Showing 30001 words to 33000 words out of 158722 words

Chapter 11 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

367

me kudin ba to ba Wanda zai shigar musu sai da izini,shima ba kwana ba idan da kwana to Wanda ya shiga shima sai an biya Masa kudinsa daban,yini ma sai an biyawa mutum zai yini a wajen,bangaren masu kudin ma shi ba wani me kyau can ba kawai Dan akwai kujeru da fridge ga toilet ko Ina tiles sannan har wanki ma da guga yi musu akeyi zasu iya dauka a cikin Yan gidan yarin suna biyan mutum hakkinsa Yana musu.
Spark da wayarsa da komai amma ya canja layika gaba daya sai in shi ya Maka magana sannan kasan shine,in banda Kamal da Rafeeq da ya nema ba Wanda ya nema sai Mummy dinsa me kaunarsa itama ya kirata amma sauran ba Wanda ya kira sabo da duk sun yarda zai iya kisan Kai.

Spark bakin ciki ya taru ya Masa yawa ya rasa Inda zai sa kansa,Naila kuwa tsabar bala'i sai da ta bada cin hanci aka barta ta shiga dakin Spark,tace wato ita duniya dai ko Ina me kudi yake akwai banbanci a lahira ne kawai kowa zaici kwal ubansa Kai daya muke, ranar ba wani me kudi,palon ba kowa bedroom ta shiga a zaune ta hango shi ya hada Kai da gwiwa Yana hawaye shi daya.

Naila tana shiga a hankali take sanda,ya ganta tun shigowarta,a ransa yace wannan Dandaudun ko maye shege tsinanne,Naila da karfin hali zama tayi a gefen gadon nasa, cikin Muryar Maza mazanta da take amfani da ita tace Allah sarki hakuri zakayi kaddara ce,wallahi ka saki ranka idan sharri aka Maka zaka fita watarana,Allah zaka fadawa kawai,gidan yari idan ka saki ranka akwai dadi ma itama wata rayuwa ce ta musamman Kuma zaka yi nishadi,ka kwantar da hankalinka ka saki ransa idan sharri aka Maka uban Wanda ya Maka sharri yaci... dan me..Kai Dan kut...nace durun....kai...duk bata karasa zaginba idan ta dakko sai ta saki ta kama wani.

Ka tsaya kana kuntatawa kanka kana namiji aradu ka fito a dama da Kai,karka bari kanka ya kulle,gidan yarin bata rago bace aradun Allah,gidan Maza malam anan zaka tabbatar da namiji ne kai, anjima kadan yau za ayi gala rawar solo ka fito kayi nishadi karfe biyar za a fara har dare, Spark a ransa yace iyyeee a gidan yarin? Bai San a fili ya furta ba,Naila tayi dariya tace ai har koroso kullum sai anyi da wasanni kala kala kazo muje na nuna Maka komai ka huta da bacin rai, tunawa yayi da Dandaudu yake magana sai ya bata ransa ya daure fuska,Naila tace wasa nake Maka ni ba Dan daudu bane kawai Ina kama da mata ne shine Yan gidan yarin Nan suke fada min haka,amma wlh ni ba Dan Daudu bane sunana na gaskiya Jamilu,Spark ya Kalli Jamilu wato Naila sosai,murmushi ta saki a ransa salati ya saki kawai yayi shuru shi Kam wannan mata Maza ne gaskiya bai yarda ba sai dai Matamaza.

