Showing 21001 words to 24000 words out of 158722 words

Chapter 8 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

368

bude Ido na kalle su ko zanyi saurayi,wai yaran dangi ne gida gida duk dangi ne,Mohsin yace kina Jin wahala ko baza ki iya ba ko da matsala ki gudo gida kinji ko ki kirani a waya kinji ko? Tace ae naji Yaya,I will miss you,ka kular min da kanka,Jikin Nan natural a adana shi,zan tsananta bincike ko Kai ba Dan Abba da Umma bane ya kamata ayi bincike,zai wahala ma ba musaya aka yi musu a asibiti ba,Dariya suka yi Mohsin yace a gida aka haife ni ba a asibiti ba kinga dansu ne ma, kiyi hakuri ki samu wani yarinya, Nooo... rayuwa sai dai Yaya ta furta tana dariya,wasan su kenan tun Umma tana kulasu yanzu zuba musu Ido take yi.

Hajiya Tagwadas ce ta shigo da uwar akwati anci uban gogoro kamar Yar yorubawa tace yawwa ke 'yata fito mu wuce me napep zai kaimu tasha,Umma tace to kuje Naila Allah ya tsare,Naila tace ke Umma Tagwadas daukar min jakata ai ke zan raka unguwar bazanyi wahala ba, ni sandata kawai zan dauka waye yace kice na rakaki shike nan jakar ma sai na dauka ,Naila dai da kyar aka lallabata ta saka riga da skert na atamfa sabuwar da aka Dinka mata,tayi mata masifar kyau,ai suna ficewa daga gidan ta ja skert dinta sama ya dawo wajen gwiwa duk kaurinta a waje ana kallo,Tagwadas tasan taurin kan Naila yanzu sai tace ta fasa zuwa, ita da take so a can ta samu me kudi yace Yana son Naila cikin Yan uwan nasu shike nan ta samu hanyar shigar su burinta kenan shi yasa ta zuga Umman Naila tace zasu samo kudi da miji na gari me Naira.

Suna cikin Napep Tagwadas tace gidan da zamu je basu taba haihuwa ba,Kuma ance matsalar a mijin ne,Naila ta zaro ido tace to ga shawara ta samun kudi Umma Tagwadas,tace Ina jinki Naila,me zai Hana muje ayi min askin Maza me kyau ayi min Daadaa, nayi shigar Maza kawai na koma namiji sai na basu magani ko zasu dace Kinga idan suka dace mun zama masu kudi musamman ke da kika yi hanyar magani,idan naje a mace baza suyi Amanna da maganin ba

Hajiya Tagwadas tace wannan maganar taki ta kama hankalina muje kawai shagon aski akwai gidan kawata a can layin sai mu siyo kaya a gwanjo na Maza ki shirya tsaf, Naila taji dadi sai suka wuce shagon aski, Naila ta zauna tace ayi mata askin zaratan samari masu ji da kansu ta zabi wani kala Daadaa,aka rage gashin kuwa tare da kwashe gefe da gefe aka tura gashin ya koma baki wuluk sannan aka yi mata Daadaa a wajen gashin me yawa, ba karamin kyau tayi ba, suna fitowa suka wuce Kasuwar Kofar Wambai Gwanjo suka siya na Maza kala biyu manya manya kayan masu Fadi,gidan Kawar Tagwadas suka je a can Naila ta fara shirinta, ta samu Bandage ta tube rigarta ba bra ta nade kirjinta tana zagayowa dashi ta gadon bayanta ta manne breast dinta da fatar jikinta ta sake mannewa da seletape,kirjinta ya dame daf kamar bata da Breast sannan ta saka kayan mazan barma barma,sai ga Naila ta fito a Dan matashin saurayi me kama da mace.

