Showing 3001 words to 6000 words out of 158722 words
Chapter 2 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
makarantar addini Data boko, bangaren mata ma daban na masu ciki daban,duniya guda ce,amma duk Wanda su masu daurin rai da rai ne to sunfi kowa more rayuwa a ciki sabo da su an San har abada ba fitowa,sabo da nishadinsu aka tanadar musu abubuwan nishadi,haka lokacin maulidi ma ba a barinsu a baya.
Naila tana ta Shan kallon Yan iska iya Yan iska,a ranta tace dole na zama tsagera Tantiriya,a Nan sunana na daji Tantiriya zai min amfani,bangaren daurin rai da rai ko ma'aikatan ciki basa shiga wajen sai da dalili sabo da zasu iya kashe wasu iya Kaci dai hukunci daya ne dai Wanda suke ciki daurin rai da rai tunda yanzu in ance Wanda ya kashe a kashe shi to fa ba a kashewar, gomnati bata sa hannu, a haka ma masu kwakwaran hanya da kudi ake fitar dasu ba a sani ba.
Tantiriya dai ganin an dameta da kallo suna nema su ganeta sai daki ta canja na wasu malamai ne Wanda kaddara ta fada musu, su biyar ne a dakin shi yasa ta koma can taga suna da tsoron Allah baza suyi mata komai ba,Bata son cudanya da mazan. malaman ban sai kallon Naila suke tunaninsu Namiji ne Dandaudu,Sallama tayi da Muryar data canja ta dole ta Maza amma duk da haka sai aji kamar ta mata, Malaman Nan tana shugowa duk wanda ya Kalli Jamilu Terror sai yaji gabansa ya Fadi sai yaji Yana wani son Dandaudun,gaba dayansu,basu sake shiga wani hali sai da Naila tayi magana, babban malamin cikinsu a kalla zai Kai 50yrs a hankali ya hadiyi yawu wani tsoro ya kamashi sai istingifari yake Yana furta a ransa Allah na tuba na kamu da son Dandaudu Allah ka kubutar dani,shima Malam Jilani Yana kallon Jamilu Terror sai kuwa yaga ya saki murmushi,wani narkewa yayi a zaune wani matsananciyar kaunar Dandaudun yaji lokaci guda,Malam Usama kuwa har baya son ya kyafta Ido da kallon Yaron Dandaudun,Naila kuwa dariya take a ranta a fili kuwa ta maze,wani gadon karfensu ta ja gefe can karshen bango ta Kai bed din ta kwanta a abinta.
Babban malamin Sharu ne ya Kalli Dan uwansa Malam Usama ya rada Masa kasa kasa tare da dafe saitin zuciyarsa yace Akaramakalla kana jin wani masifa data ke neman fada min kamar ni da tilawata izu sittin naji me kalar Dandaudun can ya birgeni namiji ne fa,Ina kallonsa naji zuciyata ta hau bugawa wani kaunarsa ta kamani yaro namiji Dan uwana kamar Dan cikina ni malam,ku sani a addua Dan Allah,Usama ma kasa kasa yace nima Dan ubanka haka naji gaba daya sai naji ya tafi da imanin....da sauri ya danne bakinsa da tafin hannunsa, yace wannan jarabawa ce Allah zai mana mu halkanta mu dukufa da addua,Naila ce suka hada Ido da Malam Jilani ta saki wani murmushi,Jilani kirjinsa ya dafe ya fado cikin su Malam Sharu shima Murya kasa kasa yace yayi min murmushi wlh sai naji sonsa ni dai na shiga uku barin dakin nan zanyi,shima Alaramma Garzali Yana satar kallon Naila Yana dauke Kai,Naila ta daga Masa gira daya tare da kashe Masa ido,Zuciyarsa ce ta fara bugawa da sauri Kafafunta ya kalla sak irin na mata ya bude baki,abinka da an Dade ba a hadu da mace ba ji yayi kamar ya rungume Jamilu Terror, ai tashi yayi ya fice daga dakin Yana salati a ransa,shi kadai uban zufa ya hada
Yace Ina zan sa kaina yau naji Ina son Namiji,a daren malam Jilani yace saukar Qur'ani ya zama dole, a daren haduwa sukayi kowa ya bude Qur'ani kwana suka yi suna addua Allah ya cire musu son Da namiji Jamilu,Naila tana ta baccinta gefe daya ita hankali kwance ta samu dakin malamai ba ruwanta,su kuwa suna ta surfa addua akan Allah ya tsare su da Jamilu.
