Showing 87001 words to 90000 words out of 158722 words
Chapter 30 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
aka rangada mata wai bai gane ba,tana kallo Wahida tana bashi a baki Yana Sha,Mummy sallama tayi Masa ta tafi,Naila idonta ya ciko ta mike da sauri ta shiga kitchen,tana shiga sai kuka,tun tana yi a hankali sai ta fashe da kuka har wani shidewa take, tana Jikin Sink ta Dade tana kuka taji shigowar mutum da sauri ta fara kokarin goge hawayenta,Muryar Spark taji yace me kike yi ne,Muryarta tana rawa alamar kuka take tace plate nake wankewa,are you crying? Da sauri ta juyo fuskarta sharkaf da hawaye,kuka ne yaci karfinta ta fice da gudu daga kitchen din ta fada dakinta,kamar me ciwon ciki haka ta rike ciki tare da dafe bango ta durkusa tana tsafiya a haka da ruku'u tana rusa uban kuka ta fada Saman bed tana ta kuka,Wahida ita tuni ma ta tafi tana murna ganin Naila tana kuka.
Spark ne ya bude kofar da sauri ya sameta a zaune tana sharbar kuka,yace menene kike kuka haka? Me aka miki,Wahida tace....cikin masifa Naila ta dago tana kallon Spark tace haka ka iya Wahida kaza, Wahida komai Wahida can't you see I'm in love with you? Spark tsayawa yayi yace oh dama ba aikin ne ya kawoki ba sone kenan,wallahi ina sonka ba zuwa nayi na cutar dakai ba,Jamilunka ce Naila ce nasan ka ganeni yau ta mike tsaye tare da matsawa jikinsa sosai,saura kadan ya rungumeta Dan ya danne zuciyarsa ne,yace to me yasa kika boye min baza ki zo min a Jamilunki ba,zaki rufeni kina boye min abubuwa ta ya zan yarda dake shi yasa kawai na zabi wata Kuma yanzu kin San dai anyi sa rana ma tuni sabo da a shirye nake ma gobe friday za a daura aure wallahi kinji na rantse ba wasa nake ba aure za'a daura min gobe inshaallah.
Tana tsaye tayi mutuwar tsaye ya fice ya Bata waje,ranar Naila kuka ta yini yi ta kawana Bata iya ko lekowa ba,Kuma tace wlh bazan bar gidan ba na gani yanda za ayi dani.
Washe gari Naila tana ganin kamar wasa sai Taji abokai ana ta dariya ana tsokanar Spark sai murna yake ta leko ta kofa Taga ya fito Yana zuba kamshi da wata uwar shadda me tsada da babbar riga farare ba kamarin kyau yayi ba,a bokansa Suna cewa kayi sauri fa time ya kusa,Spark ya fito Yana washe baki suka fice,sai wurin 4pm sai gashi sun shugo da su Kamal,Naila tana kwance a kan gado tana ta faman kallon pics din spark da bai San ta dauka bama,tana hawaye tana kuka,Spark harda cewa yau sai nayiwa kaina guda wlh,abokai sai dariya suke,Yana cewa aure yazo na kira shi ya amsa,Kamal yace muje reception din,suka Kuma ficewa da su Rafeeq,Mummy tana gidan Mima ana ta shagali tace wai ni naji kamar ana cewa Kano akaje dauro aure su da zasu je gidan Maman Wahida wai ya haka ne,Mima tace to Dan iskan yaro komai har lefe Dana hada Masa kwashe abinsa yayi wai da kansa zai Kai Kuma ni naji Maman Rafeeq tace itace ta Kai lefe,ni na rasa gane wannan kan aure amma koma mene wlh da sanin Papan su Spark tunda ai danginsa ne suka Kai kudi da komai,ni gaskiya auren Nan akwai wata a kasa Spark munafuntar mu yayi komai ya hana mu muyi daga Ubansu sai Yan uwansa sai Kuma abokai ni wannan wanne irin yaro ne,Mummy tace ni nayi mamaki ya hanani na tsoma bakina a harkar aurensa wani bikin arziki ne wai ace sati daya jal har an saka rana an daura aure.
