Showing 84001 words to 87000 words out of 158722 words
Chapter 29 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
Spark Ido a wando tace Kai Sir abarka....tana zaro ido,yace what? Mikewa yayi tsaye,Naila tace Subhannallahi maganina baya aiki wlh ka ganta Kai Kai Kai Inci nawa ce? Kallon Inda yaga Naila tana kallo yayi kunya ta kamashi shi sai yanzu ya gane ma abin da take kallo,dariya ta bashi yace inchi tara ce,ko kina so? Kai ta fara sosawa tace ae,a'a,ae,a'a.
Tsaki yaja ya wuce sama Naila ta bishi tace tsaya sir,a ranta tace Kai maganina bayayi wlh,Sir tsaya mu gani.
Spark harda karawa da gudu yace ni wannan na rasa gane mata,dariya ya ba Naila ta dinga dariya tace kan uba Zuru sunan wani gari.
Washe gari da yamma Taga yaci wankan da Bata taba ganin yayi ba,mamaki ya kamata,sai ga Wahida taci gayu ta shugo,sorry Baby na ajiyeki kina jira,tace ba komai my love muje, Spark yazo a gaban Naila ya rikewa Wahida hannu,Naila tayi sauri tazo ta raba hannu ta fisge hannun Spark,idonta ya ciko da kwalla,tana Ina Ina tace am...um....wallahi ...nice....nice...hannunsa ya kwace yace muje suka juya zasu tafi ta jawo Spark da karfi,ya kalleta,tace zo muje kaji...hannunsa ya fisge...gabansa ta tare da gudu ta tsaya,taki magana Kuma,gefe ya tureta zata Fadi yayi Maza ya rike abarsa wai kar ya Fadi yace matsa ransa a bace,matsawa tayi tana kallo suka fice,Naila tace bazan yi kuka ba ta daure dai bata yi kukan ba,amma zama tayi ta kasa magana.
Sai dare ya dawo ta kulle shi a wajen Yana ta knocking tana Palo ta zauna ranta a bace haka ta mike sanda taga dama sannan ta bude Masa ta koma a fusace ta zauna,ya kalleta kawai yace Wahida tace a gaishe ki,ko kulashi Bata yi ba,ya sake cewa tace kin iya girki,shuru tana fushi idonta ya ciko da hawaye,mikewa tayi fuuuuu tayi cikin bedroom, dariya ya zauna ya dinga yi yace saura ki cire hular gashin da kanki,ai kuwa kamar ya sani Naila sai gata ta fito ba hular gashi da kanta a bude ba glass wai Dan ya ganeta,Spark ya nuna Sam bai gane wace ba,aransa dariya yake kamar ba gobe,Naila ta zuciya tace gobe inshaallah zanje saloon a sake yi min Daadaa zansa kana nan kayan Maza na gani ai dai dole ya gane Jamilu ce.
A dinga sharhi Dan Allah
Kuyi hakuri fa wlh
Uzuri ke rikeni Kuma Ina so na muku da yawa ne.
A rike Amana fans Dan Allah karku fitar badan halina ba Dan Allah.
AsmaBaffa
[12/16/2023, 8:05 PM] AsmaBaffa: PAID GROUP
Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger
+22790795939
🏫 TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK 1
56-60
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
Page naku ne
Mom Khalisat
Alhmdllh for everything
Aisha Umar
Ummu Maryam
Faeeza
Golden pretty
Hajia Baba Nunuwa
Maman Samha
Hey lovelies
Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?
Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?
Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?
Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?
Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din
https://wa.link/49vn47
Sai da yayi wanka ya fito Yana zuba kamshi cikin kananan kaya marasa nauyi wasu sky riga da dogo wando wasu milk,Naila tana zaune a Palo kallo takeyi abinta yazo ya zauna ya Sha kyau,kallonsa ta sata ya mata kyau sosai tace Kai gaskiya bazan bari Ina kallo a kwace shi ba mene ma amfanina wai ne Ina mace,har sai na koma nayi Daadaa zai gane ni,amma dai nayi nayi kitso mana na Yan gayu kitso dai ai Yana fito da aslin fuskar mutum,to ko kayansa zan saka,a'a me ya kaiki calaba zanyi,tana ta tunani yayi magana ya Kai sau hudu bata ji ba,sai da yayi da Dan karfi yace keeee Cheffff.....Juyowa tayi da sauri yace me kike tunani haka? Naila tace Babana na tuna idonta ya ciko da hawaye ,wayarta ce tayi kara ta duba taga Mummy,dagawa tayi tace Hello,Mummy tace Nasiba Yankan Kauna na samu labari me dadi,bugawa nayi in miki godiya aikinki Yana kyau,kinji har ya samu mata yanzu ma zancen aure akeyi wlh dangi ana ta murna Kuma gata Yar uwarsa,Naila wani bakin ciki ya cikata ta daure tayi murmushin yake tace ai aiki Yana kyau a ranar kaka yazo da kansa Alhmdllh,sabo da haka ana daurawa zaki ji Alert inshaallah,ke ni sabo da murna ma ranar zan Kara miki kudi,ke sai dai ranar daurin aure tace na gode su Mima duk zamu samu lokaci har gidanku zamuje godiya,tace Allah ya kaimu.
Tana kashe wayar ta zamo daga Saman kujera suuuuuuu ta dire gwiwoyinta a kasa ta juya tare da kifa kanta a Saman kujera tana Dan danne hawayenta, Spark yace lafiya? ba komai ta furta, yace to me kika dafa? Tuwo,yace wai Baki da wani girki sai tuwo,ni bana cin tuwo ko yaushe,taya za ayi ta yiwa mutum tuwo a gida,kawai ma Dan na taba zama a gidan yari ne amma ni a baya ma bana son ganin tuwo,kullum tuwo miyar taushe,tuwo miyar kubewa,kuka,gyada etc oh can't realize that I'm tired of eating tuwo? everyday tuwo,tuwo tuwo for God sake,bazan ci ba ni,Naila tace tayi dadi miyar,yace komai dadi bazan ci ba,kiyi min Briyani rice,ko pilaf rice,Naila tace Biryani Kai Dan India ne? Sannu sai ka bari kaje India Kaci a can ni in ba a film ba Ina na taba Jin Biryani,sannan pilaf take ko me a bakinka na taba ji yau,ni Yar gargajiya ce,yace to dafa min Indomie amma indai tuwo ne bazan ci ba.
Tashi Naila tayi ta shiga kitchen ta sake duba YouTube yanda ake dafa Indomie ta Sha hadi,ta Dora Indomie ta dafa kwai kawai guda takwas,gefe ga Indomie tana dafawa,harda yin jajjage,aka yanka albasa me lawashi,carrot,da green beans duk a ciki,kafin ta kwashe ta bare dafaffen kwanta sannan ta juye Indomie a plate tare da jera kawai guda uku a tsakiyar Indomie,ta dakko wani dogon green chilli ta wanke ta saka shi a haka tsaye ta tsakiyar kawai ukun,ta wanke ganyen salat ba tare data yanka ba shima aka jera su a bayan green chilli sai tayi Yar flower dinta a tsakiyar girki,aka soka fork a gefen ta fito irin gwana tayi girki,Spark tunda ya hango plate din daga nesa da ganye falaa ya dinga dariya a ransa a fili ya fuske,ta kawo tace gashi.
Karba yayi yace professional cook ah'ah wannan girki haka,Nail tun kafin yaci ta zuba masa Ido tana so yaci taji da dadi,Spark yayi spoon Daya yaji tayi dadi yace best chef in the world,this Indomie sweet woooo ah'ah,Naila sai murna tace style nayi tana wasa da yatsunta yace kin iya,kitchen ta koma ta koma, ta kwaso kawai biyar a plate ta zauna tana cin abinta,yace to wannan girki irin na kasar waje daga china kika koyo ne? Naila tace Allah ya kiyaye ai mu sai dai a kwaikwayeni badai na kwaikwayi wani ba,Spark ya ciro ganyen salat Daya yace to wannan ya ake Masa? Naila tace kamar ba Dan gayu ba gutsira zaka dinga yi,Spark ya balli salat a ransa yace na koma cow yau, Kuma kace baiyi ba aji haushinka ya zanyi so ne ya ja min ya cinye salat Yana cin Indomie,green Chili kuwa daukewa yayi ya boye a kasan kujera kar tace bai ci ba salat sai ya cinye tas da Indomie,Naila ana ta murna tace zan sake dagewa amma da ya kushe bazan yi ba.
