Showing 132001 words to 135000 words out of 158722 words

Chapter 45 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

388

cikin dadi ba wani takobi,Nurse tace ai Kai zaka aikata Spark banyi mamaki ba,idan ka gama da ita ai ka rasa Kuma,bazan rasa ba inshaallah,ku likitoci kullum sai mugun fata,sanda Naje nayi aure na da wa nayi shawara shike nan ban isa nayi komai ba sai a dawo ana damuna.

Su Goggo dai sai da suka tabbatar an siyo magani sannan suka yi sallama da Naila zasu tafi gida Kuma,Naila ta bawa su Rayya powder da jambaki da sabulai na kwalliya cikin na lefe ta eba,ta bawa su Goggo ma suka ce baza su karba ba suje su kwashe mata kaya dama kawaye ake bawa kawai.
Rakasu tayi har mota suka tafi,daga can Spark yasa cikin cousin dinsa yace ya Maida su gida na Kano su kawayen Umma ne sun waye a sasu a jirgi zuwa Kano,su Kuma na riga sunfi kusa da Jos a sasu a na Jos ya rakasu har kauyensu sannan ya dawo,Yana murna zai samu kudi yayi yanda ake so kuwa.

Naila da kyar ta koma sama tayi wanka ta kalkale ko Ina a jikinta ta fito ta shirya a hankali ta saka atamfa half boubou wacce gaba yafi bayan tsayi da skirt,ba karamin kyau tayi ba,tayi daurin dankwalinta me kyau Wanda shima daurin koyo take faman yi kullum a waya iri iri,tana da basira shi yasa take iya nadawa kanta.
Tana shafa turare ya shugo bedroom din,Nan take ta koma kalar tausayi dan kar ma Spark ya ganta normal,abincin da Mummy ta kawo ya shugo musu da shi yasan fitar ma matsala ce a wajenta.

A baya idan ya Kalli Naila sai yaga tana Jin dadi amma yau sai yaga ta dauke Kai da sauri duk ta diriri ce ta fara soshe soshe kamar me kaikayin jiki,yace wai me nayi ne? Naila tace wa ta nuna kanta tace ni a'a ba abinda kayi,kalle ni to hannayenta ta hade waje daya ba tare da ta kalle shi ba tace to ni da na kalle ka Kuma sau nawa Kuma ko a prison ai na kalleka da yawa tayi dariyar dole Kuma duk Bata kallonsa sai kallan gefe da gefe take,hannayenta ya ruko a hankali,idon Naila ya ciko da kwalla,yace mene ne? Ko Kari kike so ne? Kai yanzu idan nace ka Kara sai ka Kara yi?

Wa yaki dadi da gudu ma zanzo,Naila shuru tayi tare da canja zancen tace ni dama gidanku ka kaini,gidan Mummy? gidanku na asali gidan Mima naga da yara kannen ku da yawa sai ka kaini yau ma na yini mu Saba da su sosai,Spark ya gano wayon Naila, yace ni ba gidanmu bane,ko ance miki ni gidanmu ne ban taba kwana ciki ba,to kira Chikar Gayu tazo ,tace baza ta zo ba sai yamma, Gani na isheki nima ai Chikin gayu ne idan ita Chikar gayu ce to ai nima Chikin gayu ne,zaki sa ma na kulle gidan gaba daya,shuru tayi ya dakko ta ya Maida ta gefen bed din suka zauna ya hada musu tea da kayan soye soyen a Baki yake bata har suka koshi,ya kwashe komai ya Kai kitchen masu aiki sunzo suna ta gyara gidan ko Ina, shine ya gyara bedroom din ya samu har ta fara bacci,tashinta yayi da kiss a baki,ture shi tayi da sauri tana harararsa, yace makwaftanmu sunzo gasu can sun Kai su biyar.

