Showing 120001 words to 123000 words out of 158722 words

Chapter 41 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

363

Karar motoci suka ji da Uban kida suna zuwa gidan suka saki sautinsu,Mima tace ai Spark ne yayi aure sai abinda kuka gani Kuma,kannen Spark gaba daya kasa hakuri suka yi suka fice Compound kallo,Spark yasan sa Ido suka fito yi,dariya yayi kawai yace wai Dan uwanka ma a zamanin nan bayanka yake so ya Gani,nafi karfin ku yara bazan fado kasa ba always Spark On top ne,Driver ne ya bude masa kofa ya fito ya zaga ya budewa Amarya,Su Badia suna ta kallo tace Uhmmm kofar ma sai ya bude mata sai kace Yar me kudi,Kansa ya zura cikin motar Yana yiwa Naila rada yace,behave well nasan ke Oga ce,Naila kafa daya ta zuro,Kannen Spark harda leke suka hango farar kafa ta Sha lalle me kyau,Anam tace to ai ba fara ce me kyau ba,bakake ma akwai kyawawa wlh sunfi ma fararen kyau wasu,mu a fada mana haske duk danginmu ba baki,Hannunta Spark ya riko ta fito,Kanta a lullube ,Arham yace ai dole dai a bude mana fuskar, Spark Goggo ya mikawa Naila yace Amana,zuwa yamma za a dauke ta,Make shi Goggo tayi tace to fitsararre mu Kuma ayi ya damu? Yana murmushi yace kwana zakuyi mana kuga Abuja gobe a maidaku a jirgi,Goggo tace Dan nan ni bana son na shiga jirgi matukar ba Makkah zanje ba,kawai Dan fitina da asarar kudi a iya Nigeria zamu hau jirgi aradu baza muyi asara ba baza muyi Maka asarar kudi ba,Rayya tace Goggo wlh sai dai ke a Maida ke a mota sai cutar mu kuke yi da tuni a jirgi zamu zo mu koma,Yaya Spark a biya mana zamu hau mu,Spark ya tsaya a cikinsu sai surutunsu suke suna dariya da nishadi.

Yan uwansa duk mamaki ya kamasu mutumin da baya dagawa kowa kafa wai shine tare da Yan kauye suna wani hira da dariya,Badia tace su Spark an fado,Arham yace ni wlh ya birgeni na koma fan din Amarya ma,irin wannan nake nema Ido rufe,Kuma ma ai a kauye akwai Yan birni a birni ma akwai Yan kauye,idan Kuma kunce talakawa ne duk ba da arziki aka haifi kowa ba sannan babu me mutuwa a binne shi da dukiya,Kuma yanzu ta tashi daga Yar gidan talaka ta zama matar me kudi.

Ai kai Arham Dabba ne wa yake ta Kai cewar Badia,su Googo Naila ta rike tace muje ciki,suka tafi ciki a hankali tare da Amarya suna ta guda har cikin palon,Mubarak ne yace sai ka bamu kyautar mu da ka mana alkawari, Spark yace ai dai Kwa bari na shiga dakin Amarya gobe na baku cikin nishadi,Suka ce ba damuwa barshi sai goben maybe ma zaka fi bamu da yawa,yace wai nawa kuka ce ne? 50k muka ce,yace gobe Kuma ai sai 100k sabo da Ina Ango na sak,suka ce a barshi sai goben,suka juya da mota suka tafi har Spark din,Rafeeq kuwa Misam yake wa magana yace

Shi yasa na tsani Yan gidanmu wlh Sam basu da hankali,ji wannan sa Ido haka,Misam yace Kai kake saurarar su ma,wannan Badiar tafi kowa Munafunci sai kace ba yan uwa ba,Kai Ana dabbancin a gidan Nan wlh yanzu zasu saka baiwar Allah a gaba.
Rafeeq ya furta ai wannan daidai take dasu bana jinta Allah yasa idan suka fada musu bakar magana su rama.

