Showing 78001 words to 81000 words out of 158722 words
Chapter 27 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
nake, akan mace har nayi hawaye.
Naila kuwa murna take kawai ta fito ta shiga zaga gidan tana Shan kallo sai da ta gama kallon ko Ina sannan ta shiga kitchen Dan girkin data iya kadan ne Dan ma ta koya a wajen Sheyi,Irish ta soya da kwai ta dafa tea ta zuba a flask ta kawo dining tana jerawa,Spark ne ya fito fuskar nan murtuk,Naila tunaninta Bai ganeta bane shi yasa,a hankali tace sannu sir,ga breakfast,Spark yayi zuciya a ransa yace bari na ci idan ta kashe ni ita tayi asara,ya zauna a fusace a kujera tana murmushi ta gyara glass dinta ta hada Masa tea tun daga yanda ta hada Masa tea yasan wlh Naila ce duk abinda yake so ta sani gashi nan, Bismillah yayi tare da addoui yace a ransa idan na mutu Allah na yafe mata sabo da son da nake mata,Allah ka zama sheda,Naila dai taga Yana addua bata San me yace ba,tea din ya dauka ya fara Shan abinsa zama tayi a kujera tabbacin ta Saba da shi gashi shi tsiyar so baya buya,Naila a nutse ta dinga mika Masa slise bread din Yana karba,sai faman satar kallon juna suke,shi dai baice mata kala ba,amma itace tace Sir abincin yayi? Ko kulata baiyi ba wani haushi take bashi ma harara ya watsa mata tace a ranta bai sanni ba Bai ganeni ba Allah sarki bai San Jamilunsa bace .
Mima kuwa ganin Chikar gayu bata ji amma Kuma ta shiga ranta sai tace wannan itace daidai da Spark za yi maganinsa,sai ta kirata har dakinta,Chikar gayu ta zo zata durkusa,Mima tace Chika ya sunanki na gaskiya ma kika ce? Suhaila,suna me dadi,Ina so muyi wata magana tace to Ina jinki, zaki auri Dana? Chikar gayu ta zaci Misam ne da sauri tace ae me zai hana ai kina da kirki Kuma tunda na shugo gidan Nan nasan Ku mutanen kirki ne,a ranta Kuma tace karya nake ku ba mutanen kirki bane Yan wulakanci in kuka ga talaka ne mutum, Mima tace Spark nake so ki aura,Chikar gayu wani gumi ne ya keto mata tace a ranta ai Naila sai ta kashe ni Allah ya tsareni da cin Amana,a fili tace a'a Mima kiyi hakuri wlh bazan iya ba dama wani ne a ciki ba Spark ba,Spark ya haramta a gareni,ba Wacce zata ce baza ta so shi ba amma Banda ni wlh kiyi hakuri a canja min wani,Mima tace to kuwa sai dai ki bar gidan nan,Chikar gayu tace gari da yawa ai maye baya cin kansa,dama ni karya nake miki baku da halin arziki yawwa in fada miki gaskiya Ina da gatana,karki ganni a nan kice bani da gata,Mima tace to hada kayanki ki bar min gida,tace ko baki ce ba dama,ta juya ta fice kayanta ta tattaro tayi wanka tun a gidan ta canja kayanta masu kyau ba Wanda zai ganta ya rainta ta fito Palo tazo ta jefawa Mima Jakarta tace gashi nan dama aro su nayi Dan Allah a kone su ko a kaiwa dangi a kauye.
Kuma bari kiji nafi karfin na muku bauta shi yasa kuka ga Ina muku rashin mutunci iri iri yawwa, danki Kuma bazan aura ba a likawa wata mu bamu gaji cin Amana ba yawwa,ta juya tana murguda duwaiwaka tace ayyiriri mamarrrrrrrrr......ta wuce tana jijjiga jiki tana waka,Mima baki ta rike tace ashe da Karuwa muke zaune.
Chikar gayu tace Allah ya rabamu da zuriar masu kisan Kai mugun iri,ta juyo ta Kalli Mima tace byeeeeee....
