Showing 69001 words to 72000 words out of 158722 words
Chapter 24 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
cikin talauci ko za a samu su farfado daga talaucin.
Kawai iyaye sabo da talauci hauka ne ba bincike ba komai suka barta ta taho ita kadai gidan su Beauty, ranar Kuma Naila suka karbo dinkunanta,Chikar gayu tayi mamaki ganin me kama da Jamilu mace,Sai da Beauty ta bata labari,Chikar gayu ta dinga shekawa Beauty dariya tace dama na fada miki kika ki yarda,harda kukan soyayya ai gashi Nan,Beauty tace kawai ta bani tausayi da naji labarinta shi yasa na dage zan taimaketa,Naila tana wajen tace a'a a'a ni ba a taimakona ke kiyayi Tantiriya wlh a gidan Maza fa na zauna Dan kin bada Gundunmowa shine zaki ce zaki ce taimakona kike,bara nazo ko maula? shawara kika kawo fa,Chikar gayu tana kallonsu tace to yanzu Munji magana ta wuce a fada min aikina, Beauty tace wallahi Naila kin Allah gareta amma ba komai,Naila tace wannan fa yiwa kaine kika sani ni me zan miki gaba,Chikar gayu tace ku bani aiki na naji please,Beauty labarin Naila ta kwashe ta bata da Kuma aikinta gidan Mima zata je a matsayin Yar aiki kawai ta dakko sirrinsu taji labarinsu shike nan aikin?
Naila tace Wanda ya miki iskanci ki koya Masa hankali ki tabbatar Yan gidan idan basu da tarbiyya to ki koya musu ita kin gane ai,Chikar gayu tace anzo Inda nafi kwazo bawa duk wani marar tarbiyya to ya koma me tarbiyya zan basu tarbiyya.Naila tace an gama zamu dinga waya kina can gidan ni Kuma Ina gidan su Beauty na Abuja zan kula da bangaren Dan Mummy Ashraf kenan,zanci uwarsa daidai gwargwado sai na hada Masa bomb,bala'i,tuggu da sharri na,Ke Kuma Beauty abinda ya kama na kudi kawai ki dinga samo mana,Bafa kyauta ba yawwa bashi kike bani ki dinga rubutawa Spark zai biyaki,ko a Ina idan bukatar kudi ta taso to kawai ki ranto min bashi na dauka a wuyana Spark zai biya karki ji komai nasan dole zai kwakwulo gidanmu za a bashi number ta shike nan zamu hadu a Abuja idan ta kama ma kiji an daura aure ko irin na Yan India ne yanda suke zaga Abu ana mangale.... mangale....mangale....Kuma wlh bazan ce NAHI ba.
Chikar gayu tace ai wlh karki ce Nahi wlh ki aure shi kawai kuyi choreliye dinku a turaka,Naila tace ai har chori merii sai mun yi,Beauty tace ku hada da Tere liye Naila yafi dadi, Shewa suka yi.
Spark kuwa tunda ya koma gidansa yaki zuwa gidan kowa har Mummy din yaci gaba da Uzurinsa,sai da yayi settling komai nasa a wajen aiki sannan yace ni dana daura Shirin aure Ina naga ta zama,Jamilata tana jirana,zan ajiye sarakan bani bani mata,amma Kuma Yana ta kiran number Naila ba dare ba rana shuru,wata Yar karamar hauka ya fara da yaji yayi sati guda Yana kiranta tun wayar tana ringing har ta daina,Bai San wayar Naila ta fada ramin bulo ba wajen haura katanga,har chaji ya kare ta kashe kanta.
