Showing 42001 words to 45000 words out of 158722 words
Chapter 15 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
Masa kamar yanda nima haka bari Daddyna ya fitar dani wlh sai na fitar da Jamilu ko arzikin Daddy zai kare muje muyi auren mu,wayyoooo jamiluna ta fara Shure Shure a Saman pillow tace yanda nake Allah ya bani kyau na ba laifi, gani da haske na, chass dani,nasan sai na birge Jamiluna.
Sake hango damatsan Jamilu tayi a ranta Yana taku ingarman namiji take ta hangowa,wani irin zaratan Maza,ranar haka Beauty ta kwana tana faman nazari akan Jamilu masoyinta, Garzali kuwa a daren har Istihara yayi ko zai samu a nuna masa a mafarkin ko Jamilu mace ne amma sai ya hango Jamilu da katon Hajiya Babba,a firgice ya farka Yana neman tsari da wannan mafarkin shi Kam,yace inshaallah ba haka bane idan kuwa hakane to Jamilu mata Maza ne,haka ya koma ya kwanta.
Washe gari da asuba Naila suna tafiya masallaci tayi sauri ta tashi tare da yin alwala tayi sallarta tayi addua sosai Allah ya rufa mata asiri kar a ganeta,tace naga makiya sun fara sa Ido a kaina,tana cire Hijab din Malam Sharu Yana shugowa saura kadan ya kamata Allah ya kiyaye amma yaga kamar ta zare abu daga kanta, gashi da sauran duhu da sauri ta daga bargonta ta jefa a kasa ya kunna haske da sauri yaga ba komai ya kalleta sosai Naila ta daga hannu haka tana addua,Malam Sharu yace wai Kai Jamilu wanne addini kake yi? ayi mutum baya zuwa jam'i,Naila tace ban yarda da limamin ba bazan taba bin kowa sallah ba a gidan Nan duk babu na gari bare a bishi sallah,kowa shegen kansa ne mummunan Abu ya aikata aka kawo shi akan me zanbi mutum sallah, bazan bi kowa ba,ban yarda da Imanin kowa ba a gidan Nan, tawa Sallar nake yi.
Malam Sharu yace Allah ya shiryeka ka gane jam'i ba abin wasa bane,Naila tace Ameen shi yasa ni ka ganni PHD ne dani wajen minding business dina,kaga shi yasa akace babu kyau shiga abinda ba ruwanka kasan irin hujja ta ne? Ina da hujja me tsauri amma mutane baku San wane mutum ba ko me yake Shirin yi sai ku dinga shiga lamarinsa,ko ka manta hadisin ne Yana daga kyan musulunci ka bar abinda ba ruwanka,to mu a arewa yanzu kowa nunawa yake yafi kowa ilimi,hankali,da wayewa,kowa yayi addininsa Malam Sharu nima addina nake yi ba ruwanku.
Malam Sharu yace mu dai gaskiya ce sai mun fada ko za a sa kanmu gabas a fille sai mun jawo aya da hadisin idan mutum bai dauka ba ruwansa,Naila tayi murmushi Allah ya bada sa'a, Kuma Ina tabbatar muku watarana sai kunji kunya,Kun sa min Ido,Kun San dalilina a dakin nan? Yace sai ka fada,Naila tace wani Assignment nake amsawa Ina gamawa zaku ga dalilin,Allah ya kaimu Jamilu cewar Malam Sharu.
Baccinta ta koma ta barsu sai wurin 11 ta tashi ko makarantar gidan yari Naila bata taba zuwa ba amma Spark shi Kuma Yana zuwa duka boko da ta addini,sai da tayi wanka ta shirya duk a cikin toilet sannanta fito da kayan data cire,tace ga zafi ga manyan kaya Ina fama wlh,ta wuce bangaren Spark masu tsaron wajen suka ce ya tafi makaranta,Naila ta dinga mamaki ta nufi makarantar, tun kafin ta karasa ta hango gashin kansa Yana sheki,dariya ta kamata tace dole kanwar naki shegiya wuya ta sake shekewa da dariya,Juyowa Spark yayi kenan ya hango Jamilu a window Yana ta faman Masa dariya,suna hada Ido tace ajeboooo.....ajeboota an koma yaki da jahilci sai dariya....dariya ma ta bawa Spark yace yaron nan ya takura min a rayuwa.
