Showing 60001 words to 63000 words out of 158722 words
Chapter 21 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
jikinsa a sanyaye, tana zuwa ta fada Jikin Mohsin ta dinga rusa kuka,abinda ya bawa su Umma mamaki kenan,gaba daya sai ransu ya jagule,ba haka suka San Naila ba, duk yanda akayi da matsala,Mohsin ya riketa Yana lallashinta,yace menene Naila? Naila taci gaba da kukanta da kyar aka lallasheta,yau ma'aikatan ma da take musu habaici sun samu lafiya shuru bata ko kulasu ba,Mohsin da Umma da wuri suka tafi jiki a sanyaye wannan zuwan bai musu dadi ba Sam,halin da suka ga Naila ya tashi hankalinsu matuka.
Suna tafiya aka sake kiran Naila tazo inji Beauty,Beauty ta dauki wani mugun wanka na masu kudi,Leshi ne a jikinta me masifar tsada fari da golden,mayafinta,jaka da takalmi duk golden kana Ganinta kasan ba karya Malam,Naila ta fito da Maka Makan kayanta na Maza,Beauty ta zubawa Jamilu Ido tana mamaki tace ai wannan bai fi mate Dina ba a ashe yaro ne amma gaskiya wannan kamarsu daya da mace,amma ba komai tunda Ina son Jamilu yaran ma ai sunfi iya soyayya,da fara'a Beauty ta karaso tana karkada mukullin motarta me tsada,Zama tayi tace Jamil harda gyara sunan tana dariya,Jamilu Murya ya bude irin namiji sosai yayi murmushi, yace Babyna barka da zuwa ,Beauty kauna ta ratsata ta mike tsaye tace yau gaisuwa me kwaso shoki zan Maka tasa hannu biyu ta wani kwaso wawan shoki ta dago tana cewa Ina Kwana,Naila ta saki dariya tace a gaisuwar ma harda me Shoky?
Beauty wayarta ce tayi kara ta daga waya tace Chika kin karaso? Chikar gayu tace Ina gate yanzu zan shugo,Chikar gayu ce me napep ya sauketa ta Sha atamfarta riga da skert sabuwa ta coka daurin ture kaga tsiya ga wani glass ta saka abinta ta Sha kyau,tana zuwa suka rungume juna da Beauty,Chikar gayu ta ajiye Jakarta gefe tace gaisuwa me albarka tace Shegiya Beauty ya gidan?Beauty tace lafiya Yaya me Unguwa? tace tuni na gama Episode 1, Episode 2 zan shiga.
Beauty tace ga fa my man Jamilu na ta nuna Jamilu ,Chikar gayu ta Kalli Jamilu ya dora p-cap dinsa yana tsaye yana bouncing yana bubbudawa irin namiji din nan hannayensa biyu cikin aljihunsa, Chikar gayu ta Kalli Jamilu tace Beauty anya baki cuci kanki ba kuwa,wannan me zai iya Idan anyi auren,Naila ita abinda ya dameta shine tafiyar Spark da zai bar gidan bata su take yi ba ma shi yasa jinsu kawai take,sunyi hira sama sosai Jamilu ya koma ciki,Chikar gayu tace wannan zubin Dandaudu gare shi Kinga Beauty wlh ki kama namijin gaske wannan me zai iya,taba Golden Globes ma gagararsa zaiyi,karki aure shi fa tun a daren farko aji kunya,Kinga Beauty Ina jiye miki, Beauty tace ni Ina son abina haka gashi kyakyawa haka.
