Showing 63001 words to 66000 words out of 158722 words
Chapter 22 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
sun gudu harda su lukaku sun fece da Babangida,da Imrana Dan fillo,Kai harda Bajahilci ya fece wlh,Dan Indo ya mike zumbur Yana busa sigari yace amma Jamilu ya raina mana hankali amma ni nayi sanadiyar fitarsa Kuma ni na dauki alkawari ni zan dawo da Jamilu gidan yari Kuma a namijinsa dole Dan uwatas sai na Mori wahalata,Goje yace ka daina cewa Jamilu sunansa Naila fa yace gashi a takarda a rubuce,Kai Dan uwarka muga takardar nan na Kara karantawa Dan Indo ya sake karanta takarda yace karya ne wlh mu zaki wa iskanci yarinya,mu fa Yan kasar Nan ne,karya ne wlh,yanzu kun gane kowa yayi shuru da zancen nan kar ma'aikata suji,idan aka dawo da ita ba uwar da zasu mata bangaren mata za'a maidata,amma idan na dawo da ita a namijinta haka za a maidota cikinmu,Kai wlh ko ta Katanga sai na sa an wullo mana da ita
Nan take Dan Indo ya bugawa yaransa Dake waje waya Wanda yake basu aikin kisa ko wani aiki yace kuna Ina? Suka ce mun dauki hanyar Kaduna,yace ku dawo baya ta haihu ku koma a cikin yaran da suka bar gidan yari akwai wani me suffar mata sunansa Jamilu Tantiriya zaku ganshi da riga da wando na Jean wasu Maka Maka wandon kamar buhu sai a sakaka a ciki a daure,to ku bisu duk Inda kuka ganshi ku dawo dashi,idan baku ganshi ba ku kirani zan Nemo address din gidansu duk Inda yake sannan zaku ga gashinsa duk tara gashin namiji Dan uwatas bazai tara gashi irin na Jamilu ba,sannan Daadaa ce a kansa,suka ce an gama oga suka yi youturn nan take suka juyo.
Scoler ne ya taho Yana karairaya yace oh ku kuwa ku kyale yarinya karku keta mata haddi wannan ba daidai bane tsakani da Allah,indai da so da Amana ai ruwa ba zai ci gwani ba,sabo da Allah da Manzo anbi an ishi Yar uwa,yarinya ta fita,tunda taimako kayi tsakani da Allah ku kyale Yan mata Dan Allah ta tafi da kayan nononta can Spark ya samu na zuka, dama watakila ya Saba a nan anga wajen hutawa yarinya taga me kudi ohh ke duniya ni naga kiyayya,yarinyar nan Jamilu kiri kiri taki kaunata anga me kudi an manne Masa ah ahayyeeee wuuuuuuu Ashe tana karbar Hallare inji Jamilu da fada tace Hallare,to Dan Ubansa wallahi ba ruwana da fadar Naila Jamilunsa sak babu batun canja suna,
Shewa Scoler ya sake yi tare da dukan cinya yace Shegen kaya Spark ai tunda naga Dan banzan dan Nan Yana wani shining Yana sheki Inda kasan da inji ake goge masa fata kullum nace ba banza ba Ashe dai madarar Nido yake samu wajen Jamilu,yarinya can fa ta tare wajensa inji washer daya Dan Daudun,ai dole Jamilu tayi kuka to an Saba kullum da bankade between inji bature yace Between her leg ahayyeee chassss Spark ansha gara.
Dan Indo yace shi yasa yarinyar nan bata taba shiga cikin gwamitsin Maza ba,ba a ganin sallarta,Ashe tasan me take boyewa,yau shekarata uku rabona da mace ah dole a dawo min da Jamilu karya ne wlh cewar Dan Indo ya mike Yana zaga wajen.