Suna shiga tafkeken palon sai kamshi da Sanyi kawai ke tashi,kullum gidan da kida kamar yaran Arna,Palon ma kida suke ji a manyan Speakers sai da suka shiga sannan aka rage kidan sosai amma yana tashi kasa kasa,Goggo tace bayin Allah a kashe mana kida addua zamu yi,sai lokacin Anam ta kashe suka zauna da Amarya a Saman Carpet.

Naila Amarya anci gaba da kukan karya kasa kasa ta wani langabar da Kai anyi kasa da shi tana wasa da zoben hannunta me tsada da Spark ya saka mata a mota,Mima ma Jin Amarya tana kuka tace a ranta amma yarinyar nan muguwar criminal ce,Addua aka yi sosai sannan Maman Rafeeq da tafi dama dama a ciki itace ta yiwa Amarya nasiha,harda cewa Kinga dai shi dan dangi ne ato ki girmama masa yan uwa sannan kema su girmama ki,ayi hakuri da juna, tunda kika ce kinji kin gani kina so dole sai ayi hakuri,Mima tace ya zama dole kuwa,Goggo tace shine dai yaji ya gani yace Yana so Kuma,yo mace ke auren namiji ko namiji ne ke auren mace? Sadaki ya biya wuri na gugan wuri million guda sadaki sannan aka bashi,Yar masu shanu ce fa Wanda suka gaji arzikin dabbobi,Mima kirji ta dafe tace what? Serious fa? Million Daya? Goggo tace ai harda mota sabuwa gal tana can wajen Ubanta yayanta yana boris da ita a cikin gari, yo a dauki wannan zizar a sadaka ne,kallon wannan kawai yayi ai sai ya samu nutsuwa.

Kalleta fa baki ga kalarta bane?ai ba matar yara bace,ku godewa Allah ma da muka baku da wuri ba sai da muka bari ya kwanta a gadon asibiti ba kawo ruwa kawo ciyawa ana so ya farfado.

Dukkansu kallon kallo suka fara Goggo daga magana daya sai fadar magana take musu iri iri,Tani tace Kunga mu ku bamu waje sallah zamu yi,Mima tace Anam nuna musu yanda ake amfani da toilet din basu sani ba na sani,Goggo tace Kalli hakoran mu dukkan mu hakoran Makkah ne a bakunan mu har Yan matan nan su Rayya duk munje Makkah kasa me tsarki,har akwai wata toolet da bamu gani ba,ki tambaya kiji ko da kike zuwa Makkah bakya haduwa da Yan Fulani duk mune ko Ina,wlh babu wani abinda zaku yi bamu iya siya ba,a Daji kawai muke ne, ba rayuwa muka sa a gaba ba.
Mima tace da Haram ba,Goggo tace wlh yarinya ki kiyayeni ba a wasa da Fulani ba a kawo mana raini sai na sa a batar dake duk kudinki,mukus suka yi ba wacce ta sake ko tari sunji tsoro ko su Goggo suna daga cikin criminal basu sani ba,basu San Goggo barazana tayi musu ba kawai.

Tani tace a kawo muku kayan arziki irin wannan iyayenta su yarda da danku suna son Yar su amma suka dauka suka bashi ita Amana,mutum me daraja,yaro ya samu yarinya duniya guda zai samu ya moreta, yayi mata ciki, ta haifa Masa yara amma ku zauna Kuna fada mana magana,Baku da tsari Kai dan Allah ku canja tsarinku, ku canja hali, Sam halin ku baiyi ba,baku yi ba,Kun sire min wlh,nononta kadai aka bashi ya isheshi rayuwa bare a Kai ga lu'u lu'un,duk Yan dakin kunya suka ji Yan matan da samari suka shiga boye dariyarsu,Maman Rafeeq tace Dan Allah kuyi hakuri haka,Tani tace Allah to a dinga zaginmu a fakaice, yarinyar nan fa ba nonon jaka gareta ba bana saniya bane na mutum ne,yau na tabbata bazai bari ta sake ba,Kuma kawai an baku ita kwasha kwasha shine ake zagin mu,jarababben Dan naku ma da naci, in banda kwarzaba me zaiyi yarinya Kun jawo mana asarar kudi sai mun dinga kawo mata magani kar ya lalata ta,Lateefa tace to kuyi hakuri ku taso muje kuyi Alwala.

