Showing 102001 words to 105000 words out of 158722 words

Chapter 35 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

379

so kawaye su Kai ta,Mohsin yace iskanci ne kawai ya fice.
Dakin Naila ta bude ba komai ciki sai katifa ta Sha gyara da bedsheet, Spark yace Alhmdllh sa key,Naila tace ban gane ba.
Key din ya kalla yace bani key din idan wani ya shugo fa.

Wai me zaka yi? hanashi key tayi ta fice daga dakin tare da Maida key din wajen Umma ta saka bra ta saka riga me dogon hannu sannan ta zuro hijab ta dawo dauke da ruwa da lemo a tire,wai security kika saka kenan? Naila tace ba dole ba ka bari mana a kawoni ko mene sai kayi,shike nan ba abinda zan taba? Naila tace ae,zaki zo ne ai zan fanshe,komawa tayi ta kawo Masa sandwich da Samosa duk ita tayi abarta Kuma sabo da shi tayi,Naila an dage da koyon girki sabo da a birge miji,ganin tana so yaci, sai ce Masa take yi Kaci kaji,yace bazan ci komai ba sai kin koma kin cire rigar Nan da kika saka,kina yi zan ci,Naila ana so aci girkinta,tace yaushe zan koma cire riga a cikin mutane,cire a Nan yanda kika saka ki cire, sai na ci abincin, ta cikin hijab ta cire ta zauna da vest dinta ko bra din ya ce ta cire.
Yace hijab fa a'a cire,Sai dai idan baza Kaci ba ta furta,fisgo hannunta yayi ta fado Saman katifa.

Tsaya nifa ba abinda zan miki hugging naki kawai zanyi,rungumeta yayi a jikinsa,tasa hannaye tayi hugging nasa back,Naila da anji Jikin Spark sai jikinta ya mutu murus,abinka da shakuwa an Shaku,kasa katabus tayi sai ma sake kankame shi da yi,a hankali ya dago fuskarta tare da tallafar fuskarta ya fara aika mata da kiss,Naila Idanuwa ta lumshe tsayawa yayi Yana karewa fuskarta kallo Yana dariya kasa kasa yace bude idon to,suna a rufe tace baza su budu ba yanzu, ci gaba yayi da tsotse bakinta,tun tana Dan sharewa har ta kasa ta fara Maida Masa martani , tana juya bakinta cikin nasa kamar zasu cinye juna,Spark yace kaga Yar gari,kin gama wayewa,Naila taji kanta ya Kara girma an yabeta har da sake bada himma zata nuna wayewar,Batasan Wato yake mata ba.

Juyata yayi tare da zaunar da ita tsakanin kafafunsa bayanta Yana Saman kirjinta,A hankali yana shafa wuyanta har ya gangara tare da sa hannunsa ta cikin vest Abu ko bra,Naila zama ta gyara tana Jin dadi,harda ajiyar zuciyar bata sake magana ba sai dai tayi ta faman Sosa idonta, tana tsoro kar tayi Nishi sauti ya fita, yace bata da kunya,yace Ko ba Tantiriya bace ne? Naji tayi mukus,Ido ta Sosa tace itace mana,ya naji kinyi shuru ke da zanji kalamai na tashi,Naila tace nayi hankali tare da dawo da hannayenta ta bayansa ta rike shi Kam,Spark yace au baza kice komai? Haka kawai nayi ihu ka dinga min dariya daga baya, na daure abina,kiyi abinki ni ba abinda zan miki Kinga a musulunci ba a so duk abinda kayiwa matarka idan tayi ihu ta nuna taji dadi daga baya ka dawo kana mata dariya ko kana tsokanarta to zata dinga Jin kunya ta daina shi yasa akace ba kyau,nima Kuma idan nayi ihuna kika min dariya daga baya ba kyau,Naila tace ni dai wlh sai na Maka dariya sai na tsokaneka,dariya suka yi.