Goje yace har na hango kaina da Jamilu Ina ninkaya cikin bahar maliya,Yan Daudu suka saki shewa, Inshaallah baza ku samu sa'a akan Yar uwa Jamilu ba,bi'izinillah ta fita kenan wlh ah haka kawai kune kuka kera mata Between din? bafa ku bane,ita kanta hattana kirjinta Breast din Nan gani tayi sun fito rana tsaka kwatsam ta Sha jinyar abinta tun suna kurji har suka nuna yo sai ace za ayi mata Iko,Dan Indo Mari ya zubawa Scoler,Scoler ya kurma ihu yace naga wuta naga wuta Yana fifita fuskarsa da hannu yace washer zo mu bar wajen Yan mazan Nan kar su nakasa mutum, Kuma dukkanku kwalelenku Jamilu ya fita kenan ba dawowa.
Naila kuwa tunda suka fita da wasu mutum ashirin da biyu kowa ya tarwatse ya kama hanyarsa daban,Naila ita da Bajahilci suke sheka gudu,sabo da gudun tsira Bajahilci baiji sanda Naila tace ita macece ba Sam,sai yace Jamilu biyo ni kawai kasan ni Ba Jahilci sunana kaina baya kullewa muje karka je gida Kai popular ne wlh duk Wanda ya zama popular a waje to da wuri ake ganewa, Naila tana hakki tana gudu magana ta kasa sai daga Kai kawai,Dan bandage da aka daure kirji ma ya zame ya gudu garin gudu, amma basu tsaya ba yace bafa mu tsira ba Jamilu za a iya biyo mu Kaga Sha kwana ta wancen lungun ka san fa a wajen gari muke sosai ta barauniyar Hanya zamu bi mu fada cikin gari idan muka bi direct hanyar mota za a iya kama mu.
Naila tasha kwana ga wani shegen katon gidan gona ana ginawa anyi Katanga da tsayi Kuma,Bajahilci yace haurawa zamuyi fa Jamilu,Naila tana hakki ta tsaya da kyar ta iya cewa bazan iya ba,Bajahilci yace bari na gani ko zan iya dagaka,ya kama kaurin Naila ya dagata sosai hannayensa a kaurinta tayi tsayi sannan ta kama Katanga tana Bajahilci matsa gaba gaba,ya matsa ta kama sosai ta haure ta dirga kasa,lokacin taji karar fadawar wani abu kamar karfe daga jikinta,amma Bata kawo komai ba,shima ya hauro yace Maza muje suka ci gaba da gudu yi suke ba ji ba gani har magriba ta fara,lokacin su Kuma yaran Dan Indo da mota suke ta yawo ita Kuma Naila Bajahilci ya hanata bin hanyar mota yace za a iya kama su.
Suna ta gudu har suka kusa isa titi,Bajahilci yace to Kaga nan ba a samun abin hawa na haya yanzu ka iya Hawa bishiya? ai Naila dama ita tun a kauye ta kware a rashin ji tace duk tsayin bishiya wlh kamar biri yace hau muje Jamilu,Naila ta kama wata katuwar bishiya dalaf dalaf ta haye can sama, Bajahilci ma ya hau,Naila tace kishirwa nake ji wlh,yace sai dai kuwa kayi hakuri,ni kaga daga nan tashar Lagos zan wuce sai Lagos kafin a gannni Kuma tab Allah yasa bani da iyaye,Naila tace ni gida zanyi yace wlh sai kayi a hankali Jamilu zasu iya bibiyarka har gida kayi suna a gidan,ka boye kanka wlh karka bari ko a layinku a San ka gudo yanzu shigar dare za muyi, Naila ta gaji ta kwanta a Saman reshen bishiya, ta kasa magana ma sabo da gajiya da yunwa ga kishirwa ta dameta,Aminu ba Jahilci yace Ina wayarka Jamilu ka cire layinka fa ka karya shi wlh Kai wayar ma kanta ka jefar da ita za a iya tracking,Naila ta fara duba waya a jikinta tasan tabbas da waya ta fito a garin gudu ta jefar da wayarta ma,tace ta Fadi a hanya wlh,wayyo Spark gashi ban rike number ba dame zan kira shi na gama yarda da wayata a hannuna,ai ni wannan fitowar da nayi bata da amfani,Bajahilci ko magana baiyi ba shi dai ya cire wayarsa ya rabata da layikansa.