Washe gari da safe mazan gidan yarin masu uban yawan masifa Yan matasa dattijai,tsofaffi duk gasu nan iya kallonka da munana da masu kyau duk gasu nan,duk kalan laifinka akwai ubanka a ciki ko wanne da bangarensu, bangaren mata daban na maza daban,haka ranar ziyara sai an gama da maza sannan a bude mata ba Wanda ke haduwa da wani tsakanin mata da maza,gashi Sabo da lalacewar ta kasar mu dakuna sunyi kadan,toilet,komai babu na kirki,haka uniform ma babu sai wata riga da ake bawa Maza lokacin ziyara,sai sutura kayan gida amma basu wuce kala uku ko hudu,haka bangaren matan yawanci basu da bra,wasu Kuma suna da ita,wacce tafi wata karfi ma zata kwacewa wata ko an kawo mata daga gida,Naila dai itace mace daya kwal a bangaren Maza Wanda babu Wanda yasan Hakan har Ma'aikatan kaf a namiji ne Kuma ana zargin Dandaudu ne,Naila bata da ko bokiti ,gashi wai a gidan Yari zata yi gayu.
Yanda take nunawa Dandaudu ne kawai, tana zaune a cikin dakin Malaman tace akwai ruwan zafi? Ya Sheikh bana tsarki da ruwan sanyi sabo da na koma mace ni, na hana kaina amfani da ruwan Sanyi,tana magana tana zuba uban karairaya wai dole Dandaudu ne,gaba daya malaman Nan suka saki baki suna kallon Jamilu duk ya tafi da Imaninsu,cikin rada da tsoro Malam Sharu yace addua bata karbu ba mu sake dukufa wlh, Mallam Garzali ya a hankali ya saci kallon Jamilu sai kuwa suka hada Ido,fari tayi Masa,da sauri ya yayiwa Sharu magana kasa kasa yana yi min fari wallahi,kansa ya sadda kasa duk ya rasa Inda zai sa kansa.
Naila ce ta shiga aika musu da fari tare da dage musu gira,Kasa karatun suka yi,Kamar ruwa ya cinye su ba Wanda yayi motsi,sai zuwa mazan bangaren nasu keyi suna kallonta ana labarin an kawo kyakyawan Dandaudu Dan matashin yaro,kowa yazo sai ya tafi da kaunar Dandaudu Jamilu a ransa sabo da kyau da farin jini irin na Naila,Naila taga suna ta zuwa kallonta ita bata sani ba,tace bayin Allah ruwan zafi nake tambaya zanyi tsarki mu yanda muka koma mata ai mata sai da ruwan zafi harda yin tafi da hannu Irin na Yan Daudu,suka dinga tuntsira mata dariya ganin namiji matashi me kuruciya ta karfi ya koma mace, a dakin malaman ba Wanda ya bata amsa karshe ma kowa Uzurinsa ya fita,Naila tashi tayi tana tafiya tare da zuba hannayenta a aljihun bujen wandonta ta fito
Ko Ina mutane ne lungu da Sako ba masaka tsinke,Naila tace ashe duniya ce guda a gidan Yari,tana zuwa taga uban layin botikai da fanteku harda languna tun na zamanin da,tana zuwa ta dauki botikin wani na roba an cika shi da ruwa ta dauke ta Kara gaba, da tambaya ta samu taga Toilets gasu nan ko wanne ta leka duk an lalata su wasu Kuma Kashi ko Ina dama maza ba tsafta ba wasu,Naila ta rasa inda zata shiga dole sai da ta wanke toilet din sama sama sannan tayi wankan ba sabulu ta, ta daure kirjinta tam tam da yankin Atamfa ta Maida kayanta ta shirya tsaf sannan ta fito ta Maida botikin,wasu shahararrun kartai suka taso zasu yi mata duka Allah ya kawo DanIndo wanda kowa tsoronsa yake a gidan mugu ne na karshe,yana kallon mazan yasan yaran Goje ne,yace me Jamilu ya muku? suka ce ruwa muka ebowa Goje tun safe muke layi kafin muje mu dawo ya dauke yayi wanka,Naila tace ku fadawa Goje din Dan babansa na dauka kayan gomnati ne muna da hakki,dariya wasu suka dinga yi da kyar DanIndo ya kwaci Naila yace ku bari zai zuba masa,wani ya gama buga ruwansa Sabo da zalunci Dan Indo ya dauke ya zuba a bokitin Goje yace kuje,Ya Kalli Jamilu Terror wato Naila kenan yace jeka ka bugawa yaron can wani ruwan
Naila tace bazan buga ba,wani gigitaccen Mari Dan Indo ya hada mata kumatu biyu sai gani akayi Jamilu tuni ya fara buga ruwan tana kuka sai da ta cika botikin sannan Dan Indo yace ware daga nan.