Naila tana fitowa Hajiya Tagwadas ta tafa mata tana dariya,Naila tace daga yau Sunana Jamilu,karki manta fa Jamilu nake,tafiya suka yi sai tasha.
Naila har suka karasa tasha bata yiwa Hajiya Tagwadas magana ba ko sau daya,ta fito daga Napep tana wulwula sandarta tana wasa da ita da gani ta kware da wasa da Sanda salo salo take wulwula sandar,kafin kace me duk ta ja Yan kallo an taru ana kallonta ana ta dariya, zaton kowa Namiji ne, sai da ta gaji ta daina lokacin sun samu motarsu me kyau aka sa musu kayansu suka shiga mota sandarta akace ta kawo a sata a bayan mota tace aradu ban badawa,ai sai naji kamar nayi wata mummunar mantuwa bada ni ba.

Ana fara tafiya Naila tayi bacci har akaje bata San anje ba sai da zasu sauka aka tashe ta,sai ta tuna ashe fa Abuja zasu,Hajiya Tagwadas tuni ta sauka ta fito musu da kayansu,sannan Naila ta fita itama tace garin kamshi iri iri uhmmmm,sai munje gidan ma zaki gani tun bama gidan sojojin ba,Naila tace uhmm yanzu mene next? Taxi suka shiga ta kaisu katafariyar unguwar gidan Mummy ta nufa direct sabo da sunfi dasawa ta dan fi saukin Kai,Hajiya Tagwadas tana buga gate me gadi ya leko ya ganta ya Santa Nan take ya bude kofa Yana washe baki,Suka shiga suka ce ah sabon Dan aiki aka kawo mana ne suna kallon Naila Jamilu.

Naila tace wuce nan yaro ni da nake da shanu nafi karfin aikatau,shuru suka yi, Tagwadas tiryan tiryan ta kaisu har palon Hajiya suna shiga suka sameta zaune a kujera ta kafa tulun shisha a palon tana faman zuka tana feso hayakin waje, Naila ta zaro ido tare da furta kaga dattijuyar banza, ke Inna kiji tsoron Allah tsofai tsofai ai idan lokacinka ya wuce to ya wuce,ko kara'i kike yi ne? Hajiya Tagwadas ce tace Kai Jamilu dalla rufe mana baki,Mummy ko ta tasu bata yi ba bata San ma Allah yayi mutane ba a wajen a haka itace me saukin Kai.

Tagwadas ta Fadi a gabanta tare da mika gaisuwa kamar taga sarauniya tace ranki ya Dade ajiyar Dana na kawo miki Dan kawata ce ki dan bashi dakin zama ya zauna kafin naje na dawo,Naila ta bude baki mamaki ya kamata,zata yi magana Tagwadas tace karka ce komai Jamilu zamu raba gari,Mummy tana ta bulbulawa huhunta shisha tace okay fine barshi kije,tace godiya nake uwar dakina,kudi a zube a gefen Mummy ta irgo wasu ta mikawa Tagwadas tace ya mutan kauye? Tagwadas ta furta Naje kauyen waccen satin kuwa suka ce a gaishe ku,hannu ta daga mata tace ya isa tashi ki tafi,ko kallon Naila bata yi ba,Naila tana kallo Tagwadas tace Kai Jamilu ka zauna a nan zanje na dawo,Naila ta tabe baki tace to tare da cakewa a Jikin sandarta tayi wata tsaiwa akan sandarta yanda Fulani ke yi,Mummy Yan aiki ta kira tace gashi Nan ku kaishi masauki ku bashi abinci ya koshi a nuna masa komai,Naila dai tana kallon ikon Allah.

Me aikin ce tace muje ko part din maza ta nuna mata, sannan ta kawo mata abinci ta nuna mata toilet a cikin dakin sannan ta fice,Naila taci ta koshi tayi wanka ta kulle kofar da key sannan ta canja kayanta na mata doguwar riga marar nauyi ta material tare da saka hijab ta gabatar sallolin da ake binta tayi addua, bayan tayi Sallar Isha ta kwanta bacci dake dare yayi.

