Showing 96001 words to 99000 words out of 158722 words

Chapter 33 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

398

yaje gida lfy,Naila kamar bata gani ba,shuru shuru ba reply ya daure har zuwa dare sannan ya sake kira sai da ya kira yafi sau biyar sannan Naila ta ga a haka ji tayi tayi missing dinsa baza ta iya share shi ba.

Spark ko da ta daga baiyi complain ba,kawai ya mata uzuri ,Naila a ranta tace wato ma baiji haushi ba bai damu ba,me kike yi? Bacci,amma naji ki fess? to bacci nake ji ni ta furta ,hmm yaji kamar fushi take yi yace alright,Yana so suyi waya yaji Muryarta gaba daya taki bada fuska shi ya rasa me yayi mata,kawai yace good night ya datse wayarsa,ita kanta bata so ba.

Umma tana kusa da ita tace Ashe kuwa zaki koma gidan miji ba shiri wannan iskancin ba a gidan nan ba,Yana miki magana kina wani share shi, sannu Naila karfa ki manta Yar gidan Hashimu Dolo ce ba kowan kowa ba,a gidan nan baki isa ba wlh.

Spark kuwa Yana zaune ya tallafe fuskarsa Yana tunani,kwanciya yayi jiki ba karfi yace Spark kwanta karka kashe kanka akan mace,Mace sai ta haukataka,duk yanda yaso ya share amma ya kasa sai faman tunanin Naila yake,gidan gaba daya ba dadi bata Nan.

Fitowa yayi sanye cikin Kayan baccinsa Silk olive color, a hankali ya nufi kitchen ya dakko lemon gongoni ya zauna a Palo tare da kunna tv Yana kallon American film a zahiri amma a ransa Naila yake tunanin gaba daya,zata susuta shi gaba daya.

Naila ma tunanin Spark take yi a haka tayi bacci,sai asuba ta tashi bayan tayi sallah tare da Azkhar ko bacci Bata koma ba ta fito ta shiga kitchen ta fara hada musu break fast sabo da yara Yan makaranta,tana yi tana gyara gidan, kafin Yan makaranta su gama shiri ta gama komai tana wanke wanke ma,Abba Yana dakinsa shi da Umma ya mike ya leka ta window Yana ta kallon Naila tana aikinta,farin ciki ne ya kama Abba,Umma ya kira yace Yar Inna taso Kiga yarki tayi hankali,Umma ta leka itama tana washe baki tace shi yasa naji karar kwanika hannu ta daga sama tana cewa Allah na gode Maka,Abba yace Alhmdllh ya mikawa Umma hannu suka tafa a hankali ba tare da sauti ya fito ba, sabo da farin ciki da murna, Naila har masifa akewa yara Dan iskanci ku shirya ku tafi makaranta sai Kun makara, ke zarah baza ki Sha shayi ki tafi ba,Ke kuma Hidaya ki hadawa Aslam shayin mana sai Kun makara,Hidaya sanye da Uniform ta hada musu shayin suka Sha tare da doya da kwai da Naila ta soya, Suka karya sannan suka tafi makaranta,ta sake wanke kwanikan da suka Bata ta gyara wajen da dakunansu duk ta gyara,Umma da Abba ma karyawa suka yi sannan Abba ya fice wajen kayan miyarsa Yana mita Yana cewa ni wannan sana'ar ta isheni wlh kullum mutum sai ya zauna a rumfa kayi ta zama a benchi, basir ma ya kamani,ni na gaji gwara a canja min wata sana'ar.

Naila sai da ta gyara har dakin Abba sannan tayi wanka ta zauna ta karya ga Spark Yana ta aikin kira bata daga ba sai da taji itama muryarsa take so ta ji sannan ta kirashi back,yana dagawa again baiyi complain ba ko kadan uzuri ya sake mata Naila Kuma so take lallai sai yaji haushi,Gashi bata iya Masa rashin kunya,Yana Jin kalau take sai ya mata sallama abin Yana damun Spark sosai.