Wahida ce ta shugo palon da gudu tana rusa kuka wlh ba Dani aka daura ba,Daddy yace da wata aka daura a Kano shima labari yaji,an zalunceni anci amanata an yaudareni,Mummy tace ya tabbata, ta kira Spark a waya tace Kai kana Ina Dan uwarka?
Yace Ina airport ni da amaryata mun wuce Honey moon,Wayar Mummy ta katse tace zai iya aikatawa bata San Spark Yana gari ba,tace ai Banga amfanin biki ba, uban kowa ya watse ku tashi jama'a kowa ta tafi dakin mijinta tayi bautar Allah ango ya tafi turai da amarya kowa ta hada shirginta biki ya kare.
Amma wannan ango anyi marar kunya cewar Maman Misam tace ah biki ya kare Kam,Mima tace a fadawa masu girki su sauke tukunya.
Mummy sai bi take part part tana cewa biki ya kare kowa ta mike ta tafi gidan mijinta a tashi a tafi, Mutanen kauyensu suka ce to Dan kawai ango ya tafi sai a fasa biki haka akeyi,to abinci kuke so kuci ance an fasa kuje ku dafa a gidajenku babu me ciyar daku yau.
Spark sai dare ya shugo gidan wanka yayi sannan ya shirya cikin kayan baccinsa riga da wando sky ya fito yayi kyau,dakin Naila ya bude ya sameta tana ta faman hada kayanta a akwati tana kuka zata bar gidan gobe da sassafe, hannayensa a aljihu yace Ina zaki je Jamilu? ban sani ba tana hawaye,dariya yayi yace haba kawata,tafiya zakiyi ki barni baza ki tsaya Kiga first night ba? Naila banza ta Masa,rungumeta yayi ta baya,ta fara fisge fisge tace ka sakeni zan zageka wallahi,sau nawa Kuma kika zageni ni,haba my wife,I'm sorry ya furta Yana kokarin cire mata riga,mamaki ya Bata,ta kwace kanta da kyar, tana huci yace wlh yau sai na taba Boobs, tsaki ta ja ya turata Saman bed ta fada Kai ya bita,tsalle ta buga ta dire a kasa,tace wanne irin rashin Imani ne wannan kayi aure kazo zaka keta min mutunci,Spark yace wlh gwara ma ki tsaya yaje ya sawa kofar key,Naila ta fashe da kuka tace wlh bazan yafe Maka ba,Spark wayarsa ya zaro tare da kiran Mohsin yace Yaya Mohsin gata tana ta kuka kayi mata magana,Wayar ya mika mata Naila ta karba tace Hello Yaya,yace Na'am yace Naila kinci amanata Ashe dama a gidan namiji kika je kika tare,yanzu idan ba mutumin kirki bane da tuni ya lalata miki rayuwa,wannan takaicin wlh yasa da yazo ya fada mana komai da rayuwarku a gidan yari Umma ta fusata tace lallai indai Yana so a daura aure Kawai,mu Kuma yau aka daura miki aure da shi sai ki zauna da hujja tunda haka kika zaba,Kuma karki Kuma kirana daga yau,Umma ma karki nemeta kije mun fita hakkinki mun daura muku aure,Naila ita Sam Bata ma ta fushin da suke yi da ita,kawai mamaki da murna ne suka kamata amma a zuciyarta,tace zanzo Yaya dole ka hakura wlh,Wayarsa ya kwace ya kashe,Naila tace gidan zanje ka bude min kofa,Spark yace ai kinzo kenan tunda kika kawo kanki,fuska ta bata sosai tare da furta ka bude min kofa nifa ba Yar iska bace,Spark a nutse yace ni kuwa shine Dan iska ne ni.