Abba direct gidan Malam Isa ya tafi abokinsa akan suje zance wajen Batoola, Malam Isa yace wannan mayaudariyar Kai baka San ma me tayi ba? to tayi aure tuni yanzu idan da rabo to an samu.
Abba da mamaki yace Batoolar? Yace kwarai kuwa,Abba yace to shike na itace tayi asarar samun miji Irina,amma Batoola ba karamar asarar miji tayi ba,har Ina cewa kwana biyu idan na aureta zan huta da fadar sunan Kubra sai aji Ina cewa Batoola amma kullum kiran sunan mace daya Kubra zo,Kubra yi kaza, Kubra kaza,amma idan na Kara ai na huta da kiran sunan ko da na kwana biyu ne,Malam ya isa ya dinga dariya yace dama Kai sabo da ka samun canjin kiran suna zaka Kara? Abba yace Allah ya Gani da ace Batoola sunanta Kubra to ko sonta bazanyi ba,fadar sunan ya isheni haka kullum babu ranar banza sai nace Kubra,amma Batoola ta cuceni da na tsaya na koya mata yanda ake hada jullof da kifi yanzu wani zata je ta dinga dafawa,Malam Isa dariyar abokinsa yake yace sunan Wanda ta aura Usman,Abba Yana ji to su karanta ita da Dan Usmana,dama Kubra ta fita komai,ai Yar Inna itace mace dama Batoola har wata macece,Yar Inna Inda kasan a hadisi aka rawaitota bata tsufa,sallama yayiwa Malam Isa ya koma gida,Yana shiga gidan ya iske Umma ta fito daga wanka tana bawa Jaririya nono,ya Kalli nonon yace Yar Inna ki dinga godewa Allah,Kalli Mohsin harda matarsa da yarsa amma Kai ba Sha nonon ba,Kalli Naila dan Allah ta saki Hidaya ta karba,itama ta bawa Aslam ga yanzu da Jaririya ta Kuma karba ai ke wlh macece,Umma tace Kai ni yi min shuru yanzu fa kace aure zaka yi,Abba yace to na fasa nayi mata fata fata nace kar ta sake kulani ni ke nake so,Umma tayi dariya Abba bai San Umma tasan Batoola aure tayi ba
Umma tace Allah ka koreta? fata fata nayi mata me zanyi da wannan banza ma,da ace na auri Batoola gwara na zauna kullum in ta goyaki,yanzu gobe suna ko Yan uwa zasu cika gidan anjima to kar wacce ta hau min gadona yawwa idan ma zasu kwana to su kwanta a kasa ni Kuma Ina Saman gadona,Umma tace ni wannan jarabar taka ta isheni fa duk Sha'ani sai ka kunyata ni a mutane sai mata sun cika daki sai kazo ka haye gadon Nan,ni da gidana ba me takura min.
Ana gobe suna Umma dinkunanta sun Kai kala shida,kayan jaririya kuwa kaf Mohsin ya hada mata komai da komai,Abba kuwa ba uwar da iya,amma Mohsin a sirri ya siyo katon rago yasa wani ya kira Abba kofar gida ya kawo Masa ragon,yace Mohsin ne yace a kawo Maka,mutumin Mohsin ya kira a waya ya daga,yace ka bawa Abba wayar,aka bashi waya Abba yace hello Dan Albarka,Mohsin yace Abba gashi Nan karka ce nine na siya Maka idan ka Kai kace Kaine ka siyo kawai sabo da Umma ta daina rainaka ,Abba yace Allah sarki Allah yayi Maka albarka na gode,Abba gidan yaja rago ya shiga da shi,Aslam da Zarah suna Murna Abba ya siyo mana rago,Abba yace Mohsin ne ya siyo amma yace kar nace shine ya siyo min kawai a barshi ni na siyo,kuce ni na siyo,Aslam da Zarah Dake yara ne suka ce kuwa Abba Kaine ka siyo yeeeee,Umma tana jinsu tace Allah ya kyauta.