Naila jiki ba kuzari ta mike tace ya zanyi yanzu tafiyar ma da kyar nake yi kana gani ga mutane kowa ya gani sai ya gane sabo da Allah wannan abin kunya Ina zan kaishi,Spark yace ni tafiyar ma birgeni take yi wlh sai naji kamar sake yi nake yi,taso na dauke ki,Zasu ce bamu da kunya,ai gwara suce bamu da kunya akan a Ganki kamar wata Yar kaciya Kuma da gefe daya fa kike tafiya,Spark daukanta yayi cak ya fice da ita Yana mata rada a kunne,tana wutsil wutsil da kafafu,har Palo ya kawota ya ajiyeta a kujera sannan yace bata min lokaci zata yi na dakko muku ita,Yan layin ne dukkansu sun San Spark sabo da shi Spark duk Inda ya shiga ana zama da shi lfy duk Yana zuwa suna gaisawa da makwaftan sa,sabanin wasu suzo unguwa babu Wanda suke kulawa sabo da suna da shi,babu kyakyawar mu'amula da mutane,ba abinda zai faru na jaje mutum yaje ko na farin ciki yaje,ko Kuma Ta'aziyya,wani maigidan ma sai makwafcinsa ya rasu bai sani ba,baya kula kowa ya fita da sassafe ya dawo da dare bai ma San me ake ciki ba a unguwa,wani iyalan sa ma bazai bari suyi harka da kowa ba,wani abin kuma idan ya same ka kafin ma Dan uwanka yazo makwafcinka yayi Maka shi,shi yasa Spark Yana zuwa duk abinda ya faru har gudun muwa yana bayarwa komai kudin mutum.

Yaran layin indai yaga wasu ko bai sansu ba Yana basu kudin school sai yayi ta rabawa yara alawa da kudi,duk sun San Spark matan ma da basu sanshi ba sun San sunansa a baki.

Zama yayi a gefen Naila yace wannan duk makwaftan ki ne,Kinga Hajiya Babba,ga Aunty Maryam,Aunty Maijidda,wannan Ummu Salma,Kinga Aunty Naja'atu,Naila da fara'a ta gaishe su suka amsa tace Sunana Naila,suka ce kamar yanda ya fada miki makwaftanki ne mu da fatan watarana zaki kawo mana ziyara,Spark yace zan kawo ta ai gidan ko wacce,Hajiya Babba tace ai ka kyauta wannan shine zaman tare ai hakkin makwaftaka ne,ace sai dai talakawa suyi mu banda mu ai bai dace ba sabo da Allah ya rufawa kowa asiri,Naila haka duk langonta ta mike tana daidaita tafiyarta ta shiga kitchen.

Ruwa da lemo ta kawo musu sai kayan gara da aka yi mata dublan da Alkaki harda Chin chin ta kawo musu,tace Dan Allah kuci idan ma baku ci ba sai na zuba muku abinku a Leda,kadan suka ci suna hira,Hajiya Babba tace Amma Spark matar nan taka Yar Fulani ce ko? Spark yace sosai ma,tace ai naji maganarta gaba daya gata mashaallah kayi dace,harda cewa na gode cewar Spark.
Sun Dan jima sannan suka tafi,Naila tace gwara na zauna a palon kar wasu suzo,kafin ta rufe baki kuwa sai ga wasu makwaftan suma sun zo,suma Spark ya gabatar dasu basu Dade ba suka tafi,sai Kuma ga Yan uwan Spark Badia da Anam,sai wasu Yan matan su biyu suka zo,sai Arham,da Shahid suka zo gidan.

Badia tunda ta shugo take kallon gidan tana wani tabe baki,Naila tace sannunku da zuwa,iya mazan ne suka amsa da fara'a ba ruwansu amma su Badia ko amsawa basu yi ba,Badia tace Kai ku zauna mu da gidanmu suka zauna,Naila tunda Taga haka sai ta kama kanta suka gaisa da mazan kawai ta share su Badia,au mu baza ki gaishe mu ba? haba yara Kuna kannensa ni zan gaishe ku Yayanku nake aure fa.
Arham yace da gaskiyarki Aunty wlh karki gaishe su.