Shuru tayi Masa ta tsaya a Jikin kofar,Amarya jimiluna zo ki kwanta ba abinda zan miki am serious gobe har gida zan kaiki ma,Naila tace ban yarda ba kawai ka cuceni bazan zo ba,wai baki yarda dani ba bana son taurin Kai wlh zan fasa kaiki gidan na kulle ki a daki kin san halina,Baki ta turo gaba tare da makale kafada tace kaje wajen abar kaunarka ku kwanta ,tashi yayi ya bude mata kofar yace jeki Madam gobe idan kika ganni da Wahida karki damu mutane da kuka,tsoro Naila taji,ya fice daga room din ya haura sama,Naila tunawa tayi da wahalida ta fito ta bishi da sauri tana cewa gani mene ne?nifa Malam ka dameni ta furta tana shiga bedroom din,kallonta ya shiga yi sanye cikin Kayan bacci wando dogo da Yar riga me gajeren hannu pink da adon cartoon a jiki,yace me kike haka kamar yarinya Naila ta karasa Jikin bed din ta zauna a gefen tace Gani,Yar tsuka yaja tare da furta idan zaka kwanta ki kwanta ya furta fuskarsa ba wasa, haka Naila ta samu ta Dan kwanta badan ranta ya so ba ta kwanta a gefe,murmushi ya saki me kayatarwa a ransa ya furta haba ai gashi nayi maganinta na huta da raini,light ya kunna ya karo hasken yakwanta a gaf da jikinta, tana jknsa tsoro ya cika mata zuciya,a hankali ya Dora hannunsa a hips dinta,Naila Bata yi motsi ba tayi mutuwar tsaye sabo da tsoro cike da nutsuwa ya dinga matso da hannun zuwa cikinta a hankali ya jawota tare da manta jikinsa.
Naila ji tayi Hallare a mike abinka da so baya iya barin mutun ya dauki wani mataki,gaba daya haushin Spark take ji idan ta tuna Wahida,magana ya mata a kunne yaji bakin na Naila ya mutu, shuru,yace kece Jamilu? Naila tace ban sani ba,dariya yayi ta da maida hannunsa Saman cikinta Yana shafawa a hankali Yana wasa da kyakyawar cibiyarta,jikinsa ne ya dauki rawa sosai itama Naila haka,hannayensa y sake sawa a hankali ya janye rigar Naila sama wacce ba bra ba komai,rigarta take kokarin gyarawa amma ya hana Hakan,kokawa suka fara sosai yace wait wait,Naila ta juyo da kyar a jikinsa suna facin juna tace please Stop,bana so Allah,yace oh wai karfi kike gwada min,jikinsa ya fisgota ta fado yasa hannaye tare da rungumeta a jikinsa,wani kamshinsa me sata nutsuwa, Dan Allah ka bari, wai kin daina so na nane? Oh ka ganeni? Murmushi ya saki Yana shafa gashinta ya furta tun ranar Dana fara ganinki gidan Mummy nasan Jamiluna nane,amma shine kaje kake son wata? Da kika zo gidana kince min kece ? Sannan why zaki boye min kanki? Kin sanni na sanki a zaman da muka yi ya dace ki min haka? Me yasa ko mene da kika San nine baza ki fada min ba,baki yarda dani ba,kin san zuwana gidanku nawa? Kin san ta ya ma aka yarda na aureki,dama na fada miki ni ta dole ma sai na aureki idan nayi niyya sai idan Allah baiyi ba,karki sake min irin wannan shirmen naku na mata da yarinta da gajeren tunani,kinzo kina wani boye min fuska Kuma sai baza min duwawu kike a gida badan Allah yasa ni ya Sheikh bane da tuni me kike tunani? Ina sonki kin sani zan iya hakuri Dake ne? da na sani ma da kika zo tuni nayi sex dake Kinga gobe sai ki sake zuwa gidana,kuka Naila ta saki tace wlh sai na tafi gidanmu,dama ai gobe zamu tafi,bukatar maje Hajji Sallah yarinya tunda na aureki saura Wahida,idan na zauna Allah ya tsine min bazan zauna da kai ba,ta karfi ya riketa yanda baza ta iya kwacewa ba,rigarta ya cire mata gaba daya,ta gaji da kokawar ta hakura kawai.