Abba dakin me jego ya koma anyiwa Jaririya wanka ana gasa mata cibi ya karbeta yaci gaba da gashin cibiyar da kansa,Umma dakinta taje tana shiryawa ya kawo mata Jaririya lokacin tana shafa Humra,yace an samu lafiya harda shafa turare da kuwa sai warin gardi gata bata nono Kubra,a gefen bed suka zauna Abba harda zugewa Umma zip din riga ya wani wangale rigar, Umma tace dama duk sun cika har ciwo suke min bata Sha da yawa,Abba harda taba nonon ya Kalli Umma yace da zafi? Umma tace ae,yace muje na tatse shi kwarya a zubar, dariya Umma tayi tace sai kace wata saniya kaima ka Sha ku hadu da Jaririyar ku shanye shi,Abba yace uwata ta dade da yayeni wlh kice zaki dawo Dani jaririn dole,to ni wata 20 ma Ina Shan nonon uwata,ba 18 aka yayeni ba,to naji dan Allah cewar Umma.
Yana suna mutanen kauye sunzo Yan Fulani dasu gaba daya,suna ta aikin suna,ga makwafta sun shugo duk da Umma tace ba taro za ayi ba amma Abba yace wlh shi sai anyi taro har da tirsasa Mohsin lallai ya bawa su Hidaya kudin Dj,haka aka dakko Dj,washe gari suna Abba an Sha shadda ruwan Toka sai hada hada yakeyi,shi Mohsin ma Abba dariya yake bashi sai kace wani ango kamar yau aka taba Masa haihuwa,
A layin har tsokanarta suke,ranar Kuma sai ga Spark yazo shi bai San ma suna suke ba,a wata dalleliyar mota me tsadar gaske driver ya kawo shi,Mohsin ya kira a waya yazo ya same shi,tunda ya saci wayar a wayar Naila Yana yawan kiran Mohsin,Spark mota driver ya bude Masa ya fito a hankali cike da ji da mazanta ya tsaya a Jikin mota kusa da gidan Abba,Yana kallo Hidaya ta jawo zugar kawayenta sai iyayi suke sun dauki wanka suka wuce ta gabansa sai kallonsa suke,suna wani canja salon tafiya,dariya suka ba Spark wacce tafi kowa iyayi ya kalla kamar bai kalleta ba yaga mayafin ma a hannu ta rike kamar masu biki yace au suna fa akeyi,dama har yanzu ana bikin suna,Dj ne ya saki sauti su Hidaya tun kafin su karasa suke uban rawa,Hidaya tafi kowa zakewa,yace duk yanda akayi wannan kanwar Naila ce amma Naila ta fita kyau,jikinsu ma Daya bane,Hidaya wata Yar firit ce Bata da kibika ko kadan sai iyayin tsiya da giggiwa.
Mohsin ne ya karaso wajen da fa'a yace Ashe ka karaso Spark mota Mohsin ya bude ya shiga shima Ashraf motar ya koma sannan ya mika Masa hannu suka gaisa,Hira suke yi sosai sun Dade suna magana kafin daga nan yace ya kamata naga Umma na Mata barka,Mohsin yace gidan ne akwai mata da yawa ban sani ba ko zaka iya shiga,yace zan iya ni wacce Yar katuwa nake Jin kunya muje kawai,Mohsin yayi dariya sannan suka wuce ta Inda ake Dj mata sai kallonsa suke suna yabawa,wasu har suna cewa Dan waye wannan a kasar na,Spark dai har kofar gida,Mohsin ya shiga ciki tare da fadawa Umma ai saurayin Naila ne yazo wannan Spark din na prison,Umma tace Innalillahi wa innailayhirrajun Ashe saurayin Naila ne,gaskiya naji dadi Naila ta da saurayi Allah me Iko,Daya dakin da ba kowa aka Kai Spark ya shiga,Umma taci gayu ta Sha kyau dama gata fara tana zaune a kujera,Spark da sallama dauke a bakinsa ya shiga dakin,Umma ta amsa tana kallonsa yanda ya sake mugun haske da kyau abin ba a cewa komai,a kasa ya durkusa tare da gaida Umma ta amsa da fara'a sannan ya mata Allah ya raya tare da karbar Yar yace ya sunanta? Umma tace Basma, mashaallah Allah ya mata albarka,Bai Dade ba ya ajiyewa Umma 100k ya fice Umma tana ta godiya.
