Showing 9001 words to 12000 words out of 158722 words

Chapter 4 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

366

tace aka yi min sharri dai sannan ni Kuma ina da gata na ba aiki naje ba,labarin Zaka bamu Muji ko zamu iya wani abu akai,sai lokacin Rafeeq ya dago yana kallonta sabo ya gane labarin nata karya ne ko gaskiya ne,mamaki ya kamashi ganinta kamar mace haka.

Amma kafin ta fara labarin wani kaikayin ciwon sanyinta ya hada ta gaba daya ta rasa inda zata Saka kanta gashi so take ta Sosa gashi maza ne a wajen sannan tana tsoro kar a kamata, a ranta tace Kai uban wa na ajiye wai in Sosa abina,a ranta tace ai da kunya Kuma a gaban maza,Zullo tayi tana daga zaune tare da Jan yaji shiiiiiiiii.......kafarta ta dora kan daya tana mutsu mutsu,taji kaikayi ba sauki dai ta mike tsaye ta sake komawa ta zauna tana so ta Sosa, duk sai kallonta akeyi banda Rafeeq da Islam ba kikawai har ma'aikatan, Naila tace gashi ba a komawa ciki a dawo Kai wannan rashin yanci da yawa yake Susa ma ba dama mutum yayi.

Bakinta ta toshe da sauri ashe maganar a fili ta furta,tunawa tayi a cikin gidan kaso su Kam Babu kunya ba shayi,Islam waya ya daga ya mike ya matsa gefe,ganin Islam ya tashi ta saci kallon Rafeeq tunaninta baya kallonta ta saci kallon mutane taga kowa harkarsa yake

Baki ta tamke kamar me tsotsar alawa tasa hannu a gabanta Saman wando ta haka ta Sosa kadan ta sake satar kallon Rafeeq da mutane ta sake sosawa da karfi,harda lumshe ido taji Kam Salama sai ta manta ma taci gaba da susarta,Rafeeq yana ta kallonta dariya ta cika masa ciki a ransa yace yaron nan bashi da lafiya,dagowa yayi da sauri ta cire hannunta,cikin muryarsa me kasa kasa da gadarar gaske yace me kake sosawa?
Kai mene haka kaikayi?a wajen neman mazan ka kwasowa kanka? ya tambaya, ko kunya ya daga masa Kai a hankali yace ance sanyi ne ya kamani Dan Allah baka taho da Dan wani karfe ba? Wani mugun kallo ya mata Wanda ba Shiri tayi mukus tana tsiri tsiri da Ido

A hankali yace sabo da kana da infection sai ka dinga Susa a gaban kowa baza ka iya hakuri ba,Naila tace a'a wlh bani da shi ya jumbo Yana kaikayi ace bazan Sosa ba kasan kuwa bala'in da nake ji,Kuna da asibiti kaje mana shuru tayi yace karka bata min lokaci ka bamu labarinka,lokacin Islam ya dawo Shima ya zauna yana Sauraren labarin Jamilu,tiryan tiryan ta basu labarinta kaf amma suma binne su tayi ta barsu a namiji ce ita Kuma sun yarda.

Wace Naila

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA

AIDA MAMAN TASNIM
❤️❤️❤️


FREE PAGE


WANNAN NOVEL NAIRA 300 NE


Account number
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank

KATIN MTN
08061929616

'YAN NIGER GA NUMBER
+22790795939



Kar a manta da Sharhi fans please.

Ina godiya gare ku masu godiya da masu addua






AsmaBaffa
[12/4/2023, 2:39 AM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI



Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA
GARE KI❤️
AIDA MAMAN TASNIM


6-10


Page naki ne
AUTARESS




Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx

Ina kuke masu burin suga sun kawata gadajensu da hadaddun bedsheets? Ko Kuma blankets kike nema? Masu aurar da yara ko kannai da ke kanki uwargida indai kitchen utensils kike bukata
To kukanki yazo karshe.kuyi joining group din R&U exclusive kitchen and more
Ku more wa idanun ku da kayan kitchen Yan yayi na gayu da zannuwan gado na kowanne kasa Zaki samu acikin farashi Mai sauki
Kuma Maza Bata barku abaya ba idan Kuna bukatar a hada muku lefe nagani na fada na amarya Kona uwargida wato na fadar kishiya duk Zata hadamuku acikin kwanciyar hankali.idan ma akwatunan kawai kuke bukata duk inkuka tuntubi Rumaisa zaku ganewa idanuwanku
Tana Kano state Kuma Tana tura Kaya kowanne state afadin nageria harma da kasashen da muke makwagtaka dasu
Zaku iya tuntubarta ta wannan number
07034559202