Tana fitowa Misam ya shugo Allah yayi shi da neman matan tsiya gashi mata suna rububinsa sabo da shima ba karya,Chikar gayu ya Gani ta fito tana karkada jiki zata fita,Bai taba kulata ba sai yau,yace Chik....da iyayi Juyowa tayi ya kalle shi Yana birgeta a rayuwa yanzu Kam tasan yanda tayiwa uwarsa fitsara Ina zata bari ma suyi alaka.
SANARWA
DAN ALLAH YAN PAID GROUP KU RIKE AMANA KARKU BAWA WASU KYAUTA.
ITA TA KASA SIYA KE KIN SIYA KIN BATA TA PRIVATE TASAN BA SIYA TAYI BA DOLE TA BAWA WASU A HAKA ZASU TURA SHI GROUPS DA YAWA.
YAU DA ACE ITA KADAI ZATA KARANTA TA PRIVATE DA SAUKI SAI KU BAYAR A WATSA SHI A GROUPS
WLH DA AYI WANNAN GWARA MUTUM BAI SIYA BA.
AKWAI CIWO GA WRITER DA WANDA SUKA SIYA.
AsmaBaffa
[12/14/2023, 8:24 PM] AsmaBaffa: PAID BOOK
Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger
+22790795939
🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI
BOOK 1
51-55
Official
By
AsmaBaffa
Sadaukarwa gare ki
AIDA MAMAN TASNIM
Page naki ne
HASEENA AHMAD DAURA
Hey lovelies
Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?
Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?
Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?
Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?
Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din
https://wa.link/49vn47
Chikar gayu tsoro taji yanda tayiwa uwarsa rashin kunya tab ai bai ma dace ta so Danta ba tace ni bana zafafawa kaina amma dai bari mugani,karasawa tayi har kusa da Misam ya zaci tsayawa zata yi sai ya ga ta daga Masa hannu wani ta wuce tana rangwada ta bude gate ta fice abinta,horn yayi masu gadi suka sake bude Masa gate ya fita da motarsa hadaddiya.
Chikar gayu tana tana tafiyarta a gefen hanya Yana tafiya a hankali Yana binta Yana mata horn tunda ta juya ta ga shine bata ko kulashi ba taci gaba da tafiya harda yin tafiyar nigogi tana dangale kafa Daya tare da basarwa tana bouncing,canja wata tafiyar tayi ta Yan gayu tana yanga tana tana tafiya shi Kuma kamar maye Yana binta a baya Yana kallonta Yana dariya, ganin Yana ta binta yaki hakura, ta kira Naila bata daga ba sai da ta sake dagawa lokacin Naila suna dining spark Yana ta Shan tea dinsa,kallonta Spark yayi ya danna tsaki kadan,Naila wayar ta daga tace hello a hankali kasa kasa karta dame shi,Chikar gayu tace ke fa na gudo na kasa hakuri wai babarsu na auri Spark dinki Dan Allah ke kinji marar mutuncin mata,Naila tace ae gwara da kika gudu kin kyauta min Allah ya miki albarka amma da kin yarda wlh da Kinga halin Tantiranci,Dariya Chikar gayu tayi tace,a'a Hallaren dinsa tayi min kadan,Naila tace dama daidai nice ai,ah dama ai se ke, bani da kudi fa an koreni ba ko kudin sallama,Naila tace akwai kudi a kasa zan tura miki 100k ki turawa gidanku ko 70k ce wlh su rage radadi,a Ina kika samu kudin? Mum mana,Chikar gayu tace ikon Allah ni kuwa na cuci kaina sai nayi rashin mutunci ko ficika ban samu ba,a'a wannan rashin kunyar taki tayi karki dagawa kowa kafa amma a dinga sanin ya kamata kwaila kinji,Chikar gayu tace nice kwailar? Ae mana baki ji tarihinsu ba fa aikin banza kika yi dole fa ki koma gidan nan,ki kwantar da Kai pls amma karki yarda da auren nan sai dai a canja miki wani.
