Showing 75001 words to 78000 words out of 158722 words
Chapter 26 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
cewar Mummy,Naila tace gaskiya fa sai local mutane Ina yinki uwar dakina,Spark Muryar ce take Masa gizo a kunne sai yaji kamar yasan Muryar,kallon Naila yayi yaji kamar Jamilunsa wlh,amma ai Naila bata waye haka ba,Yana ta kallonta a sace duk ta rufe fuska da gashi da glass ya kasa tantancewa amma wlh kamar Jamilunsa,Mummy ce ta mike tsam tace Nasiba Yankan kauna bari na kawo miki abin motsa baki,Mummy tana tashi Spark ya mike zai fita Naila ta kurawa saitin Hallarensa Ido,kallonta yayi yaga ta kurawa jikinsa Ido,fuska ya daure kamar bai taba dariya ba,yace ke lafiya? Ina Naila ai ta Lula kallon Hallare ya ta koma,yace ke wai baki da hankali ne me kike kallo,Naila tana kallo tace wait sir, are you out of your mind? are you normal? Naila tana kallo tana matsawa tace Sir sorry Ina bada magani baka da lafiya,abarka bata aiki,Spark tsaki ya ja ya juya ya fice Naila ta tsaya a palon tace yaki ya bari a gani amma ba komai dole sai na ganta bari naga gidansa.
Ko Mummy bata jira ba ta jira ba ta fice ta shiga motar tabi bayan motar Spark amma Ina motarsa ta bace mata gidan Mummy ta koma,tana shiga Mummy tace Ina kika shiga ne? waccen Dan naki Aljanu sun aure shi bazai taba aure ba sai Kun tashi tsaye Mummy tace ke Dan Allah wlh anyi anyi yayi aure yaki baya son ko wacce mace,Naila tace sai an Masa maganin aljanu Kinga ni yae film ce amma Ina Bada maganin aljanu,Mummy tace wlh indai zai warke ba matsala bani da burin da ya wuce naga Spark Dina yayi aure,Naila tace dole sai na tare a gidansa idan ta kama har kakana zan kawo ayi Masa magani,Mummy sun matsu Spark yayi aure suka ce ba komai kawai zan Masa dole ma ya bari ayi Masa magani.
Naila a ranta tace oh na canja shigar Maza nazo Dan na samu shiga karshe na fada prison,gashi yanzu a banza nazo a Yar gayu sun yarda dani Kuma,Mummy tace idan zaki iya farawa to gobe ki ajiye film din nan Ali nuhu ya canja wata idan ya warke kina da 1million,yanzu zan sa a miki kudi dubu dari biyar a accnt in kin gama aikinki zan baki cikon kudin,Naila tace an gama yo film din banza na fada masa ya nemi wata suyi rawarsu,gobe zanzo ki kaini gidan da kanki,Mummy tace ba damuwa,Naila tace karfa ki Ganni da shiga me kyau wlh bani da wani kudi mu kin san harkarmu ta celebrities haka muke da karya da fake life amma idan kika ga gidanmu kare bazai shiga ba,Kinga Ina Hawa mota na gyara jiki na sa kaya masu kyau to da cuta zata kamani shike nan sai dai aji ana neman taimako a gidan radio,Mummy tayi dariya tace ai mun sani dama.
Naila ta gama ta fito tace yanzu ta spark nake tukun kafin na dawo kanki,wai dama Ashraf shine Spark amma ba karamin munafuki bane Yana jina Ina nemansa Ashe shine ya min banza sai ya gane kurensa tunda ya raina min hankali bazai taba gane ni Naila bace sai na sake cin tudu biyu a soyayya,tunda ya Soni a Yar gidan yari to yanzu Kuma zai Soni a Yar gayu.
Ashraf Kuma tunda ya fita yake tunanin wannan yarinyar yace anya kuwa wannan bata da hadi Jamiluna,bari Allah ya hadamu idan da rabon na sake kallon Jamilu timbir ai shike nan,zata gane kurenta duk gashin Nan sai na cire shi in na samu dama ai nasan kalar boobs din nata da can wajen Garejin, ai nafi tantancewa idan na sake gani,murmushi ya saki yace Allah ya sake hadamu wayo zan mata.
