Showing 45001 words to 48000 words out of 158722 words

Chapter 16 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

371

tayi dariyar manya tace uhm uhm fa Beauty kar muzo muga ana tsinewa Jamilu muga ana rusa kuka,Beauty tayi dariya tace Allah ya tsareni da zagin Jamilu har abada,wallahi da zanga malamai ma sai nasa sun mana addua Allah ya Kara mana dankon soyayya da Jamilu.

Hajiya tace lallai kinyi nisa baki San iskancin soyayya ba idan ta tashi maganinki,Beauty tace ki mana addua kawai Hajiya amma idan Allah yasa muka fita daga gidan yari zamuyi aure Jamilu zaiga soyayya a karuwata zan shiga gidan mijina ba kunya ba komai sai abinda Jamilu ke so,Hajiya tace Allah ya nuna mana tace Ameen,kina Jin labarin nayi aure idan kika ganni Hajiya kawai ki kirani da Karuwa, ai zansa Daddyna ya bibiyar min hakkin Jamilu shima sharri aka Masa, Daddyna me kudi ne Kuma Kinga Yana da kafa gashi Senator ne har sau uku yayi senator yayi minister na tsaro da wasu mukamai duk ya rike,Hajiya tace mashaallah,Beauty tace Babana Yana da Dabban kudi,wani jahilin kudi ne dashi,Hajiya mutuniyar kirki tace mashaallah Allah ya Ida nufi.

Ameen cewar Beauty,Chikar gayu ce tazo ta wuce da littafanta zata je Islamiyya,Beauty tace zan kamaki a school ne yanzu zanzo nima,Chikar gayu tace wooo ta zaro harshe ta Kara gaba,Bangaren mata ma haka yake gasu nan ba kalar da babu manya da yara,ga Yan iska Nan tatattun gaske da Wanda kaddara ta kawo su,iya shege kala kala wani bangaren ma kida suke ji a Bluetooth speaker suna ta faman tikar rawa ta fitsara,duk a nan su Beauty suma suka sake wayewa idonsu ya bude suka zama basu da kunya basa shayin uban kowa.

Makaranta Beauty taje ta samu Yan mata suna girgiza wai ana gasar girgiza Boobs aga wace tafi iyawa sai shewa suke a class,Malama bata shugo ba a Islamiyya suke wannan iskancin,Chikar gayu da nata ko girman kirki babu amma tafi kowa zakewa kamar zata cire Kafadunta, Beauty tana zuwa ta ajiye Jakarta ta shiga ciki tace ga rawar Jamilu,haka zan na masa a Palo idan munyi aure,guda suka saki da shewa ana dariya,Chikar gayu tace saura luwaluwai muga wace gwana anji Beauty ta lashe gasar, Nan ma suka fara har malama tazo suna ta fama sai da ta musu magana sannan suka San tazo ma.

Abban su Mohsin Yana bencinsa a zaune Yana ciniki sai ga wata bazawara ana ce mata Zainab Kai zaka rantse Bata taba aure ba ta dau wankan yan birni tana taku dai dai,tunda ta taho yake kallonta sai kace Dan iska, Zainab tana zuwa yace Zainabu Abu me tagwayen suna Allah ya kawo miji na gari ko da kuwa nine,Zainab tayi dariya dama har gulmarsa suke a layin yanda yake Mayen mata ba uwar da ya iya sai son mata,tace kayan Miya za a bani,Abba Yana washe baki yace kice yau dadi za a ci naga gidanku kunfi dafa shinkafa da wake,Zainab a ranta tace kaji mutum marar mutunci ya fada min magana a wayance,a fili tace ae a zuba min na Dari biyar, ai kuwa ya dinga antaya mata kayan Miya Yana kallonta ba ledar yake kallo bama Zainab din yake kallo Yana ta faman zubawa ya bata yafi na dubu daya,hannunsa sai rawa yake karrrrr karrrr, Zainab ta karbe kayan Miya,yace cucumber fa ga salat ai girkin zaifi dadin ci,tace kudina sun Kare,hannu na rawa yace ai sai a baki ko kyauta ne zo ki karba haba kamarki ai sai da kayan lambu, ya dakko hannu na rawa zai zuba a leda sai ga Umma ashe tana labe tana kallonsa ta cikin gida ta fito fit....