Ball taje ta karbo tace ba wata makaranta da zanyi wai shi irin yasan darajar ilimi to ai ba Wanda ya isa ya min dole sabo da haka ni ball zanyi,harda daga Masa ball din ya gani,tayi gaba filin wasan sai da yamma yawanci ake yin ball ita kadai a fili tana ta wasanta da ball bata iya komai ba,Spark ko gama lecture bai bari anyi ba ya fito ya taho wajen Jamilu,a hankali yake tafiya ana wani gayu ana basarwa hannu daya a aljihu anci kana nan kaya tracksuits ne a jikinsa rigar me hula a baya, bakake da ratsin fari,kafarsa sanye da Sneakers,Naila tace shegu kudi ko a Ina suke basa buya wa zai ce shi a gidan yari yake,ji yanda ma duk Yan bangaren da suke a VIP din nan sai kyau suke da kiba to zasu ci abinda suke so gashi basu fita ko Ina uhmm.
Karasowa yayi Inda Jamilu ke ball dinsa shi kadai,hannayensa duka ya zuba a aljihu yace saka muyi,Jamilu ya jefa ball suka fara Yana ta zubawa Jamilu yanka da oc ta ko Ina bai iya komai ba,sai dariya take tana so ta kwace ball din sai faman yanke Jamilu yake hannayensa ma a aljihu sai yanzu ya cire hannayen,Naila sai taro shi takeyi kar ya wuce da ball ya cinyeta, zuwa tayi tasa kafa a Jikin tasa kafar zata kwace kwallon ai sai ta Fadi tim a kasa,Jamilu ba karfi ko na anini,dariya yayi yace ka dinga sakin jiki haka wai ko yaro ne indai namiji ne ai Yana da karfi duk da Kai yaro ne,Naila sai tayi halin matan na son girma tace wlh a'a da kadan ka girmeni tab, Spark ya kalleta yace anya Jamilu anya kuwa,Mene? ta furta tana dariya, zo na taba kirjinka Jamilu,Naila ta hade rai tace idan gay kake yi ka Fadi gaskiya malam, kyale zancen yayi yace a ransa sai na taba kirjin Jamilu dole wlh, suka ci gaba da ball dinsu, Naila sai faduwa take ana zuba mata yanka, taci sa'a ta kwaci ball amma Bata yi komai ba ya kwace tace wlh ban yarda ba ya kamata a kawo rapefree,yace to a samo.
Goje ne yazo wucewa Naila tace Goje yawwa tsaya ka zama alkalin wasannan idan anyi mugunta ka busa please,Goje ba usur ba komai yace ai na Saba da fito wajen kiran karena sanda Ina gida ku fara,suka fara har su Naila suka samu Yan kallo a wajen da yawa suka tsaya suna kallon Jamilu domin shike kawo su wajen, Spark Dan girman Kai ne baya harkar kowa.
Goje ya shiga da gajeren wandonsa da singleti ya saka kwallo a tsakiya sannan yayi fito da baki yace ku fara,Spark ya cillawa Naila ball ta fara tafiya yazo ya kwace Yana rabarta ta zube a kasa ta Fadi wai ya bigeta,alkalin wasa ya busa fiiit aka mikawa Naila ball ta buga wai an bugata da kasa, ta bugo kwallo Spark yaje ya kwace ta bishi zata kwace ya dinga yanketa Yana wasan kura da Naila Jamilu a filin, ta gaji ta manta ta rungumo kugunsa ta rike shi Kam Kam tana haki, Spark kamar gunki haka yayi poster ga Goje Yana ta busa anyi rike amma basa jinsa sai faman fito yake bakinsa har ya gaji,Yana zuwa ya dagawa Naila hannu yace an baki red card, sai lokacin suka dawo hayyacinsu ta sake shi da sauri tana dariya cikin hakki tace to kana gani zai kashe ni da gudu,Red card aka baki ki fita.