Bata farka ba sai washe gari da safe bayan tayi Sallar asuba take ta koma bacci tana sharara uban bacci har 11am sannan yunwa ta tasheta,wanka tayi ta sake nannade kirjinta ta manne da Seletape ta Maida kayanta na Maza Wanda ta zo dasu a jikinta, kayan matan Kuma cikin Inda ake ajiye kaya a dakin sip Nan ta bude ta boye su a ciki sabo da kar a kamata sai ta bar kayan mazan kala daya kacal da magungunanta na siyarwa na gargajiya duk suna cikin Jakarta,ta nufi part din Mummy,tazo shiga kenan taji suna ta fada da mijinta.

Mijinta Alhaji Aliyu yace wallahi aure babu fashi sai nayi shi,ni Kuma baka isa ka Kara aure ba sai dai idan bana raye ko baka raye,Kai zan iya kisan Kai,zan iya kashe ka na kashe kaina wlh,indai ka Kara auren Nan sai kaga ba dai dai ba zaka San wa ka aura,ba a abinda kika isa kiyi karamar Yar iska,tace to mu zuba mu gani waye zaiyi kasa,yace mu zuba ya fito a fusace ya kusa yaci karo da Naila tace cikin Muryar maza Sannu kayi hakuri,Ina kwana? Hannu kawai ya daga mata ya wuce abinsa dake gidan ko Maza ma free to enter ne.

Palon ta shiga da sallama ta samu Mummy ta zube a kasa tare da Kifa kanta a Saman kujera tana rusa uban kuka,Naila tace akan kishiyar wlh kin bada mata ai ko ni Jamilu da ace macece ni to bazan yi haka ba,baki hadu ba,Mummy kishi na cinta ta manta ma yaro ne Jamilu sai tace baza ka gane ba,wlh wlh tunda na aure shi bai fi a irga ba muke saduwar aure bashi da lafiya gabansa baya aiki sosai gashi ban taba haihuwa ba duk nayi hakuri dashi na zauna a haka shine zai min kishiya,Naila kamar babba tace share hawayenki Waraka tazo miki Allah ne ya kawo miki magani har gida Inshaallah daga yau sai kince Hallare ta isheki,Dan Nan mene Hallare? Naila tace Abar da kike kuka a kanta.

Naila taci ga yanzu ni Kinganni sabo da sanin kan aikina ba kalar da ban sani ba,ke me ya kaiki auren gajere?,irin tasu fa shape din kubewa garesu,kin san okro? Kubewar Miya Banda me kahon barewa,kin san a kubewa ma akwai doguwa to ba kalar doguwar ba, Yar gujub din itace irin ta mijinki,Ina ganinsa nasan tasa ba pole bace,ni fa muna hada Ido da namiji to tsirara nake ganinsa, harda tafa hannu tace duk wani Dan uwana namiji zigidir nake ganinsa,Mummy tace wallahi Dan nan ta megidana haka take kubewa sak,ah na fada miki ai muna yin clashing dashi na hango shi tumbir Zigidir, Mummy tace Allah da baiwa yake,Naila tace a daji na girma ni a Nan fagen na kware,ai gado nayi a wajen kakana tun na goma Sha biyar baya da suka shude sana'arsu ce,ba wanda yayi gado a kaf dangin mu sai ni nan Jamilu,Ina bada magani idan ta kama ma dole sai na gani to sai na ganta nayi mata aiki da kaina da hannuna,Hajiya ta saki baki tana kallon Jamilu,Naila tace ae fa idan ta kama to sai kalleta,ta nuna idonta da hannu tace akwai wani sirri a idona Ina kallonta lalurar dake wajen zata fito sabo da taga abinda ta gani a cikin idona.

Tace kina so na baki maganin ki yarda da Allah,bani zan warkar dashi ba Allah ne amma idan ya zama Sila sai Kiga kin dace,Mummy tace kawo na gani,akan sana'ata kice sai na kawo kin gani ma,in kina so sadaka zan baki in bakya so ki bar min abina wannan maganin da kin san aikinsa da ko million nace siya zaki yi.