Tashi tayi ta fice,tana fita ta koma wajen su Goje har hudu tayi taje tayi sallah a boye malaman dakinsu jam'i baya wuce su,suna fita take yin tata kafin su dawo, suna mamaki Bata zuwa jam'i iya wuya a daki take sallarta,wanka tayi a toilet din ta shirya tsaf ba Wanda ya taba ganin jikinta,kaya ta canja suma sai masu kauri burma burma na Maza,harda shafa turaren da Scoler ya bata sai wajen da ake musu wasan Solo lokaci zuwa lokaci,Yan solo sunzo harda Yan film an kafa kida an fara cashewa kowa ya zauna ana kallo wasu suna ihu suna liki,sai ga Spark kamar ba a gidan yari ba ya Sha kana Nan kaya sai shining yake dake sabon zuwa ne gashi kyakyawan gaske fari,ga kyan sura da diri,ga kwarjini da cikar haiba,Jamilu abokinsa ya fara dubawa a wajen can ya hango Naila zaune a gefe daya bata shiga gwamitsin kartai,kujera ta nuna Masa a gefenta,wasu munafukai harda gulma dama tunda naga kalar guy Nan nasan shima Yana harkar Daudu,Terror an samu Dan uwa,Spark hannu ya mikawa Naila yayi sallama,Naila ta kalle shi kawai ta basar ta share,Yan Solo suna cashewa wata Yar bariki har da zuwa zata rungume Spark Naila tace ke dalla matsa na saka miki guba ki shaka ki mutu bar Nan Dan uwarki tana zaro ido ta koma Yar Zara,tana zare Ido tana magana ta Maza ta Yan Zara,amma duk da haka mace sak.

A hankali Spark ya dago Kai ya Kalli Naila,dariya ta kusa kama shi,a ransa yace ikon Allah namiji ta karfi sai ya koma mace to naga Dan ubansa ta ya zai canja Banana dinsa,ai sai ya yanketa kawai idan ya isa,shi kadai Yana tunani sai ga scoler yazo Yana rangwada yace da Naila Tantiriya ta? Jamilu Naila ya kalle shi yace Na'am my love Ina ka shige ne Ina ta missing naka.

Dandaudu Scoler yace ahayyeeeee Yana tafi yace Dan ma har yanzu kinki yarda kiji dumin jikina,Naila tana shagwaba tace ai karka damu Darling tana so tayi kuka,Scoler ya dafe kirji yace na shige su ni Yar Nan karka bari hawayenki ya zubo tawan mene ne? Jamilu Yana rangwada yayi fari sannan yace ba Kaine ba sabo da Allah haka ake saurayin kaki zuwa zance bare ko kudin zance ka bayar gashi Dan liki ma bani da kudin yi,Scoler yace Dan Allah daina fada jiya aka turo min kudi ungo yasa hannu a aljihu ya zaro Yan Dari bibiyu na dubu biyu ya mikawa Naila,badan yau Saturday ba Alqur'an sai na rungume ka cewar Naila,amma anyi rashin sa'a yau cikar shekarar kakata ta wajen uwa goma Sha biyar da mutuwa,ranar bakin ciki ce sai nan gaba.

Scoler yace kiyi hakuri amma gaskiya kakarki ta cuceni data mutu ranar asabar ai sai ta bari zuwa lahadi Sunday yanzu je kiyi liki,Yan wasan kwaikwayo suna ta uwar rawa a fili, Naila ta mike tace zaku ci ubanku sisi bazan lika muku ba,caca zanyi muku,ta wuce ciki filin rawar,Dj harda fadar sunanta ana ta cewa Jamilu Tantiriya Allah ya tsare mana Kai,Naila ita da kanta dariya ta kamata ta dinga dariya,mazan Nan sai kallonta suke ana ta son Jamilu sai kuskus ake yi.

Naila ta zaro Dari biyu tayi mata rikon tsauri ta tsaya kusa da budurwar me tikar rawar tace a duwawu zan lika miki taje ta manna Dari biyu a duwawun budurwar Nan,da karfi tace aradu ciko ne ciko jama'a,Kuma ta rike kudinta Kam sai ta manna sai ta zare kudinta Yana makale a hannunta, mc Yana ta zugata Dan ta lika tace na ki wayon wlh ficikata baza tayi ciwon Kai ba akan me duwawun ciko ba, ana kallo ta fice tana cewa ciko ne wlh kar Wanda ya lika sisi gwara muci tsire ciko take mirgudawa,na taba maimakon naji wajen Yana karkarwa sai naji yayi dubush baya motsi kar kuyi asarar kudinku,suna ta dariya Yan gidan yari,amma sai da wasu suka lika kudin sosai,Scoler ya Maida kudinsa aljihu ya fasa likin yace asararru