Akwai Wanda suke kira da Muler ya shugo yace shi suyi da Spark yace to,suka fara ball da Spark da Muler,Muler mugun kwaro ne a ball har ya fi ma Spark iyawa,Naila tana waje tsaiwa ta gagareta ma sabo da gajiya sai zama tayi a kujerar Yan kallo tana hutawa, mazan suna ta zuwa karshe ma shiga suka yi da yawa aka raba kwallo, harda Spark ko wanne gida da Goal keeper, suna ta yi Naila tana ta kallo tana nishadinta ganin yanda Spark yake kokari a ciki,ya iya ball sosai,sai da suka kwashe kusan 2hrs sannan Spark ya fito a gajiye ya barsu suna yi wani ya shiga a madadinsa,Naila da su Scoler Yan Daudu sun taru suna ta kallo su a dole mata ne,Scoler yace Ina zan iya hada jiki da Maza su balla ni Ina zaune cikin rufin asiri,wani labaran yace Kai Jamilu ka Mori saurayi Kalli yanda yake tafiya Inama nice,Naila tace gata sunanta Spark ai Yar budurwar tayi tsaya ma kuga ta karaso, Scoler harda fifita da hannunsa yace Dan Allah ya jikin Spark din Yana sparking kuwa ahhhh ahayye ke Kam Jamilu kin caba ga farin jini ,ni dai gaskiya kinci amanta ,Jamilu ya Kalli Scoler yace ai kasan so shi tsuntsu ne tashi yake daga kan wannan ya koma kan wannan,Labaran ya furta ai ni bana bakin ciki Kun dace tunda ban sameka ba Jamilu to uban kowa ya rasa,Tantiriya ta mike tace mun tafi Shan shayi ni da Baby Spark,Spark ya jita ya daure fuska ya tsani Dandaudu a duniya,ta bi bayan Spark suka tafi,Spark shi tunda ta rungumo kugunsa abinda yake ji a jikinsa game da Jamilu ya tashi hankalinsa, Sam tunani yake sosai akan abin Nan, me yasa wai ko ya suka hada jiki sai yaji shock,tsaki ya ja yana tafiya ya juyo ya Kalli Jamilu yace a Ina ake soya kwai? Jamilu yace kawo a siyo Maka,kudi ya zaro dubu daya yace guda biyu za a soya sai tea,Ina da bread,Naila tace to ni uku za a soya min Kai biyu tea cup biyu,yace karka sake ka kawo min a bude,Jamilu yace an gama ta juya ta tafi tace banza ta Fadi,ta tafi wajen masu siyen tea Maza ne dankam suna ta Shan tea, can ta iske DanIndo tace ya man how far,Yace a dey woo da wata katuwar muryarsa,flask Dinka dayan nan zaka bani,Dan Indo ya kurbe ragowar shayinsa yace let's go, suka tafi taje ta karbo shi, sabo Dan karami da shi me kyau,Dan Indo shi Yan dabarsu da basu fada gidan yari ba suke kawo Masa duk abinda yake so,yanzu zai sa a gama da mutum Yana daga gidan yari,Kuma manya har kiransa suke Yana gidan yari Yana bawa yaransa na gida umarni ana zaluntar bayin Allah, su kashe duk Wanda suka ga dama,kullum cikin Kwangila yake iri iri da shugo da miyagun kwayoyi, Naila Allah ya dorata a kansa,Yana ji da ita,yayi yayi ta bashi dama yasa a kwato mata hakkinta taki tace sai ta fita tukun, ta karba ta sake dauraye flask din sannan ta siyo shayin ya Sha hadi sosai,aka soya musu kwai ita uku shi Kuma biyu, harda siyo wata butter ta leda ta karasa kashe kudin duka.