Yau kwana yayi da farin ciki da murna yaga me kama da Jamilunsa,Allah Allah yake su sake haduwa,Naila ma tafiya tayi taji dadin ganinsa Kuma ta fahimci bai ganeta ba,ga kudi zata samu nan take ta bugawa Chikar gayu waya tace ki bar gidan Mima kice za a miki aure ki dawo gidan Mummy ki dinga hada mata tuggu kina gana mata azaba,Chikar gayu ita kaunar Misam tuni ta kama ta ma, bata yin abinda akace tayi iskancinta kawai take a gida,duk abinda akace tayi ba shi zata yi ba ta buwayi kowa ta gallabe su,idan akace ta soya dankalin sai ta soya doya,in akace kosai sai tayi yamballs,kowa yanzu tsoron sata dafa Masa Abu yake sabo da an San ba shi zata kawo ba anyi anyi bata ji,Misam dinma bai san me take ba domin bai cika zuwa gidan ba.
Chikar gayu tace ni bazan koma gidan wata ba na Saba da Nan gaskiya ni nayi miji sabo da haka a gidan surukaina nake bazan zubar da damata ba,Na hadu da wani cool guy,kije kiji da aikinki nima nawa nake yi, Naila tace ba komai wlh sai nazo gidan na tona miki asiri,Chikar gayu tace ba komai nima Ina ji da nawa ai iya shegen sabo da haka na gani Kuma na yaba,Kuma tunda na kulla Masa sai na aure shi inshaallah,kin fasa basu tarbiyyar? ae na fasa idan na aure shi nafi bashi da kyau ,Misam ne ya shugo gidan sanye da yard me tsada fari yayi kyau,Chikar gayu wayar ta kashe ta kalle shi ya galla mata harara,tace an musulunta ashe yau anje masallaci,ashe kana sallah ai ban sani ba,Rafeeq ne ya shugo Chikar gayu ta gane shi sai yau ta ganshi a gidan tace ai da Gani ba tambaya kaga munafuki dama shima a nan yake,kafin Rafeeq ya kalleta ta mike da gudu ta fada kitchen tana cewa shinkafata zata Kone, ba girkin da take yi,lekowa tayi kadan suka yi Ido hudu da Rafeeq Baki ya bude zaiyi magana ta hau rokonsa da hannu yayi shuru kar ya fada tana nuna Masa yayi shuru da hannu,Baki ya tabe,Misam yace ke kawo mana abinci Yana harararta.
Chikar gayu ta shige tana dube dube sai ga kyankyaso kato ya fito daga cikin wani lungu, da sauri tasa tsinken tsintsiya ta tsire kyankyason ta dora a plate ta rufe ta fito kamar abin arziki tace sannunku ta ajiye a gaban Misam tace gashi tana yin kasa da Kai,Misam yunwa yake ji Yana bude plate yaga katon kyankyaso a soke a Jikin tsinke,mikewa yayi Chikar gayu ta mike tare da kwashewa da gudu ya ya bita suka yi waje da gudu,tsayawa yayi yace sai na harbeki idan na sake ganinki Yana huci,ya dawo ya samu Rafeeq ma ya fice shi Yana jinjina rashin Jin Chikar gayu.