Suna nan Spark ya fito duk suka bishi da kallo,taji ana gaishe shi ana kiransa da Spark,Beauty tace Chika gashi can shine ya fitar Dake,Chikar gayu ta mike ta isa Inda yake,bai san tazo ba yaji mace tace Yaya Spark, da mamaki yace to wace kuma a Ina na samu Yaya a gidan Nan,ya juyo Chikar gayu tana murmushi tazo ta rusuna tace Ina Kwana,yace lafiya Alhmdllh,nice wacce Ina cikin mutanen daka fitar masu kananan laifi, Allah ne yasa aka zaba dani a Wanda zaka fitar,amma magana ta Allah laifina ba karami bane amma ikon Allah ba yanda za ayi dani, dake ba hakkina haka aka fitar dani a cikin masu kananan laifi,zuwa nayi dama na ganka nayi Maka godiya,naji ana ta Spark Spark nace sai kace wayar cellular ashe kuwa gaka Mashaallah Dan chamai dakai,Allah ya saka da Alkhairi,ubangiji yasa ka shiga Aljanna silar haka,Allah ya baka mace ta gari,idan kuma kana da mace to Allah ya baka ikon Kara mata kishiya,kasan mata biyu sunfi kullum ba hutu shine ka cika cikakken namiji,yau kana nan wajen taliyarka da Miya,gobe ka koma wajen shinkafarka da wake,amma ace mace daya kullum fa taliyar ce ai dole ka gaji, to dama godiya nazo yi na gode na gode sosai,Spark tunda ta fara magana yake saurarenta amma tunda yaji tayi shekaru a gidan yari yasan zata aikata ma abinda yafi haka, ta fitsare a gidan yari, yace ba damuwa na gode nima,tace to ta juya wajen Beauty tace muje gidan naku to yau a nan zan Kwana gobe sai Kaduna.
Ana gama da ziyarar Maza aka bude mata,su Chikar gayu an hadu ana ta caf cafkewa suna iya shegensu,da mata kawayensu,Beauty motarta cike da tarkace na ci snacks ta dinga rabawa mata Wanda suke tare,Wanda tasan talakawa ne futuk harda kudi dubu biyu biyu ta bayar da yawa,Chikar gayu su ba masu kudi bane ama da ledarta ta alawoyi da biscuits ta rarraba musu tana cewa ayi hakuri mu gidanmu ba harka,sanda na koma gida ma shinkafar gidanmu ta kare da tuwon masara na fara karo,ayi hakuri gidan mu ba harka mu Kam,ana ta dariya.
Ranar Monday Spark ya shirya barin gidan,Naila tana zaune yace a nan VIP zaki zauna ke kadai kin jini ko? Naila tace ae,yace bana so ki dinga shiga mazan nan idan ba dalili kinji,tace ae,yace karki bari a kalle min ke duk Wanda ya kalleki ban yafe ba,tana jinsa yace zan dinga zuwa ko yaushe ba sai lokacin ziyara ba,ki zauna zan fitar dake kinji,tace to tana share hawaye.
Yace ga kayana nan kiyi ta sawa komai zan dinga siyo miki kinji,Naila tace t.....t..to ta fara kuka,Spark yaga kukan Naila bazai kare ba ya gama shiryawa ya Mike ya kwashi wayoyinsa yace zan tafi to? Mikewa tayi hawaye shabe shabe a fuskarta jikinsa ta fada ya rungumeta tana ta uban kuka,Dago fuskarta yayi a hankali ya hade bakinsu waje daya a hankali yake aika mata da sako,kafarsu ce ta gagara daukansu suka fada Saman kujera,Naila tana jikinsa ta janye kanta da sauri,amma tana jikinsa,cike da shagwaba me hade da kuka tace baka..b...baka fada min ta ya kasan ni Macece ba,murmushi yayi yace ranar da kika Sume ya bata labarin komai,idonta ta rufe da wuri tana dukansa a kirji tace shine ka kallar min gareji na,Ashe Kaine ka ajiye min pad,yace yes kinyi amfani da abarki Kuma kika ce mutanen boye ne,dariya suka yi wayarsa tana ta ringing Rafeeq ne yake kiransa zasu tafi