Spark ne ya sakko daga step ya daure fuska ba wasa ganin su Badia, System dinsa ya dakko ya sa a charge sannan ya dawo ya zauna ya jawo Naila ya dorata Saman cinyar sa,Arham yace Yaya Spark ya kalle shi babban yatsa ya dagawa Spark wai yayi dai dai,dariya Spark yayi yace yaro kayi biyayya ka samu aikin yi,Arham yace ai tun jiya nabi ma,Dan Allah ka bani kudi na siyi wani agogo da wando,Spark yace ai baka da matsala indai kabi Amarya ba wando ba har da rigar ma sai a siya Maka,Shahid yace gaskiya Yaya wlh ka iya zabe,Spark ya mika Masa hannu yace mu gaisa,Naila dariya tayi tayi derere Saman cinya tace Arham Dan shiga kitchen ka debo muku drinks nidai bazan tashi ba,ya shiga kuwa ya debo musu harda kayan gara din ya zubo musu,a hankali Naila ta zame ta koma Saman kujera,Badia taki ci tace sai kace mayya,Spark yace to da mece ke? Ai mayyar ce ke duk gidanmu ai kece kike kama da mayun,ai kece full definition na mayya,Anam tayi dariya,yace Ido kamar na kwado zaki zo ki min iskanci,ko baki San gidan wa kika zo bane.

Naila ce ta katse maganar tace ya ka bar System din a can? so nake tayi charge,tace okay tun safe muke baki ai,ni fa Chika bata zo ba har rana tayi,Spark fuskarsa ya dora a Saman kafadarta yace zata zo ne.
Spark kannensa ya kalla mata Wanda basu da aure yace kai kuyi Maza ku saka kuka kuce Papa ya muku aure akwai baiwa a cikinsa,Arham suna dariya suka ce Lallai Yaya ka fara canjawa baka taba fa shiga harkar mu amma gashi yau sanadin aure muna ta Hira harda dariya,yace ka taba ganin me Iyali shashasha? yanzu ko kanka na shafa sai kayi albarka yaro,har su Badia dariya ya basu,Da kuwa ni kaina bani da albarkar bare na shafawa wani yanzu kuwa yaro kayi kokari na sa ma albarka binka zata yi, sun Dade suna cin dariya Spark yayi aure ba zaman lafiya,suna komawa gida suka hau bawa Mima labari,wlh Yaya bashi da kunya har muka taho tana cinyarsa,Mima tace ku kuka Kai kanku ai ,Kuma ko me tace Mima wlh baya musu Inda kisan rakumi haka take jan sa cewar Badia,tace itama ashe irinsa ce tayi shuru har da gyara zama sai faman rada suke yi,Mima tace wannan anyi tambadaddiyar Amarya,ai zanje ne da kaina.

Kwanciya Naila tayi a kujerar tayi matashi da cinyar Spark Yana ta mita yace ko dan Nono ban taba ba yau an hanani sakewa sai an jawo min ciki ya fito banyi komai ba ban more ba Amarya ta samu ciki yau lafiya gobe Amai...kafin ya rufe baki Misam ya shugo, ya tashi Naila yace ke tashi kar gaban rigarki yayi kasa Mayen mata yazo kar ya ganar min nawa na sunna,Misam yaji haushi ya juya zai tafi Spark yace Allah ya raka taki gona dama ni haka nake so duk kunbi Kun takura min,Misam dawowa yayi yace to na fasa tafiyar ya zauna,Rafeeq ne ya shugo shima yace girki ne ya kawoni Muji hannun Amarya,Spark yace sabo da matarka ce ba,ko ni banci ba bare kai,a dinga godiyar Allah Spark, jiya ka koshi fa da dare, Amarya ba ta ciyar dakai ba,Naila duk rashin kunyar ta sai da taji kunya,su kuwa ko a jikinsu,Spark yace girkin akwai dadi ba'a koshi ai,Misam zaiyi magana Spark yace karka ce mana komai ato, baya so ya tonawa Misam asiri yace Yana neman mata,dariya Misam yayi yace zan baku mamaki wlh,Rafeeq yace Ashe Spark sabon Uba zaka yi kwana Nan? Uban wa?Spark ya furta yace sai dai uban wasu ba nawa ba, Mummy zata yi aure Ashe cewar Rafeeq,Spark yace shine Kuma Ubana,Rafeeq yace naga Sai zumudi Mummy take,Misam yace ai tuni na gane Maman Spark Harija ce,ai wajenta yayi gado,Ubanka ne Hariji marikin ka dai shine me mataye,Naila tana ji a ranta tace yau na shiga uku sai buzu na,Hannun Hariji na fada shi yasa abin yayi yawa sai hawaye ita kadai ta boye fuskarta a Jikin Spark suna ta hira ita Kuma tana ta kuka,Spark yaji dumin hawaye a jikinsa da sauri ya dago fuskarta yace me aka yi miki Kuma? Naila tace ba komai,Rafeeq ne ya Kalli Misam suka hada Ido yace ka tsorata Amarya ba ruwana,Misam yace ni me nace daga nace Hariji ne sai kuka,idan kasan zaluntar yarinyar nan kake yi ka fada mana,Naila tana goge hawaye tace ni Allah ya Gani zaluntata yake yi,bana son soyayyar nan Dan Allah ku kaini gida.

