Showing 114001 words to 117000 words out of 158722 words

Chapter 39 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

393

Bf din ne?dariya Naila tayi tace ai gwana ce ni a kallo sanda Ina kauye, almajirai ne suke turowa iri iri,sai muyi musu wayo mu Karba aro mu buya tare da su Rayya mu ga...katseta yayi Yace Ai yanzu Allah ya shiryeki ko?tace sosai na shiryu Inda kaga carbi, ,Karba yayi yace thanks Dear,karki sake kallo kinji,tace me zan kalla Kuma gata mijina kullum in kwana da ita in tashi da ita, in Kalli ta uban wa ni Tantiriya kowa yaje da Hallarensa billahillazi,ga fara can a gidan.
Mohsin yace kuje Dan Allah,Beauty tace sai tawan Ina sonki ranar gaskiya ko agaban waye,Naila tace ke dai kici gaba da bawa Yaya Kindirmonsa na tafi ni,suka fice abinsu .

Suna fitowa Chika taje gidan yari da wuri taga Azima ta bata katin ta dawo,Lokacin Naila ta canja kaya wani Leshi dankarere blue black yaji hadadden dinki na musamman kana Ganinta ba sai an fada ba kasan an kashe kudi a jikinta.duk kayanta har lefe an shirya shi a mota Daya da dattijai biyu,mota Daya Kuma kawayen Umma su uku ba Hajiya Tagwadas Naila ta hanata zuwa, kar a ganeta yanzu,Mota daya ta Amarya da kawayenta Dije,Rayya,Chika,gaban mota Dije ce,Baya Rayya,Chikar da Amarya,motoci ne masu tsada da kyau,tana mota Umma tazo tace Naila kinji fadan da na miki ko? Naila ta washe baki tace ae.

Abba ne yazo shima yace Naila muna Nan muna aiko miki da addua kinji,kibi mijinki sau da kafa tace Inshaallah Abba,komai yace kiyi kinji tace angama Abba,yace danginsa abokansa da Yan uwansa kaf ke da duk Wanda ya shafi mijinki ki mutunta shi ki girmamashi,sannan karki rowa, Banda rowa a hana dangin Miji abinci ko abokai,kowa yazo gidanki ki tabbatar yaci ya koshi,kiyi koyi da uwarki Kubra amma Banda masifarta.

A mazan yanzu ba Wanda zaki Masa masifar Ummanku ki zauna lafiya baki isa ba komai son da yake miki,aure Kuma karki ce soyayyar nan da kuke yi a waje itace zaku yi a cikin gida,da banbanci, ayi hakuri da sannan karki ga mijinki Yana da kudi ki matsawa dukiyarsa lamba ke sai kinci dole na rabaki Naila,ki kula da mijinki ki tattale shi Kinga dai matan yanzu gasu Nan ko Ina kullum cikin kallon Maza suke suna kawo musu hari nima nan da kyar na Sha.

Sannan karki yarda ya kiraki shimfida kice a'a ko ki dinga Masa yanga ke gaki me baiwa,akwai karuwai a waje,Naila Ashawo Kwando kwando gasu nan a Abuja,zaki gansu bulbul duk kanjamau ce da su,karki bari Naila ya fada neman mata ko ba komai ya dakko kanjamau Kinga kin cutu,muna kallo zaki rasu,wand bama fata muna miki addua kinji.

Naila tace yawwa Abba haka nake so,in kinje danginsa ki bude Ido ki nutsu ki karanci kowa ki iya zama da kowa kinji,Kuje Allah ya tsare Allah ya kaimu lafiyaaaaa....Abba ya karasa da kuka Alhmdllh Allah ya cika min burina na aurar da Yata mace lafiya ba cikin shege ba Dan shege,ba Wanda ya tsallaka min ita,ba abin kunya,ga Mohsin ma Dana guda ya Kara aure, wannan abin murnane da alfahari a wajena, wai yau ni Hashimu Dolo ne ya aurar da yarsa mace dansa Kuma ya Kara aureeeee ......sai yayi cikin gida Yana kuka.
Har masu Kai Amarya da driver dariya suke kamar ba gobe.

Waye Spark ne?


Ayi hakuri bacci ne ya daukeni



A dinga sharhi pls






AsmaBaffa
[12/23/2023, 12:08 AM] AsmaBaffa: Paid group 300

Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank

Yan Niger
+22790795939

🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI

BOOK 1

81-85

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKU NE
Ummin Saddiq
Aunty Nurse Zaria
Uwar Batoola


*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262


Ashraf Ahmad Maleek, kakansu wato Maleek Dan asalin kasar Somalia ne,Matarsa Zeenatu Yar asalin Nigeria ce Katsina state,Maleek hamshakin me kudi ne tun a zamanin da,Zeenatu matarsa tun tana karama ta fara bin Maza,Wanda gidansu suna da rufin asiri baza ace babu ce ta kaita ba.