Dan Indo bai taba jin fata me laushin ta Jamilu Dandaudu ba,ya tsaya sai kallon tafin hannunsa yakeyi shima Yana mamaki,Sam ba fatar namiji bace da shi.
Naila tana sakkowa sai ga wani Ma'aikaci ya tari Naila yace kai waye da za a hana Hawa Saman tuka tuka kazo ka hau, uban waye ya aikeka? Naila da taurin Kai take kamar ba ita ke cin duka ba,ta Kalli Ma'aikacin ta nuna kanta da yatsa tace nice Tantiriya Jamilu ko a garinmu haka sunana yake kaina akwai kwari ba a cina da yaki,ma'aikacin ya Kalli Naila an zagaye su ana kallo,yace Zaka ga Tantiriya munga Iyayenka a taurin Kai ma sunyi laushi a nan gidan bare Kai da ka Maida kanka Dandaudu gafalalle, Naila tace banda ni cikakken Tantiri ne ni Ina kallon ku Ina Maida kaina namiji,Kai Ma'aikaci kayi a hankali zan iya tsille ma takashi ato, su kansu ma'aikatan tsoro suke ji,juyawa yayi zai tafi, Naila tace nayi marking dinka sai na sa maka guba,sai na farke Maka takashi,Dani kake zance,ma'aikatan sun Saba da tsagerancin Yan bangaren daurin rai da rai tunda suna gani shine karshen hukuncin,dole ya tafi.
Naila ta fashe da kukan karya tace Allah ka Saka min ni Jamilu Ina ganin rayuwa Yar Takashin ma ban samu ba tunda nazo naki yin farin jini,ana ta kyalkyala dariya,tace Mummy data yi sanadin zuwana gidan nan ya Allah kasa Danta ya mata dukan tsiya watarana.
Akwai Yan Daudu da yawa a gidan Yari da Kuma Yan luwadi wasu ma a gidan suka lalace sabo da rashin mace a kusa, tunda suka ga Jamilu Tantiriya gaba daya sai hadiyar yawu suke gashi kyakyawan gaske komai irin na mace gaba dayansu sai kaunar Naila,har da Wanda ke ciki masu hanu da shuni sai suka fara neman gindin zama wajen Tantiriya Jamilu,Naila a ranta sai dariya take shekawa su sun zaci namiji ne kowa ya kaimu da sonta har Wanda ba Yan luwadi ba.
Rafeeq zaune yake gaban Mahaifiyarsa Mima wacce ke faman kallonsa tana bin Aljihunsa da kallo tana zaro idanuwa tana kallo tace banga Aljihun ya dago ba? Na shiga uku kar dai ace haka kazo hannu yana dukan cinya, Rafeeq ba tare da ya sake cewa komai ba ya jefa hannunsa a aljihu Kudi ya zaro Wanda sun kusa dubu hamsim ya Mika mata,jiki na rawa kamar yau ta fara ganin kudi kamar ba a gidan kudi take ba ,Allah ya maka Albarka wannan waje naka na Shawarma Allah ya karo customers
Sam baka yi kalar me Shawarma ba wlh yaro kamar Dan gidan Salman Khan kalar kudi amma ficika babu,Yan mata sai rububi aljihu ba komai wannan kusan dubu hamsim din wata nawa kayi kana Tarawa? Rafeeq wani takaici ne yake kamashi a duk sanda Yazo gidan iyayensa,mikewa yayi yana Shan kamshi fuskar nan a murtuke da kyar ya iya bude Dan bakinsa yace na wuce ni yana cewa haka ya fice daga daga katafaren Palon Mima din Wanda ya gaji da tsaruwa, compound ya fito motoci ne gasu nan iri iri a gidan masu tsadar gaske gidan ko Ina sojoji ne ke tsaronsa kana gani kasan na babban Soja ne gidan..