Tana masifa tace to namamajo ke zo Dan uban uwarki ta fisgo Zainab ta juye kayan miyar tana masifa tace Yan iska barayin banza,wallahi Allah na kallonku a haka ku bude Baki Kuna zagin gomnati barayi barayi bayan duk gaku nan barayine kowa ya samu dama sai sata Yar iska me hanci kamar gurji,zaki ci cucumber ai hancinki ne cucumber din,wato Kinga banza ta Fadi,Umma ta gyara mayafinta ta zuba mata na dari biyar dinta, tace ungo jeki idan kin fasa Kuma a baki kudinki ki tafi wani wajen,Zainab karba tayi sum sum ta wuce tana cewa nifa ba ni nace ya bani ba,wallahi zan jawoki na miki mugun duka na karyaki na karya banza,Zainab ta tafi kawai,Abba ya sadda Kai kasa Yayi mukus,Umma ta Harare shi tace Kai Kuma la'anarka a mata take ko? baka da aiki sai son mata,a haka kamar Dolo ashe wayonka a mata yake, hannun Abba taja suka shiga cikin gida,duk masifar Umma bata yiwa Abba a gaban mutane sai dai watarana a gaban yaransa take cin ubansa,tace haba Hashimu ai dama ni tunda aka kaini gidanka a matsayin amarya naga kasan hanya fes kabita babu gargada nace da wata a kasa,watana biyu a gidanka na samu ciki ana zuwa ganin amarya na fara amai ashe har ka jefa kwallo daya,to billahillazi baza ka ebo min cuta ba,baza ka jona min kanjamau ba,idan aure zaka yi kayi kawai ni ban hanaka ba, Allah ne yace ku Kara,tunda mace daya ta Maka kadan ka Kara yafi min kwanciyar hakali.

Abba anyi mukus da kyar yace ni ba aure zan Kara ba,Umma tace na fahimceka fa Hashimu mace daya ta Maka kadan,Ina da lalura watarana baka iya hakuri....Hidaya ce ta shugo gidan da markade ta dakko ta tsaya Jin me su Umma suke,Umma tace bar nan Dan kutmar....ta dura mata ashar, ba shiri ta ajiye markaden ta fice runfar Abba taci gaba da sallamar mutane.

Umma tace abinda kake yi yaranka kake zubarwa da mutunci a unguwa sai gulmarka akeyi Kai ko kunya baka ji,na baka dama idan kaga wacce tayi Maka ka fada min Danka zai Maka auren duk abinda ake kashewa zai kashe Maka bazan hanashi yayi komai ba, ai Kai ubansa ne mahaifi,ni bani da bakin kishin da za ace na haukace akansa,Ina sonka dole zanyi kishi ba macen dake son kishiya a duniya amma ni da wannan halin naka gwara ka Kara auren tunda ai da a baya ba ruwanka da mata ko kulasu baka yi,yanzu kuwa ka gaza hakuri,Abba Yana kallon Umma har ta gama kamar zaiyi kuka yace Allah na gode Maka daka bani mace ta gari, na gode ya rungume Umma yace kin yarda nayi auren? Alhmdllh yau ku rufe gida a masallaci zan kwana Ina Sallar dare.

Umma a nan ta saki baki dama fada tayi bai Kai zuci ba ta zaci bazai iya ba zaiji tsoronta, tace wallahi karya nake ban yarda ba Hashimu,baza ka Kara aure ba na isheka ni kadai,
Hashimu yace maganar farko ita sarki yake karba wallahi an karba,ni baki isheni ba,ga kullum masifa masifa kice bana miki komai,kiji tsoron Allah Umman Mohsin ni aurena zanyi,Umma salati ta saki tace na shiga uku Hashimu daga wasa wallahi ni wasa nake,Kuma indai akan masifa ne na daina yi Maka daga yau zan gyara Halayena,Hashimu yace ki gyara din ai Yana da kyau auren ma ai sunna ce me kyau,Umma sai kuka sosai,Hashimu yace kiyi hakuri kici gaba da neman warin sigari kina shaka kafin ki samu lafiya,Umma ta saki kururuwa tace wallahi Hashimu butulu ne Kai,Hashimu yayi mukus kamar Dan Dolo ya fice abinsa wajen sana'a,daga ranar Kuma ya daina kallon mata shi a dole aure zaiyi bayan ko bazawarar babu ma,duk arahar kayan miyar ya daina wai zai samu dahir mene zai dinga batawa kansa lokaci Yana kallon banzaye a waje.