Daga haka ta fara guduwa Bariki sai a nemeta a rasa, sai sanda taga dama take dawowa gida,idan ta dawo zata zo da surutu masu tsada da kudi in tayi kwanaki kadan ta koma,su biyu iyayenta suka Haifa yayarta ita ta gari ce Bata Dade da aure ba Allah ya mata Rasuwa a ka bar Zeenatu wacce Bata Jin magana ko kadan,sai yawon karuwanci ta sa a gaba,iyayenta sunyi kuka sun gaji sun mata addua sosai,a yawon karuwancinta ta hadu da Maleek shima ya leka Bariki ya Maidata dadiron sa har Soyayya ta kullum tsakanin su, suka tuba daga Bariki suka dawo gida aka daura musu aure.

Bayan ya aureta ya dauketa zuwa kasar su can Somalia acan Kuma Allah ya bata ciki ta haifo Danta namiji Uzairu, daga shi Bata sake haifar namiji ba sai mata,ta Haifo yarta ta biyu Salamatu,Khudrah,Yusra,Lateefa,sai Allah yayi mijinta Maleek ya saki Zeenatu.

Bayan ya saketa sai ya auri wata matar a can kasar sa ta haifar masa Surayya,Rafeeqah,daga Nan sai matar tasa ta mutu, ya dawo Nigeria Abuja suka daidaita aurensu,Zeenatu tace ita baza ta koma kasar Somalia ba,sabo da Yana sonta ya tattaro yaransa suka dawo Nigeria gaba daya,sai da yaransu suka girma kaf suka aurar dasu bayan kowanne da karatusa da sana'ar yinsa,duk yaransu sabo da kyawawa ne babu wacce ta auri talaka a ciki ko wacce me kudi ta aura a garin Abuja.

Salamatu wacce aka fi sani da Mima itace ta fara aure,ta Auri matashin Soja me ji da kudi Ahmad,Allah ya Bata haihuwa,haihuwarta ta farko Khalid ta Haifa wanda shima Soja ne babba a yanzu a Lagos yafi zama tare da matarsa da yaransa hudu.
Na biyu ta haifo Nazeer lokacin anyiwa sauran Yan uwanta aure amma a cikinsu mutum hudu basa haihuwa,taso ta haifi yara mata sabo da ta basu su kyauta su rike amma Maza take Haifa,gajiya tayi ta hakura tana sake haifar Ashraf wato Spark kyakyawan gaske ne na karshe, ita kanta tana sonsa amma haka ta hakura ganin Yar uwarta Surayya ta damu da shi,kullum Ina Danta sabo da Spark kullum sai tazo gidan,kullum tana siyo Masa abubuwa,Mima tana yaye shi ta kaiwa Surayya har gida tace gashi nan ta bar mata tsakani da Allah har abada ya zama nata,babu ruwanta Kuma ko shiga safgarsu baza tayi ba.

Surayya sai murna amma Sam mijinta Alhaji Aliyu baya son rike Dan wani shi,kawai sai ya tsani Spark,tun Yana yaro har Spark yayi hankali yasan Mijin Mummy baya kaunarsa,gashi Mummy ta shagwaba shi sabo da haka ma Yana gama secondary ta dinga koya Masa business iri iri Kuma Allah ya taimake shi din,Makarantar Soja ta sashi sai da yayi nisa yace bazai iya ba shi,a haka tana lallaba shi ya daure har ya gama ya fito a Soja sak,ana turashi yaki wata kasar yayi resining dama ba so yake ba ya bar aiki,dama shi ya gaji Yana so ya dinga tara sumarsa da shanawa duk babu kullum aiki aiki duk yayi duhu zai lalace yace bazai iya ba,baza a canja Masa halitta ba haka kawai akan fatararsa ta lalace gwara ya zauna da talauci.

Yo Mummy ta gama shagwaba shi baya Jin magana,gashi da mugun ra'ayi idan ya kafe a Abu sai dai a kyale shi,ba a Masa dole shi,ya taso ba abinda yake nema ya rasa, Alhaji Aliyu Kuma baya sonsa tun asali,zagi hantara duk Yana Masa har ma ya daina jin haushi, Mummy kasar waje ta turashi yayi masters akan business,dama tun Yana secondary take biya Masa kasar waje tana kaishi, Yana zuwa hutu can ya shakata har ya girma kullum a tafiye tafiye yake kasa kasa baya rayuwa sosai a kasa Nigeria.