Tana dawowa ta shiga sai taga wannan karon ba a hanata shiga ba,samunsa tayi yayi wanka ya canja kaya,ya Kalli Jamilu yace kayi wanka,Jamilu bai San tarko ya hada Masa ba so yake ya ganshi ko ba namiji bane,sai ta shiga toilet dinsa tsaf da ita,ta saka key sannan ta tube tayi wanka,Bata zo da seletape da bandage ba bare ta mamme boobs dinta sai ta tsallake boobs din tayi,bata zubawa bandage din ruwa ba kar ya lalace ya cire tunda tayi wanka da safe,kayanta ta karkade ta mayar ta shirya sosai ta fito,Yana jira yaga ya fito daure da towel sai yaga ya fito da shirinsa yanda ya shiga sai dai ga alama yayi wankan,yace ga lotion dina ka tube kayan ka shafa mai,yace a'a zafi bana shafa mai ni da zafi, Spark yace hmmm a ransa yace zan Tara a gaba dole da sai na ganka Jamilu,a fili Kuma ya jawo flask yaga ta hado da wani Dan cup Wanda kana Sha zaka jefar, na take away ne in mutum na so ana basu idan ka siya tea.
Ya zuba tea din ya Dandana yace not bad amma a dakko Madara a Kara wannan gidan rayuwa cikinsa sai da Madara,Naila ta dakko peak da aka kawo Masa aka rasa da me za a fasa sai wajen me shayi ta koma aka fasa mata ta dawo suka sake tsulawa a shayinsu itama ta zuba Nata,ta dakko bread kamar nata me dadi ta saka kwai a tsakiya tana yaga tana kora ruwan tea,kallonta yayi shima ya fara cin nasa,tace wai mu Maza me yasa muke da Yaudara ne? Spark yace Gender dinmu ce haka,ta cika baki da kwai da bread tace uhmmm? Yace yeah,tace kune dai masu Yaudara, ai da ganinka zaka yi Yaudara ba kadan ba Spark,mata nawa ka cinyewa Bado? dariya yayi ba shiri yace da ace nasan mata ai ta Katanga zan dinga haurawa part din Mata na zama kwarto a gidan Nan,dariya tayi ta sake kurbar tea tace nufinka Kai virgin ne? original ma kuwa,Naila tace kaji tsoron Allah fa,yace da gaske ai ni da ace nasan mace to Beauty zaka bani kawai naje can, yanzu sai ka haura? Ina nan zan sa a kawo min ita ba Wanda ya sani ma.
Naila tace lallai da kuwa kaga namijin kishi,ya Yagi bread and egg Yana cin nasa a wani gayence yace egg din ma ba dadi,tace to kawo ta dauke ledar kwai tare da furta do you think i will beg you to eat? So you can't beg me to eat?ya tambaya, tace yeah,Spark yace ai naga baka da Imani ko kadan ya kwace ledar Kwansa yaci gaba da ci har suka gama ya wanke hannunsa da sabulu tare da kuskure bakinsa,Jamilu ma haka,yace sai me aikin nawa,Jamilu yace gani,yace Start to ya koma kujera ya kwanta Yana kallo Yana danna wayarsa
Naila sai da ta fita ta samo tsintsiya ta siyo harda mopper duk gasu Nan ana siyarwa,ya bata kudi again ta siyo bokiti dasu plate da spoon da duk wasu tarkace na bukata amma sai shegiyar tsada dake a gidan yari ne, tazo ta fara shara Yana binta da kallo komai irin na mace, shi kansa daurewa yake yi gaba daya bai taba ganin namiji haka ba ko mata Maza ne kuwa,Jamilu Yana ta aikinsa sai da ya gyara ko Ina neat har toilet ya wanke Kal Kal,Naila a ranta tace ko a gida bana aiki Ashe dai na iya gashi Ina bautar kato,naki yiwa uwata da ubana nazo Ina yi a banza.