Harira tazo wajen zata Masa wayo Abba ko kallonta baiyi ba,Harira tace Hashimu Allah bar mana Kai,yace ko kiyi addua ko kar kiyi idan Allah yaga dama zai barni mana,Kuma watarana dole zan mutu,na nawa zaki siya ya furta ba mutunci,Harira tace ta dubu uku,Hashimu ya millira mata uwar tsada ta dinga mamaki haka ta bar wajen ba fuska,Umma Kuma kwana biyu sai kuka sai bacin rai,gashi shuru Mohsin bai zo ba,yau Allah ya kawo shi da yamma,Yana zuwa Umma ta mike daga Inda take zaune tana gyara wake tace muje ciki,Shi dai Mohsin ya ganta duk ba sukuni tayi yagai yagai da ita,yace Umma lafiya dai? Umma tace hmm Dan nan Abbanku dai aure zai kara,Mohsin Dake namiji ne ko a jikinsa Maza ba ruwansu da kishiya,yace Umma shine duk kika damu haka na zaci wani abin ne ma,wacce zai aura? Umma tace shi yasan wacece ni dai yace har yanzu bai samu ba tukun amma tunda ya furta ai sai ya samota,to Umma a kanki zata zauna tazo ta zauna mana halin Abba ma kadai ya koreta.

Umma tace baza ka gane ba Mohsin wata macen da niyyar sharri take shugowa burin Matan yanzu idan an auro su kawai su Kori uwar gida ko su jefa mutum a masifa,wata bin malamai tazo ta hanamu sukuni wata babu mutunci a harkarta,wani auren idan anyi ya zama sanadin fitarka daga gidan miji kenan shi yasa kaga bama son kishiya,Kuma dai kishi halak ne,Mohsin yace to kiyi hakuri inshaallah ba abinda zai faru Allah yasa haka shine Mafi alkhairi,Umma tace hmmm dama nasan baza ku goya min baya ba,Mohsin yace Umma gwara tun wuri mu hadu a samowa Abba ta kirki wacce zaku zauna lafiya shike nan kawai,Umma tace a'a bana son ta kirki nafi son wacce zata buwaye shi ya saketa,Mohsin yace tab kin san Abba ba wani iya saki da zaiyi Umma nidai ga shawara nan,tazo a samo Yar banza tayi ta gana miki azaba Kuma ya kasa sakinta ai gwara ta kirki,Umma tace to shike nan,Mohsin yace a makwaftana akwai wata Fatima mijinta ne ya mutu yaranta biyar amma duk suna can Kaduna dangin ubansu sun karbe yaran ita kadai ce,tana da kirki da hankali a hadasu da Abba kawai,Umma tace babu wata ta kirki a kishiya Malam kawai kace ka hada baki da ubanka Kun munafunceni ta saki kuka.

Mohsin yace kefa kika shawarce ni ban san zancen ba wlh,tashi ka bani waje,Mohsin ya Mike cikin shigarsa ta kana nan kaya masu kyau yayi kyau ya fice,babu me kallon Mohsin yace Yana da aure ma,Yana fita Abba ya tare shi yace Mohsin kaji zan Kara aure ko? Mohsin yace ae yanda yaga Abbansa Yana ta murna ka rantse an kawo amaryar ma,sai yaji tausayinsa yace Abba wace matar? Yace ku nake jira dama mu taru muyi shawara a samo min ta kirki,Mohsin sai da yayi kwalla,Abbansu Yana bashi tausayi matuka,yace to Abba ni na samo Maka Umma ta Santa ma a makwafta na take, sunanta Fatima,Abba yace Fatima bintu,Batoola,Mohsin sai da yayi murmushi,yace to ai da bazai raka ubansa zance ba,zanzo da abokina Malam Isa,sai ka nuna mana gidan,to gobe kuzo da yamma zan sanar mata,yace to Allah ya muku Albarka,Allah ya tsareka,Allah yasa ka a Aljanna Firdausi,ubangiji ya tsare min Kai da dukkan yarana, Allah ya fito min da Nailanka,Sai lokacin Mohsin ya washe baki anyiwa Naila Addua.