Gashi da Nasibi a rayuwa,tunda suka taso su ba musu fada duk abinda kayi daidai ne,su kansu su Mummy iyayensu sunyi duniyanci kadan, daga baya suka tuba,basu basu wata tarbiyyar kirki ba bare su bawa wani.

Spark kullum kudinsa na bunkasa ganin mijin Mummy ya tsane shi sai ya Gina gidansa katafaren kawai ya koma can,Alhaji Aliyu da kansa yace Spark ya daina kulashi sabo da bakin ciki yaga yaro ya girma a gabansa yazo ya fishi kudi.
Mummy suna yawan zuwa asibiti akan rashin haihuwa amma sai ace kalau suke mijinta ne da matsala,sannan baya iya biya mata bukatarta,a haka ta hakura take zaune da shi,ya Sha gwada nemo aure Mummy ce take ruwa da tsaki ta Hana auren ta hanyar masifa da tijara .

Tunda taji ance ita kalau take kullum suna yin fada da Aliyu zata Masa gorin haihuwa tace hakuri take alfarma take Masa,ga shegen son kudi duk family din su Mummy haka suke su da sunga me arziki to shine nasu,sannan duk kusan kangararru ne basu da kyawawan halaye na iyaye mata,shi yasa tunda mijinta Taga lallai aure zai kara da gaske Taga ita bata haihu ba,ta ya za a kawo wata idan ta haihu ita shike nan baza ta samu gado ba,akan gado taga gwara ta kasheshi.

Tana tunanin ya zatayi idan ta kashe shi ta tsira kar a gane itace sai katsam Jamilu yazo me magani dabara ta fado mata ta aikata.

Bayan Mima ta bada Spark sai ta sake haifo namiji Misam ta dauke shi data yaye shi sai ta bawa Dan uwanta Namiji Uzairu lokacin Dansa Daya a duniya tal wato Kamal, ya dade da aure Kuma ,sai ta Kara Masa da Misam,bayan an bashi Misam sai Kuma ya Kara aure duka matansa suka dinga haihuwa sai da suka haifar Masa yara takwas Kamal shine babba shine Kuma mate din Spark,abokin Spark ne tare sukayi school,amma a kasar waje Kamal shi Engineering ya karanta ya dawo Yana aikinsa Yana samun kudi,ya Gina gidansa shima sannan Yana da budurwa har an kusa biki ma.

Misam shi matar Uzairu ce bata kaunarsa,idan mijinta baya gidan sai ta dinga dukan sa tana zagin sa,idan mijinta na gidan ba Wanda take so kamar Misam a gaban miji,Yaranta sune yara su take wa fada da tarbiyya,Misam ko me zaiyi baza ta yi Masa fada ba, har ya taso ya girma ya fara yawon dare amma bata taba yi Masa fada,tana kallo Uzairu Bai sani ba Idan ma taga zai gane sai ta boye ta kare zancen kar ma ayi Masa fada ya shiryu,har Misam yayi nisa a neman mata sannan Kuma Kamal ya gaji ya fadawa Abbansa Uzairu,Uzair hankalinsa ya tashi an bashi Amana.

Yaransa kaf gasu Nan a shirye amma na wata an bashi ya lalace a hannunsa sabo da rashin kula,ya dawo lallai sai Misam ya shiryu Misam yace kayi sake Baba da baka bibiyar Amanar ka, ka manta matarka azzaluma ce kawai ka barni a hannunta ba ruwanka da bincika me ake min Ina ta nuna Maka ka gane kaki sai da na lalace, yanzu bazan daina ba nasan mata nayi nisa,kullum ana bata min rai ba dole na tafi Inda zanji dadi ba,Ba irin nasihar da bai yiwa Misam ba yaki ji,sai addua ya koma a dalilin haka ya saki uwar gidansa gaba daya Kuma yaki dawo sa ita har gobe.
Kawaici irin na Mima Bata taba zancen ba tasan Kuma me Misam keyi, tana yi Masa nasiha ma amma bata taba zancen ba a wajen wasu, ko da kuwa ace danginta ne, tunda ta bayar ta Bada tsakani da Allah, babu bincike ya zama Danka duk da tana Jin ciwo tasan ana zaluntar Misam a gidan amma ta hakura.

