Showing 93001 words to 96000 words out of 158722 words
Chapter 32 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
da iyalina kar kuzo kuga abinda ido bazai dauka ba,sannan ni kaina tsawa bana iya yi mata tsoron abata nake ji matata tafi karfi na sallamamme ne ni,duk abinda ta muku ba ruwana bazan iya daukan mataki a Kai ba sai abinda tace shi yasa take juyani son ranta
Yanzu da kuka fado daki da Kun iske bamu gama bafa Ina tsakiyar harka ai Kunga Kun jawa kanku,ashar Mima ta dura Masa tace Kai duk iskancin da kake ji da shi dai dai nake da Kai Dan uwarka mu kake gayawa haka sabo da ana kyaleka,na fada Maka auren Wahida ya zame Maka dole,in ba ma iskanci ba haka zaka ce wasa kake dama, Spark yace ni gaskiya na fada na Gani wasa nake yi ni,Kuma ga Wahida ta fada idan na taba zuwa zance gidansu, sannan ban taba fita da ita ko Ina ba itace take zuwa,sau Daya ma na taba kiranta tazo zamu fita Kuma muna fita banyi Nisa ba nace motar ta lalace dole ta shiga taxi ta koma gida,waya ma ita take kirana Kuma duk sabo da Babyna nake yi Dan taji haushi Kuma mun shirya na aureta,babban Yaya ya sani shine ya nemo min aure shi da Yan uwan Papa, Papa ma ya sani duk sunje daurin aure da su aka daura.
Mima taji takaici tace to ni ba abinda ya dame mu wlh sai ka auri Wahida ko na tsine Maka,Spark yace uhmmm ni dai wlh magana ta Allah bazan aure ta ba sai dai a tsine min Kuma harda ke domin danki ne za ace ya watse ya lalace maybe ma na shiga kidnapping na fara ta kanki,gwara ma ki sa min albarka kar nazo ko na koma bin mata nazo wajen Mummy cikin dare Inda Bata da mijin Nan na afka mata Kunga tsinuwa tayi aiki,Salati suka saki suna tafa hannu,Mummy tace Spark ni zaka afkawa harda hawaye tana cewa wai dan daga raina dan cikina Dan yayata uwa daya uba daya zaice zai afka min,Mima tace abin yaci tura lallai ka Kai karshe a iskanci,Spark yace idan aka tsine min nace ai, Allah sai naje ta kanta Mummy zan fara in ta kamama na biyo ta wajenki Mima,Mima tace na shiga uku bazan tsine Maka bama Allah ya kiyaye min,Spark yace ato ana tsine min zan fara kidnapping duk Yan gidanmu sai na tsince su ko kudi ko rai,Mummy tace harda ni? Kece ma ta biyu cewar Spark,ko na fada neman mata Dan akuya zan koma kowa na samu ba kanwa babu Yaya.
Daddy Yana Jin haka yace da Wahida ke ki hakura wannan yaron bashi da mutunci kina Jin iyayensa ma abinda yake fada musu ni na zare hannuna ya mike,Wahida kamar mayya cewa take nidai Ina sonsa haka tabi Daddy tana rokonsa haka suka shiga mota suka tafi gida.
Mima tace zaka San ni na haifeka Spark,Naila ce ta fito ta Sha wanka tazo gaban su Mima ta durkusa tace Ina kwananku,Ruwan ashar kawai taji Mima tana ce mata Karuwa kinwa Dana asiri ya haukace ba abinda baya fada mana wlh sai an sakeki zaki ce na fada miki banza Yar talakawa Yar matsiyata,sai nasan waye ubanki,Naila banza ta musu tace bari na kawo muku ruwa Dan Allah karku tafi ta mike ta shiga kitchen ta kawo musu lemo da snacks ta ajiye a gabansu tare da tsiyaya musu ta mika musu.