Ba'a wasa da Yan daurin rai da rai ko sun kasheka to fa su hukunci daya dai gashi Nan shi yasa budurwar Yar film sum sum ta koma wajen rawarta bata ce kala ba duk tijarar da Naila tayi mata,kamar ba gidan yari ba yanda ake likin kudi ana zuba naira Banda Spark bare Jamilu Naila da ba gatan kirki shi yasa yaki lika sisi,Scoler ne yazo yace me yasa wai Baki yi likin ba? Allah ya hana likawa irin wannan masu yada badalar kudi haka Malam Jilani suka ce Kuma na dauki wa'azinsu,Scoler yace munafukan malamai Allah yasa kar su kashe Maka zuciya ka daina Daudu,Naila tace a'a wannan ko Sudais ko shureim na Makkah ne suka zo bazan daina ba Daudu yanzu na fara,Scoler yaji dadi yace yawwa ko Mufti Menk ne karki dauki wa'azin,Naila tace hauka nake Daudu for life.

Spark Yana jinsu ko harkarsu bai shiga ba.
Tunda Spark ya zauna baiyi Magana ba daka kallo sai danna waya har ya gaji ya mike zai tafi abinsa Naila bata kulashi ba itama,sai da ya tafi tace Dan iyayi wai shi me kudi dan ya samu ma Ina kulashi sai nayi maganinka.
Tashi tayi ta koma dakinsu Inda kasa kasa tana jiyo surutun mata dakin wasu a Jikin dakinsu yake,Naila ta Dora kanta a Jikin bango tace da karfi Ina son daya a cikinku,Mata ta bangarensu sukaji magana,wata a ciki ana ce mata Beauty tace Ina sonka nima sunana Beauty.

Kasa kasa Naila taji tayi tsalle tana murna,tace Inama da kofa da na Kalli fuskarki,sunana Beauty aka bawa Naila amsa mata sai shewa suke a dakin,Naila tace mashaallah zamu dinga zance ta Nan sunana Jamilu me zamani,Beauty tace daga Jin Muryarka ka hadu,Naila tace da zaki Ganni sai kin dalalar da yawu na hadu,Wata a ciki tace nima Ina sonka,Naila tace duk ku taho Ina sonku ni na mamajo ne ko wacce zan iya da ita,ya aka ji da rashin da namiji a kusa? Beauty da karfi tace muna fama wlh duk gamu taron balagaggu,Naila tana dariya itama da karfi tace iceko bakwa warin balaga? Malam Garzali suna dakin suna jinsu su tunda suke ma basu taba Jin Muryar mata ba sai yau,Kunya duk ta kamasu manya dasu gasu malamai Jamilu duk ya takura musu,ga kaunarsa duk ta kamasu sun rasa sukuni,Beauty tace Kana da waya? Naila tace me kika ce? Banji ba,kana da waya? Naila tace Allah sarki maraya ne ni,Beauty Yar gidan me kudin gaske ce itama kaddara ta kawota tace karka damu zaka yi waya me tsada zansa Daddy ya kawo amma sai munci gaba da soyayya Naila a ranta tace dole na dage naci kudin Beauty, Su Malam Jilani suna jinta sun kasa karatunsu da suke faman yi,Beauty tace da dare zamuyi free call ta jikin bangon nan,Naila tace karki damu sai anjima bye.

Ta Kalli Malam Jilani tace ku malamai ba a morarku sai dai ku Mori mutum wato tunda nazo Kun San maraya ne ni amma ko sisinku ba a ci haka aka koyar daku a Islamiyya,Malam Sharu ya zaro Dari biyar yace ita kenan gareni ungo Dan Allah ka canja wani dakin Jamilu,Naila tace tab Ina nan so kuke ayi min fyade,Malam Garzali a hankali yace mun shiga uku mu dai.