Abba yace Allah ya tsareka a duk Inda kake Allah ya doraka akan makiyanka,ya tsareka duk wani sharrin masu sharri,Allah ya azurta min Kai,ka shahara kayi suna a duniya Suna na kirki bana sharri ba,Mohsin yace Ameen ko ba komai ta wannan bangaren Abba yafi Umma bai taba yiwa dansa baki ko ya Fadi wata mummunar kalma akan yaransa, bai taba ba,Kuma indai kayi abin kirki yaji dadi sai yayi ta surfa Maka addua ,shi fada da nasiha ne bai iya ba Sam,iya jaraba Kuma ba'a fada da shi ko me zaka yi Masa,sai dai idan ka bashi haushi ya kauracewa mutum Kuma bazai gaba da Kai ba,kowa ya sanshi Yana da baiwar da ba kowa ke da irinta ba,amma wasu basu fahimta dolancin nasa kawai suke hangowa sun manta da cewa Allah baya halittar dolo kowa ka gani da baiwarsa.

Tantiriya yau da dare babu abinci bata je wajen Spark ba,tana can wajen su Dan Indo tana Jin hirarsu da suke duk hirarsu babu ta kirki sai ta shuka tsiya da Kuma zuga wasu suna so su koyawa wasu wani mummunan ta'addancin, layin su Dan Indo kowa ka gansu da shi to ya gawurta a kisan Kai,ko kidnapping da fashi da makami etc, su kuwa Yan Daudu suma a bariki suka yi kisan Kai aka daure su, Dakinsu ta dawo ta samu ana ta daukan karatu,zuwa tayi tare da gyara p-cap dinta ta zauna a gaban su Malam Sharu tace nazo daukan karatun, Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh suka shiga furtawa,Malam Jilani yace addua ta karbu Allah ya shirya Terror Allahu Akbar,haba ai gwara kayi Ilimi ka rage iskanci.

Suka fara bude Qur'ani Naila tace daga baqara zan fara tilawa,ta nutsu tayi Bismillah ta fara rera karatunta,duk cikinsu babu me iya karatun Jamilu ma,duk wani harafi sai da ta bashi hakkinsa tana da basira ba kadan ba,duk suka tsaya suna Jin Jamilu mamaki ya kamasu,abin ya daure musu Kai,gashi Kuma Muryar mata,Kuma Muryar dama Dan Fulani suke ji,kowa yazo daukan karatu sai ya zauna Jin karatun Jamilu.

Spark Yana can ya gaji da jiran Jamilu Yana so yazo ya siyo Masa abinci amma shuru,tsaki yaja ya fito sanye da 3qtr blue da riga armless fara hannayensa cikin aljihunsa Yana tafiya Yana taku dai dai,da tambaya ya karaso dakinsu tun daga nesa yake Jin kamar Muryar Jamilu Yana rera karatun Qur'ani me dadin gaske, ciki ya shugo dauke da sallama,Jamilu Yana Jin Muryar Spark yace sadakallahul azim na gama, Muryata tsaraici ce babu kyau haramun ne ehe tayi yanda Yan Daudu ke yi, Malam Sharu suka dinga mamaki, Malam Sharu ya mika mata Hadisai yace Malam Jamilu Bismillah,Naila tace sauri nake yi kasan fa nice Tantiriya budurwata tazo amma bari nayi kadan,ta karanta ta fassara yanda kowa zai gane,ta karbi wani shima tayi daga Nan tace Babyna yazo fa zamu tafi mu caskale.

Ido suka zaro, Malam Garzali ya furta an gama karatu Kuma anci gaba da Daudu shiriya har yanzu bata zo,tace ku daina yankewa mutum hukunci kawai nayi karatun ne Dan kusan ni ba jahili bane Ina da ilimi kawai a yanda na tsinci kaina to bazan yi aiki da shi ba tukunna sai nan gaba,Malam Jilani yace Subhannallahi Allah ya shiryeka wallahi mutuwa Bata jira,Naila tace ni kuwa nasan da haka tunda ko a makwaftanmu anyi mutuwa,an harbi mutum da bindiga ya mutu a gabana a kauye, kaga kuwa nasan zata zo Kaina watarana,Spark yace Inshaallah ba yanzu ba uhm uhm Yana karkada yatsa,shi dai Spark baya son Mutuwa sai da ya bawa mutane dariya,Malam Jilani yace kaga Dan banzan yaro Kafi so a barku kuyi ta sheke aya,wallahi kuji tsoron Allah ku daina neman juna namiji da namiji tirrr, Jamilu ya furta amma Allah yasan gaskiya watakil ma na fiku a wajen Allah.