Maman Rafeeq Hannun Amarya ta rike taji Laushi tace a ranta ba abin kayi magana ba ayi Maka cari,bari na fada a raina laushin nan kamar bata aikin wahala.
Toilet Lateefa ta kaisu cikin wani bedroom hadadde ta shimfida musu Sallaya manya da yawa sannan ta fito suka bar musu dakin suka koma Palo suka fara gulmar rashin mutuncin dangin Amarya,Mima tace Kinga Goggo nan kamar zata dake ni.

Anam tace Kuma da sai kuyi shuru, baku kyauta ba wlh ai ko ba komai suci darajar Spark yanzu sai sunyi ta gulmar a can,Mima tace who cares? suna ta gulma,Arham su mazan jira kawai suke a bude musu Amarya su ganta,Mima tace wannan naci da yawa yake wai gidan Spark din ne Baku sani ba,ba sai kuje ku ganta ba a can,wannan fa taron mata ne,Kun samu a gaba,amma sabo da basa Jin maganar iyayensu kin tashi suka yi,funfurus suka yi a wajen sun zauna a kujeru wasu kuma a kasa.

Su Goggo Sallah suka kasaru ta azahar,Naila ma tayi harda wanke fuska da sabulu tana idar da Sallah ta fara shafa powder tana gyarawa,tayi Yar make up dinta sama sama tayi kyau sosai ta sake shafa turaruka har Jikin kayanta da mayafin sannan Goggo tace ni wai ya naga idon ba alamar anyi kuka ne? Naila tace na rantse kuka na dinga yi na gaske fa,Abbana na tuna ta sake kebe baki,Goggo tace to ya isa kinyi kukanki,tace yanzu karki sake rufe fuska kyale shegu su ganki ai ba mummuna bace,kawar Umma tace yawwa ta Dora mayafin a kanta ta bar fuskar a waje, suna zaune sai ga Anam ta shugo musu da abinci ta ajiye,ta fice da sauri tace na ganta wallahi ta hadu,Badia tace tayi dariya Kinga hakoranta? Anam tace a'a,to rufe mana baki yanzu haka karyayyen hakori gareta,Badia ma ta dauki wani abincin ta shigar musu da shi Dan ta ga Amarya,taci sa'a Naila na magana ta ganta taga hakora masu kyau reras,sai ta fito tace na tabbatar ba karya.

Mima tace ahh Dan fa kyakyawa fa kyakyawa ce gaskiya, magana ta Allah tana da kyau wlh ko ita zata yi kanta baza ta yi haka ba amma fa ba kyan hali bata da kunya,Anam tace bari na sake Kai ruwan nan na ganta again,ta dauka kenan Arham ya kwace wai shi zai Kai,Mima tace je kice su fito Palo zasu fi sakewa,amma ni kar su bata mana dakin yara su fito ato.
Amma kin San masifarsu kice su fito zasu fi sake wa.

Anam ta shiga tace Amaryar mu ku fito Palo wai zaku fi sakewa,suka mike,kawar Umma a ciki tace wlh su Goggo Kun kwato mana yanci sosai,gashi sai lallaba mu akeyi ana Jin tsoron mu,Goggo tace ai ba a bari yanzu Kai ya kulle, ke kyaleni nan zuwa na Makkah sau takwas, a waye nake karrr ba me daga min Kai,wacce shinkafa ce banci a Makkah ba,wanne tayal (tiles)ne ban gani ba,su Tani wlh duk sun je yafi sau uku,haka su Rayya duk an biya musu sun je,shi kanshi Hashimu Baban Naila tun Yana saurayi mahaifinsa ya biya Masa yaje har sau biyu,Umman Naila kanta zuwanta biyu Makkah.