Chikar gayu tace bazan koma ba ai da kunya kin san kuwa abinda nayi? Naila tace to Kuma mu tsoron abin kunya muke, kawai nazo nan gidan Spark din,Naila tace baki da hankali ki tafi gidan saurayinki Daddyn Beauty kafin a samo mafita,dariya suka yi tace bari naje na hadu da Sheyi kawar ki,dariya Naila tayi tace ki turo accnt ta kashe wayarta.
Naila tana ajiye wayarta Mohsin ya sake kira,ta daga tare da furta Darling Ina Kwana,Spark ya kalleta ta kira wani da Darling,ji yayi ta furta laaa Yaya Umma ta haihu? Innalillahi Ina tsoron wannan lamari yanzu ai da kunya haka zanyi aure Ina haihuwa Umma tana haihuwa sabo da Allah ai da kunya,Ni na haihu Umma ma tazo sabo da Allah,uwa da ciki ya da ciki shike nan mu da Umma kowa yasan muna kwalbewa da miji,dariya ce ta kama Spark,yayi tari ya danne abarsa, to yanzu me ta haife? Mace ta haifa cewar Mohsin Yana cewa mene abin kunya nima ai kwalbewar nake da Hanan, kiyi sauri ki auren nan,Allah ya raya Yaya amma harga Allah Kai naso aure amma kazo a yayana baka kyauta min ba wai sabo da Allah maimakon kazo a Dan gidan Malam Isa sai ka fado a gidan Malam Hashimu Dolo,Mohsin yayi dariya yace ya zanyi nima haka na ganni,kwalele Kuma,dariya tayi tace Yaya ya lafiyar Hallare?
Mohsin yace karki dameni kina Ina ne Abuja din? Naila ta saci kallon Spark suka hada Ido tace ae Ina can,yace ki rike mutuncinki fa karki ga kamar baki da mafadi wlh kina yin badaidai sai kinci ubanki nasan halinki,Kuma karki biyewa kawayen banza,karki biyewa zuciya kizo kina aikin danasani,karki ji tausayina indai matsalar kudi ce ki fada min, karki kasa fada min kice zaki ji tausayina ko nauyi yayi min yawa kawai ki fada min,duk abinda kike so Ina nan,sannan ma kina Ina a Abuja din ni fa hankalina ba a kwance yake ba,Naila tace Yaya ka kwantar da halinka kamar kayi bako ya mutu, ba abinda zai faru inshaallah,Ina gidan su Beauty,yace to kiyi zamanki a nan Banda samarin banza,Banda daukan fansar Nan kiyi hakuri Allah zai saka miki,Naila a ranta tace nima ai Ina so na dawo gida na zauna a gaban iyayena ya kamata a kai Mummy gidan yari na samu nayi free,a fili to tace kawai.
Tana kashewa ta turawa Chikar gayu 100k sannan ta kira Umma suka gaisa tayi mata Allah raya tace Umma iceko lafiya kike? Umma tace sosai ma sai dai yaron nan Mohsin nake tausayi wlh Kinga bashi da kudi gashi a tsakiyar wata,gashi shine zaiyi komai a gidan nan abin Nan Yana damuna duk yaron bashi da sukuni ga gidansa ga gidanmu,ni kudina na biyawa su Hidaya kudin term a haka ma bashi ake bina,Naila tace Umma Inda naje Abuja na samu aikin yi har an fara biya na albashi ma sannan Baban Beauty ya bamu kudi da yawa Umma kirki ne da shi,Umma tace Allah? Naila tace Allah a gidan wasu attajirai sai shegen kudi,yaron gidan sunansa Ashraf dabban kudi ne da shi, rabona nazo ci,Spark ya kalleta yayi dariya a ransa.
Ki fadawa Yaya zan tura Masa kudin,kema ki tura min naki na saka miki wani abin,Umma tace mashaallah na daina zagin yarana daga yau Allah ya miki albarka naga ranar haihuwa,ai kuwa haihuwa yanzu na fara,na dinga haihuwa kenan cewar Umma,Naila tace dan Allah a'a ki hakura haka,yanzu idan nayi aure shike nan ana yi min ciki kema ana miki Umma bazan ji dadi,sai kace akuyoyi,mijina ai sai yaga iyayena a mutanen banza,Umma kowa aka ganshi da ciki an San me yayi Dan Allah Umma ki rufa min asiri ko zaku yi abinku kuyi Allura,ni bazan hanaku kwalbewa ba,kinga ba wanda yasan me kuke yi,Umma ki rufa min asiri Dan Allah nidai shike nan sai mijina yaji uwata da ciki,abin kunyar da akeyi a boye ya fito fili.