Muje ki rakani, suka mike tare suka fito,dama Yan gidan duk sun san Spark an gama case dinsa zai fita shi yaga dama ya zauna,Duk da haka sai da suka bi lungu da sako yayi musu sallama suna ta tayashi murna,Naila sai hawaye take yi ta kasa rike kukan nata har suka fito bakin gate zai fita ita zata dawo ciki,bai ko juyo ba tunda yasan kuka take tayi, sai da taga ya kule ta juyo ta dawo ciki,sai data dawo ta dinga kwarara kuka da ihu ta Fadi a kasa tana ta rusa kuka,mutane da yawa suka zo kan Jamilu Dake rasgar kuka,Naila kamar ranta zai fita tana cewa da haihuwata gwara barina,me yasa babu wajen karuwanci a gidan yari gwara na fada yawon ta zubar ,mene amfanina gwara a yanke min hukuncin kisa a harbe ni na huta,me yasa a gidan yari babu Bariki,gwara na shiga yawon duniya na huta da wannan rayuwa,sai kowa ya dinga ficewa ana barina nima ai ba hakkina aka kawo ni, kowa a gidan idan yazo sai yaga Jamilu kuka yake tsakaninsa da Allah abinda basu taba gani ba,duk sai ya basu tausayi sun gane shakuwar da sukayi da Spark ne,da kyar su Goje suka lallaba Jamilu ya koma dakin su na malamai,yau Tantiriya bata bari sunyi karatu ba kwana tayi tana uban kuka tana wayyo gwara zuciyata ta buga na huta,ni a yanke min hukuncin kisa,Malamai suna ta kallon ikon Allah,Malam Sharu yace ba a son bawa ya dinga yiwa kansa mugun fata ko da ace da wasa ne,Jamilu yace karku dameni zan sawa dakin nan gobara iiiiiihihi an fitar da budurwata Baby Spark,Allah sarki yau babu caskalewa,tsotsiyar da muka Saba babu wayyoooo....Malam Garzali ya zaro ido yace gwara daya bar gidan nan,Malam Sharu yace ban yarda Spark wlh Yana harkar banza ba iskancin Jamilu Terror ne kawai yake so ya bata Masa suna,ai kowa yasan Jamilu tataccen Dan duniya ne a gidan nan ba ruwan Spark.
Jamilu kwanciya yayi yace tsotsiya yau babu me min tsotsiya ya tafi, ta sake fashewa da kuka ta mike zaune da tsakar dare tana bubbuga bed tace yau ba Wanda ya isa yayi bacci a dakin nan,Malam Garzali ku tashi,Malam Jilani Malam Jilani,Sharu ....duk suka tashi tsakar dare taki bacci ta hana Yan daki bacci,Malam Jilani yace Spark ya bar mana jaraba,sand ya dauke Jamilu har mun samu lafiya yanzu ya dawo.
Spark tunda ya bar gidan hankalinsa ya tashi gaba daya zuciyarsa tana kan Naila,Sallama yayiwa ma'aikatan duka ya rarraba musu kudi suna ta godiya suna tayashi murna ya shiga mota,Rafeeq yace yau anyi sa'a ka fito yace hmm gangan jikina tana prison wlh,Rafeeq yace hmm Allah ya kyauta, ana ta Shirin tarbar Spark amma Spark direct katafaren gidansa ya wuce babu gidan Wanda yajema a ciki,Bai je wajen Mami ba bare Mummy,dangi duk sunje Murna anyi girke girke an dau wanka amma akace ai ya wuce gidansa ma,Mima tace zai aikata ai mai hali bai fasa halinsa,duk Mummy ce ta lalata yaron nan.