NAILA HASHIM asalin sunanta, Hashimu Dolo asalin Fulani ne dake zaune a yankin Jos,yawan fada tsakanin arna da musulmai ya shafi Fulanin yankin Jos Inda ake musu asarar dabbobi da rayuka,wannan yasa Iyayen Hashimu suka tashi suka shiga Minna Inda Daji ne sosai ko Yan Fulani kafin ka samu gidan wani sai ka Sha wahala,a hankali suka dinga karuwa a dajin,ko wanne bafillace yazo ya samu wajen zama har suka hada ruga guda da matansu da yaransu.

Tunda mahaifin Hashimu suka dawo wannan daji da matarsa basu taba haihuwa ba tsawon rayuwa,suna ta neman magani Ido rufe,sune gidan wannan malami sune can har Allah yasa mahaifiyar Hashim katsam ta samu juna biyu ,suka haifi dansu Hashimu,amma tunda aka haife shi halittarsa take kamar irin gaula gaula haka,irin dolaye kullum bakinsa na dalalar da yawu,tunda ya taso komai na duniya bai iya ba a haka ya girma har ya zama saurayi ya samu ilimin addini sama sama amma dalalar da yawu sai da ya girma sannan ya daina da kyar,Yana da tsafta sosai.

Hashimu lokacin da ya isa aure, neman aure ma kasawa yayi, idan aka samo Masa budurwa tofa sai kunya sai ya gudu ma ya kauracewa gari kullum Yana cikin gonaki,karshe da Mahaifinsa ya gaji sai ya samu abokinsa Sagiru Wanda yake da budurwar yarinya kwaya daya tal Kubra,sai ya nemawa Hashimu aurenta ya Masa gini aka Masa aure,ba Wanda ya zaci wai Hashimu zai iya tsinanawa mace wani Abu amma watanni uku aka ga matarsa da ciki kowa yayi mamaki a dolancin Hashimu ga matarsa da ciki

Matasa suka tasa Hashimu gaba da tsokana ana cewa matar Hashimu ta samu ciki,Ashe Hashimu yasan hanya,mata ma sai gulmar suke a gidan biki suna cewa oh ikon Allah wannan waje ko mahaukaci Yana gane shi wai matar Hashimu Dolo da ciki,lokacin Iyayensa wasu Yan bindiga suka harbesu a hanyarsu ta dawowa daga Jos sunje ziyara,tunda Hashimu ya rasa iyaye sai ya siyar da shanunsa kaf ya tafi birnin kano ya siyi gida a can suka zauna da matarsa Kubra ba uwar sana'ar da yake har suka cinye kudin shanun tas,gadonsa duk ya siyar suka cinye kudin a ciki,ya koma sai dai mutanen unguwa su dinga taimaka musu.

Wahala data ishi Kubra sai iyayenta suka siyar da sa aka bata jari kawai ta fara sana'ar siyar da kayan Miya a gida sannan ta shiga makarantar yaki da jahilci,macece kyakyawa ajin farko fara tas,shi Kuma Dolo Hashimu Yana da Dan duhu amma kadan amma kyakyawa ne sai idonsa tsulun tsulun a ciki Kuma duk dolancine ya Maida shi haka,ita dai Kubra jajirtacciyar macece mace me kamar Maza ga zafin nema,a haka tana karatun Nan bayan ta haifi danta na farko Mohsin kyakyawa fari amma ba can ba sai kyau Kam akwai shi ba karya,tana yin arba'in ta biya waec da Neco ta zana jarabawarta,Kuma data fito tayi kyau sosai.