Spark yau gidan Mummy ya fara zuwa,Yana shiga Palo yaji kida na tashi ta tara yaran mata kawaye suna ta Shan shisha a palon duk babu suturar arziki a jikinsu,Mummy ta saka wani mini skert da Yar riga me siririn hannu gata tumbur sai katon ciki,samanta sai kayan nono yayi dangangan daga kasa Kuma bata da kibar,Spark Yana kallon Mummy a ransa yace Ashe haka mummy take da mummunar kama gaskiya Alhaji Aliyu yayi hakuri wai wai samodara,a fili Kuma iya sallamarsa basu ji ba sai da ya shiga ciki,Mummy wai ita wayayya ta fito da gudu subu.. subu.. My Son Oyoyo zata rungume shi, Spark ya matsa da sauri ta rungumi iska,saura kadan matan Dake palon su fashe da dariya sai boye dariyarsu suke yi,amma spark kallonsa suke kamar mayu kowacce tana so ya kyasa,kamshinsa duk ya cika palon,Mummy hararar Spark tayi tace baka da kirki wlh na tara friends a gidan Mima anyi girki dangi an cika amma kaki zuwa haba Spark murna fa za a tayaka ka fita daga masifa,Spark dai Yana jinta yace Ina yini ya kuke ai duk na ganku a kotu mun gaisa mene za a Tara min mutane sai kowa yasan naje prison,au kaifa baka San arziki ba Spark murna fa za a tayaka,na hutar daku kowa tace Allah ya tsare gaba amma sai an wani yi min girki da yunwa aka ce muku na dawo?ni dai mun shiga uku da wannan yaro wlh wani auren za a Nemo ayi Maka ko kayi hankali,ai Mima ta shaka dama tace wlh wannan karon da kanta zata samo Maka matar aure,Spark yace tab.... ya juya yayi ficewarsa.
Gidan Mima driver ya kaishi Yana zuwa Papa da Mima suka sashi gaba da fada,Yan uwa duk sunzo suna gaida shi Yaya Spark ya zo yau,Mima tace ka fitar da mace mun gaji da iskancinka ka raina kowa ai gwara a samu me mana maganinka,Dan iskanci ace wai namiji kake so a gidan yari wallahi bazan lamunci wannan ba,ko ka kawo matar aure ko Kuma na zabo Maka Kuma wallahi idan kace baka so ban yafe Maka ba,Spark keyarsa ya sosa,tace wato na Fadi karya ko? dama haka yake musu idan bazai iya Musa abuba to Yana Sosa keya su sun san me yake nufi Bai amince ba,Papa yace to wallahi ko kaki ko kaso idan nine ubanka sai na daura Maka aure da matar da zamu zaba Maka ko a dangi ko a bare,zan Gani waye ya haifeka,marar mutunci ka Maida mu shashashu,Spark ya Sosa keya again,Mima ta make Masa hannu,mikewa yayi zai tafi Papa yace wlh zan iya sawa a Kai min Kai guard room sojoji su casa min Kai tunda baka da mutunci,ko Kai ka kawo kanka duniya? Spark ya daga yatsa daya sama wai Allah ne,Salati Mima ta saki,sai lokacin Spark yace kije Mima kiyiwa Mummy fada ta zama Samodara wlh ba kyan gani Kinga kece yayarta kije ki fada mata gaskiya ta gyara Halayenta sai kace basamudiya ni ban taba sanin haka take ba sai yau,Allah dai yasa ba nononta na Sha ba,Mima tace uwarka ce dai Ina yayeka na bata Kai ta raineka Kuma tafi kowa sonka,Spark ya makale kafada wai a'a,ajiyar zuciya ya sauke yace ai tunda sai da aka yayeni ai da sauki, hararsa Papa yayi ya juya ya fice tare da cewa sai wani Jikon.
Yana fita Mima tace nidai na shiga uku duk an rabani da yarana basa kaunata basa Jin maganata duk sun kangare ba Wanda zan fadawa yaji tsakanin Spark,Rafeeq da Misam, Papa yace ni nace ki rabawa Yan uwanki tunda kinyi dan Allah ki hakura ba dadi irin haka kayi kyauta Kuma ka dawo kana zobe ladanka.