Umma tace Allah ya shiryeki Naila na rasa ma me zance dake,yanzu na daina zagi Allah ya shiryeni,to nidai kiyi Allura a tsayar da ita idan kunyi abinku ma ba Wanda ya sani.
Dama Umma da son a bata kudi ko masifa Bata yiwa Naila ba,taji kudi sai dai tace Allah ya shirya,Nan take ta tura, Naila ta tura mata 50k,ta turawa Mohsin 150k,ta turawa Abba 20k a accnt din Mohsin tace ya bawa Abba,Mohsin yace aikin uban me kike haka da zaki samu kudi? Naila tace ,Yaya wallahi ba cinikin Bado na nayi ba,ba Wanda ya siya,abina yana Nan yayi kwantai Ina ta fama da shi an rasa me siya ya aureni ma wlh,zuwa dare zan kiraka na Maka bayani,yace Ina jira baza mu taba kudi ba sai kin mana gamsashen bayani,tace to sarkin tarbiyya wai Kai na kwarai,dariya Mohsin yayi yace oh Naila case wannan fitsara yaushe zata daina ne ta kashe wayar,Mohsin yace bari kiyi auren yarinya miji zai kashe bakinki.
Spark Yana jinta bai nuna yaji ba Yana latsa waya Yana kora tea dinsa,sai yanzu yake sake jinjina Tantiranci Naila yace Umma guda take fadawa haka yo aini Alhmdllh nayi dace,dama bana son mace wani Sumi Sumi nafi so me ji da balaga da iskanci Yar Karuwa Karuwa haka yawwa tafi,dawowa tayi ta zauna tace ya naga baka cin chips din ne? banza ya mata.
Ta kalle shi kawai ta hada nata ta ja plate din nasa gaba ya janye abinsa ya dawo da shi gabansa ba tare da yace komai ba,Naila a ranta sai murna take tace yaji dadin girkina wayyo,kasa rike murnarta tayi bata San ma ta saki murmushi ba da sauri ta rufe bakinta da hannu ta mike tana rufe da bakinta kamar wacce zata yi amai duk da ta rufe bakinta idonta da fuskarta ya nuna lallai dariya take yi,da sauri ta nufi hanyar bedroom,tsawa ya mata kee....ta juyo da sauri yace wa kike wa dariya,tace uhm uhm zuciyata ce take shi,ta shige bedroom da gudu.
Dariya ma ta bashi yace yarinya kamar Aljana,zama yayi tare da shafa cikinsa yace har yanzu banji sign na wani ciwo ba bata sa komai ba maybe,ko sai a hankali zai ci jikina cuta ta kamani,Ido ya zaro shi kadai yace mutuwa Allah ka taimakeni sai na samu yarinyar nan nayi harkoki,Spark ango ahh ranar tab sai harkoki.
Naila wayarta ta manta a dining,daukan wayar yayi ya duba missed calls Wanda tayi waya da shi yagani ta sa Darling,number din yayi sauri ya dauka ya shigar a wayarsa sannan ya ajiye mata wayarta,sai da ya gama karyawa abinsa Naila tana dakinta wata Yar aiki ta shugo tare da gaida spark ta fara gyara gidan,ba a gidan take kwana ba kullum zuwa take tana gyara gidan Banda dakinsa.
Dakinsa Kuma da kansa yake zagewa ya gyara kullum ko da safe ko da yamma idan ya dawo daga Office.
Kamal ne yayi Sallama ya shugo palon, Spark Yana zaune Saman wani Lilo da ake sashi a palor can bangare daban me circle Yana ciki a zaune Yana danna waya lilon Yana Lila shi kadan kadan,Kamal yace ya akayi suka gaisa yace please zo ka rakani unguwa,da safen nan?