Lokacin ba wahalar samun school da wuri ta samu college a nan tayi NCE kamar wasa kawai sabo da taga mijinta mutum mutumi ne,lokacin Kuma ta haifo yarta ta biyu sankaceciyar gaske kyakyawa ajin karshen karshe fara karkar da ita tsakanin Naila da Mohsin ya Kai Shekara goma,ranar Suna taci Naila.

Bayan Naila ta cika Shekara Uku a duniya Maman Kubra ta rasu sai babanta Affa ya auri wata matar Sahura me kirki,gasu basu da yara dama yarsu daya Kubra,Affa ya damu ya nace sai an bashi Naila,har ga Allah Kubra Bata so ba amma kawai Hashimu Dolo yace dauketa mana ku tafi na baka ita halak malak,ba dama Kubra ta Hana tunda Ubanta ne.

Affa ya tafi da Naila can Daji rugarsu,Mohsin yayi bakin ciki Yar kanwarsa sun Shaku duk Inda zasu je tare, Naila a ruga ta taso cikin sangarta da gata sai abinda take so,Bata San babu ba Sam,Bata San wahala ba,sai dai an sata a Islamiyya da boko,babu makaranta a dajin amma sabo da gata Affa kullum shi ke kaita makaranta a kekensa can a garin tsalle Wanda basu da nisa da garin kuma babban gari ne, sai ya kaita kuma ya dakko ta da kansa a keke,ga makarantar private ce,Naila Allah yayi mata basira da hazaka har ta gama primary ta shiga secondary tana Jin turanci sosai,ga wani bature yazo rugarsu yawon bude Ido a garin yake zaune Naila ta zama kawarsa kullum shi ke koya mata turanci har ta kusa gama Secondary dinta sannan baturen ya koma kasarsa.

Naila kaf kauyen babu me kyawunya sannan babu macen data kaita shekaru a budurwa duk da wuri ake aurar dasu,Naila har cewa suke ta tsufa ba miji sai boko,duk garin babu me taurin kanta da rashin ji,tana zuwa kiwo,tana zuwa Rafi,tana Hawa sama,duk wani Abu da akeyi a kauyen itace ta daya indai ba makaranta sai ta yi, sai rashin jin masifa a gari,Sam a kauyen karatunta baya mata amfani, amma bata da karfi,ita kullum sai dai a bita sai dai ta Mulki mutane ba dai a mulketa ba haka Allah yayita da son Mulki,duk Inda ta shiga sai ta zama shugaba, sannan tafi Jin fulatanci akan Hausa duk da tana Jin hausar Kuma tana yi,har tallan fura take yi idan babu school.

Tare da mazan dajin suke yawo da wasa,yara kanana gasu Nan sai jahilci yasa ba abinda basa aikatawa,suna caca,suna shaye shaye gashi suna neman mata,sai kani ya nemi matar wa,Yaya ya nemi matar kaninsa, haka uba ya nemi matar dansa,Da ya nemi matar uba,gashi Nan jahilci iri iri sana'arsu ce a garin, duk karatun da Naila keyi Inda kasan bata San A ba duk iskancin da akeyi a garin tana ciki, banda bin Maza su dama mazan garin basa bin budurwa sai dai matan aure suke Zinar su,budurwa ta Sha,manya da yara ba maganar iskanci da batsa da basa yi.

Affa shahararren me Bada maganin karfin Maza da maganin matan da basa haihuwa a kauyen,daga gari gari ma zuwa ake wajensa,duk Wanda gabansa baya aiki,ko baya biyawa iyalinsa bukata to azo wajensa Yana da magani sadidan,dai daikune zasu zo basu dace ba.

Shi yasa da yaga Naila jajirtacciya ce sai ya koya mata komai ba abinda bata sani ba na maganin sirrrin komai ta sani,watarana itace take sallamar mutane idan sunzo sai yace ta gansu ta basu magani, Kubra wato Umman su Naila Bata ji dadin koyawa Naila wannan Bada maganin ba na karfin Maza ai lalata ya macene a matsayin Naila yarinya budurwa amma ba yanda zata yi,Mohsin ma bai so ba amma shi Baban Naila Dolo ba ruwansa shi ai anyi dai dai cewa ma yake ai gwara ta koyi sana'a.