10pm na dare Bajahilci yace yawwa yanzu zamu iya tafiya sauka Jamilu,Naila jikinta ya mutu murus ta gaji Kafadunta sun kumbura wani wajen ma taji ciwo,ta sakko a hankali shima ya dirga suka ware sai gefen hanya yace kar mu tsaya shiga Napep cire rigarki ta sama ki jefar, Naila ta cire ta jefar a kwalabati sai t-shirt me dogon hannu yace yanzu kin koma arniya kin gane karki nuna kamar a gigice muke.
Naila tace to suna tafiya Tantiriya komai da ruwanka da sunzo wajen mutane sai ta fara yiwa ba Jahilci yare tayi hauka ta hada da fillanci harda wani Chinese na hauka duk yi take,Bajahilci sai ya basar kawai Yana irin murmushi Yana kallonta Yana daga Kai irin Yana ganewa hira suke ai.
A haka suka kwashe kusan 3hrs sannan ya nemi Napep suka shiga,ya Kai Naila har kofar gidan Mohsin sannan yace kana zuwa ka canja kaya karka bari a San ka gudo ni na wuce Lagos,Naila tace na gode sosai,yace fara bugawa in aka bude sai na tafi,kamar yasan macece,Naila tace wlh Kaci sunanka Bajahilci yace dole wlh....ta dinga buga gida,sai da aka Dade Sannan Mohsin ya taso zai bude ga tsoro a ransa,yace waye?Naila tace Hidaya ce tayi Muryar Hidaya ta make Murya,ai ya zaci ko gidansu ne ba lafiya fit ya bude kofa ya fito,tace dalla da abin kisa ne shike nan haka akeyi?,kafin ma ta juyo Bajahilci yasa me Napep yayi gaba sun wuce .
Naila tace Yaya gudowa fa nayi,Mohsin yace Subhannallahi Ina murna Ina haushi, ya jawota cikin gida ya rufe kofa, yace Naila yanzu ya kenan zasu iya zuwa nemanki ko mutanen unguwa yanzu in suka San mutum case din kisa ne a kansa zuwa suke su fada a boye sai azo a sake kama mutum sabo da kar su zauna da makashi a unguwa,Naila tace cikin rada yi a hankali kar munafuka Hanan taji,yace ai tana daki a kwance ranga ranga kafarta hannunta daya ya kumbura sumtum kashinta ne ya tsage na hannu,sannan idonta duka biyun sun fashe sun kumbura sum ko gani bata yi,me ya sameka? Wai machine ne ya bugeta nidai nace karya ne ban yarda ba.
Yau fa da asuba zaki bar gidan nan dole Naila,Naila tace ai wlh sai naga iyayena,yace ko kauye fa baza ki koma ba za a iya bibiyarki wlh can za ayi tunaninki a can kar ma ki nufi can,Naila tace to Ina zani wa na sani? Wanda na sani number dinsa tana wayata Kuma wayar ta Fadi, Naila tace yanzu dai a dakin can zan zauna bana so matarka tasan Ina Nan kayi shuru yace to tace ruwa da abinci ta shige wani dakin daban a tsakar gidan,ya shiga kitchen ya zubo mata abinci da ruwa taci ta koshi ta Sha ruwa,ta kwanta tana hutawa,Nan take bacci ya kwasheta.
Da asuba ta riga kowa tashi taje tayi wanka sosai tayi alwala sannan ta nufi dakin Mohsin,bata so Hanan tasan tana gidan tunda ta kasa kunne taji basa love tace ahh Hallare tayi hakuri yau ba a abin,nasan asuba tayi lokacin fitinar Hallare ne gwara naje na dakko kayan kafin Hallare tayi tsiya,taleka tare da tura kofar a hankali,ta samu Mohsin Yana kwance can gefe Hanan tana gefe daya,Naila farin ciki ya kamata a hankali yanda ba Wanda zai ji tace Alhmdllh Yaya Mohsin ya tsani shegiya ai na zaci zan ganta a kirjinsa,Allah ya wargaza ku kamar yanda kuka yi kwanciyar Nan Allah yasa igiyar auren ma tayi haka, ta lallaba ta tabi ta gefe,Mohsin ta tabawa kafa ya farka,ya gane Naila ce,ya fice da sauri sabo da shima yayi sallah ya makara,Naila ta bude sip din kayan Hanan a hankali,ta zaro riga da skert na atamfa wacce take a wanke a goge sabuwa,ta duba layin mayafai Nan ma a hankali ta zaro kalar atambar tana haskawa da Yar wayar Hanan din Kuma a kusa da ita ta dauka,ta duba wajen takalma ta zabo me Dan rudu wani sabo shima silver kalar mayafin,ta dauki jakar Hanan sabuwa wacce jakar takalmin ce ta hada abinta, ta bude wayar Hanan ta zare layikanta ta zube mata a gefen pillow ta jefa wayar a jaka, a kan Hanan ta tsaya tace sai kace Ubanta ne ya siya wayar ko Dan koli ne ya siyo ta fada a hankali kasa kasa tace to na dauke ta yawwa na fada miki Kuma kinji sabo da haka na fita hakkinki ki ta juya tayi gaba.