Yau cikin dare Umma ta fara nakuda,Abba dole ya farka daga bacci,Umma tace Ina Jin haihuwa ce tashi ka daukeni na rasa Inda zan saka kaina,Abba yace da wannan uban cikin kamar zai taba kasa ga kibarki ta ya zan iya kalleni fa sai kace kazar mayu,Umma tace wayyo bayana ka daukeni Hashimu kaji na fada Maka,Hashimu yayi yayi ya daga Umma ya kasa,Umma haushi yasa da ciwon nakuda ta mike zumbur ta dauki Abba Dolo cak ta jefa shi a Saman bed tana masifa,Abba yace na zaci ma shillo shilloriya zaki min ai da naji dadina,Wani takaici ya kama Umma tace ni mu tafi asibiti,Abba yace yanzu karfe 1 na dare a fita yanzu,Kai dalla in zaka samo me napep ka samo,Abba ya tashi ya fice ya bugawa makwafcinsu kofa yana da Napep ya fito yace Hashimu lafiya? Wlh iyalina ce zata haihu take ta nakuda shine za a kaita asibiti,makwafcin yace Allah sarki ai da ka iya tuki ma da na baka ka kaita kawai,Abba yace ni da ko Keke ban iya ba bare machine ko wani Napep,tunda kake ka taba ganina a kan Keke Ina tukawa, Ido makwafcin ya zaro yace Hashimu duk kiriniyar Yaya Maza suna yara amma baka iya ko Keke ba,Hashimu yace ai ko kyauta ka bani mota sai dai na siyar bazan iya tukawa ba.
Makwafcin key ya dakko yace muje amma Kai mace ma ta fika kwazo,Abba yace hmmm rabani da tuke tuken nan bazan iya ba Allah na Gani ai sai na manta na taka birki a matsayin totir ko naje na daga hand break din mota a tsakiyar titi,Makwafcin yace amma ka cika lusari ,yace Kun Dade Baku fada min lusari ba ko Dolo dama ni nace muku ba Dolo bane ni?,Shuru mutumin yayi yace ni Ina mamakin ma da Kubra take iya rayuwa da wannan Hashimu,Hashimu ya shugo Palo yace to taso uwar biyu,taka a sannu,Umma ta mike da kyar ta nuna masa kayan haihuwar data hada tace dauki muje Dan Allah kayi sauri wayyo Allah marata faya ta fashe,Abba yace Allah yasa fafunga ce ta fashe ba faya ba,ko kogi ne ya tsage kin isheni da kwailo, Allah yasa na kusa Kara aure Batoola tana nan dai tana jira,Umma dakin su Hidaya ta leka tace ke Hidaya,shuru,zafin ciwo yasa ta dirkawa Hidaya duka tace tashi ke mun tafi asibiti kuyi min addua ki tashe su kuyi Nafeela da addua,Abba ya leko yace ku hada Dani, Hidaya harda kuka tace Umma zan biku,Abba yace harkar bata yara bace ku zauna ni na isa komai,Umma Mohsin ta kira bugu daya ya daga dama sabo da cikin Umma ya tsufa shi Kam kullum a ready yake,Yana ganin kira ya daga,kasa magana tayi ta rike ciki tace wash,Abba ya karbi wayar yace Mohsin Umma haihuwa ka taho asibiti Maza private Kuma zaka biya,Mohsin yace to wanne? Abba yace asibitin Uba,Mohsin yace banji ba me? Abba yace faya ta fashe faya sauri muke ya kashe wayar.
Umma ce zata ruko shi ya kwace da sauri tare da daka tsalle ya koma gefe yace bazan manta yanda kika kusa kasheni ba a haihuwar Hidaya,muje Ina daga baya baya,Umma ta shiga napep tana wash tana cijewa,Abba ya shiga gaba wai Dan kar ma ta ruko shi taje ta shake shi,Umma ita kadai a baya tana ta Jin jiki,Mohsin zai fito ya saka kaya Hanan tace wlh ba Inda zaka ta rike shi Yana Juyowa ya kwada mata Mari ta sake shi ba shiri yaja tsaki ya fice abinsa ya hau machine ya dinga fyalla wuta,Yana kiran Abba yaji Ina suka nufa Abba sai fada Masa yake Mohsin faya ce ta fashe,Sai me napep dinne ya kwace wayar suka yi magana da Mohsin sannan suka wuce private hospital,kafin suje ma Mohsin ya riga su zuwa har ya biya komai ana kawo Umma Mohsin shi ya rike Umma ya shigar da uwarsa har ciki,ya kira Hanan yace ki shirya zanzo na daukeki,tace ni bacci zanyi sanda na haihu ni waye yazo min,dama nifa gaskiya wayata da aka sace min da kayan sawata Ina zarginka ko Kaine ka kwashe ka kaiwa Hidaya,wayarsa ya kashe kawai ransa a bace,ya kira Hajiya Tagwadas kafin ma yaje ya dakkota har tasa an kawota a Napep dinta da ake mata haya,Abba dake asibitin private ne Yana ciki,ance ya fita yaki yace duk haihuwar matata tare muke yi bazan fita ba.