A kofar gida yaga Abba tare da su Hidaya da kawayensu suna cewa Allah Abba sai ka Kara mana kudi,Dake shi Abba yanda yake tsokanar yaransa haka yake yi da kawayen yayansa ma,shi yasa duk in suka zo Abba suke neme su,Hidaya tace Abba kudin liki,Mohsin ne ya gasawa Hidaya harara tayi shuru,Abba ya ja gefe ya fada Masa waye Spark,Abba anga suruki harda nutsuwa suka gaisa sosai sannan ya yayiwa Abba kyautar ban girma ta kudade,Mohsin ma ya Sha kyauta.
Bayan suna Mohsin ya fadawa iyayensa game da auren da zai Kara ya musu bayanin komai,Umma tayi guda tafi uku sabo da murna tace Ina goyon baya,yanzu da Malam Isa da Yan uwan mahaifinku sai suke a Kai kudi a tsaida rana,Abba yace da ni naso na fara kara auren Mohsin amma tunda ka riga ni Allah sanya Alkhairi.
Hanan kuwa ta rasa gane kan Mohsin sai faman Shan magani take da turare ba ji ba gani amma shuru.
Bayan kwanaki Spark Washe gari Yana fita Office Naila taje saloon aka wanke mata gashi tare da rangada mata kitso kanana sabo da fuskarta ta fito sosai,tana dawowa gida ta samu Spark ya dawo Yana Palo a zaune.
Yace Ina kika je? Naila taji tsoronsa sosai tace saloon naje fa ka gani ta bude kitson dama so take ya ganta,taje har gabansa ta Dora kanta a kusa dashi tace ka gani ta dago fuskarta sosai tace nice nan fa,Spark yace na gani a ransa sai dariya yake a fili ya nuna Sam bai ganeta ba.
Wahida itace tayi sallama tare da shugowa ta Sha wanka harda Yar wata jaka a hannunta tana zuwa ta samu Spark a Palo Yana aiki a system Naila tana kallon film, tace honey ya kk,Spark yace Alhmdllh,Mummy ce tayi sallama ta shugo tana murna yau dai atamfa tasa tafi kyau ma,tana zuwa ta zauna tana fesa kamshi,Wahida tace tare muke da Mummy,Naila kuwa Mummy ta gaisar sai Mummy ta mata wani banzan kallo Kuma yau,ta juya tana amsa gaisuwar Spark,Naila ta kalla tace zo Ina son magana Dake,Naila ta mike ta bita suka fita waje,tace yawwa fada miki zanyi ki tsaya iya matsayinki karki shiga harkar spark my son aure zaiyi,maganin da aka saki shi zakiyi naji Wahida tana fada mana kina mata kallon banza kina shigewa Spark,bazai auri Yar film ba ki tsaya a iya film dinki,wallahi ba Yankan kauna ba ko girbin kauna kike ba ruwanmu ato.
Naila tana gama ji ta ja tsaki ta juya Palo,Wahida sai wani zuba take,ta mike ta shiga kitchen ta dakkowa Mummy lemo ta dakkowa kanta da Spark ta zauna suna Sha,Spark Naila ya mikawa nasa ta karba ta balle tana Sha,wani takaici ya kama Wahida,Amma bata hakura ba ta koma kusa da spark tana shakar kamshinsa ta fara mika Masa lemon a baki,ya dinga Sha Yana satar kallon Naila,duk kitson da taje saloon