Tana gamawa ta tattaro kayansa kala hudu duk ya cire ta shiga toilet taci ubansu da wanki sabo da tasan tsaftarsa da iyayi amma duk da haka ta fito zata shanya yace kawo na gani,ya duba kayan kafar wando da su aljihu ya kare musu kallo yace basu fita ba a sake,Naila ta gaji Dan ma kana nan kaya ne haka ta koma ta sake wankewa,ta fito yace Jamilu da ka Dan sake wankewa Banga sunyi haske sosai ba,Naila tace ni baiwarka ce wlh bazan sake ba ta fice ta shanya ta leko tace idan kaga dama ka saka idan baka dama ba ka barshi ta juya tayi ficewarta, Spark ya jinjina Kai yace ba komai gidan yari ce ta jawo min shi yasa yake ganin ni sa'ansa ne yaron da baifi na dauke shi ya zama cleaner dina ba,rayuwa kenan, shi Spark a dole anci Masa mutunci,yace kwana nan zan daina dariya ya daina ganin hakorina,ya dinga jinjina maganar yanda Jamilu ya wani zazzaro Masa Ido Yana Masa fitsara,ya nuna kansa yace niii...hmmmm ba komai.
Beauty tun jiya take so taji Muryar Jamilu amma shuru,duk ta damu kanta ga number waya ta bashi yaki kira,Naila kuwa Yar kwakwurar wayarta ta sa ta kira Beauty Wanda ita ta zaci wayar da tasa babanta ya bawa Jamilu ne,bayan sun gaisa tace to ya kaji wayar? Jamilu yace wani dadi idan Ina shafa Saman screen sai naji suwal suwal gaskiya wayar ta hadu na zama babban yaro,kinji yanda nake Jin muryarki kuwa clear wani so smooth,sai naji zuciyata tace aaa...aff idan muryarki ta daki dodon kunnena, Beauty harda dariyar farin ciki tace daga Jin muryarka my love nasan Kaci kaji jiya anzo Maka da kaji ko daga gida? Naila tace harda ragadada, Beauty tace sai watarana zan baka labarina, Tantiriya tace karki damu nima zan Baki nawa, to ya soyayyata? Beauty tace tana kashe Murya da yanga ta furta tana nan mana sai karuwa ma da take kullum, percentage nawa? ta kusa cikewa 100, Tantiriya tace har naji dadi kin san Ina sonki da yawa,Gashi baki taba ganina ba,Beauty tace duk a suffar da na ganka zan iya aurenka ko kuturu ne, Tantiriya tace da yatsuna ma kwantar da hankalinki,in kika ganni zaki ji dadi fa,Beauty tace muyi Whatsapp mana sai naga pics dinka,Naila Ido ta zaro tace yanzu Ina da wani uzuri ki bari zan miki magana,Beauty ta furta angama ogana my man.
Watace tazo wajen Beauty ana kiranta da chikar gayu, yarinya ce matashiya domin su Naila sun girmeta baza ta wuce 18yrs ba, ita ba fara ba Kuma baza ace baka bace amma tana da kyau matukar gaske,dumimi da ita da gudu ta shigo ta daki Beauty a gadon baya ta fice da gudu,Beauty bayan ta kashe wayarta ta mike ta biyo Chikar gayu da gudu,wata dattijuwa ce me kudin gaske wacce ita ba a block din Yan daurin rai da rai take ba,shekaru biyar aka yanke mata saura baifi wata biyu ba wa'adinta ya cika ta bar gidan gaba daya,Itama a VIP take me kudin gaske ce ita Chikar gayu ce Yar aikinta ta zama kamar yarta,Bata Jin magana tsokana ce da ita tun Yan gidan suna dukanta har sun daina ma.
Dattijuwar me suna Hajiya Kaltume itace ta rike Beauty tace dan Allah kyale min yarinya bakya ganin ita yarinya ce kin bata shekaru biyu haba Beauty tamu,Beauty tace wlh Dan Ina ganin girmanki ne Hajiya ba komai na kyaleta,tace na gode Queen of Beauties,Beauty taji dadi tace Allah Hajiya na Kai queen? tace ae mana,Zan iya birge mijina? Hajiya tace sosai ma ai bazai iya Kara miki kishiya ba,tace sunansa Jamilu,Hajiya tace Nice name,Ina sonsa Yana Sona,jiya ma da ban ji muryarsa ba sai da nayi kuka,Hajiya ta zaro ido tace kibi soyayya a hankali Yar Nan,Beauty tace ni wlh bazan bita a hankali ba akan Jamilu sai dai a mutu,Hajiya