Naila kuwa gari na wayewa tace baza ta sabu ba, fita daga gidan nan dole, Ina Sam bazan iya rayuwa ba spark ba,ko dai na haura katanga na karairaye ko Kuma na fita ta ko wacce hanya,gidan yari ya daina min dadi,ya sire min,fitowa tayi buguzun buguzun sai wajen Dan Indo,ta kira Dan Indo ya fito suka kebe gefe,tace Dan Indo so nake ka wuce min gaba,so nake ka daure min gindi a kasar nan ka hada da duwawuka duk ka daure min tam,Dan Ido Yana busa sigari ya sheke da dariya,yace ka gaji kenan Jamilu? Na fada maka aje aci uwar wacce ta maka sharri a gaban kowa ta tonawa kanta asiri a fitar dakai kamar Inda aka fitar da Spark Kai kaki,Jamilu yace ba wannan ba ka bar min wannan a hannuna amma a canja wata shawarar,Dan Indo yace to mafita daya ce ranar Ziyara zamu tada fada idan mun fito su Goje zasu fasa taron ma'aikatan,zansa yarana Dake min aiki a waje suzo bakin gate su tarwatsa masu tsaro,Kai Kuma Jamilu ka tsaya kusa ana fara fadan karka ji tsoro kawai ka sheka da gudu ka fice Wanda ya gudu ya gudu Kuma wlh a kasar Nan duk Wanda ya gudu daga gidan yari to ya Sha ba'a komawa ayi bincike bare a shiga nemansu wanted kawai kyale su akeyi Wanda kika ga an dawo da shi to tabbas sai idan wanine a unguwar yaje ya fadawa hukuma a boye amma ba a zuwa neman mutum idan ka tsira ka tsira kawai Jamilu,idan kana da makiya a layinku kawai ka yanka wajen Lagos ko Abuja idan komai ya lafa sai ka dawo.
Jamilu yace Allah ya kaimu ranar Ziyara zan fada a gida kar azo min ranar yace yawwa ka shirya kawai.
Tana murna ta koma part din VIP Inda Spark ya bar mata ya biya kudinta a nan take sallarta da komai nata a nutse ba tsoro da fargaba,yau da dare ya kirata a waya yaji ta daga da murna,yayi farin ciki matuka da yaji yanda ta saki jikinta ta hakura da komai.
Dariya tayi haka kawai tace Spark,yace Na'am Jamilu Kafi wuta zafi,dariya ta sake yi,yace ya gajiyar kukan to? ta fara shagwaba tace ni kayi sauri Allah kazo,Spark ya murmusa Yana Jin wani farin ciki yace sai ranar Ziyara,ban yarda ba,yace bazan samu damar zuwa ba wannan satin ma sabo da Ina gyara Office dina da abubuwa dai alot,tace to shike nan Allah ya kaimu,suka ci gaba da hirarsu wai nan duk a friend's suke har yanzu.
Wani ganganci Naila tayi kafin ranar Ziyara ta dinga rubutu me tsayi a papers da yawan gaske ranar mutane sun shagala a wajen ziyara duk tabi daki dai ta ajiye takardun,ko Ina,dakin su Malam Sharu ma ta ajiye musu basa dakin,ta fito duk wani lungu ta dinga jefar da takardun ta kwaso komai nata na kaya ta kawo dakin su Malam Sharu ta ajiye a tsakiyar dakin tayi waje wajen da ake zuwa ziyara duk an fito
Hanan ranar tazo domin tonawa Naila asiri a gaban kowa ta fadawa duniya ita macece ba namiji bace,tunda taji su Umma baza suzo Ziyara ba shine tayi karya tace zata je gidansu ashe gidan yari tazo domin tozarta Naila, Naila kuwa ta Kalli DanIndo suka yi signa,bata kula da Hanan ba,Dan Indo ya baza yaransa a wajen ya musu fito,Goje yazo ya fyalle Yar wuka ko Ina ya samo oho suka fara dure duren ashar,
Sai suka fara dukan juna suka hargitsa wajen ziyara,Goje ya daka tsalle ya ballo rashen bishiya,a wajen suma yaran Dan Indo da wasu Wanda akayi tsarin dasu suka yi kan ma'aikata da duka da ashar kowa zaneshi suke a wajen har masu ziyara ciki harda Hanan suka kamata kamar Allah ya aikosu da duka ta ko Ina bulala take karba,wani Yana lafta mata ya fasa mata gefen Ido tayi waje da gudu tana faduwa tana tashi,suna danna ashar suna fada a junansu ji kake rudududu kamar dawakai,suka nufi gate,Naila ta kwarara ihu tayi bakin gate wajen ma'aikata,su Dan Indo da jifa da manyan duwatsu,duk ma'aikatan da bindiga wasu amma tafi gaban ma su fara harbi su kansu ta kansu suka yi,Dan Indo ya fisgo bindigar wani Ma'aikaci ya danata ya dinga Harbin sama, harbin iska tas tas,kafin kace me har ma'aikatan sun watse,Naila tabi kofar fita tana cewa dama macece ni yeeeeeeeeee ku matsa dan ubanku ta fice fit ta Sha kwana gudu take ba ji ba gani,mutane da yawa Yan gidan yari aka fara tserewa an samu mutane masu laifi daurarru sunfi mutum ashirin Wanda suka fece kafin su Dan Indo su gudu can cikin gidan yari can dakunansu suna dariya,Su basu damu da guduwa ba,ba abinda ya damesu sunfi son ma gidan yari domin ko sun fita sai an dawo dasu sai sun sake laifi an dawo dasu,Kamar gidan gado haka suka Maida gidan.