Gate aka wangale Khalid babban Da a gidan ya shugo da motarsa lafiyayya,yana yin parking ya fito cikin kakin sojojinsa ya zuba kyau ya nufi wajen Rafeeq dake hanyar fita,Rafeeq Kai dai baza ka canja hali ba wlh kana ganina na shugo zaka tafi ai ka tsaya mu gaisa ko,Rafeeq juyowa yayi da kyar da shegen Iyayinsa ya mikawa Khalid hannu suka gaisa kana gani kasan Yan uwa ne na jini ba karya suna kama sai dai Rafeeq yafi Khalid kyau na gaske,sannan yafi gayu Dan gayu ne shi sumarsa ma askin Yan duniya aka mata,suna gaisawa ya juya yayi tafiyarsa ya bar Khalid a tsaye da mamaki yace yaron nan fa takamarsa ta fara yawa nema yake ya Koma kamar Spark, tsaki yaja ya wuce abinsa.
Shawarma Joint me kyau da shi Wanda ke dauke da katuwar wata rumfa an zuba kujeru da table masu kyau na Passion Wanda Idan mutum na bukatar zama yaci a wajen zai zauna,haka daga ciki ma akwai katon daki ya gaji da alatu Shima ciki kujeru ne da table na Yan gayu na cin abinci ga masu son zama cikin sirri,daga kofar wajen kuma ga hotunan abinda ake siyarwa nan shawarma,burger,chips and chicken da kayan sha Kuma, aikinsa yake yana ajiye Dan littafin Menu karami Wanda ke rubuce da iya abinda ake siyarwa yana bin ko wanne table yana ajiyewa da sauri,sabo da yana da lecture 4 to 5,a hankali wata mota me kyau tayi parking a gabansa da sauri ya barwa yaransa aikin ya koma ciki ya shirya cikin kana nan kaya masu kyan gaske ba karya yayi kyau ya fito rataye da jakarsa ya shiga gaban mota,ko kula abokin nasa baiyi ba,a hankali Abokin yace Rafeeq halina da Kai yanga sai kace masifa magana ma ta gagara wlh har mamaki nake da ake zuwa joint dinka siyen Shawarma Kai da Spark halinku baiyi ba,Spark ma ya fika rainin hankali duk da Yayanmu ne amma shi kake bi wlh Dan wulakanci ne turai ta kwance Masa Kai,mutum kullum ba Rahma ga shegiyar yanga kamar Dan gomna ga bala'i Kuma a gidan ma Spark ba Soja bane kaima haka amma kunfi sojojin ma,kaima ka koyi halinsa sabo da kuna gadara da kyau ko me oho, ka kyale spark yayi ya fika indai kyau ne,gashi da kudi shi idan yayi ba matsala tunda ya fika komai, shi dai Rafeeq ko kala bai ce ba wayarsa ya zaro Samsung yaci gaba da dannawa abinsa,a hankali cikin muryarsa me Dadi ya furta next month zanje Kano,me zaka yi? Ban taba zuwa ba yaron da akace yazo aiki ko ziyara ko me ya sawa Daddy guba an Yanke masa daurin rai da rai,yace kasan lokacin Makaranta sun Kai mu Egyft branch dinsu,so ban San yaron ba ban ma taba ganinsa ba,Islam Abokin Rafeeq yace Kai mene naka a ciki? dama Yan aikin nan Yan iska ne zasu iya gashi ance Dandaudu ne ma,Rafeeq yace Yaya Spark ne zai aikeni can wai yana da ja sabo da yasan Mummy dinsa yasan Halinta,yasan Kuma halin da suke ciki da mijinta Daddy, to me zaka masa Dandaudu na tsani Dandaudu? yace zanje ne nayi masa Yan tambayoyi ance sunansa Naila Hashim naji gidan Jamilu,Islam yace alright amma da mota zaka je? Kasan bani da mota muje ka rakani kawai,Allah ya kaimu no wahala,shi Spark din bazai bamu kudi ba? Yama bamu fa Yana accnt,tun daga haka Islam ne kadai yake labarinsa Rafeeq bai iya magana ba.