Suna haka Daddyn su Asmau ya shugo tare da yarsa kanwar Asmau wacce ake kira da Wahida,Spark yayi mamakin ganinsu a gidansa,kallonsu yayi kawai,Mahaifin Asmau zuwa yayi gaban Spark cike da nadama,Spark yace Ina Kwana,Bai zaci zai gaishe shi ba yanda Spark yake ji da tsageranci,amsawa yayi yace dama zuwa muka yi mu baka hakuri Dan Allah ka yafe min,Na yafe Maka cewar Spark,Daddy da mamaki yace haka da wuri? Spark ya furta ai Dan Adam ajizi ne dukkan mu muna kuskure,share kawai ya wuce Allah yaji kanta.
Wow Mahaifin Asmau ya furta yace ga kanwarta sunanta Wahida indai har kana sonta zan baga ita,Wahida itama kyakyawa ce wankan tarwada,Shekeke Spark ya kalleta bayan sunfi kusanci ma da Wahida,tace Ina Kwana Yaya Spark ,ya amsa,Daddy ku zauna mana,kujera suka samu tare da zama,Naila ya kwalawa kira chef...fitowa tayi da alamu ma bacci ta fara,yace anyi baki,Naila ta nufi kitchen ta shiryo kayan motsa baki ta kawo musu sannan tace Ina Kwana ta gaida Daddy,ya amsa da fara'a, Wahida kuwa wani haushin Naila taji sai harkarta take faman yi tana turo baki,itama Naila Wahida take gallawa harara kamar idonta zai fado,yanda take hararsa yasa Spark a ransa yace bala'i kar dai idon ya fado ki min asara,bedroom Naila zata koma yace Zauna,Kamal shi kanshi kallon Naila yake ta faman yi Kamar ya Santa.
Waje ta samu ta zauna,tana kumburi,Spark yace zuba musu mana kin zauna kina kallona,Naila ta Kalli Spark a ranta tace wayyo Bai San nice Jamilunsa ba ta mike ta zubawa Daddy shi kadai,yace ki zubawa Wahida my wife to be,Wahida da sauri ta dago kai sabo da ba zato abin yazo mata,Daddy farin ciki ya kama shi yace na gode Dana Allah ya Maka albarka,Wahida sai wani murmushi take burinta ya cika.
Naila daurewa tayi ta zubawa Wahida lemon ta mika mata,Naila ta ajiye a wajen ta mike da sauri fuskar nan kamar hadari,Spark yace mika mata a hannu mana kina Bata mata lokaci,kallonsa Naila tayi idonta ya ciko da kwalla ta dage ta maidata bata fito ba,ta mikawa Wahida ta rike,zata wuce Spark yace Zauna su gama ki kwashe,dawowa tayi zata zauna yace on the floor ko bakya Jin turanci a kasa,Naila ta koma kasa ta zauna a ranta tace idan Sanyi ya sake kamani ai Kai ka jiyo waye zaiji dadin idan Kuma Sanyi ya min illa ka ragewa kanka dadi bado zaiyi Sanyi.
Suna Dan Sha Daddy ya umarci Wahida yace taso mu tafi,Spark ya mike Yana sani ya dinga kallon Wahida shi a zahiri bata birge shi amma haka yake kallonta ala dole Yana wani Jin dadi,Wahida kuwa a ranta murna take tana Jin tafi ko wacce mace a duniya Spark sai wani kallonta yake kamar ta zuba ruwa a kasa ta Sha,Kamal Yana kallon Spark Yana mamakin abinda yayi duk da bai gane Naila ba shima dai Yana zargin ya Santa.
Har mota ya rakasu,Daddy yace Inshaallah zan kira Mima na gaya mata komai,Spark yace ba damuwa,dawowa yayi ciki tare da Kamal suka haura sama,Naila tana kallonsa sai lokacin ta mike da kyar jiki ba kwari ta shige bedroom tare da fadawa Saman bed,tana tunani abin duniya ya isheta.
Kamal suna shiga ciki yace me yasa kayi