataki ne? Mohsin sai karya yayi yace ai cewa nayi ban yarda ba taci duka sai da makwafta suka raba abin sannan na kira iyayenta na fada musu shine suka kirani tare da ita a gabana suka mata fata fata suka ce Kuma na saketa har na dauki takarda da biro zan fara rubuta shine ta Fadi a kasa tana cewa ta tuba Kuma zata zo ta bada hakuri, Umma tace to Ina jiranta tazo ta sameni wallahi sai na sake ramawa fada bai kare ba,Mohsin yace to Umma wai ya zuwa wajen Naila? tace ai naga amfanin Naila wannan satin aje mata ziyara tare zamu tafi da Kai da Abbanku ma,Mohsin farin ciki ya kama shi yace Allah ya kaimu Alhmdllh,zanga Naila ta,Umma tayi dariya tace hankali ya kwanta ko? Yace kwarai kuwa ai nama za a siyo har farfesu za ayi mata,Umma tace da kuwa ka kyauta,Abba ne ya shugo Yana masifa yace ni wannan aikin barinsa zanyi Allah ya kawo min wani bazan iya ba.
Mohsin ya gaida shi,Abba yace aikin nan barinsa zanyi rana ta isheni bazan iya ba,Umma baki ta tabe taci gaba da aikinta,Mohsin yace to wacce zaka yi? Wacce zan zauna a cikin rumfa cikin inuwa,kana da jarin? Ina naga wani jari ai Kaine zaka bani gwara na dinga siyar da kayan Miya,zaka iya zuwa ka saro? Abba yace ae zan iya a bani jari,Mohsin yace to an gama amma Dani za aje a saro kayan,yace ae muje tare amma wannan aiki su canja wani a madadina,Umma dai kawai girkinta take yi har Mohsin ya bar gidan bata ce kala ba,duk yanda ta Kai da juya Abba to Banda bangaren aikinsa baya tantakwaruwa akan wannan aikin.
Bayan kwana biyu Mohsin yaje ya samu ma'akatan yace Abbansa ya bar aiki su nemi wani,baturen cikin harshen turanci yace me aka yi Masa? Mohsin yace shima bai sani ba ya canja aiki ne,sai lokacin wani baki bahaushe shima gadin yake yi amma nasu sai yamma yace au yanzu Hashimu akan turancin Nan ya bar aiki? Mohsin yace wanne turanci? mutumin ya furta ai tunda masu duba aiki suka zo turawa suka dinga yi Masa turanci,suna ta turanci shi bai iya ba shine yace bazai iya aikin nan ba azo ana zagin addininsa bai sani ba,wai bazai taba yiwa yahudawa aiki ba,ba hakurin da bamu bashi ba yace sun Masa wulakanci cikin turanci anci mutuncinsa,Mohsin yayi dariya sosai ya gane so kawai Abba yake ya daina aikin,haka dai yace musu ya canja aikin yi,a ranar aka yiwa Abba rumfa a kofar gidansa.
Washe gari Mohsin ya dauki Abba suka tafi Inda ake saro kayan Miya,aka saro Masa tumatir,attaruhu,tattasai,Alayyahu,kabewa,albasa,green beans,da duk wani kayan lambu yazo ya shirya abinsa a rumfa Saman table,ga abin zamansa ya zauna yace yanzu nasan Ina sana'a.
Abba ya fara sana'a ana ta layin siye sabo da layin nasu babu masu kayan da yake siyarwa wasu a ciki,matsalar daya idan mata suka zo siyayya ko matan aure ne sai yayi ta turguza musu kayan miyar,yayi ta zubawa a leda ba ji ba gani,idan namiji ne yazo sai ya millira Masa tsadar masifa.
Naila dare yayi kaikayin Infection ya dameta amma haka take Dan mazewa ta cire katuwar rigarta data Dora a Saman katuwar t-shirts me dogon hannu me kauri, Maganar Su Beauty taji tana cewa Hello.....ta jikin bango,Naila dariya tayi tace na koma Yar Yahoo Malam Gaza, Malamai ana ta zuwa daukan karatun littafan daban daban a wajensu suna ta karatunsu amma Naila ta mike ta koma Jikin bangon Dake hade da su Beauty tace Hello Beauty na? tana Jin matan suna cewa wallahi ya amsa yayi magana Beauty kizo saurayinki yayi magana,Beauty ta matso sosai da karfi tace ya kake? I'm good, Beauty tace naji kamar Dan Fulani,wai Dan Allah Dan Fulani ne Kai naji hausar ne sai a slow, Naila yaren fulatanci tayi,Beauty ta furta Kaiiii a'a daina ni bana Jin fulatancin nan,Naila tace to ya gidan yari ya bangarenku yake? Beauty tace wlh ba dadi ai bangaren mata yafi dadi muna iya shegen mu San ranmu matan harda shewa yeeeed,Naila tace muma nan muna namu iya shegen dai dai gwargwado,tab Kai Nan kaji kuwa abinda akeyi,Naila tace ke duk iskancinku fa baza ku fada mana ba,gamu Nan da su Malam Sharu da su Jilani duk Yan iska ne mu ,Malam Sharu ya dago da sauri ya Kalli Jamilu zuciyarsa ta wani buga yanda yau akwai haske gashi ta cire rigar Saman ya kafe Naila da Ido Yana fada a ransa yace ji Jikin ma irin na mace,Malam Gargazali ya Kalli Malam Sharu yaga yanda yake ta faman kallon Jamilu
Sai yaji wani kishin Jamilu a ransa Sam baya kauna a dinga kallonsa sabo da son da yake Masa,Shi kuwa Malam Jilani Yana dorawa wasu Dake gidan yarin karatu amma ya kasa sabo da Muryar Jamilu Dake dukan dodon kunnensa kasa karatun yayi yace Dan Allah kuyi min uzuri sai gobe karatu kaina ciwo yake,Daliban nasu suka ce ba matsala suka tafi.