Rafeeq dariya ya kama yi a boye,yace Allah na gode Maka,Spark Allah ya biya yau naga tsoron Naila,dama tunda nake ban taba ganin Amarya irinta ba babu ta Ido,yau Naila ce take gudun Spark tab abin babba ne.

Misam yace to ke Amarya haka ake yi daga wasa Kuma,Naila tace ai nasan ba wasa kuke ba tunda ai ni nasan mene baza ku gane ba,Misam yace baki dauki wa'azin Yar gidan yari ba kenan,Spark yace ki daina biyewa yaran nan fa zasu kaiki su baro,Chika ce tazo gidan a motar Misam ta jiya,ta Sha gayu cikin Arabian gown,ta shugo da sallama,Rafeeq ya kalleta kawai ya dauke Kai,Misam ma haka,Spark yace dama kuka take kinki zuwa,Chika tayi mamaki tace Naila da kuka? a'a sai dai na karya Naila da bata kuka.

Naila hawayenta ta goge da sauri tana dariyar dole kamar ba komai,tace naga idonki a kumbure Amarya lafiya? Naila tace Abba na tuna,Chika tace tabara ce wannan kawai ta ganin miji in ba iskanci ba kawai ki kama yiwa mutane kuka,Kaine kake kulata ma,Spark a ransa yace wayyo cika barkono da gishiri na barbada mata,Chika ce ta Kalli Misam ta dauke kai,hannun Naila ta fisgo ke taso dalla,Spark kamar shi aka fisgo yace wayyoooo......yasan kwanan zancen,Naila kamar gurguwa haka take dingishi tana tafiya da gefe daya,Rafeeq yace agwagwa tana wanki,Spark yace zan ci uwarka wlh, dama sa Ido ya kawo mu cewar Misam,duk nasan ai Yan sa Ido ne suke zuwa Spark ya fada Yana harararsu Yana danna waya.

Chika har bedroom din Naila tace ke ban fa gane ba lafiya na ganki tafiya kamar Yar kaciya ke Naila menene haka? Naila ta Maze tace ke dalla Beauty bata yi karya ba dadi sosai fa,just that na bashi maganin yayi aikin da yawa yaki gajiya amma duk da haka wahalar kadan ce sai dadin yafi yawa,Chika ta sauke ajiyar zuciya tace yanzu naji zance,to ya love din? gashi kin Gani Ina ta shagwaba Ina kukan samun sarari da sangarta ai shi nake yi,kin San Kuma danginsa sai ka nuna musu kai ma A ce sannan ake zama lafiya da su shi yasa ai kika ga Ina ta Masa kuka.
Amma jiya Madarar Nido ai na kwankwadeta,kamar kar a daina,Chika tace Shegiya kawata anji sweet dole kiyi shagwaba,Naila tace ei mana karki auri gajere yarinya ba kowanne gajeren ba amma Mafiya yawa tasu kubewar Miya ce,Chika tace ke nifa tun yanzu ma nake karewa ta saurayin da nake so kallo,Naila tace Misam din? Chika tace ae mana amma har yanzu ban ganta ba maye boye kayarsa yake yi a boxers bare ma a kallar Masa.