Sandwich din ta dakko ta fara ci sai ta yi wayo wai tana cewa sandwich dadi,a ranta tace karya nake Kaine me dadin bari na fake da dadin sandwich nake ji,Ido ta lumshe tana taunawa tace dadi kashe ni wlh dadi,Spark ya ganeta shi dai yace ko dai nine Sandwich din? Naila dariya tayi tace na rasa me yasa motsi nayi sai ka gane,Spark shi Kam boobs yake aikin sarrafawa sai mutsu mutsu Naila take yi.
Ta bayanta ta miko Masa Samosa, kansa ya duko da shi saitin hannunta Yana gutsira,Naila tace Kwalbewa duniya ce,kwanciya yayi ya dawo da ita samansa,Naila ta Kalli Hallare harda dagawa Spark riga ta ganta kuwa a wando duk tana fitar da ni'ima,Naila ta rufe da sauri tace Allah ya baki hakuri,Bai San ma ta daga masa rigar ba,yace me? tace to Hallare ce take dalalar da yawu fa,ke fa? tace bado wai? Tace ae me yake ciki? tace aradu Hawaye ne yake ta zubowa,Spark dariya yayi yace Bado na hawaye,ya dauki lokaci Yana murzata sai da taga duk ya fara fita hayyacinsa ta kwaci kanta da kyar tace a bari sai an kawo Amarya please,yace ni da nazo yau daga dinner sai hotel zamu kwana, Naila tace Bada ni ba wlh haka kawai aje na samu ribar Hotel,ni kwana nan gaba daya ban yarda da Kai ba,da a baya wani Dan Salihi da Kai yanzu Ina abin naka kullum shahara yake.

Snacks dinsa ya zauna Yana ci yace ah yanzu an fara iya abubuwa,ai dagewa nayi naga za a barni a baya kullum girki nake koya,yace good girl ga Indomie da bishiyar salat ai kina kokari,kwana nan zaka yi tumbi,sun dade suna hira kafin yace zan wuce hotel naje nayi baccina kafin lokacin dinner,tace to shike nan abincin fa? Kadan Kaci,kafin na fito naci a gidane ai naci snacks dinki da yawa abincin ne ban ci da yawa ba,mikewa yayi yace yau hannuna albarkar da take jikinsa tayi yawa,dariya tayi yace you are so sweet,komai naki me kyau Allah ya miki baiwa,Naila tace Alhmdllh bari na kira kawayena na kauye ku gaisa,yace alright ya koma tare da kwanciya a katifar.

Fita Naila tayi bayan ta Maida hijab dinta tace Rayya tunda an gama lalle Kun wanke ku zo zaku gaisa,Rayya tace wayyo ni Allah kunya,Dan birni haka,Dije ita gwana tace ku fa baku waye ba aradu ku taho mana,suka tashi a kunyace suka shiga dakin,Spark Yana kwance abinsa Saman katifa suka durkusa har kasa tare da gaida shi Ina yini,yace lfy Yana fara'a a fuskarsa, Yana dariya a ransa kuma irin daurin da suka coka goshi kwal,ya musu irin gaisuwar su,yace ya gida? Suka ce lafiya Lau mun sameku lafiya? Spark yace lafiya Lau..lafiya Lau,ya manyan? Sukace lafiya kalau kalau wallahi,ya sake cewa ya shanu ya masu gidan naku? Rayya tace nidai Dan marakina Daya bashi da lafiya ciwon hanta ta kamashi,Spark yace to a yanka shi mana a Sha dadi, suka ce kaiiiiii hodi jam suna dariya Rayya tace ai Affana sai ya kusa kasheni,sanuwar fa wacce ta haifi Dan marakin gadonta nayi wajen kakana,Spark Yana jinsu,Dije tace nidai tsakani da Allah mijina ya sake ni dukkan mu auren mu ya mutu,gwara ma Nafee ita ta samu ciki ya zube mu kuwa shuru,Spark ya kallesu wannan tsigi tsigin yaran ma me za a tsinta a jikinsu,Jidda tace mudai Allah ya kiyaye mu musamman ni Iro Allah Bai bashi sa'ar iskanci Dani ba da tuni na boni la lalashe ,Spark Yana ta dariya a ransa yace a ransa Iro anyi dakiki marar rabo,Rayya tace kaga ni dai Ina son Sagiru na wlh amma iskancin Sagiru bazan iya ba nace ni da Sagiru kaadii fau fau aradu,Spark yace uhm Sagiru ya cuci kansa, Rayya tace Tantiriya ta dawo birni kowa a riga Yana ta kewarta.