Haka ya shirya ya fita Office cikin wani yard me masifar tsada,Kai da ganinsa ba sai an fada Maka ba Tan color,fuskar nan a hade ba fara'a yanda yake asalin Spark kowa ya kulashi sai masifa,Aikin ma ya kasa tsaki ya ja ya shiga Mota zai fita,manager yazo yace sir takardun nan zaka kawo,Spark yace karka dameni da wasu takardu ya ja tsaki ya yace da driver muje, gidan Mummy yaje,ta ganshi ransa a bace yau a spark dinsa yazo,tace kaga karka zo Inda nake bayan rashin mutuncin da kayi mana a gidanka, Spark Ido ya lumshe yace Mummy Ina Kwana? Ban sani ba ta bashi amsa.

Yace sorry Mummy daga nace zan afka miki shike nan sai ki dauki gaba dani ai idan aka tsine min nake nufi,yanzu Spark sai ka iya afka min? Spark yace idan aka tsine min ba mene bazan yi ba ai tsinuwa ce take aiki,yanzu sai ka aikata? Spark yace me zai hana kuwa,Spark ko wani ka ganni dashi Ina harkar banza da shi ai sai kayi min fada,yace Akan me? Kina Jin dadinki zan miki fada,ke da kika Raine ni Kuma kawai sai na miki fada sabo da kina neman Maza ba ruwan Spark kiji dadinki ai ko Mima ce ba abinda zance,iyakaci na dinga yawo da wandon karfe sabo da kar a biyo ta kaina.

Allah ya shiryeka yace Ameen wai Mummy ku mata ya kuke ne? Sai a rasa gane kanku sai kace masu Shan kwaya mata haka suke,Mummy tace an fara fada ne? dama wannan marar kunyar ai tukunna nama sai ka saketa da hannunka,nifa ba laifin data min kawai tambayarki nayi sabo da na San rirrin yanda zan zauna da abata lafiya,Mummy tace lallai baka da kunya,ka gama yi mana rashin mutunci a kanta yanzu kazo wai a fada Maka siririn mata, ta kasheka,share zancen yayi,tace ai baka Jin kunya Kai ka gama zaginmu shine kazo yanzu kana wani tambayata sirrin mata ya muke.

Yau da yamma Mummy ta dauki wanka sosai ta shiga motarta tana Jin kida sosai sai gidan Chikar gayu,tana zuwa ta hango gidan Malam wow tace Kai kai ya zama wajibi na shugo gidan Nan a matsayin mata,Chikar gayu tayiwa waya ta fada mata a bude gate,daya me gadin ne ya bude gate tayi parking sannan ta fito tana baza kamshi, Basiru kuwa ya saka Yar shaddarsa ta sallah Yana zaune a Palo ya hakimce Yana karkada kafa irin me kudin nan,Chika tace kayi fa aiki me kyau,yace za a ga aiki ai ki kwantar da hankalinki,aiki sai ma mun shiga dakin bacci, Mummy ce ta shugo Palo taga yaci kayan alatu sosai shugowa tayi ta zauna tare da furta wow ta zauna,Basiru Yana karkada kafa Yana wata gadara da kyar yake magana,yace barka da zuwa ya Kalli Chika yace my Watermelon Ashe yau bakuwa zakiyi Yana magana Yana kallon Mummy,Mummy ma kallonsa tayi kawai Basiru ya kashe mata Ido daya tare da daga mata gira,Mummy a ranta tace kaiii ya daga min girma murmushi ta saki,ya kwalawa Sheyi kira kamar wajensa bakuwar tazo yace a kawowa babbar bakuwa kayan motsa baki,Mikewa yayi harda zuwa ya rike hannun Chika Yana cewa Watermalone,Chika a sace ta fisge hannunta tare da gasa Masa harara tana ce Masa Banda wannan.

Amma Ina Basiru a ransa yace tab ai wlh ba a isa ba na fito a miji Kuma ace bazan taba komai ba an San hakane akace ayi film,Sama ya haura yace kizo Ina son ganinki harda masifa irin me gidan Nan.