Mummy ce ta karba ta watsawa Naila a jikinta tace kece bakuwar lemo ba a Saba Sha a gida ba,ubanki ne ya siyo Karuwa Yar film,Mima ce tasa hannu zata Mari Naila,Spark yayi Maza ya janye Naila,Naila murmushi tayi a ranta tace Inama ta mareni wlh da yau baza tayi bacci ba,Naila ba abinda ya mata ciwo irin zagin da suke mata suna zagin iyayenta,Spark yace kiyi hakuri kinji,tace ba komai rayuwa ce,da uwarki ce cewar Mima,Kai Kuma kaga hasken fata ka makale sabo da kyau ai kyau kabi kaji kunya duk kyan da Allah ya Maka,Kai kuwa Spark wlh baka da kirki shashasha ne.
Naila ce tayi magana tace ba komai ai ko don darajar haifar min shi da kuka yi gashi Kun Raine shi kuka dinga Masa tsarki Kuna wanke masa Hallare idan yayi fitsari ko don wannan ai dole na girmamaku domin kuwa Kun wanke min Hallare sannan lokacin da aka yi Masa kaciya taji Hallare taji ciwo amma kuka dinga bikinta Kuna tsomata a ruwan zafi har da Zuba Dettol,har kaji kuka yanka Masa ta Yan kaciya,Spark yace harda kosai aka dinga soya min,Allah? kaji ko duk Dan tayi inganci har ta shahara ta kawo yanzu lafiya da ita, ko Dan wannan wlh iyayen miji sunci a girmama su sosai,ko me zaku ce bazan ce komai ba tsakanina daku sai addua cewar Naila, Spark bai ce komai ba har su Mima abin ya ishe su sai suka bar gidan.
Naila ta kalle shi tace me zaka ci? Kallonta yayi yaga ko damuwa bata nuna ba yace kiyi hakuri,murmushi ta saki tace laaa ba komai ai iyayene daidai macen da Bata fama da matsalar dangin Miji wlh amma sai dai na wata sunfi na wata amma duk da haka wasu suna dace sai dai ba a rasa kananan maganganu nima Kuma a yanda ka aureni ne babu yardar su ya jawo min,Baki San gidanmu ba ai idan suka sani ko suka raina mutum to baza su yarda ba,musamman mummy itace ta raineni baza ta yarda ba tafi son harka da masu kudi,Naila tace talaka bawan Allah dama da yawa wasu masu kudin haka suke basa hada jininsu da talaka duk kyawun mace basu bari yaransu su aureta indai basu da kudi,yace bari na shirya mu tafi Kano ki hada mana break sai ki sake wanka sun bata miki jiki da lemo,Kitchen ta shiga shi Kuma ya haura sama.
Yau ma a YouTube ta Kalli girki ta hada musu yayi dadi kuwa suna karyawa ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin shadda pink wacce ya ganta da ita a jikinta gidan Mummy farkon zuwanta Abuja,yace ke cire kisa Abaya doguwar rigar ta dame miki duwawu za a kalleki,Naila taki yarda tace ai mayafin da girmansa,yace nifa ban yarda,Naila ta fara fushi amma a lokacin ya duba online ya zabi Abaya me shegen tsada,Naila tace ko ka siyo bazan sa ba kaje ka kaiwa Wahida.
Wai ke bakya manta Abu ne,Naila a ranta tace muje Kano din zaka ga iskanci kukan da ka sani irin Kaci banza,a fili tace nifa ko ka siyo bazan saka ba,ni kike fadawa haka? Naila tace ae,yace zan miki fata fata wlh naga kina kawo min raini sabo da Kinga ba abinda na miki na kyaleki ko? Naila tace kayi mana Dan ragowar ciwon Sanyina na gidan Yari ya kamaka gwara ma ka barni naje gida a Kara wanke ragowar, Dariya Spark yayi yace ai dama idan mutum yayi aure ai ba ya rasa Sanyi tunda ku mata kullum a cikinsa kuke,Naila tace kamar yanda kuke fama da Basir ba ku Maza haka mata suke faman da Sanyi,ramawa kika yi kenan? Ae mana haka kawai kace wani kullum a cikin Sanyi muke Kuma ai a Basir kuke,muje tunda baza ki Sa Abayar ba ana so ki fito a matar me kudi Alhaji Ashraf Spark kina cewa ke a'a Yar kauye muje haka, ya kira waya yace a ajiye Abayar zai karba gobe suka ce to.