Har ta fice sai ta dawo tace in tafi banyi komai ba ai karya ne Hanan ce fa a gidan,Glass ta hango na Hanan da take daukan wanka wani pink faskeke ta dauke shima tace kolabo zan fara,yanzu na koma yar kolabo Kuma,sai ta haska kafar Hanan ta ganta a kumbure suntum,ta haska idon kadan kamar an kawo wuta an dauke ta ganshi tsabar kumburi ya manne ma da kasan idon,Hanan tayi dariya marar sauti harda rike ciki duk ba sauti,tasa hannu ta latse idon Hanan,Hannan ta farka a tsorace tana cewa wayyo idona wayyo Naila ta fisgi kafar me ciwo wacce ta kumbura ta ja da karfi ta Murda ta saki ta fice fit, Hanan ta tashi tana ta dube dubenta shuru,ba kowa tana ta kiran Mohsin shi Kam Yana sallah .
Naila fitowa tayi ta koma ta dakko katon hijab again tazo tayi Sallah sannan ta surfa addua ta mike sanye da hijab,ta fito Mohsin ma Yana idarwa ko ta kan Hanan baibi ba ya fitar da machine Naila taje ta hau suka bar gidan ta rufe fuskarta da Hijab din,sai gidan Umma,Suna zuwa Abba ya dawo daga masallaci,yaga Naila mamaki ya kamashi Naila tana sauka a machine ta durkusa a gaban Abba tace Ina Kwana Abba,da mamaki Abba ya amsa da lafiya Naila tayi kasa da Kai wai tayi hankali a gidan yari, tace mun same ku lafiya ya akaji da rashe rashe da bama nan,Abba Dolo yace ei wlh nan rannan ko sati ba ayi ba Magajiya ta rasu,Magajiya Babar Sani Takwashe,na manta ma Alhaji me kosan sadaka da watan Ramadan shima ai ya rasu,haka ladi me abinci ma,Naila tace Allah yaji kansu,Abba ya su Debora,Abba yace suna Nan suna fama da kallon Maza yanda kika sansu basu daina ba ni yanzu ma kullum sai na karanta Hasbinallahu kafa Dari sabo da gubar da ke cikin idanuwansu Allah kareni dasu gashi nan duk da haka ramewa nakeyi gubar idon su Debora ce kawai tayi min yawa,Mohsin yace Abba ka rufa mata asiri muje Dan Allah gudowa fa tayi.