Ba yanda Chika ta iya ta bishi sama tace da Mummy Ina zuwa,suna zuwa Sama a palon sama suka tsaya ya Bata rai yace wuce ciki,in wuce ciki in Maka uban me sadaki ka biya? Film kika ce za ayi ai ana kwanciya a Saman bed,ai Hausa film muke yi ba Nollywood ko American film ba cewar Chika,Basiru yace dama kin San ba Nollywood zamu yi ba kika bata min lokaci to wlh Baki isa ba ni Nollywood film zanyi sabo da haka wuce ciki muje.

Chika tace baka da hankali Basiru Hausa film muke yi na musulmai,Basiru yace ba komai ai Hausa ma suna Waka da rawa a ciki sai munyi rawa da Waka tunda hakane Kuma karki sa Bra kizo muyi girgiza,Chika tace ai ban taba sanin mahaukaci bane Kai sai yau na fika iskanci wlh ta ja tsaki ta juyo wajen Mummy ta barshi tsaye,yace wlh sai nayi Yaudara a film din sai na so kawar taki komai tsufanta.

Mummy ce tace wannan ne dama mijin naki? Chika tace ae,amma duk kudinsa yake saka shadda me araha haka,to ai wasu masu kudi idan kudi yakai kudi ba sa saka kaya masu tsada,Mummy tace wannan ma gara ne wlh karki sake ya dinga raina miki hankali Yana zaginki ki rama ki zagi iyayensa,haka Mummy ta zauna tana faman zuga Chikar gayu akan taci uban mijinta kar ta daga Masa kafa...

Chika harda hawayen karya tana fada mata yanda Basiru yake zaluntarta,Mummy tace shi yasa fa wasu matan suke kashe mazajensu wlh ni bana ganin laifinsu ma,ba ruwanka zaka huta ka shana kayi abinda kake so,Chika zama ta gyara tare da gyara wayarta tace kice yanzu haka ake yi?Sosai ai mata sun daina zama yanzu,Ina ma zan San Inda ake siyar da gubar Nan,Mummy tace zaki samu mana wata kawata tana siyarwa a sirru,Naila tace idan na gaji zan kawo kudina,Mummy tunawa tayi karta jawowa kanta sai tace ke naji yanzu bata siyarwa amma zan tambayar miki ko ta dawo tana siyarwa.

Basiru Yana Jin zata tafi ya fice ya rigata zuwa Jikin motar,Chika Bata hanashi ba,Mummy ya Gani tana Masa murmushi,yace bakuwar Alkhairi zaki tafi? Mummy tana wani fari da Idanuwa tace ae sai na sake dawowa,wani zuwan ni zan kawota da kaina,Mummy tace okay bari kaima na baka number ta ko gaisawa zamu dinga yi watarana,Basiru jiki na rawa ya dakko kwakwurar wayarsa yace Af na manta babbar wayata a bedroom,Kai ai wayarce babba sai ta dinga Maka nauyi a aljihu musamman iphone nauyi ne da su,Mummy tayi murmushi tana karanta Masa number bayan ya shigar tace ko Kai kadai ma zaka iya zuwa gidana ba kowa,yace kasurgumar bazawara ce ne haka? Mummy tace wlh sakin Allah ce ba sakin mutum ba mijina mutuwa yayi kaga kuwa ai sakin Allah ne,Basiru yace sorry sorry harda dafa Kafadar Mummy sorry Yana girgizawa da hannu,Wayancewa tayi tace bari mana Alhaji Basiru kar matarka kanwata ta Gani,yace ke rabu da ita hakuri nake dama da ita ba uwar da take min na soyayya,Mummy ta furta wasu matan sai hakuri wlh basu iya kula da miji ba musamman yaran Nan,Basiru yace habawa bari kedai Hajiya Ina Shan wahala a kasar Nan da kudinka da komai mace ta zame Maka masifa ni sakinta ma zanyi,Mummy tace a'a ka dai Kara hakuri ai gwara kayi mata kishiya tunda gidan kaga part part ne,Kin kawo shawara na gode sai na kawota,Mummy ta shiga mota tana kissima irin kudin da zata samu a hannun Alhaji Basiru.