Mayafin ta yafa da hand bag da kayanta na sawa duka gaba daya yace akwai lefenki a can,Naila tace sai Nan gaba zan saka,yace muje ya daukar mata jakar tata tare da rike mata hannu da daya hannun,Suna fitowa Driver ya bude musu gidan baya a motar Naila ta Kalli Spark tace dole nayi yanga zaga ka bude min da kanka ni bazan shiga budewar driver ba,Spark Yana murmushi ya zaga tare da bude mata ta shiga zai rufe tace tsaya ka gyara min mayafina ka tabbatar bai fito ba,Spark Yana dariya ya gyara mata tare da tambaya ranki ya Dade yayi?tace yi min kiss a goshi haka ake soyayyar idan Wahida ce ai ka iya bude mata hakora.
Spark a ransa yace Allah sarki Bata San ma hararar da aka mata na rama mataba duk da cewa tayi min laifi shi yasa itama na hukuntata,zagawa yayi ya shiga driver ya kulle Masa kofar ya shiga suka ware Airport,Naila a motar ta kira Chikar ta fada mata,chika tace nima Nan da lokaci kadan zan taho biki,bikin wa? Idan kinje Kano za a fada miki,Naila ta kashe wayar ta kira Beauty tace Gani nan zuwa kano hmm tare muke da Baby fa yau Kuma Naila sai cikin jirgi ku tayani murna Naila zata hau jirgi,tace Chikar gayu ta fada min wai aure aka miki baki sani ba? Karyar Beauty ce taji komai a wajen Mohsin na daurin auren Naila,Naila tace ae mana to abinka da iyayen da suka Isa da yarsu ai na hakura zanyi biyayya,Beauty tace to ya tsinkar fure Naila tayi kasa da Murya kamar me rada tace ai yafi karfin fure sai dai a yayan ake tsinkewa sun nuna nunannu ne,Beauty tayi dariya tace nayi Shirin tarbar babbar kanwata,Dan uwarki nice kanwar taki,Naila Bata San Beauty yayanta zata aura ba har ta fara gyaran Amarya ma tana kashewa jiki kudi.
Naila kuwa har wani Shan kamshi take yiwa Spark sabo da zata tafi gida,tace idan naje fa wasu suka ganni a gari aka Kai gulmata gidan yari suka dawo nema na? Spark yace ba Wanda zaizo ai da nasan za a zo nemanki kema kin San bazan bari kije ba,na riga na Bada kudi ko ankai gulmarki baza a maidaki ciki ba,ke ko kamaki aka yi aka kaiki baza su maidaki ba,na riga na kashe case din,kin San fa Nigeria sai idan baka da kudi.
Suna zuwa Airport Naila sai kallo akeyi Yana rike da hannunta suka shiga jirgi,Naila sai murna akeyi a haka suka sauka a Kano,wani driver dinne yazo da dalleliyar mota ya dauke su,har layin su Naila,Abba ta hango Yana siyar da kayan moyarsa,Naila tace tsaya a nan na fara ganin Abbana,Spark yasa aka yi packing Naila tace bude min kofa,ya fito ya bude mata ta fito ya rike mata handbag din suka karasa wajen Abba a rumfa,Abba ya washe baki harda Waka yace ah,ah a..yan..yan..yan..ya Naila ta,Dariya suka dinga yi ba kamar Spark da bai San dolonci Abba ba, durkusawa Spark yayi tare da gaida Abba ya amsa yace Mijin Nailata,Naila tazo zata rungume Abba amma Abba yaja baya yace Kubra ta isheni matsa wannan ai raini ne uwarki nayi ke kina yi,Spark ya nuna yace kiwa naki kema gashi nan,Spark ya boye dariyarsa shi dai,Naila tace Abba ana ta arahar kayan Miya? Abba yace a'a na daina yanzu tsada nake ta yi cutar da mata suka dinga yi min nake fanshewa duk sai na fanshe kudina, Batoola ta jawowa mata tunda ta gujeni yarinya na gama koya mata salon girki yanzu nasan Usman dinta yaci kalarsa yafi sau goma,tashi kuje ciki Kun zauna a waje,Naila ta mike zasu tafi cikin gidan Abba yace Naila an Kara zama India,dariya suka yi suka tafi.