Spark yace na manta ban tayaku jimami ba ya akaji da rashin Tantiriya? Suka ce ohh Tantiriya ta barmu sai hakuri muke ta yi Allah yasa hannun na gari ta fada? Spark yace na gari ne mana tunda gashi ta hadu da Tantirinta,dariya suka yi suna Jin kunya suna rufe Baki suka ce to mun tafi,yace na gode ya mika musu kudi suka ki karba sai Naila ce ta karbar musu.

Suna fita suka dinga labari wlh kirki ne da shi Ashe suna ta bawa Umma labari ai har Hira suka yi dama Yana da magana,har wasa ya dinga yi mana wlh akwai kirki, a farko mun zaci bashi da mutunci mun ga Yana gadara da takama Ashe shima Tantiri ne a nutse yake magana baza kice shi ya fada ba,Spark fitowa yayi zai tafi Naila tazo zata raka shi ya Dan matsa nesa da ita kadan yace kar ace bani da kunya a gidan surukai,suna zuwa kofar gida yace koma gida,karki min make up lokacin dinner kuma na tsani wannan kwalliyar da mata keyi,duk kyanta Bata birgeni Sam,kiyi da kanki kawai ni bana son make up duk ta canjawa mutum kamanni,Naila tace to na huta nima.

Ana ta Shirin Dinner da yamma Chikar gayu itace babbar kawar Beauty an dauki wanka kamar me,Amarya kuwa tana wajen make Up tare da wasu kawayen ta Sha farin bride material me tsadar gaske an mata wata gown me kyan gaske ta zaratan amare,an nada mata dauri da silver gogoro, takalmi Silver jaka ma haka,make up din tayi kyau an dora mata mayafin amare a Kanta sharashara sai walwali take ta ko Ina,Ango Yasa Shadda Yar ubansu Silver kalar takalmi da jakarta da gogoro.

Su Chika duk anci ankon Leshi me kyan gaske Blue and white,kawaye an Sha wanka sunyi gayya kamar me, Yan mata tamfatsa tamfatsa sunzo duk kawayensu ne yawanci daga gidan yari suka fito,Kamal ne zaizo shima sabo da abokinsa Spark ai kuwa Rafeeq yace akwai dinner? akace ae yace ko banza na Kalli mata mu tafi Kamaluddeen,Kamal yace Allah ya shiryeka Kai ba Dan iska ba sai son kallon mata? Rafeeq yace ko banza ai na kashe kwarkwatar idona muje,Da yamma suka dira,Rafeeq lokaci nayi yafi uban kowa saurin shiryawa yace Kano sai da shadda ya fito cikin shadda me kyau wata ita ba milk ba ita Kuma ba ruwan kasa ba,suna dakin Spark shi da Kamal,Kamal yace gaskiya kayi kyau Rafeeq Allah kawo babban rabo,yayi shuru kamar Salihi,Mayen mata Misam ne Allah yayi ya kira wayar Rafeeq,kana Ina? Rafeeq yace dinner Yan mata ne iya kallonka,Misam yace amma baku da mutunci shine ko ku fada min ni shugaban mata guda,Ba komai ai gobe ma matan zasu taru ko? Rafeeq yace ai ance akwai walima mata da Maza za ayi wa'azin zama da iyali lafiya,Misam yace tab zanzo naji Ina jin wa'azi Ina zabar nawa ya nawa.

Ana ta tafiya wurin dinner dangin ango dana Amarya,Abba ya shugo gidan Yana tarkata kan Yan mata danginsu ku fita ku tafi aje ayi rayuwa Allah ya sanya Alkhairi,Wata babbar mace me suna Tani tace zanje nima nayi kallo, Abba yace Tani gidan uban wa zaki? ki batawa yara show sunyi gayu aga irinki kamar wata Tsohuwar mota hayis ba Inda zaki ai zubar da girma ne,Kubra ta cakare taci wani material an mata make up,kyan da tayi ya Isa,Dake Kubra ce sai Abba yace Yar Inna an fito? Ko ranar bikinmu baki kyau haka ba,idan an girma asan an girma,Kuma wallahi sai kika yi kyau kamar kiyi ta zama a haka,ai da bazan sake fita wajen sana'a ba gwara kullum na dinga kallonki.