Basiru ne ya dawo ciki yace Baby,Chika ta hade rai tace the End film ya kare,ko kwanciya bamuyi ba zaki ce ya kare? Chika tace ya kare gashi Nan rubutu akeyi na karshe dalla mallam kama gabanka bana son raini,tsayawa yayi zai sake magana Chika ta jawo takalminta me tsini ba shiri ya fice.
Shirye shirye tayi itama na tafiya Kano,washe gari ta wajen Mummy ta biya ta daki cikinta a haka ta samo address din Misam har Office dinsa tace bari na dawo daga Kano nasan ta Inda zan bullo Masa.

Naila tunda taje Kano ake Bata magungunan gyara da kudinta Kuma tana siyan wasu,Yau zasu je zance wajen budurwar Mohsin,Naila a waya ta kira Spark ya daga Yana fushi sabo da Bata taba kiransa ba idan ya kira ma sai taga dama take dagawa sannan idan ma ta daga baza tayi maganar kirki ba, daga gaisuwa shike nan,abin Yana yiwa Spark ciwo matuka,sai da kiran ya katse sannan ya kirata back ta dauka,tace Ina yini? Lfy Alhmdllh,dama unguwa zanje nace....sai kin dawo kawai ya kashe wayarsa,hankalinta ne ya tashi amma ta danne ta shirya ta zabo atamfa cikin kayan lefenta wata Indigo ta saka riga da skert kamar an aunata,tace wai Lefen Umma har akwati Sha shida aka kawo? Umma tace gashi kin Gani ai sun kashe kudi,tace to ki kwashi wasu mana a bawa su Hidaya da Zarah suma su Dinka,cikin shaddojin Kuma Abba ya dauka,Yaya Mohsin da Aslam,Umma tace wa yace miki haka akeyi? Ai Dan kiyi Masa kwalliya ya zuba miki,to ai dai ana kyauta ki zaba Hidaya da Zarah su zaba a bawa my love Mohsin da Abba ki duba sunyi yawa fa,shike nan zan fada musu an gode.

Mohsin ne yazo yace fito mu tafi mana,Naila ta fito da Jakarta da mayafi duk sababbi,Umma tace ki gyara mayafin Nan sosai bana son wannan iskancin na yaran zamani mace me aure ba a banbanceta da budurwa bai dace ba, wasu mazan suna tare su a hanya idan mace tayi shigar Kamala ba me tareta yace Yana so,amma yanzu mayafin da wasu matan auren ke yafawa ko budurwa sai taji kunyar fita da shi, Naila an zama matan aure cewar Hidaya tana kallonta,tace ai kuwa Hidaya baki ga sai Shining nake ba? Hidaya tace na gani ai,Naila tace to Hallare ce ta jawo shi yasa kika ganni haka,Hidaya kunya taji tace ke Aunty,Naila tace ah to Kuma baza a Fadi gaskiya ba sai a zauna ana boye boye kamar me bin Maza,Mohsin ne yace Dan Allah muje ko kunya bakya ji naga ranar da zaki hankali ki fara kunya Umma fa tana jinki sharewa takeyi,Naila tace to ai ta San harkar itama gashi nan ta siyo min kayan gyara.

Suna fita taga mota me kyau Sabuwa wata zata Kai ta 2m,Naila tace motar wa ka aro? yace ke baki sani ba to mijinki ne ya bawa Abba,Abba yace ya bar min ita nine Dan zamani Allah ya tsare shi da tuki,da fa wai siyarwa zaiyi Umma tace wlh ba Wanda zai siyar, Naila tace yayi kokari Spark gaskiya,nayi dacen miji,shi yasa nake sonsa fa,Mohsin dariya yayi ya fara driving,yace Naila na fahimci Baki San Hallare ba shi yasa kike wannan iskancin,wlh na Santa kaji Yaya to bari kaji na Santa sosai sau nawa Ina kare mata kallo,Mohsin yace ai shike nan magana ta wuce,yanzu me zaki siyawa Amaryar? Naila tace a siya mata turare mana,tace Yaya ya Hanan wai? Yau a gidanka zan kwana,Yace kishi take Abba ya fada mata zanyi aure in kika ga haukar da take ya Baci,Naila tace to ya nonon nata? Yace ai yanzu nake kallonsu kullum sai anyi yawo ba riga tun Ina kallo a dadin Rai har sun sire min,yanzu ma ni haushinsu nake ji,kullum Kuma sai an bude,Naila ta dinga dariya,tace duk duniya ban taba ganin Dabba irin Hanan ba,da haka ake birge miji,Mohsin yace uhm ni yanzu na Amarya nake Hange na gaji da nata Abu duk sun Sha iska sunyi Sanyi sun huce,Naila ta dinga dariya tace yau dole na kwana a gidan,yace a satin Nan zamu tare a sabon gida kafin ayi bikin.