Samanta ya koma tana kasa,hannayensa biyu yasa a hankali cikin salon da zai hanata sukuni ya fara kissing wuyanta Yana shakar kamshin Naila me Sanyi,mukus kake ji Naila ta kasa kukan da take ta daina,idonta ta lumshe,Naila a ranta tace karka daina Kaci gaba,a hankali ya gangaro fuskarsa Yana kare mata kallo gashi ya kunna light,cikin salo ya hade bakinsu waje daya,Naila tana zukewa amma ta gaza hakuri tace haba Tantiriya kibi yarima Kisha kida kawai ke da kike ma Tantiriya shi da bai amsa sunan bama ya fiki kwarewa,Naila ta fara Maida Masa martani kamar ta Saba,sai sake makalkale Spark take,muryarsa na rawa yace da dadi? Naila tace babu dadi Sam,baka da dadi ,murmushi ya saki,tace auren miji Dan duniya ai ai sai addua ci gaba ya zanyi,dariya yayi kawai ya matsa gefe yana cewa a'a a barshi,tace to haka nake so,wlh baki isa ba ya dawo tare da dorawa daga Inda ya tsaya,gangarowa yayi a hankali har zuwa kirjinta,ganin manyan Boobs dinta jajir ya sake rudewa,a nutse yake binta duk kuwa da rudewar da yayi,Naila tace duniya sabuwa a ranta.
Ganin zai wuce gona da iri Naila ta kwaci kanta da kyar,gaskiya ni na gaji ba Wahida kake so ba, Spark yace akwai lokaci yarinya,baccin karya tayi,shi hakan ma ya wadar da shi indai zasu kwana bed daya,a haka bacci ya kwashe Naila, shima daga baya rungumeta yayi a jikinsa sai bacci.
Washe gari ya rigata tashi,Beb...Beb ya shiga tashi a hankali ta bude idonta suna hada Ido yace tashi kiyi sallah zanje masallaci cikin Mayen bacci ta bude bargon ta fito ta manta ba kaya a jikinta ga haske,Spark ne ya kalleta wani farin ciki ya kamashi lallai shikam yayi dace wannan kirji a cike haka,ba zato taji kiss a goshinta tare da furta I love you,Naila tace uhm ka ga dai nonuwa ai dole kace, matsa ta tureshi daga jikinta tare da rufe jikinta da bargo,dariya yayi tare da ficewa sanye cikin jallabiya,Sai da ya tafi Naila ta mike a haka daga ita sai pant a haka ta shiga toilet da addua tace Kuma duk Dan iskan Aljanin da ya kalleni ban yafe ba,tana wanka tana tunanin wai da gaske auren aka mata,irin son kudin Umma ta tuna tace nasan Umma da son kudi wlh tsab zata Yarda,Shi dama Abba nasan ba abinda zai ce
Tana fitowa bayan tayi brush da alwala Sallah tayi sannan da asubar ta dinga zabgawa Chikar gayu waya,Chikar gayu da kyar ta daga cikin bacci,lfy Naila? Dalla ki tashi Ina can Ina ta soyayya Baku sani ba,Chikar gayu tace Abi dai a hankali kar ya cuceki,Naila tace kina Ina wai? Ina gidan Mummy taki,ta zama kawata na tare acan,na je mata a matar me kudi makwafciya,Naila tace me gaskiya wannan Mummy din tasono ce wlh Kuma ta yarda? Sosai ma ai dakikiya ce ke na yarda kanta da motsi tsab zata iya kashe mijinta bata ganewa,karar tafiya Naila taji tace sai anjima zan kiraki ya zanyi tun jiya yake latseni,Chikar gayu tace zai cuceki,Bata San Naila aure ne da ita ba,Naila bata fada ba tace na zama yar duniya ni yanzu na muku nisa ba abinda ban sani ba,jiya ba irin gaisuwar da bamuyi ba ni da Hallare,mun gaisa mun Kuma gaisawa nace Hallare ban sanki ba tace kwana Nan zaki sanni nima zan sanki,Chikar gayu watsakewa tayi tana dariya tace,Naila ki kiyayi Hallare Kinga hmmm,Naila tace,Naila volume ta rage na Muryarta tace jiya tana gefena abata Yar sumulmul,Chikar gayu tace ke kika Santa ni ba ruwana Ina Nan gidan Mummy sabo da tsabar tabara fanta ma da Madara nake hata na Sha banza ta Fadi,Naila tace to ya zata tona asirin kanta? Chikar gayu tace saura kadan zaki Sha labari,Chikar gayu tace karki sake yaci lallai ya so Wahida ya daga miki hankali wlh ki rama,Naila tace bazan iya ba zuciyata ta mutu yanzu tun daren jiya ba batun ramuwa bani da sa'a a kan Spark gaskiya,ke ni na gaji da walagigi soyayya ta gama kassara min rayuwa,gwara kullum Ina gefen Hallareta
Spark ne ya nufo bedroom tana Jin tafiyarsa ta kashe wayar ta fada Saman bed tayi baccin karya.