Bayan Misam duk sauran Yan uwan suna haihuwa su har su Babar Wahida,mace daya ce Bata haihuwa itama, ita Kuma uba daya suka hada da su Mima, Yan ubanci yasa ta hanata Dan ita,Ahmad Mijinta shine ya dauki Rafeeq da hannunsa ya bawa Yusra itama yace ai babu dadi kin bawa Wanda kuke uwa daya uba daya kin Hana waccen Dan Kuna yan Uba,Mima tace ni wlh banyi niyyar Bada Rafeeq ba duk yarana kyawawan ciki duk na bayar dasu,yace kika Bada Spark ma wato ita waccen Dake Yar uwarki ce uwa daya uba daya,me yasa yanzu zumunci ba ayi Dan Allah? ba kara ba komai, kowa Keke da Keke wlh ni na bata Rafeeq ya dauke Rafeeq ana yaye shi ya bata kyauta.
Duk Wanda suke uwa daya uba daya da Mima sai da suka ji haushi.

Shike nan Mima ta tsaneta sosai sannan tayi mugun sawa Rafeeq Ido,ta takura Masa har ya girma idan yaje gidan sai ta dinga tambayar shi me da me ake Maka? Kana cin abinci? Bata dukanka? sabo da haka Rafeeq ya daina zuwa gidan ya tsane su gaba daya har su Khalid ba ruwansa da kudinsu da kayansu,shi yafi son wacce ta raine shi, akan a zageta gwara a zage shi,ba Wanda ya isa ya taba Masa wacce ta Raine shi,ita Kuma Yusra mijinta akwai kudi amma ba wani sonta yake ba,aurenta yayi sabo da sha'awa tana Masa biyayya iyakar iyawar ta amma baya Gani,ya tsaneta ma sai auri saki ya iya, Dake shine baya haihuwar, gashi da mugun son kudi Yana da kudi amma baya ciyar da iyali,kullum gidansa garau garau ake ci a haka ma da taimakon Rafeeq,Yusra tana Shan wulakancin da namiji tayi tayi ya saketa yaki Kuma Bai fasa wulakantata ba,duk abinda tayi Dan ta birge shi to fa bata birge shi, shi tsabar mugunta ma baya so wani ya taimaka Masa a gidansa amma shi zaici me dadi a waje zai sa suturar da yake so sannan zai hau motar da ya ga dama amma banda iyalinsa,Rafeeq ganin haka ya fita shirginsa,Spark ne ya dauki nauyin karatun Rafeeq da komai nasa,da kasar waje zai kaishi yace a'a ya barshi a Nan Nigeria sabo da Mama babu Mai taimakon ta sai shi, Spark yace ya Fadi sana'ar da zai iya ya bashi jari,yace ai shi joint za a bude Masa,anci dariya aka bude Masa Kato me kyau da ma'aikata da komai shike nan ya zama Baban shawarma joint,ga school dinsa Yana zuwa private da hostel dinsu sabo da tsakanin su da gida akwai nisa shi yasa.

Mummy Kuma tunda Taga Yana samun kudi Yana taimakon Yusrah mamansa wacce ta Raine shi sai haushi ta sawa kudin Rafeeq Ido,sai ya tara kudinsa a accnt sai tace lallai sai yazo ya bata kudi,ta dinga ta karbe kudin ta hanashi gaba ta hanashi baya,ko yaushe a Dora jari Spark yake watarana Kuma Misam Yana bashi,Khalid ya siya Masa mota amma ya siyar ya Dora jarinsa shike nan suka yi fada da Yan uwa Dan me zai siyar da mota ya Dora jarin Shawarma,Sai ya daina kulasu du sai yaga dama, ya fita harkar kayan su, ko an bashi baya karba tunda ana Masa gori a dinga sashi Yana yin abinda baiga dama ba.

Mima kanta sai Kara ta kaiwa Spark ta Rafeeq ya daina kula su gashi gashi,ya same shi ya Masa fada shine ya Dan sakko,amma idan ba Spark ba da Misam ba ruwansa da sauran,shima tarbiyyar tasa da gyara sai dai bai Kai sauran lalacewar ba.

Bayan an bayar da Rafeeq Mima tace ta gama Bada yara a duniya, sai ta haifo mace Kuma,a da matan taso ta raba sunfi dadin raino da tankwarawa,idan macece Bata da matsalar Maza sai yanzu Kuma ta haifi Bisma wacce itama tayi aure da yaranta biyu tana zaune a Uk,sai Badia itama tayi aure da yarta Daya a garin Bauchi,su ma basu da wata tarbiyyar kowa harkar gabansa yake babu me yiwa wani fada,Wanda kake shiri da shi to da shi kawai zaka yi zumunci.

Daga Nan Mima ta haifo Waleed,Atif,Arham duk makarantar sojoji sukeyi matasa dasu,sai Kuma ta haifi mata biyu Anam,Zainab suma duk sun zama Yan mata haka marasa tarbiyya ne,ga kudi ga sakaki na iyaye sai abinda suka ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login