Spark dare da rana waya na hannunsa Yana gwada kira,gajiya yayi ya fara neman number wasu na gidan Yari amma abin haushi ba number Wanda ya karba a gidan yari,gashi abin haushin bai da number kowa na Yan uwan Naila,ya gama sakankancewa shine Nan zai fitar da ita ai ga wayarta ta isa komai,shi yasa bai ma tsaya wani sanin a wacce unguwa gidan su Naila suke ba,a fili ya furta zanje gidan yarin ai wajenta da kaina naji lafiya,Dan wulakanci ko ta nemeni wato na tafi ta daina sona ma ai shike nan ya mata kyau.
Ni Jamilu zata manta Dani ni Naila zata share.
Spark ya rasa Inda zai sa kansa ya rasa sukuni kwata kwata.
Naila kuwa ta Dan koyi mota amma hannu bai fada ba haka ta hakura tace Spark yaki samuwa a waya duk number Dana hada wrong mu tafi gobe Abuja ko Allah zai hadani dashi kafin naci uban Ashraf.
Spark shima yace gobe ya kamata na tafi Kano gidan yari kawai idan ma maidani za ayi ciki gwara a Maida ni na sake sabon haka foundation a zuciyarta ya zanyi,Allah yasa ba Foundation din Toka na gina ba.
Washe gari da wuri Beauty ta Kai su Naila tasha suka shiga motar Abuja,ita Kuma ta koma gida,Spark Kuma da safe da wuri ya bi flight sai Kano Yana murna zaiga Jamilunsa har nishadi yake yana wani latsa waya anci shegen wankan shadda sky tana kyalli,gashin Nan yaci gyara,Naila kuwa a mota tana ta zazzagin Mummy tana fadawa Chikar gayu halin Mummy, Chikar gayu tace Yar shegiya sai na kulla mata bakin ciki.
Naila tace da shegen danta Ashraf ai gani nan zuwa na dinga bibiyar Mummy kenan har sai na ganshi Dan ubansa.
Har akaje zagin Ashraf suke ta fama ita da Chikar gayu,suna sauka Naila tace yawwa Mummy Allah ya dawo da Tantiriya iskanci salo salo shafi shafi sai naga karshenki,yanzu a Yar wanka zan fito Yar masu kudi Yar kolabo,zaki ga tsiya,Jamilu is back,Chikar gayu tace stoci sun sauka,eftoci sun sauka,Naila ta dauki jaka tayi gaba Chikar gayu ta binta a baya tana mata wakar Star na cikin India Singham....dararam...dararam...su da kansu suka yi dariya.
NA GAMA FREE PAGE
END OF FREE PAGE
300 ne 1,2 &3
Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger
+22790795939
Hey lovelies
Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?
Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?
Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?
Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?
Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din
https://wa.link/49vn47
AsmaBaffa
[12/13/2023, 8:25 PM] AsmaBaffa: PAID GROUP
ACCNT NO
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK
KATIN MTN
08061929616
YAN NIGER
+22790795939
🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI
BOOK 1
46-50
Official
By
AsmaBaffa
Sadaukarwa gare ki
AIDA MAMAN TASNIM
Page naku ne
Maman Afrah
Hajjafatty
Oummu Twins
Umu Afrah
My Num
Mom Twins
Ruky
Masu audio ban yarda a juya min novel zuwa audio ba Dan Allah.
Hey lovelies
Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?
Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?
Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?
Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?
Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din
https://wa.link/49vn47
Direct gidan da Beauty ta basu address aka kaisu dake tayiwa masu gadi da kula da gidan magana suna knocking aka bude musu suka shiga har ciki aka musu iso,gidane na gaske part uku,ko Ina ya hadu sai kallo suke yi suka dauki daki daya su biyu,Beauty me dafa abinci wata yare Sheyi ta kira tace taje gidan anyi baki zata ci gaba da yin abinci,Sheyi sai gata nan da nan,Naila tace amma gidan nan ya hadu gaskiya Beauty suna da kudi wai dankari,Chikar gayu tace Allah ya azurtamu Ameen.