Umma da su Mohsin
Da kannen Naila Hidaya,Aslam,da Zarah idan suka je garin Naila ko ta kansu bata bi kamar ba Yan uwanta ba,ita bata so ma suzo tunda taji suna cewa zasu dauketa a maidata birni ganin ta kangare da yawa shi kanshi Affan tafi karfinsa bai isa da ita ba shi yasa ya amince su dauketa din.

Naila fuskarta me Dan Fadi ce me dauke da hanci dan cas baiyi tsayi can ba Kuma ba gajere ba normal hanci ne da ita me masifar kyau,idanuwanta Dara Dara masu kyau,gata da gashi amma irin na Fulani yawanci ja ne ba Baki wuluk ba gashinta jaja dashi kamar na akuya duhun nasa kadan ne ba baki wuluk ba,gata da saje, doguwa ce me Dan kauri ba ramammiya ba Kuma ba me kiba ba,tana da masifar kyan diri gata fara da ita.

Mohsin kuwa School of Nursing yayi Kuma ya samu aiki a Aminu Kano,yayi gidansa me kyau na matasa masu rufin asiri ya auri budurwarsa da suka Dade suna soyayya Hanan kenan Yar gidan Dankoli,Yar talakawa ce futuk a birnin,bayan ya nutsu Yana aiki Yana Dan zuwa kasuwar kwari Yana business na shadda, a haka ya samu ya canjawa iyayensa gida me Dan kyau ya sake gyara musu shi sosai, kayan abinci duk wata shine ke kawowa a gidan,haka kannensa shi da Kubra ke daukan nauyin komai nasu har makaranta,shima Hashimu mutanen unguwa suna ta Masa fada ya samu sana'a,cikin ikon Allah an kawo turawa suna aikin wani gidan ruwa da titin kwalta sai suka ebi masu gadin man petir dinsu na aiki sabo da yanda mutane ke sace musu,cikinsu harda Hashimu shine ya daina zaman banza ya samu gadi.


Ranar da Naila ta fara bin Yan caca a garin,mata da Maza suke haduwa sai su raba dare suna caca amma bai wuce a sa Dari biyu Dari biyar baya wuce haka,tunda Affa ya ganta a ciki ransa ya Baci,ya nemi waya ya kira yarsa yace azo a tafi da Naila abin ya fara yawa.

lokacin ta zana jarabawa sun gama Neco,Naila macece me son gwaninta,tana so tayi abinda babu Wanda ya taba yinsa,ranar da Naila ta shirya saka Gagarumar caca a garin wacce babu irinta sai ta sanar ta sa Budurcinta a caca ana gayyatar kowa duk Wanda yaci ga Naila kyauta zai bare a leda,Kuma a ranta karya takeyi kawai tayi ne Dan ta Bata musu lokaci ta gudu, har shela tasa aka yi a garin, matasan,dattijai kusan kowa dake kauyen Sai da ya shiga cikin cacar har Wanda basa caca, tana so tayi abinda wani baita yi ba,ranar Kuma aka yi da yamma an fara caca Naila ta rike sandar kiwonta ta wani coge a jiki a gefe tana kallo,ana ta buga caca sai aka samu wani Dattijo Malam Ya'u ya lashe gasa, Naila tana ganin haka ta sheke da dariya tace karya nake dama nima caca nayi muku,kowa yace Bata isa ba.
Malam Ya'u da ya lashe gasa ya gigice yace karya ne wlh sai an bani hakkina,Naila ta arce da gudun tsiya da Sandarta

Ana haka kawai sai ga Mohsin yazo a machine dinsa lifan sabo dal yayi parking a gabanta,tana ganinsa bata San ma daukanta yazo yi ba tuni ya karbo kayanta a wajen Affa ya karaso wajen hanyar Inda suke cacarsu,Malam Ya'u yace wlh zamu hadu duk Inda na ganki sai na nemi hakkina, Mohsin kiranta yayi ta taho tana son Mohsin sosai,sai yace sabon machine na siya hau na danaki kiji,zata hau baya yace gaba zaki hau fa,dole ta hau gabansa,tace Yaya Dana ni naji dadi kayi sauri, ya sata a gabansa yasan a baya zata iya dirga ta fece bata Jin magana tana Hawa kawai sai gani tayi an hau babban kwalta sai birni,tayi kuka tayi ihu ta kira Affa yafi dubu amma sai da ya kawota birni dama bata taba zuwa ba tunda aka kaita can,Malam Ya'u yace wlh ko za a Shekara dubu indai Ina raye idona idon Tantiriya sai na karbi hakkina.