Naila tana gidan Yari kwananta biyar taga zalunci iri iri,ma'aikatan ma Idan kayi laifi zasu iya maka duk muguntar da suka ga dama iyakaci Idan ta asibiti ce a kaika asibitin gidan kason,ga wahalar ruwa,sai mutum yayi sati baiyi wanka ba sabo da kasar tamu ba ci gaba,kazanta kadai ya Isa ka kwashi cuta,komai yayi karanci a ciki,ga mutane masu laifi sunyi yawa ba wajen Saka mutane tunda Wanda ya saci akuya ma kaishi ake gidan Yari,a masu kudinmu Babu Wanda zai Kai musu agaji ya gyara musu tuka tuka ko toilet da dakin kwana musamman gomnati wannan hakkinta ne,musamman bangaren maza yafi Muni da kazanta za a hada mutum biyu a sarka daya a daure su ko Ina zasu je tare Idan daya zaiyi Kashi ko fitsari dole agaban daya zaiyi ko mene,Hakan yasa da yawa sun zama Yan gay suna Neman Yan uwansu maza haka matan ma da yawa Neman junansu suke maimakon a samu gyaran Halin sai Kuma a lalace a ciki,harkar daba da rashin gaskiya wasu duk a ciki suke koyowa,rashin kunya,taurin Kai da fitsara iri iri duk koyo akeyi a cikin gidan gyaran hali,Naila tana zaune a jikin wata bishiya sunci aiki sun koshi tun safe suke noma a can wani bangare suna gyara ciyawa,sun hada uban zufa,Basu samu Salama ba sai da suka yi nisa,duk haskenta tayi Dan duhu , jikinsu furu furu,Dan Indo ne ya zauna kusa da ita su ko a jikinsu har kiba ma wasu keyi a ciki,Naila bata San sanda hawaye ya fara zubo mata ba.
Dan Indo ya kalli Jamilu yayi dariya sosai yace ashe dai Jamilu Tantiriya Kai karamin dan iska ne? Da kace baka ji kai Tantiriya ne, Naila tana share hawayenta tace kana gani a haka zan kare rayuwata a wannan masifar wallahi sharri aka min ban aikata niyyar ko kisa ba,DanIndo yace da ka adana kalamanka ba maganin da zan Maka,kawai abinda zan fada Maka tunda baka da karfi sai taurin Kai ka kiyaye yiwa mutane nan rashin kunya,wlh watarana Idan suka gaji zasu karairaya ka su watsar,kayi biyayya,mun fika iskanci,Kai iskancinka na Daudu ne Amma tunda kaga muna musu biyayya to kawai kayi, kana gani dai a gabanka suka sa karfe suka cirewa Hamisu farcen babban yatsa Kuma ko a jikinsu, Naila ta goge hawayenta ba tare da tace komai ba,kafin ta rufe Ido a cikinsu aka zabi shugabanni suna sasu aiki Wanda ya kamata na tsafta da gyaran wajen kamar a makaranta,mazan sun dawo da tsawa da duka sun kora kowanne aiki,Amma Naila kin tashi tayi suka zaneta kuwa Amma ko gezau da uban taurin Kai take,Inda taci Sa'a duka gidan kaunarta suke haka kawai basu San ba gender dinsu daya ba.
Indo ce ta kwala mata Kira da Tantiriya dake yanzu kowa haka yake Kiran Naila da Jamilu Tantiriya domin ita ta radawa kanta sunan gata gata da farin jini Allah ya bata kowa Yana sonta suna daga mata kafa sosai amma bata da kunya ga taurin Kai,ta matsu iyayenta su kawo mata ziyara ko zata samu kayan canjawa da Dan kudin siyen abubuwa,a haka sai da taga dama sannan ta mike ta shiga cikin Yan gidan suka ci gaba da aikinsu amma sun rasa dalili Bata son cudanya da Maza sai ta