Umma tace wai baza kaje bane? Abba yace a'a haka kawai naje na zubarwa da yarana mutunci wlh tsab naji kida zan taka, Kinga ai girma ya Fadi kuje ku dai kawo Basma nayi miki rainonta,tace madararta tana dakina Jikin bed,yace to ya karbi Basma Umma ta fita ta tafi tare dasu Hajiya Tagwadas ansha gayu.

Naila ta Sha anko itama ta cakare ta zuba kyau kamar a saceta kawai Spark take jira,ba a dade ba yazo a mota ana tuka shi ya hakimce a baya sai kace shine angon,shadda sky ya saka shigen color din ankon da Naila ta saka,baya ta bude ta shiga gefensa,Yana ta kallonta yace kinyi kyau sosai,Amarya da ango sun karasa wajen Event suna waje ana ta musu ruwan pics sannan aka Bada sanarwa Amarya da Ango zasu shugo,salon kida aka canja.
Amarya da Ango ana rakosu ana wata musu buzzer suka shiga tar da zauna,Rafeeq tuni suna ciki shi da Kamal,Spark ne ya karaso tare da Naila rike da hannunta suka nemi wuri tare da zama,ko wanne table da abinci da kayan Sha gasu Nan.
Babbar Kawa aka Kira Suhailat Chikar gayu,Chikar gayu ta fito wannan fili ana nemanta,tun daga Jin sunan kowa ya baza Ido yaga wace Chikar gayu,Chikar gayu mikewa tayi akayi harrrrr ana kallonta,ta isa gaban Mc ta karbi Speaker tace Alhmdllh sabo da farin ciki a bani kidan Chika,aka saki sauti Chika tayi rawa iya rawa kamar me ita kadai kwal ta iya chashewa,Naila ce taje da Dan takunta kadan tana mata liki,Su Hanan ne suka shugo da kawayenta suna cin magani.

Naila ce ta radawa Chika maganganu sannan Chika tace a tsaya da kida zata Dan Bada tarihin Amarya a takaice,Sai dariya Chika take bawa mutane domin rawar tata ma ta iya shege ce,Speaker ta karba tace na tabbata kowa yana Jin Hausa a Nan sabo da haka ba ruwan mu da turanci America ma uwata,aka yi dariya.

Tarihin Amarya ta bayar a takaice a nutse Kuma, aka tafa mata,sannan tace Alhmdllh Alhmdllh nasan Amarya baki gaji siyar da dankunne da tozalin tsofaffi ba,Baki gaji siyar da mazari da Alli ba wannan sai Dan koli,Naila tace gaskiya ne wannan, sannan uwarta Bata kulla omo dan awo cewar Naila,bata da kanne ma bare ayi mata fitsarin kwance a mayafi ko Ango ya taba Jin zarnin a Jikin Amarya sanda Yana zuwa zance? Idan ya taba ji ya fada,Naila tace sai dai kamshi wlh,yeeeeee yan mata suka saki shewa.

Hanan ranta ya baci ita da kawayenta masu zugata,tun a wajen ta fara kwalla,tace ba Wanda yasan sirrina sai Naila,wallahi wallahi sai sun San sun min habaici,sai na lakadawa Amarya duka bari a kawota a ranar a gaban mijin nata shege munafuki ai shine ya Fadi sirrina.

Naila tace sabuwar Miya sabon tuwo,me za ayi da tsohon tuwo sai dai almajiri wlh ko a jefa a bola,Chikar gayu tace Kainuwa dashen Allah Amarya Beauty an gaji arziki gaba da baya, fara me farar aniya babu Mai ba sabulu natural daga Allah ce,hakora reras ango ka dace,Naila tace da gani ba yunwa a jikinta Kai da Ganinta kasan ta Sha Madara ta koshi tayi brush da Naman kaza,yayana yayi dace,yanzu nasan yayana ya auri mace, na tabbata ango kayi dace domin ka samu mace ta gari wacce zaka samu nutsuwa a cikin gidanka,wacce zata kula da Kai da danginka da duk wani Wanda ya shafeka.