Mohsin yau ma an Sha sabuwar shadda ana wajen Beauty zance Beauty ta kira Mohsin 2+2,Mohsin yace mene 2+2? Naila tace sai nazo gidanka zan nuna Maka 2+2,a ranta tace boobs 4 rigis amsar kenan ,a fili Kuma tace sai nazo yace Allah ya kaimu.
Yaushe zaki je wajen Umma? tace jibi inshaallah zanje nayi barka yace to Allah ya kaimu suna ta hira,bayan kwana uku da Kai kudin auren Beauty,yau ta shirya zata je gaida Umma tayi mata barka,Umma anji Yar me kudi da sauri ta tasa keyar Hashimu Dolo tace muna da bakuwa yau mu shiga kitchen,yace yau Me za ayi mata ne? kin san wannan ba irin Yar gidan Dankoli bace Hanan marar kunya marar mutunci,Umma tace ai dole wannan sai da nama babbar bakuwa,Abba yace ya ilahi bamuga ta zama ba ya figo bowl ya fara gyara kayan Miya,Umma Kuma tana girkin ko kunyar yaransu basa yi domin su yaran ma idan da sabo sun saba,tare da Abba suka gama girkin Nan tas,ba uwar da Abba bai iya ba na aikin gida,shine yayiwa Jaririya wanka ya sa mata pampers da kaya ya shiryata tsaf harda wani sa mata hula ta yara me adon ribbon a jiki,Umma wanka tayi ya Bata Basma shima yaje yayi wanka ya canja yadinsa fari me kyau harda sa hula suruka zata zo,su Hidaya suna dawowa Abba yace ayi Maza ayi wanka a shirya yau big Aunty zata zo,suna Murna dukkansu suka yi wanka kowa yaci kwalliya da kaya me kyau suka sake gyara gidan Yana ta kamshin turaren wuta.
5pm sai kuwa Beauty tayi parking da motarta wata fara ciki Kuma komai pink,ta Sha farar shadda me tsada wani kamshi kawai take yi,harda Dora mayafi a kanta ta rufe Rabin fuska wai kunya,ta shugo tayi sallama,Zarah tace ga Aunty tazo,Beauty ana murmushi ana kasa kasa da Kai ta rike hannun Zarah suka shiga cikin palon tare.
Tayi sallama Abba harda yiwa Umma rada kinji kamshi Yar Inna,Umma ta fuske tana cewa sannu da zuwa, Beauty irin ta kirki me hankali ta zube a kasa tare da gaida su Umma suna amsawa,Su Hidaya suka gaisheta sannan Umma tace zauna mana a kujera sannu da zuwa.
Beauty ta zauna tare da sanda Kai kasa magana ma kadan kadan takeyi,Hidaya tana ta janta da Hira amma wai kunya ta hanata sakewa,Abba ficewa yayi gudun kar ya Fadi wata magana suruka ta ganshi wani Dolo,ya fito da sauri yace bari na gudu daga gidan kar bakina ya jawo min Suruka ma tasan na cancanci sunana Hashimu Dolo,yace Hashimu yi ta kanka bar layin gaba daya,ai kuwa Abba sai ya bar ma layin gaba daya ya fece.
Sai gab da magriba Beauty ta mikawa Umma kayan jaririya masu tsada harda atamfa da Leshi masu tsada tace Umma zan tafi,Umma tace abincin ma kadan kika ci fa,Beauty tace Umma naci fa da yawa tana murmushi ta fito Hidaya da Zarah suka rakota har Aslam,ta basu dubu biyar tace gashi ku siya sweet,sai godiya suke suka amshe,Beauty tana tafiya Abba ya bugo waya yace