Malam Jamilu a dawo lafiya cewar Malam Sharu,Naila tace yau darajata ta sake karuwa na sake samo sabon suna,Malam,Dandaudu,Dahara,Jamilu, Terror, Tantiriya,ga Kuma Yar Yahoo har naci waya da dubu goma,duk ni kadai,Juyowa tayi bayan ta mike tsaye ta Kalli Spark suka hada Ido, Ido daya ta kashe Masa,da sauri ya dauke Kai tare da shugowa dakin gaba daya ya mika musu hannu suka gaisa,gadonta ya hango ya gane na Jamilu ne tunda yaga kayansa a Kai,Let's go ta furta tare da ficewa waje,Bin bayan Jamilu yayi,Malam Sharu yace Allah ya shiryeku ku gane gaskiya,duk tunaninsa neman juna suke.

Spark yace yunwa nake ji dama,Jamilu yace sai kace na haifeka wai, kawo kudi a siyo Maka,Dan aiki nane Kai fa albashi zan biya cewar Spark, Jamilu ya karbi kudi suka tafi tare har wajen abincin ma, sai hakuri duk bai yarda da tsaftarsu ba amma yunwa bata da hankali,a wajen ya tsaya,Jamilu ya tafi siyo Masa shi Kuma ya kira Kamal yace wai baka fadawa masu kawo min abincin ba? Yace na fada musu gobe zasu dinga kawowa,wasu masu reception dake Kano Spark ya biya kudi kullum za a kawo masa abinci da rana shike nan.

Jamilu Yana siyowa suka taho suna surutu tana bashi labarin abinda ya faru tsakaninsa da Mummy har aka kawo shi gidan yari sai dai ya boye bai ce shi mace bane,suna shiga palonsa ya zauna taga ya linke kayan sawarsa,Abincin ya fara ci yace Kai baza Kaci ba? Jamilu yace na koshi yau naci wajen su Goje,Yana cin abinsa yace zan karawa Yan gidan nan tuka tuka guda biyu biyu both bangaren mata da Maza,sannan zan sa ayi musu Solar ta ruwa kowanne bangare naga babu ruwa suna Shan wahala,Zan fitar da masu kana nan laifi zan biya musu kudin tarar da suka kasa biya,sannan zan karawa Mata toilet block guda zanyi,suma mazan haka,sai wasu abubuwan da suka lalace duk zan biya a gyara,ya ka gani? Naila taji ya wani birgeta, tace amma zaka yi aikin Allah wlh mashaallah Allah ya biyaka da Aljanna,yace Ameen Allah nayi tawasli da shi Allah ka bayyana gaskiya na bar gidan nan,Naila Jamilu yace Ameen Ameen tare dani,yace see you a matsayinka na wa? Dariya tayi tace a matsayina na dan aikin me aikin Allah, ko baka so na fita? yace ba laifi in ka fita Ina murna,Jamilu yace baka kaunata bari na tafi,Spark yace ka zauna a nan mana ka dawo nan da zama,ka dinga tayani hira,Naila ta zaro ido tace a'a zan dai dinga zuwa ko yaushe,bai matsa ba yace okay fine,so yake Jamilu ya shagala ya samu ya lalube shi ya tabbatar namiji ne shi yasa yace ya dawo wajensa da zama,a ransa yace koma yane dai yazo watarana zai shagala yayi bacci wlh sai na cire Masa wando ko na taba kirjinsa naji ban yarda da wannan Jamilun ba.

Yana cin abinci Yana hada uban zufa,Naila ta dauki Dan karamin mificinsa na roba ta durkusa a gabansa kamar me daukan karatu ta fara Masa fifita,Yana cin abincinsa harda lumshe Ido




Ayi hakuri na makara yau bana gida ne


Sharhi please

Free page


Account no
0175487861
Asmau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login