Mota suka shiga suka nufi gidan Allah yasa unguwar ba kowa yasan Naila ba sabo da Bata Dade da zuwa daga kauye ba ta fada prison.
Gidansu suka nufa tare da tsayawa a kofar gidan sannan Spark ya daukar mata kayan suka nufi cikin gidan,Khalil tsohon saurayin Naila ya kwala mata kira bai San tayi aure ba baya gari,ya karasa kusa da Naila yace Naila duk irin son da nake miki shine kika biyewa me mota sabo da yana da kudi.
Nan take Spark ya daure fuska ya fisgi hannun Naila suka yi ciki
suna yin sallama su Zarah suka dinga murna ga Aunty Umma ga Naila tazo,Hidaya kuwa tana zaune tana gyara Salat ko wani murnar kirki babu, Naila tana ganinta tace Yar bakin ciki an fara ne? Ki dinga addua kina da cutar hassada,Umma ce ta leko tace bana son wulakanci ke daga zuwa ma,Dan me baza tayi murnar ganina ba sai ta zauna tana aikinta,Idan zaki shugo ki shugo,Spark Yana gefe Yana ta kishi da bacin rai namiji ya kula Masa mata, Umma tace shugo mana ai an zama daya ka zama Dan gida,Spark ya shugo shima suka shiga Palo,Naila tace Umma harda canja kujeru sababbi? Umma tace ai har waya na canja,Abba ne ya shugo gidan daga ji ana zancen waya sai ya shugo palon yace Tecno ce me sunan mijinki Spark na biyar,Umma tace Spark 5 ke Naila,Abba mikewa yayi yace bari a kawo ruwa.
Umma ganin suruki tace yanzu zan tashi,Abba yace Yar Inna bana son haka sai Kinga suruki ki nuna ta Allah ce ke,ai hutawa kika Saba yar Inna, barshi ki huta ya fice yaje ya siyo lemo da ruwan roba da kudin aljihunsa ya shugo,Hidaya tana kitchen ya leka ya dakko plate Yana cewa na kashe kudi yau haka lemo ya tashi a kasar Nan? Wlh Dan ba Kara bazan sake ba yau dinma karambani ne,ya zuba ya Kai har Palo,yace Kaine Bako ka Sha, Spark bai fara Sha ba Abba yace kasha karka jawo min asarar kudina abin duniya yayi tsada yanzu,Harara Umma ta zuba masa a boye yace. Bari na koma bakin aiki na ya fice.
Naila tace Umma Ina Jaririyar? bacci take tana daki,Mohsin ne ya shugo palon dauke da sallama,Naila harda ihu tace darling hannu ya mika mata suka tafa yace na manta ma munyi fada,tace ai zamu shirya,gaisawa suka yi da Spark sannan suka fara Hira,Umma taje ta karbi Hidaya ita Kuma taje ta gaida Spark ta zauna ana hirar da ita,Naila tace Hidaya an fara kyau ga hanci Yana ta mikewa ashe zakiyi kyau,Hidaya ta zumburi Baki ta mike ta fice ta shiga kitchen tace Umma kiyuwa Naila fada a gaban bako sai disgani take,Ke Kuma ki dinga hakuri ke baki San wasa ba, Naila wasa take miki ke bakya ganin yanda suke da Mohsin ne.