Sanda tazo sun Sha wahala da ita da kuka da zagi da masifa sai ta koma kauye,gashi Anki yarda har ta hakura ta saki ranta,daga zuwanta ta samu samari amma duk ta kore su wai lallai sai sunyi bleaching sun koma farare.

Umma Kubra tana da Kawa Hajiya Tagwadas a layinsu,sai watarana Tagwadas tazo tace tunda Naila ta Dan kusa wata guda a gida ta bata aronta zata rakata Abuja gidan Yan uwanta su gaisa, masu kudi ne,daga can ma watakil Naila ta samo miji,ai dama Kubra sai murna taji masu kudi tace ba komai zata rakaki,Naila tunda taji wai zata yi rakiya Abuja har sati biyu tace baza taje ba,Mohsin ma yace gaskiya a'a amma Ummansu Kubra ta nace ita zata tsine musu idan Naila bata je ba,dole Mohsin ya hakura yace Naila taje,shine Naila ta shirya yau zasu tafi,Umma ta shiga kwalawa kira

Umma....Umma....yawu cike a bakin wacce aka kira da Umma ta fito tace Naila tafiyar ce ne? Naila tace ae Umma daga kauye sai Abuja tunda daga can zamu wuce kince na biya na gaisar da Affa ko? Ai gwara ki bi Hajiya Tagwadas kije Abujar Nan wallahi wannan dolon uban naku ba komai yake tsinanawa ba shima sai dai a bashi,Naila tace Dan Allah Umma ki daina yiwa Abba haka bai dace ba Kuma a gaban mu haba wannan fa yawa kike Umma.

Umma share Naila tayi taci gaba da magana idan kinje Abuja ki bude idonki ki gano hanyar samun kudi ko kanwarki ma Hidaya kizo ki jata karki biyewa babban yayanku Mohsin da shegiyar bokon nan marar amfani,Ina boko Taga amfani a kasar Nan ka gama duk karatunka mutumin da ko primary Bai je ba bakauye sune masu kudin kazo wai kana neman aiki a karkashinsa sabo....yawun da ya sake cika mata baki ta zubar tace jeki Allah ya tsare ki kyale su Mohsin kuje kauye ku gaida ubana ki wuce can garin kudi Abuja garin Alhazawa,Naila kyakyawar gaske ajin farko tayi dariya tace maganin da Affa ya koya min shi zan Kara koyowa gaskiya naje da sana'ata Abuja,tunda a nan Yaya Mohsin ya hanani Bada magani,Umma tace ni kaina bana son wannan sana'ar Ina mace Ina siyar da maganin karfin Maza,Naila tace sai ni wlh burina kenan na dinga gyarawa mata mazajensu Ina fixing din wacce ta samu matsala in ta kama ma na kalla,Harara Umma ta balla mata tace haka na muku tarbiyya ki zama me class ai gwara in kinje can ki dinga gayu kina samo alhazawa masu kudi kina cin kudinsu,Baki Naila ta tabe tace nidai gwara na samu halak dina tallan maganin karfin Maza tunda Ina da nasibi Akai kina ganin awwalu matarsa bata taba haihuwa ba amma da na bashi maganina ya warke yanzu yaransa biyu a kauye.

Sannan nan tsohon Nan Tafida abokin Affa da zai Kara amarya ni na tsumashi ki duba tsufansa amma sai da na Masa garanbawul ya Mike,ga wannan Dan lukutin Alhaji shehu,Allah ya rabamu da Maza Yan lukutaye Dan Ina Jin kunyarki ne Umma da na Baki labari,Umma wacce ta zubawa Naila Ido baki bude tace ke fa halina Dake bakya Jin magana ba Wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login