Duk kawayen su Chikar yawanci daga gidan yari suka fito babu na gari sai dai dai kowa shegiyar kanta ce shi yasa basa Jin kunya ana fada zasu saki shewa,Chika tace jama'a a gurguje bamu iya tashin hankali ba duk da cewa Kawata Nawwara wato Beauty tana da abokiyar zama

Sabo da haka zan danyi nasiha ga Amarya,Beauty idan kika shiga ciki kika tashi hankalin ango to kinci amanata ni babbar Kawa,ko da abokiyar zamanki ta tsokaneki ki to ki nuna mata zaren ba kalar yadin bane, ki mata fatan shiriya idan Kuma anyi rashin sa'a tana da motsi a kanta to karki sa kishi a ranki ki tsaya iyakar iyawarki na ganin cewa an sadata da asibitin masu rangwamen hankali,Bamu ce idan an tabaki ki kyale ba,a'a bamu gaji haka ba,ba ruwanki da tsokana amma ana cewa kule kice chass amma a wajen me gida,yeeeeee ayiririri sai Chika lallai a nuna mata gidan kaso ba karya ba cewar Yan matan,Chika cikin nutsuwa taci gaba yanzu kishin fada da hauka jahilci ne da rashin sanin darajar Kai,a wajen me gida ake nuna kishi, Idan ta bashi Sadine ki bashi sukumbiya,aka kwashe da dariya a wajen,Rafeeq Yana dariya yace wannan yarinyar ban taba ganin Yar iska irinta ba,wai Sukumbiya,Kamal yana ta dariya yace ai dole suyi Yan gidan yari ne fa kaf kawayen maybe,waccen matar Spark din itace key na iskancin ita take musu rada.

Sabo da haka Amarya a zauna lafiya da miji,mudai Munji dadi da iyayenmu basu gaji siyar da tozalin mata da Alli ba,Mun gode Jama'a Allah ya Maida kowa gidansa lafiya ta mikawa MC waya,Hanan ta kumbura iya kumbura ta fusata,Mohsin ango Yana jinsu ba yanda ya iya da su yaso dai ya hanasu amma sun shammace shi,Bai zaci haka zasu yi ba,yace maganin Hanan kenan da ta taba Naila ita zata dinga sasu suna mata rashin mutunci,bata San Naila ba,da ace bata kula Naila ba da lafiya za ayi bikin a gama,Naila ta koma ta zauna kusa da Rafeeq tace baka gaishe ni ba Ina Auntynka,Rafeeq yace ni kawar Nan taki badan Yar duniya bace da na sota ma,Chika? Yace ae ita amma duk danginmu mu kare a Yan gidan yari fisabilillahi,Naila tace gobe za a dakko malamar mu me yin wa'azi a gidan yari ta bangaren Mata,Matashiya ce irinmu amma akwai ilimin addini da hankali wlh ga wa'azi da koya zamantakewar aure,yanzu ku Dan masifa ma malamar me wa'azi yan gidan yari takewa wa'azi duk malaman duniya,Naila tace gwara irin tamu,shekarata ashirin a gidan yari a can aka haifeta yanzu an fitar da ita shekaru biyu da suka wuce Bata fi 22yrs ba wlh sai baiwar wa'azi,Rafeeq yace Allah ya kaimu ai harda Maza maji wa'azin,su Chikar ne suka gayyato mana malama Ikram,wlh indai kana son Chika zan Maka hanyarta,sai nayi shawara cewar Rafeeq,Kamal yace Amarya ango Yana harararmu ki koma wajensa kishin masifa ne da shi,Naila ta mike ta koma wajen Spark.

Anci an Sha anyi liki,su Hanan anyi kyau anci Leshi harda zuwa fili ta rike hannayen Mohsin tana rawa duk cikin kishi,tana ta uban tikar rawa harda Karin haushi take tikar rawar tana yi da sauri da sauri kamar mahaukaciya,duk ta zauce,Mohsin yaga abin yayi yawa yace karfa ki sumar da kanki,kida slow music ki dinga uban rawa haka kowa na kallonki a mahaukaciya,Hanan ko kulashi bata yi ba kawai ta hada zufa tana haki tana tikar rawa a firgice harda dukawa,tana cewa uban kowa ya Gani bana kishi,Ta fada da karfi kowa Yana ji, Spark ya dinga dariya yace Kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login