Kawai mutum idan talaka ne sai a manta da yaje Makkah, Alhajin ma baza a dinga fada Masa ba ko Hajiya,me kudi kuwa ko bai je Makkah ba kila ma Amurka yake tafiya duk Shekara,ana tafiya Makkah Ibada shi idan ya hau jirgin Amurka zai ware amma sai kiji ana Alhaji ya dawo ne,Anam tana jinsu tana dariya,Tani tace ai talaka shi kullum sai an nuna Masa bakin ciki a rayuwa, Alhajin ma ko Hajiya bakin ciki ake Masa sabo da bai iya Jin kida ba,bai iya saka damammen kaya ba Yana fitsara yana badala,bai waye ba ake ganin talaka,me kudi ko jahili ne to wayayye ne ai ya waye.

Palo suka dawo Goggo ta Kalli su Arham tace Kai Ina abincin mu na uwar rainon Ango? ni na shige su Maza sun tarar mana a Kai,duk Dan nono na da yayi saura sun kalle min shi,dariya suka yi ba shiri har matan,ke Naila Dan ubanki ki dinga saka hijab Kinga kallon da suke miki ko Ango Bai miki irinsa ba,ni dai Ina ganin bala'i da masifa a gidan nan,zasu cinye Amaryar da Ido,kannen miji ne ku ba kyau wlh,kallon ya fita daga na musulunci,wlh duk sai kunci ubanku idan baku bar palon nan ba,Mikewa suka yi sabo da masifar Goggo badan sun gaji da kallon Amarya ba suka fice, Arham ne ya kawo musu abincinsu na gidan Mummy saura kadan ya taka Goggo bai kula ba,Goggo ta durma masa dundu,ya sunkuya Yana ajiye kayan,tace dan ubanka karya ni zaka yi,tunda muka zo dama naga kana daga min gira Karuwa ce ni? da aure na da komai,Arham Kara ya saki Yana Sosa bayansa ya fice Yana hararar Goggo.

Goggo tace wai a cikin ku wace uwar Angon ne? aka nuna mata Mima,tace shi yasa take ta uban takama,Naila kuwa su Goggo suka yi suka yi taci abinci taki ci,sun rasa dalili,Badia tace idan kunya kike ji ki koma bedroom kici,Naila kamar doluwa wai ita a dole amarya me kunya, tace a'a yace kar naci sai an kaini can gidan,Goggo ta tsaya da cin abincin tace Dan ubanki kashe kanki zakiyi? tun safe Baki ci komai ba sai kinje gidansa,Naila a hankali ta furta ai munyi alkawari da shi ne, ni bazan karya ba,Duk na dakin dariya suka yi,Anam tace tab lallai namiji zaki biyewa? ai kuwa zai kaiki ya baro,wlh wayo zai miki kije ki danni kaza yayi maganinki,Naila taki ci Kuma da gaske Spark shi yace ko zata ci taci kadan karta cika cinkinta ya tanadar musu better.

Goggo ce ta sata gaba tace Dan ubanki muje daki mu zaki wa iskanci,ta kora Naila dakin da suka yi sallah harda rufewa ta mika mata plate din fried rice da hadin salat,ta kawo mata fruits,da ruwa da lemo,tace wlh idan baki ci ba sai naci ubanki a dakin nan.

Naila tace ni za a sa na dinga bijirewa mijina tun yanzu,haka tana ci kamar zata yi kuka sai da taci ta koshi dama yunwa take ji, Goggo ce ta bude Jakarta da wani tsumi a roba tace shanye ragowar,Naila ta shanye tas tace karki sake ya ga wani magin mata a wajenki,Naila tace ai na sani Goggo ai kawai ko me yaji daga Allah ne natural ba Kari, Goggo tace yawwa yar gari,idan Kun Saba ma zaki ga Yana baki kudin kina siya,wasu mazan Kuma da iyayi sai suce ni bana son shaye shayen Nan,ni kawai ki zauna yanda Allah yayi ki,kina zama Kuma wangalewa zakiyi shike nan Kun dinga fada kenan,karshe ko ya fara neman aure ko neman mata,sai an dage da gyara yanzu.

Banda Kuma na hauka ko me aka baki ki Sha ko a dinga baki abubuwa kina matsi dasu ko wanne hauka karki karba zaki kashe kanki,Naila tace to an gama.
Kwanciyarta tayi a Saman gadon tace bacci nake ji,Goggo tace kiyi abinki domin da dare baza kiyi ba 'yar nan.