Batoola kuwa an daura mata aure Abba bai ma sani ba shi kuwa Mohsin har daurin aure yaje amma yaki fadawa Abba suka barshi Nan Yana jiran Batoola,sun hada baki akan kar a fada masa Batoola tayi aure sai sanda ya koma zance yaji.
Ana ta jiran Umma ana mata addua Abba yana ciki tare da Hajiya Tagwadas tace Dan Allah Hashimu ka fita ka bamu waje wai me zaka gani ne wannan masifa da me tayi kama Kai ko kyankyammi baka yi? Abba yace gudan jinjina da Rabin raina Umman Mohsin na fita na barta ai bazai yuwu ba Sam,haka aka kyaleshi,mata suna taimakawa Umma ana kokarin fiddo da Baby Hashimu yace kar ku kashe min dana wlh karku soma.
Allah yasa dai Umma ta haifo yarta mace kyakyawa da ita kamar Yar Mohsin da Naila suna kama,Hashimu bayan an goge jajirya katuwar gaske aka miko Masa yace macece bazan Kalli tsaraicinta ba ku nadeta a zani,haba ai ba tsari na Kalli na uwa na Kalli na 'ya, aka nadeta tare da Mikasa duk ya dame su a dakin,ya karba ya mata adduoi sosai a kunne sannan ya taba kumatunta yace.. Yan... Yan.. Yan kin ganni sunana Abba,Hashimu ne idan kin girma zaki ji inkiyata mummuna wacce baza ta miki dadi ba Hashimu Dolo,Nurses sai dariya suke kamar me, Mohsin Abba ya kawowa Yar Yana cewa kaga kanwarka ya ka ganta katuwa kamarku daya,uhm ansha warin gardawa a ciki da Wiwi Allah sa kar ta samu cutar warin Kashi,irin wannan wari data shaka tun tana ciki sai addua,Mohsin shi kansa Abba dariya yake bashi sai kace a kanta aka fara haifar Masa yara,sai murna yake yace sai nayi sati guda ban siyar da kayan Miya ba sai bayan suna,Mohsin yace Allah ya kaimu shima yayiwa kanwarsa addua sannan yace ya Umman Abba? garau take da ba lafiya ba ai baza ka ganni a waje ba,Mohsin a ransa yace ta wani fannin Uwata tayi dacen miji.
Naila washe gari da wuri taje gidan Mummy a taxi da katuwar akwatinta zata koma gidan Spark da zama,Mummy tace gaskiya na yarda da gaske kike harkar nan,Mummy ta shirya cikin kana nan kaya matsatsu ta yafa Dan guntun mayafi tace muje,Naila ta zaro ido tana kallon Mummy a ranta tace tab,motar Mummy suka shiga,Mummy ta tuka suka nufi gidan Spark, Yana bacci kasancewar ba aiki yau Sunday, har gidan Mummy ta murza hancin motarta ciki, bayan tayi parking Naila tace nazo gidan mijina gidana,tana kallon gidan tunda take bata taba ganin gidan da ya tsaru haka ba sai yau a gidan spark,gidane Wanda an kashe Masa kudi iya kudi,ko da ya fito daga prison sai da aka sake canja kusan komai na gidan, ga motocinsa Nan masu tsada iri iri, duk Inda ake neman gida to gidan Spark ya Kai,Spark ne ya fito Jin mota ta shugo Masa gida,Sanye yake da gajeren wando baki da Yar tshirts brown ba karamin kyau yayi ba duk kuwa da cewa daga bacci ya tashi.