Umma ita kadai ce a gidan yara suna Islamiyya da yamma lis sai Abba yayi sallama ya dawo a gajiye Yana Nishi ya zauna Saman kujera,tace Kai Kuma lafiya? yace yau Nasha aiki jarkar Mai biyar na dauka a wajen aiki duba min kaina na fara sanko ko? Umma ta watsa Masa harara tace yanzu sabo da lalacewa akan ka dauki jarkar mai biyar shine abin gajiya haka har wani sanko zai fito Maka,Abba yace ke kinji nauyi ni gaskiya idan haka zan dinga yi zan bar aikin Nan bazan iya ba,Umma ce ta fashe da kuka,da sauri ya kalleta da Dan cikinta a gaba sanye take cikin riga da zani na atamfa,yace lafiya taki magana sai kuka take yi,yace haba Kubra menene? ta sake fashewa da kuka,Abba duk ya rude Yana tambaya menene? Sai da kyar tace Dan cikina nane yace a dauke shi,Abba ya bude Baki yace ta Ina yayi maganar? ya akayi ni banji ba, through placenta ya fada min uwa ce kawai ke gane yaren danta,Abba ya kalleta yace yanzu Kubra na gaji amma baza ki tausaya min ba,taya zan dauki jaririn Dake ciki? tace ai idan ka daukeni to ka dauke shi,Kubra gata me kiba Abba Dan tsurut haka ya Mike ya yunkura Yana Nishi ya dauke ta da kyar suka tsaya a tsaye,tace kaji wai a zaga da shi yace,Kubra nauyi ne Dake wlh kamar buhun sugar kiyi hakuri kuka ta fara ya fara zagawa da ita a hankali da kyar Yana Nishi,sai da taga ya Sha bakar wahala sannan tace yace a cinyarka zai zauna shi,Abba ya ajiyeta da sauri Yana Nishi kamar me,ya zauna ta zauna a cinyarsa yayi zuru da Ido ransa a bace sai da taga yara zasu dawo sannan tace to danwake zaka yi min yau yace shi zai ci,Abba ya kalleta kawai ya Mike ya shige daki tare da kulle kofar ya sa key shi bazai iya cewa bazai yi mata ba tunda ya Saba Yana yi mata watarana.

Mummy tunda aka kama Spark hankalinta fa ya tashi matuka kuka ba dare ba rana,duk ta rame ta lalace burinta taje taga Danta,sai lokacin ta tuna da Jamilu fa Yana can shima ta dalilinta,share zancen tayi duk da suna waya da Spark amma Sam hankalinta baya jikinta, Mima Kam abin a ranta yake dukanta Wanda ba Wanda ya gane Hakan sai dai a ganta duk ta fige ta rame,Daddyn su Spark shi kansa abin Yana damunsa amma ba yanda zaiyi.

Mima tana dakinsa ya kalleta a hankali Sam bata hayyacinta duk ta rame,tambayarta yayi yace meke damunki ne ko tunanin Spark ne? Mima murmushin karfin hali tayi tace a'a...idonta ya ciko da kwalla sai kuka bata San sanda ta fashe da kuka ba,Daddy ya kalleta cikin shigarsa na kayan manyan sojoji Yana Shirin fita,yace sai hakuri fa kaddara ce sai dai addua.

Rafeeq ne ya shugo ya same su a haka da sauri Mima ta goge hawayenta ta nuna ba komai shima Rafeeq duk da yaji zancen su bai nuna yaji ba,gaishe su yayi kawai sannan Mima tace ya school din? yace Alhmdllh,Kuna waya da Spark kuwa? yace dazu ma munyi waya da shi ai shi baya cikin wahala part dinsa ma daban,Mima tace yayi kyau na kira shi yaki dagawa ai,dole yaki dagawa ni banga laifinsa ba Yana da gaskiya,Ku Baku bari anyi bincike ba Kun kasa tsaya masa Wanda Kun San gaskiya bazai aikata ba amma kuka goyawa iyayen Asmau baya an bata Masa suna sabo da Yan uwantaka,dama Aunty ce ta aiko ni tace ki bata sakon na Kai mata,Mima tace to tana wani bata rai ta dakko sakon ta mika Masa a leda tace yaya kudin baka kawo ajiyar ba, fuska ya daure yace na bawa Aunty ya juya tare da ficewa abinsa.