Kwanciya kowannen su yayi Yana saurarar Muryar Jamilu a dakin kowa da abinda ke damunsa na son Jamilu a ransa, Jamilu kuwa bai San ma me suke yi ba yaji an daina karatun,suna ta hirarsu Naila tace Kai ku wai Kuna kwana da wando? Malam Sharu ya Kalli Malam Jilani suka hada Ido tare da girgiza Kai,suna Jin su Beauty harda guda kamar zasu Kai amarya wata a ciki tace wannan sai dai a tambayi Yan dakin su Karima sune Yan kungiyar kwana ba wando mu nan harda Pampers muke like mazaunanmu,Naila tace amma baku more rayuwa ba ai idan Kuna so ku Shana kuji dadin bacci ku dinga kwana da wando,Beauty tana dariya tace ka bani kunya wlh rannan wata tayi Hakan kyankyaso ya dinga bin wajen,Malam Sharu riga yasa tare da toshe kunnuwansa,Jilani yasa hannu ya toshe nasa,Malam Garzali kuwa kunnuwa ya bude shi wannan hira dadinta yake ji
Malam Garzali yace da sauran mazan wallahi ta tuna min da matata Sayyada,Malam Sharu yace hmmm tunda aka kawo Jamilu nake tuna Mariyata yau rabona da iyalina Shekara nawa ana daukan hakki a gidan yari,ya dace a dinga hada aure a gidan yari,Malam Jilani yace kamar ka shiga raina ya Akii da an fito mana da matan gidan yarin kowa ya zabi dai dai shi a daura mana aure, su Jamilu suke hirar amma su Malam Sharu sun fisu Jin dadin hirar kamar kar a daina,bayan sunyi sallama Malam Garzali yace har Kun gama hirar? Jamilu yace ae,a'a ka sake kiransu mana kuyi yaran suna da kaifin hankali,Jamilu ya dinga dariya yace wato Kam ni Jamilu aji tsorona ni da kaina Ina kiyayar kaina,Budurwarku ce ko tawa ni na gaji da Jin Muryarta to,Malam Jilani yace ai kuwa kayi dace Jamilu yarinyar akwai zakin Murya sai kace matata Suwaiba,Naila dariya take a boye tana ta zurma malamai suna sakin zance cikin kamewa.
Bangaren Spark kuwa Yana bangarensa shi kadai,duk ya damu ya rasa Inda zai sa kansa ba abokin hira ba abin yi,abinci ma ya rasa me siyo Masa tunda ya shanye yogurt da juice dinsa sai biscuits su yake iya ci kawai tunda yazo gidan,wata matsananciyar yunwa yake ji,ga uban zafi AC dinma ta daina yi,kallo tun yanayi har ya gaji,gashi sai samu Dan aikin da ya Masa ba bare ya samu dan abokin hira,tsaki yaja ya Mike ya fito hannunsa dauke da Dan karamin mifici Yana fifita, takaici na cinsa a ransa yace dama ni nasan Asmau babu alheri a kanta,a jikina naji dama sai ta jaja min masifa,ko tana raye Allah ne yasan masifar da zan fada amma gashi da ta tashi mutuwa ma sai da ta tafi da rayuwa ta a haka ma Allah ya taimakeni ban kwana a gidan ba ai da sai an hada Dani an kashe shike nan ta ja min amma duk da haka gashi dai ta mutu ni Kuma hukuncin daurin rai da rai badan Ina addua ba shike nan nima hukuncin kisa za a yanke min.
Beauty ce ta sake kwalawa Jamilu kira tana ta Hira ga Naila kaikayi ya isheta tace da Beauty Ina zuwa zanje na karbo sako zan dawo karki bacci sweetheart,tace to Ina jiranka wlh hira da Kai dadi akwai nishadi,Naila tace Allah sarki ai Ungozoman din data wanke ni me fara'a ce tana min wanka bakin Nan a washe gata da katon baki tana magana tana tintsira dariya shi yasa na taso da abin dariya da Surutu bakina baya shuru,ta fito zata buya tayi susarta tana fitowa wani bangaren duk duhu tana sauri tana bi lungu da sako duk yawanci mutane suna daki wasu suna waje suna Shan iska, Inda bishiyoyi suke ta nufa sauri take kawai ta buya tayi susarta kawai tayi karo da mutum karon da tayi da shi sai da ta Fadi har kasa sabo da macece ita ba karfi.
Spark ne ya haska wayarsa yaga Jamilu yace Kai wai baka da karfi ne duk ka kashe zuciyarka ji yanda kazo ka bige ni Ina zaka je haka, Naila tsayawa tayi tana kallonsa,yace Kai wai baka sanni bane mene haka nifa ba Dandaudu bane bana son wannan kallon,Naila mikewa zata yi ta kasa kafarta ta gurde,tace Dan Allah Dan taimaka min na kasa tashi wannan kafar zaka danna min ta koma dai dai ta murde.
Spark wani haushi ya kama shi amma yace ni ban iya ba,Naila tace shi yasa ba a son mutum fari kalarka da yawa sabo da irin wannan baku da tausayi ,oh tunaninka tausayinka zanji? Ae mana baka da Imani abin yayi yawa ka rage,hmmm kawai yace Ina zan samu abinci? Naila tace dare yayi ai kasan nan ba freedom ba a yin abinda aka ga dama, Dan Allah ka tafi