Naila tace kawata kiyi sauri akwai dadi kar mu barki a baya,tausayinki nake ji,to nice jaraba ma nayi kwantai duk anki so na,wannan Misam din sai wani iyayi yake min na ma daina kulashi,muje ki tayani girki abinci wai suka zo ci,da nace bazan yi ba,Chika tace kiyi mana karki dogara da surukanki wannan marasa mutuncin ba kawowa zasu yi ba sai sunga dama,gwara ki zage ki rike mijinki,Naila a ranta tace rike Miji manya bari kiyi kiji tukun.
Fitowa sukayi zasu shiga Kitchen Misam yabi Chika da kallo,har ya hango irin dadin da Chikar zata yi ma,Rafeeq yace tunda za ayi bikin Mummy ni zan dakko malamar gidan yari zan bawa Chika kudi ta dakko mana ita mu da bama bin mata ma rage zafi da zancen harkoki ko banza naji Badala.

Spark yace idan za kuyi aure kuyi aure ku daina walagigi Kuna tangal tangal da rayuwar ku,ni Kunga kullum Ina da komai a gidana duk Inda naje zan dawo na samu,Rafeeq yace yaushe ma na fara balaga ni tab naje na tsufa da wuri,Spark yace to kar a dinga yawan zuwa gidana ana kallar min mata kuje kuyi ta iskancinku a gari.

Naila tace me za a dafa musu ne? Chika tace a musu me sauki jollof din taliya,Naila tace Baby baya son taliya fa gaskiya,Naila tace ita dai tuwo zata yi,Chika ta dinga dariya tace Amarya guda da tuwo ai sai ayi dariya,ta Dora taliyar haka ba a son Naila ba,taji nama da hadin kayan lambu, kida Rafeeq ya kunna,Chika tana kitchen tana tikar rawa, har suka gama komai suka shirya a dining sannan Rafeeq Wanda dama shi daga School yake ya riga kowa zama a dining,Misam ya zauna harda gyara riga Yana cewa girkin Amarya zanci,Spark yace Amarya me dadin tuwo da Miya yau me taliya ce kenan,Naila ta tuna Indomie dinta da salat.

Chika bata da kunya tana ganin Spark ya tashi tana zaune tana rawa,Misam ya kalleta yayi murmushi,Rafeeq yace ashe su Chika dai ko Ina da ku rawar ma an iya,Chika tace Kai a gidan yarin ma mune shegun ciki,Rafeeq yace naga alama kece akan kin fito daga gidan yari kika dinga rawa,Chika tace ai kowa ranar sai da na raba musu alakoro suka kalla,Misam yace na hanya ma ai sun gani,tace ai gwara ni bani da permanent uhm uhm...a cikin hot....Rafeeq yaci gaba da cin abincinsa,suna zaune suna ci suna Hira harda Chikar gayu ita da Rafeeq suke hira,Misam abincinsa yake ci baya kula su,wata yarinya ya latso a waya ya nuna Rafeeq yace Kalli,Rafeeq ya leka ya kalla harda kashe Ido daya duk sabo da kallon mace,yace tayi ka sa pics Dina ko zata kyasa na yaudare ta,Dariya Chika tayi wai ya yaudareta wato ma ba aurenta zaka yi? Rafeeq yace a'a wanne aure Kuma ai ni da kike Gani Yaudara ce burina,ba Kuma abinda zan taba mata kawai na yaudari mace na wuce amma matan ma sai su dinga tafiya wajen Yan iska,da wajena suke zuwa ai da sun huta, ba gara ba zago zan yaudare su kawai suyi gaba lafiya lafiya,Chika ta samu hanya tace wasu kuwa sai bin mata ana lalata musu rayuwa.

A dinga bibiyar mata kamar yaran akuya,tana magana tana kallon Misam,yasan da shi take,tace sai lalata kannen wasu,'ya'yan wasu,yayyen wasu,matan wasu aikin kenan,me za ayi da Maza irin wannan basu san darajar mata ba Sam,ko aurensu kayi basu iya dainawa sai dai ka mutu da bacin rai,Misam ya gama daukan zafi,Spark ne ya fito zai tafi masallaci Sallar Azahar,Rafeeq ya fara dariya ashe an musulunta,Spark yace Chika rabu da su kije kiyi sallah abinda zai amfane ki,Chika ta mike ta wuce bedroom a kass,Misam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login