Turarukan suka shiga Shopping mall zasu siya,Mohsin Zai biya kudin Naila tace Ina auren me kudi zaka siyi Abu Ina wajen matsa ni taje ta biya kudin sai gidan su Beauty,Naila taga har cikin gidan suka shiga, tace me zan gani wai? Wannan ai gidan su Beauty ne,dariya Mohsin yayi yace itace amaryar Ashe babanta shine nake zama Masa a shago,gashi ya bani gida sabo part biyu ba Nisa da daya gidan nawa ga Kuma yace naci gaba da juya wannan shagon halak malak,Naila tace amma nayi murna,Ashe Kai na dinga yiwa zance a gidan yari,yace wlh,Naila tace akwai tsiya Yaya Hanan da amarya fa za a gwabzu,Mohsin yace wannan bata fada,yarinya shuru shuru saliha ga iya soyayya ai Hanan sai dai ta zalunce ta.
Naila tayi dariya a ranta tace zaka ga Saliha ganin idonka.

Beauty ansha gayu cikin Abaya me tsada ta fito suka rungume da Naila tace amma wlh Kun raina min wayo amma naji dadi ko ba komai na nadaki a madadina tunda ban auri Yaya ba yayi Kuskuren zuwa a gidanmu, nasan zaki zama wakiliyata yawwa a adana min shi,Beauty harda Jin kunya wai ita ta gari Naila tace duk fake ne nasan komai yarinya,tafawa sukayi suna ta hira suka bar Mohsin a zaune shuru.

Ya gyaran Jikin? Beauty ta tambayi Naila,tace Inda kika min kwatancen na fara zuwa tuni ma suna goge min skin sun bani su lotion da sauransu,sai harkar kamshi,sai dare su Naila suka wuce gidan Mohsin.

Hanan tana Palo kawayenta sunzo sun zauna in banda tsinewa Mohsin da Maza baki daya ba abinda sukeyi suna zugata, wallahi karki sake Amarya ta takaki ko shi ya takaki,Hanan tace Ina zan yarda ai wlh tunda naji zancen nan shi da zaman lafiya sai dai ya Gani a makwafta,masifa da bala'i ya dinga ganinsa kenan.wata a cikin kawayen me hankali tace ni Kuma a shawara ki kwantar da hankalinki Kuskuren da kika San kinayi ki gyara,sannan karki tayar Masa da hankali domin zai sake tsanarki ne wlh,tun Yana sonki zai daina gaba daya,idan kuwa kika kwantar da hankalinki an San akwai ciwo amma daurewa akeyi, mijinki na gari ne ki daure ki lallaba abinki shine kadai zaki siyawa kanki mutunci.

Ko mutuwa zakiyi wallahi aure bazai fasa ba, Maza basa fasawa,idan kika daina nuna Masa kishi sai yafi Jin kunyarki ,surukarsa zaki zama wlh Kuma zai dinga tsoronki,duk abinda yake ciki akan auren sai kinji labarin ya fada miki,ke ko fada suka yi sai ya fada miki,kece uwar gida amma mu muke Bada kanmu har a kawo wata sama ta Kai tazo ta kwace mijin ko tayi sanadin mutuwar aurenka.....da masifa suka hayayyako mata to sannu ustaziya mu zakiwa wa'azi to baza ta kwantar da Kai ba salon a takata kenan Yar bakin ciki,kawar wacce a cikinsu ma itace karamar tace shike nan Allah ya Bada sa'a,suka ce Ameen munafuka.

Naila ce tayi sallama kafin ta shugo a palon,da Sauri Hanan tace kanwarsa ce karku kulata itace ta je gidan yari taje a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login