Abba ya saki salati yace gudowa? Duk tsaron Dake gidan yari kika iya gudowa Naila, Gwara tun wuri ki koma ciki kafin su damke ki,wannan ai cin amanar kasa ce,cin amanar hukuma ce, duk da naji dadin ganinki gwara ace su suka sallameki da kansu, Mohsin yaga abin na Abba ya zarce saninsa yace Kinga muje ciki,Naila ta mike zasu shiga Abba yace Allah ya tsare Naila amma Ina jiye miki,Umma kuwa da katon cikinta Wanda ya girma suka sameta ta kafa wutar gas a hancinta tana Kona wata takarda wacce take nannade da tabar Wiwi,tana shakar warin da sassafe,Mohsin yace Umma Zafa tayiwa Dan cikinki Illa wallahi,to kawai sai na kashe kaina akansa? ku rabu Dani,Naila ce ta shiga ta kwace wiwin ta take da kafa tace Yar kanwar mu ko kanin mu zai iya zuwa da nakasa,Umma tace laaaa Naila ta rungume Naila tana murna tace ta ya hakan ta faru,Naila tace irin tserewar,Umma tace tsugunu bata kare ba,ai wucewa zanyi,zuwa nayi na ganku dama ,kina da wajen zuwa ne? Naila tace Inshaallah akwai mafita ku dai kuyi min addua,Umma tace to shike nan Allah ya tsare a Kuma tsare mutunci a kiyaye,Banda taurin Kai,Naila tace to ayi a bani shayi na Sha,Mummy ta duba flask tace akwai ruwa,da sauri Naila ta hada tea ta shanye tace idan su Hidaya sun tashi ku fada musu na fita daga gidan yari Umma,My love zan wuce ina da number Dinka a kaina zaka jini Inshaallah,Mohsin yace to Ina jira,leda ta dauka tare da zuba kayan data dakko na Hanan dalayin wayar Hidaya ta karba
Naila ta nufi kofa tace to sai kunji ni,Mohsin Tausayin Naila ya kamashi,da sauri ta fice tana ficewa da hijab din Hanan har kasa ta tsaya a zaure tayi kuka sosai ta goge hawayenta,sannan ta nufi titi da sauri ta shige Napep tana barin layin yaran Dan Indo suna zuwa gidan su Naila,su Umma sai hani suka yi Yan daba sun fado musu gida suna bincike,basu kula kowa ba Kuma ba Wanda ya kulasu suka gama dube dubensu sannan suka fice suna duba wayarsu har gidan Mohsin suna zuwa sai Hanan kawai,Naila a Napep ta saka layin Hidaya a wayar Hanan data dauka,ta zauna tana tuna number Spark ko wacce ta kira sai dai taji wani ko wata ya dauka tayi missing number a ciki ba daidai take hadawa ba,tsaki ta ja ta hada number Beauty ta kira Allah ya taimaka wannan daidai ta hada bugu biyu aka dauka,Beauty cikin Muryar bacci tace na'am waye? Naila tace Jamilu ne,na gudo daga gidan yari bani address na gidanku,Zumbur Beauty ta mike tace ka bawa me napep din waya,Me Napep ya karba Beauty ta Masa kwatance sosai sannan ya mikawa Naila wayarta,GRA ya shiga da ita wata katafariyar unguwar,hadadden gida na mamaki a nan yayi parking yace ga gidan Nan nasan ma me gidan ai yayi fice,Naila Hijab dinta ta cire ta dawo namijinta sak,Beauty ta kira a waya tace muna kofar gidan,da sauri Beauty ta fito ta biya me napep kudi ya tafi,Naila ta gyara p-cap tace muje ciki suka shige,bangaren Baki ta Kai Jamilu ta bashi daki sannan ta koma wajen me aikinsu tace ta hada mata lafiyayyen Kari.
Naila kuwa sai kallon gida take faman yi tace umm Aljannar duniya bari nayi wanka,ta mike ta bude toilet da komai da komai a ciki ta sake wanka na musamman ta wanke gashinta sosai ta fito,body lotion ta Gani a mudubi ta shafa tana kallon kanta a mudubi tana taje gashin nata Wanda ta warware daadaa din dake kanta,ta dinga duba tarkacen Dake mudubin harda mayukan gashi da Kuma powder da abubuwa kayan Hanan ta saka a jikinta har sun so suyi mata kadan sabo da Naila ta fita kiba ta cika kayan fam fam,ta zauna ta shafa powder harda saka maroon jambaki tayi kyau kuwa sosai kuma tayi daurin ture kaga tsiya ta tsaya a mudubi tana kallon kanta tace amma fa Allah yayi halitta haka nake dama....bayanta ta juya tace wai wai gaskiya Alhmdllh better thing,Ashe haka Allah ya halicceni, Allah na gode Maka dole in godewa Allah ahhh kalleni Naila,Jamilu, Tantiriya dariya tayi tana shafa fuskarta a haka Beauty ta shugo ta isketa,wani wawan birki taci da tire a hannunta tace me zan gani