Fita Naila tayi ta bude Jakarta ta kwaso su gasu nan a kulle a leda Dan mitsil mitsil gari ne green da wani red,ta kawowa Mummy tace gashi wannan kala biyu ne,Dan girki zaki Masa shi kadai dai dai cikinsa ki juye Masa ki tabbatar ya cinye tas shike nan daga lokacin ki tafi bedroom ranar kika yi wasa sai an kaiki asibiti an miki dinki,Mummy dai badan ta yarda ba ta karba,Naila tace to ai kunyi fada ta ya zai ci girkinki yau? tace kiransa zanyi na bashi hakuri,kina tunanin Hakan zai sa ya yarda Dake ai zaiyi tunanin da wata a kasa wai ya kike hakane kin fa haife ni duk da ni namiji ne amma baki da wayo,Mummy ta Kalli Naila da sauri wannan gatsali da yaron yake yi sai kace danta Spark babu mutunci a harkar su.

Naila tace ki jira shi ya sakko da kansa sannan ki Dan bashi hakuri sama sama sannan ki sa Masa amma da wuri haka ai sai ya raina ki,nifa da ace ni macece ba Dan iskan namijin da zanwa biyayya ni mamaki ma kuke bani da kuke nacewa mutum haba,Mummy ta saki Baki tace ikon Allah kai nifa na haifi yayanka ma ko yayarka ta biyu bare kai,ka kula kana gidana Ina taimaka maka da abinci kana fada min magana ba ladabi,Naila ta kalleta tace bani maganina na bar miki gidanki ni haka nake Ina da kirki Ina da zafi, kaina da kwari idan na birkice hmmm.

Mummy sama ta haura abinta Naila ta baje a kujera kamar gidan ubanta harda kiran Yan aiki,wata tazo a ciki tace zubo min abinci ki hado da hantar kifi, Yar aiki tace babu hantar kifi,tace to hantar kaza fa? Babu itama,zabo? Babu hantar zabo?,Naila tace shima comon zabon abin banza? tace ae,tace to ta Dan maraki? Akace babu,tace ta rago fa? Yar aiki tace sai ta Sa gaskiya,Naila tace uhm uhm bana cin Naman Sa sabo da ai cin Amana nayi shanu dabbobinmu kawai sabo da cin Amana naci namansu Bada ni ba,Yar aiki tace sai kace me bautar saniya, a'a daga India nake Naila ta furta da Muryar maza,Uhmm me zan kawo yanzu? Nasan ma babu Koko kawo min abinda kuka dafa banda shayi.

Naila dai tana gida har kwana uku suna shiri da Mummy sabo da maganin da Naila ta bata,Kuma mijinta ya fara sakkowa sun ma kusa shiryawa gaba daya shi yasa yau Mummy zata Masa girki da magani,taci gyaran jiki sosai za a angwance,yau wankan data dauka ma na musamman ne, Naila tana kallonta sai shanawa take a gidan masu hanu da shuni har yanzu Kuma bata ga wani namiji yazo gidan ba basu je gidan sojojin ba,ta dai kira Mohsin ta fada Masa komai normal.

Mummy Dan faten wake da doya tayima Alhajinta yaji kifi,Yana son kifi iya cikinsa yanda Naila tace haka tayi,part dinsa ta nufa ta Kai Masa yace zo Halima,ta koma zata zauna ya jawota jikinsa yace Hali dubu tawa ko kefa ai gwara da kika hakura nayi auren mene aciki kece fa ta gaban goshi,wallahi ba wacce zan so sama da ke a duniya,Mummy tace uhm ta kakalo murmushin dole tayi dai tace ci abincinka ko na baka a baki,yace da zan fi son Hakan,ta dauki spoon ta fara bashi a hankali Yana ci,har ya kusa cinyewa bai sani ba sabo da dadi sai da ya cinye tas sannan ya Sha ruwa sosai,har zai kwanta yace naji na gaji ne sai ya dauki carbinsa Yana tasbihi ya kwanta a Saman bed dinsa,Mummy ta kwashe kwanikanta tas ta fice ta wanke Kal ta Adana sannan ta koma wajen me gidanta,carbin ta samu ya jefosa kasa tana zuwa ta daga hannunsa taji ya saki alamar ya mutu rai yayi halinsa, murmushi ta saki tace akan kamin kishiya wallahi gwara ka sheka can Kai ka isa mutumin banza butulu,Kuma dole group na company naku su ajiye million goma in Sha bushasha ta,Hannu ta Dora a Kai da kururuwa ta fito tana ihu tana bako ya kashe min miji,Magani ya bani na karfin Maza ashe guba ya bani Mummy ta zunduma waje ta tara mutane ta kirawo makwafta,ta hau kiraye kiraye na Yan uwa da abokan arziki sannan ta kira police suka dungumo gidan, gida ya cika makil,Har Hajiya Tagwadas ta kira a waya ta taho hankali tashe domin ita har ga Allah burinta ta samu shiga a cikin masu kudin danginsu ta dinga samun kudade shi yasa ta kawo Naila ko zata Saba da su ta samu saurayi a cikin Yan gidan tunda suna yawan zuwa gidan sannan tasan watarana Mummy zata iya tafiya da ita cikin dangi kuma sai suka canja su gwada maganin ko Mummy zata dace mijinta ya warke ta haihu.