Mohsin zaune yake Saman Sallaya Yana addua cikin tsakiyar dare Naila yake ta yiwa addua,Hanan ta farka tace wai har yanzu adduar ce kazo ka kwanta karka kashe kanka akan wata,ko kallonta baiyi ba,haushi ya kamata tace wannan Naila din kwai tsinanniya ta Hana mijina sakewa,a fili tace yau kwana nawa kaki kazo ka sauke min hakkina Kuma kasan Ina bukatar namiji a kusa,bai ko saurareta ba,ta ja tsaki tace wlh bazan yarda ba sai na kaika Kara wajen iyayenka kazo ka min abinda nake bukata, mikewa yayi ya bar mata dakin ya dawo Palo,tashi tayi tace wlh baka isa ba akan Yar iskar kanwarka ka wulakantani tazo Yana sallah ya tada sallah ta fado gabansa, ai kuwa ya Kifa mata Mari ya makar da ita gefe ta Fadi can gefe wanwar, sallarsa ya tayar, sabo da ta hanashi sallah ta dinga kururuwa amma bai fasa sallarsa ba har ta gaji.

Washe gari da safe ta riga shi tashi sai gidan su Mohsin Yana bacci Bai San ma ta tafi ba,tana zuwa ta samu Umma suna karyawa da yara yau ba school, tunda Umma ta ganta tasan ba lafiya ba,dama ta tsani Hanan bata mata kyauta kadan take jira,Abba kuwa Yana zaune abinsa ya gama karyawa Hidaya tana aikin gida yara suna wasansu.

Hanan ta gaishe da su Umma tare da fashewa da kuka,Umma tace in kin gama kukan Kya Fadi abinda ya kawo ki,ai ni kukanki farin cikin ganinsa nake yi Hanan Maza ci gaba wlh Inda kisan Ina kallon film din India sabo da nishadi,Hanan sai ta daina kuka Jin furucin Umma ta daure tace karar Mohsin na kawo,Abba ya mike zai tafi wajen aiki yace ki fadawa matar gidan gata Nan ta isa komai ya fice abinsa ya barsu,Hanan tace Umma Mohsin Yana zaluntata kawai hakuri nake zama da shi,Umma tace da ubanki zakiyi idan ba hakuri ba kowa hakuri yake ai nima da kika ganni me wari nake nema ban samu ba haka na hakura sannu shafaffiya da Mai, Hanan tace ai nawa yafi na kowa domin baya biya min hakki na kullum sai Sallah cikin dare,idan cikin dare yayi shuru Yana yiwa Naila Addua Kuma ko kema ai naga ba haka mijinki ke miki ba, Umma salati ta saki tace laaaaa wayyo sannu ai ni macece ta kwarai ni haka nake Masa irinki mahaukaciya shi yasa kika Ganni Ina shanawa sai abinda nace to na cika mace,ke fa? zaki min iskanci idan ke surukar zamani ce nima itace dai dai nake dake,marowaciya ko Dan kwai baki taba dafowa kince a kawowa Tsohuwar Mohsin taci ba,bare Dan sabulun wanka da wanki,kije ki tambayi tarihina a kauye kiji har saniya na taba bawa surukata kyauta Dan kawai na samu shiga,ke kuwa ko cinyar kaza daga ke sai danginki, Kun takurawa Dana sannan dare ma bazai huta ba ubanki zai miki cikin daren?

Duk fitsararki na haifi Wanda suka fiki ke idan da Naila tana Nan kin isa ma kizo har gida ki fada min kice wai mijina ba haka yake min ba,in Haifa miki yaro ki aura kizo Kuma ki ci min mutunci Yar matsiyata,Hanan tace to wallahi idan na fada halaka shi ya ja ai Ina ganin Maza gasu nan,Umma ta daga hannu sama tace ya Allah ka fito min da 'yata Naila tazo taci ubanki har gida, wayar Umma ce tayi ringing ta daga sai taji Muryar Naila,ta manta haushin Naila take ji sabo da Hanan taci mutuncinta, tace Naila ce wai? Naila tace ae Umma itace Jamilu ba,yawwa a dinga gyarawa sabo da tsaro ko kice Tantiriya is better Umma,ya gida ya kowa Ina Yar bakin ciki Hidaya? duk kowa lafiya Naila,iceko kina lafiya? tace to gashi nan dai a fadawa Yaya my love ya kirani da wannan number

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login