Naila ta kwanta sai bacci kamar gidansu, Spark ne ya kira wayarta Goggo na dakin ta dauki wayar tace kasa kasa bacci take,Spark yace okay,kar a tashe da wuri gwara tayi abinta yanzu,Goggo tace ubanka Kai fitsararre,wayar ya kashe yana dariya shi masifar Goggo dariya take bashi,gata a waye ba ruwanta.

Spark Chika ya sake kira yace an gama hada bed din? tace ae tun dazu ma har Yan aiki sun gyara ko Ina yanzu kayanta nake shirya mata,yace yawwa Yar Albarka Allah ya baki yayana ko ta biyu ya Kara Dake,Chika tace amma baka kaunata wlh,ni kaninka nake so,Yace to Allah yasa,tace Ameen,yace kin bude kayan Lefen Nan? tace ae yace a kwai Nighty din Nan zaki ganta wata gantalalliya pink,kin ganeta? Chika tace ban gane ta ba,yace wata tsirarar riga haka,wata zaki ganta tafi ko wacce watsewa da tambadewa? Chika tana ta dariya tace na ganta yace to ki ajiyeta a Saman bed ba ruwanki da ita.

Chika ta ninke ta tare da ajiyeta a Saman bed daga Dan kasan pillow kadan ta fada Masa Inda ta ajiye, har su towel duk sababbi aka saka guda biyu biyu komai sabo aka canja,Spark Yana ta waya da Chika yana sata tana shirya kayan da suka dace ba sai an nema ba,Yini tayi tana aikin,abinci sai dai taga an kawo mata take away lafiyayyen da kayan Sha.
Tana gamawa ta dawo aikin Naila itama wannan ba sai sunyi waya ba ta san komai,tana gamawa yamma tayi likis, sallah kawai ke tsaida ta da cin abinci,sai da gidan Nan ya koma neat ko Ina an gyara shi Kal Kal,ta hau turare gidan da kayan kamshi, ko Ina lungu da sako,har makwafta sai da aka raba musu kamshin.

Naila tana ta bacci lokacin dangi ma duk sun tafi sai Yan gida sunce ai a hankali zasu je gidan Amarya ganin gida.
Goggo ce ta tashi Naila tace taje tayi wanka,Naila tace nayi a can ni a kaini haka na gaji muje can ni yayi min wankan da kansa,Goggo Baki bude take kallon Naila tace zaki tashi ko kuwa,Ga kayan da zaki sa kin San komai da kanki kika zaba ma wai ni wacce irin fitsara ce ne wannan? Kya fada min wanka da miji.

Naila tashi tayi taje tayi wanka,suka sake wani hada mata na turare tayi ta fito ta shirya,Cikin Material Dan kasar India tayi kyau dinkin riga da Skert ne,sosai tayi kyau,Kawayen Umma ne Suka tayata shiryawa sannan suka fito kaita suma duk sunyi wanka sun canja kaya,Maman Rafeeq,Lateefa,sai Badia sune suka rakasu domin Ango shi baya African time har ya turo motoci aka kwashe su zuwa gidan.

Chika tayi wanka itama ta canja kaya tana jiransu,suna zuwa duk wata addua sai da suka tsaya aka yi sannan suka shiga ciki a Palo sai da suka yi suna ta kallon gida suna guda,ko Masu kudi suka Kalli gidan sai sun Kara bare talakawa da mutan kauye,za a saka Naila a dakinta tace can ne Goggo waccen ne dakinsa.

Dan Allah ku dinga sharhi
Idan ba a sharhi bama iya typing..

Masu Sharhi Ina matukar godiya.




AsmaBaffa
[12/28/2023, 3:04 AM] AsmaBaffa: PAID GROUP 300

ACCNT NO
0175487861

YAN NIGER
+22790795939

🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI

BOOK1

86-90

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

Page naki ne
MOM SAFWAN


*MISKI 4in1 Hamil musk*🌹 munkawo original miski daga *Egypt* miskin da indai kinyi amfani dashi zakiji dadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login