Wanka Chikar gayu ta shiga tana fitowa Naila ma ta shiga tayi wanka suka fito suka shirya cikin kaya masu sauki sauki,Sheyi tana ta girki sai kamshi ke tashi,Naila tace Ina so na koyi girke girke na gargajiya dana zamani amma bani da lokaci,yanzu idan Spark ya aure ni me zance da shi? Chikar gayu tace wlh tun wuri ki koyi girki da zaman nan haka, me kike yi baki iya ba ai kuwa zaki ji kunya,Naila tace ai yanzu na dinga dan lekawa kitchen wannan Sheyi din ta dinga koya min ko zan iya.
Ai kuwa lokacin Naila ta shiga kitchen,tayiwa Sheyi magana da turanci Ashe Sheyi ta iya Hausa ta gaske,Naila tace to maganar gaskiya Sheyi Nan da kika ganni hotiho ce,ta gina bata shiga bace ni domin kuwa ba uwar dana iya na girki gashi na samu mijin aure,ki taimaka Sheyi ki koya min su Amala irin taku da Sakwara,da miyar Ugu yake ko ogu oho muku,Sheyi da Ogbono Soup me yauki da dandanon sabulu sabulu haka,Sheyi tace Ogbno soup ce me dandanon Sabulun? Naila tace haka take mana miyar,da banku,miyar Egusi da sauran su,Sheyi tace ba matsala zan koya miki sosai,Naila tace na gode.
Kamar abin arziki Naila tace ke Yoruba ce? Sheyi tace ae kina Kashi a leda ai ko? to gaskiya ki dinga tsaftacce muhallinki,Sheyi tace ai mun waye tuni wannan sai na kauye,Naila tace haba ko ku fa amma ododuwa ku dinga tafka Kashi a leda ba tsari ku canja hali wlh,abinda kuke yi bakwa kyautawa a kasar irin Nija Mama Africa uwar Africa gaba daya,yanzu dai ki koya min girkinki iri iri,Sheyi tace karki damu kyakyawa,Naila tace Allah me kika ce kyakyawa? Yes nah Sheyi ta sake tabbatarwa,Ya kika ga saurayina zai yaba? Sheyi tace ai ko waye shi karya ne ace bai yaba ba, Naila ta tsaya tana kallon girkin Sheyi tace Spark zan ci kudinka gani nan bisa kansu Ina iyo, Naila ficewa tayi ta tafi zaga cikin gidan tana Shan kallon haduwa,Chikar gayu ta Gani tayi waje ta fice,Naila tace halina da Chikar gayu rashin daraja gidan ubanwa zata je,kafin ta rufe baki sai ga Chikar gayu ta dawo,Naila tace Ina kika je? tace yawu naje na tofar wannan gidan ai yafi gaban a tofar Masa da yawu ko a toilet,Naila tace ke anya kuwa a birni kika girma,duk kyan gida Dan ubansa ki tofar da yawunki Inda kika ga dama amma banda gidan Spark,duk shegen da ya tofar min da yawu ko na juna biyu ne bazai Kara zuwa gidana ba,Chikar gayu ce tace zo muje mu Sha shayin Wiwi,Ido Naila ta zaro tace iskancina bana shaye shaye bane,a gidan yarin kika koyi Sha? Chikar gayu tace ae wasu ne suke dafa mana ta Katanga ake cillo mana da bushashen ganyen Wiwi muna dafa shayi,Naila tace baki da hankali Chikar gayu,kina mace wannan ai na Maza ne,Dan Allah mu Sam me zaku dinga kwaikwayo Kuna koya a rayuwa, Chikar gayu tace iyye ke wata ta kirki ce kin gwamitsa da kartai ba gwara mu ba,Naila tace Chikar gayu ki kiyayeni aiki na kawoki ki min in kin gama Spark zai biya kiyi abinda ya dace za a biyaki,Chikar gayu tayi dariya tace cinikin biri a sama,dariya suka yi Naila ta furta gaskiya beauty tsakani da Allah tana shanawa Bata da Yaya bata da kani,Chikar gayu tana ji tace yo ai ni da babanta ma zai so ni duk katon cikinsa tarairayar kayana zanyi, Naila ta sheke da dariya,Chikar gayu tace wlh tumbin Baban Beauty bala'i wai gashi da cin tsiya yazo mana visiting watarana Kinga yanda yake cin abinci kamar wani zai kwace kamar ba me kudi ba, inda kisan kura, Naila tace ni bama haka ba sai hakoransa na tsakiya daya cire fafaroma, hakora dai suka fice yo ai ba daya bane biyu ne ko uku ya Ilahi nace da kudinsa ya sa na roba mana,Zo Kiga Beauty yanda take kuka tana ce Masa Daddy ni ka saka hakora wlh idan zaka ce s din nan dariya kake bani,Naila tace ke Chikar gayu da munafunci,to Kuma mu ai kowa kallonsa muke tsaf, ko zaren dinkin shaddar mutum ma sai mun kalla.