Spark kuwa Zarah ya dauka tare da dorata a cinyarsa Naila ta kalleshi ta Masa inkiya da hannu tana hararsa wai ya sauketa,Murmushi ya saki ya mata banza,Mohsin ne ya radawa Naila yace aure zanyi bikina ko sati biyu bai kai ba,Naila tace wayyo dadi kasheni,yace sai Kinga ma amaryata zaki San nayi dace kin Santa fa,Naila tace Allah? Yace kin San kuwa ya take? Naila tace ya kirjin nata yake tunda Kai a Nan la'anarka take,Mohsin yayi dariya suna rada yace a tajamjam,Naila ta sheke da dariya,tace na Maka murna ya bayan?yace wuhuhu ai tarago guda ne,Naila tace to dole mu tashi a tsaye da gyaran Hallare,Mohsin yace ai tsumani zakiyi amma sai ta Saba zan Sha maganin fa kar na wargaza mata Bado,Naila tace Kaka zaizo biki zan Masa waya ya taho min da wasu nima har mijina zanwa saiti,Mohsin yace ke Naila har kin San Abu,Naila tace uhm gobe dani za aje zance,ya zama dole mu tafi ki ganta da kanki, Spark sai haushi yake ji Naila ta share shi tunda aka zo Kano take Masa yanga,ganin kamar ransa ya baci sai ta dawo ta zauna kusa dashi,duk da haka shi dai wai ta daina kula dashi sai complain yake mata.
Umma ce tazo suka yi ta Hira da shi sai bayan La'asar ya musu sallama bayan ya bawa Umma kudi,ya fito Naila ta rako shi yace to Madam zan tafi duk Inda zaki je sai kin fada min ko Nan da kofar gida ne,Naila tace to,yace sai me? tace ai ka sani kaima kudin gyaran jiki Kuma zamu yi biki,yace zan sa miki a accnt,Pocket money fa? Kudi ya zaro ya bata,tace na gode,saura wani ya miki magana ki tsaya kulashi, ya shiga mota sannan ya sauke glass kasa yace I love you,tace Wahida fa? Harararta yayi yace na gaji da zancen nan ya daga glass sama yace da driver suje Kawai suka tafi,wani ne makwafcin su naila zaiwa Naila magana taji spark yace ki koma gida fa,Ashe shi Yana ganin matashin yace driver ya tsaya,Naila gida ta koma kawai.
Tana komawa Umma sai murna take tace Alhmdllh kinyi miji Naila,Kwanciya Naila tayi a Palo Umma tace fito girki da aikin gida ba shegen da zai miki,Sai kayan gyaran jikinki na siyi wasu duk mun siya kadan za a karo sai Kuma na Skin Budurwar Mohsin tace zaku dinga zuwa tare,Naila tace to ai dai a bari na huta.
Tun a jirgi Spark yake faman kiran Naila taki dagawa sai yanga take Masa,kiran duniya sai ta Sa wayarta ma a silent,tace kaje ai ka kira Wahida sabo da ka raina min wayo a gabana sabo da cin fuska wlh sai ka bani hakuri tukun ai ka maidani ba mace ba ma.
A dinga sharhi pls nafi saurin typing
AsmaBaffa
[12/19/2023, 3:38 PM] AsmaBaffa: PAID GROUP ONLY
Accnt no
0175487861
Katin MTN
08061929616
Yan Niger
+22790795939
🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI
BOOK 1
66-70
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
Page naku ne
Maryam Idris Kabir
Ummy Aysha
Lubabatu Mijinyawa
Mmn Nasree.
Momy FARUK
Oum Aariz
Aeesha
Rukayyarabiuadam123
Reina
Sadiya Muhammad
Hajjafatty
Hey lovelies
Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?
Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?
Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?
Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?
Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din
https://wa.link/49vn47
Spark uzuri yayi mata
yasan taje gida Kuma maybe wayar tana jaka,Yana zuwa gida ya tura mata text message cewar