Naila bata gane batu ba,sai da Mummy ta shaketa tare da kifa mata Mari tana jijjigata tana cewa matsiyaci ashe maganin kisa ka bani ka kashe min mijina ta dinga zabgawa Naila Mari, Naila zuciya ta ciyota ta dauki sandarta ta bugawa Mummy iya karfinta a kanta Nan ma Mummy da sharri ta sulale ta fara suman karya farrrr farrr, Naila ta jefar da sandar ta haye ruwan cikin Mummy ta dinga rama marinta mummy duk ta shanye Marin nan wai bata sani ba suma take, Naila ta daga hannaye sama tace a tafi dani da hujja Allah shine shaidata,wacce Bata San alkhairi ba butulu.

Da ace baki saka Masa guba ba maganin Dana baki kika saka Masa wallahi da aurenki ya daidaita maybe ma ke da kishiya shike nan watakil ma ki haihu kinwa kanki, ta ciro takalminta ta bugawa Mummy a Baki baki ya fashe amma duk Mummy wai suma take bata sani ba bayan tana Jin komai.

Mutane kafin kace me gida ya cika dam ko Ina manya Maza da mata,ga dangi ta ko Ina suna ta parking motoci ta bangaren mata da Maza,da kyar aka banbare Naila daga kan Mummy, kuka ta saki taje ta shaki Hajiya Tagwadas tace Allah ya isa d...da ...da .kika...kawo ni Nan...duk kafin kace me sojoji ta ko Ina a gidan matasan samari hadaddu suna ta dira dangi, a tsakiya aka saka Naila duk an zagayeta ana kallonta mutane har sun firfito da waya,ba Wanda ya gane macece,Misam ne ya Dana bindiga yace wallahi duk Wanda ya daukar mana hoto sai na harbe shi,ai kowa a tsorace yayi kasa da waya wasu ma jiki na rawa suka kashe wayar,Mummy dai tana can mata suna ta yayyafa mata ruwa da ta farfado tace wayyo mijina sai tayi farrrrr luuuuu da Ido sai suman karya, suna ta fama sai da kyar ganin za a gane ta sannan ta farfado gaba daya ta kurma uban ihu ta fado cikin mutane da gudu ta isa Inda Naila take ta Kai hanu zata shaki Naila,lokacin Naila zuciya taci karfinta hannunta ta rike gam iya karfinta ta lankwasawa Mummy yatsu,Kara da Ihu Mummy ta tsala tace a dake ka a hanaka kuka ga Mari ga tsinka jaka, ta sake Kai daya hannun Naila kamar Dan biri tayi tsale ta dane Mummy ta shake Mummy,Misam a ransa yace tunda yaron can yake fada haka yana da kamshin gaskiya ya kamata ayi bincike me tsanani.

Mummy ta kwace kanta da kyar tace namiji ya rungumeni Kuna kallo wayyo...namiji ya rungumeni fasiki ne, Naila hawaye baya tsayawa a kumatunta Taga dai Maza manya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login