Palo suka koma ta zauna Chikar gayu taje ta dafa shayinta na Wiwi ta dawo da abinta a cup,Naila tace shedan yau aiki zaibi ta kanka Chikar gayu kiyi Bismillah kafin Kisha shayin Wiwi din nan tunda shedan komai za aci sai yazo ya tsoma baki, Maza ki Masa bakin ciki kar ya Sha miki dadi,Chikar gayu tayi Bismillah ta fara kurba tace ai da ta hayakin nake Sha bazan Bismillah ba zan fara zuka sabo da shima shedan ya zooka ya shake a makoshi.
Chika tana zuka Naila ta kwace ta hankade keyar Chikar gayu tace ke a gidan yarin har wiwi kika koyo sha? Da Allah ku dinga sanin abin kwaikwayo,mene wani Wiwi kina mace dan Allah ki bari ki gama min aiki na lafiya idan yaso daga baya ai Kya Sha abarki,taje ta zubar,Abinci suka ci sannan suka kwanta suna hutawa.
Zuwa dare Sheyi ta Dora girki ta kira Naila tazo ta koya Naila ta shugo kitchen,tukunyar ta leka tace yawwa ai na gane wannan girkin miyar Egusi ce ko zamu yi,yawwa Sheyi idan kika wanke namanki sai ki watsa a tukunya Yana tafarfasa Yana zabalbala sai ki yanka albasa Sheyi ki barbada curry da Maggi,Maggi ki samu me karfi yanda zai bada dandano,ki dakko manjanki idan ya daskare ma ba matsala duk daya Sheyi.....Sheyi ce ta tadakatar da Naila tace ni nake koya miki ne ko ke kike koya min? Naila tace kece mana ai practical nake,Sheyi tace ki tsaya ki koyi Abu idan kinki ke zaki ji kunya a gidan miji,Naila tace Allah ba yasa ba bakinki ya biki, yanzu na tsaya nuna min,Ehem haka zaki ce Yan mata,Sheyi ta shiga koyawa Naila girki har suka gama tare Naila ta gane yanda zata yin miyar da tuwo ko Sakwara ko Amala etc.
Chikar gayu tana Palo tana kallon tashar wakokin Nija,a haka Naila ta dawo ta sameta ta zauna tare da yin shuru ta lumshe Ido tana Jin wakar tace na Lula tunanin Spark gamu can mun fito daga mota mun shiga shopping mall Yana rike da hannuna,gamu can na rakashi Office...muna soyewa a cikin Office,ya dannawa kofar key, yasa key Chikar gayu,gamu can ya kaini awon ciki asibiti mum fito a hadaddiyar mota,ya tafi dani aikin hajji,Gani ga ka'abah,daga can mun wuce America,laaaa snow.....na haihu a can mace na samu,Chikar gayu tana kallonta ta rufe Ido wai tunani take yi,daga Jin kida sai haihuwa Kuma,Naila tace baza ki gane ba,ni nasan me nake ji na rashin Spark Ina zan ganshi?