Naila ya kalla ta canja glass yau tasa brown ya mata kyau,sanye take cikin atamfa riga da skert sun masifar mata kyau,ga gashin ya yarfo a fuskarta ta yafa mayafi kawai ba dankwali a kanta mayafi ne a Saman kanta,Spark dariya yayi a ransa yace haba yarinya sai dai kiwa wani basaja ba ni Spark ba,yace wannan karya ne Naila ce yace ni da na zauna tare da ita mun kwana bed daya ma lokacin tana Jamilunta,Bata gaji da wasan nan ba lallai yarinyar nan yarinyar nan da taurin hanci take,Ashe da rabon zanyi kallo na biyu kenan,murmushi yayi a fili tare da danne lip dinsa na kasa da hakoransa na sama,ya Bata rai yace wannan fa, good day sir cewar Naila tana wani sirara Murya,kallonta yake sama da kasa murmushinsa ya kasa boyuwa yace ashe dai Yar wanka ce ko Kuma basaja aka dawo yi min,Mummy tace gata nan zata zauna da Kai zata dinga Maka girki,sabo da kana zama da yunwa ko ka dinga yi da kanka Ina raye bai dace ba,shi tun da ya yaji zancen yasan da wata a kasa Mummy ita tasan me Naila ta fada mata,Kuma shi yasan Naila dai zagin Ashraf take zata dauki fansa kenan ya furta a ransa,wow wannan yarinya amma zan bari naga ni me zata min ta dau fansar ita Kuma Mummy idan bata yi wasa ba kwana nan zata shiga prison domin indai ya tabbata Naila ce wannan to wlh ko makawa babu fansa tazo dauka,Mummy Taga Yar gayu ta yarda da ita Kai duniya,da wani bagidajene yazo baza ma ta kula mutum ba,shi sai yanzu ma ya gano bakin zaren,yace lallai yaro yaro ne Kuma mace mace ce tab,zanga ni ya za ayi dani.
Spark shi bai San tuni ma Naila ta kwantar Masa da Hallare ba yanzu ma magani tazo ta Masa ba tare da ya sani ba shine dalilin zuwanta gidan, shi Kuma yace dole nayi taka tsan tsan da Jamilu yanzu haka ma tunda ta gano nine Ashraf to ta daina so na tabbas,amma bari na gani ya zama dole na kula da me zata yi sannan na dage da addua Allah ya rabani da Sharrin Naila ta shiga bani tsoro,ashe da gaske take, jikinsa ne yayi Sanyi sannan yaji haushin Naila matuka da tazo da niyyar cutar da shi,yace amma ba komai ni Kuma wannan karon indai su Mima sun kawo min matar aure ko wace zan aureta kawai,gaba daya Nan take ya canja kala idonsa ya canja wani tsantsan bacin rai ne kwance a fuskarsa,yace maimakon ta hakura muyi aure kash,juyawa yayi yace zata iya shugowa na amince ta zauna ya wuce kawai ya haura sama.
Naila tasan kayanta ta hango bacin ransa tace hmm baya so shi wata ta rabe shi Allah sarki abin kaunata shi Jamilunsa yake so,Mummy Nan take ta turawa Naila kudin rabi a accnt tace ki kula da shi sosai ina so aljanun su fita kinji,Naila tace an gama,ni daga Nan ma sana'a zan kama na daina harkar film,Mummy tace yanda kika gani amma kin hadu da Jinin arziki zaki ci Naira ki more matukar Spark ya amince da zabin mu yayi aura.
Naila tana shiga ciki a kasa ta zabi bedroom ta shiga ta ajiye kayanta tana ta murna tace wayyo Allah dadi yau Gani a gidan Spark dina,shi Kuma Spark Yana sama ya zauna a gefen bed yayi shuru kawai mamaki yake wai dama Naila ba sonsa take ba amma ko da zata dau fansa a tunaninsa idan ta gano shine Spark zai ci darajar son da take Masa,tagumi ya zuba hawaye zubo Masa a Saman kumatu,yasa handkerchief tare da gogewa,kasa komai yayi wankan ma kasa yi yayi ya koma ya kwanta kawai,mikewa yayi ya sake zama tare da hargitsa gashin kansa ya furzar da wata iska me huci,yace ni na taba soyayya irin wannan haka tunda