Da kyar aka kawo sojoji da ma'aikata over suka daidaita gidan yarin ranar ba ziyara ta kare Kuma,kowa ya gudu an fasa ziyara abinci ma duk Wanda suka zo dashi sun kifar da abincin sunyi ta kansu,Wasu daga cikin Wanda basu tsere ba Dake kowa yasan Jamilu sunji da kunnen su yana cewa yeeeee mace ne dama ni a suffar Maza nazo.
Anan Kuma kowa a ciki aka dinga tsintar takardun Jamilu a ko Ina a gidan daki daki kowa ya karanta sai takaici da bakin ciki da cizon yatsa.
Malam Sharu suna shugowa suka ga takarda da komatsan Jamilu suka dauka suka fara karantawa kamar Haka
Ni Jamilu Terror Wanda aka fi sani da Tantiriya dama karya nake ba namiji bane ni,sunana Naila,harda rubuta abinda ya faru da ita tun daga zuwanta Abuja har shigowarta gidan yari, in short tayi bayani.
Idan baku yarda ba ku duba kayana na dakin su Malam Sharu,Malam Sharu ko gama karantawa basu yi ba, da gudu suka bude kayan Naila,da Hijab suka fara cin karo,suka dakko panties na mata suka dakko vest ta mata,sannan suka dakko seletape da bandage,sai ga pad ma sun zaro,takardar suka Kara dubawa suka ci gaba da karatu
Wannan Selatape da shi nake manne albarkatun kirjina,sannan a karshe Panties Dina na barwa malam Sharu gadon su halak malak ya dinga sawa domin tunani,Kun nuna min kauna na gode na gode kwarai,shi yasa na nemi dakin Malamai na zauna sabo da na tsira da budurcina.
Naku har kullum
Jamilu Tantiriya.
Ai Nan take labari ya cika gidan yari har bangaren mata sai da suka ji ankai mace bangaren Maza a matsayin Namiji.
Dan Indo daya karanta takarda yatsa yasa a Baki ya kwarara ihu yace Inda nake neman mace Ido rufe na samu na kwashi harka,Goje yace wlh da nasan macece ni zan fara yi mata filla filla, kowa ya karanta takarda sai zage zage da bacin Rai,aka cika dakin su Malam Sharu kamar ana ganin kayan lefe haka ake kallon kayan Naila filla filla ana bakin ciki,Scoler yace da na sani ai ko nono na taba, ranar Maza group group suka yi ana tuna abubuwan da Jamilu ya dinga yi na mata amma suka kasa ganewa macece.
Wasu suka dinga zagin su Dan Indo da suka fitar da Jamilu a sadaka.
Wanda suka dinga tura min 500 na gode kwarai da gaske,Kun San novel Dina baya wuce 300 amma Kuna tura min 500
Na gode kwarai da gaske
Allah ya saka da Alkhairi.
Aci gaba da sharhi
Ina godiya.
1,2,and 3 za ayi Kuma 300 ne duka in ka siya sau daya shike nan
BOOK 1
FREE PAGE
Accnt no
0175487861
Katin MTN
08061929616
Yan Niger ga number da zaku tuntuba
+22790795939
AsmaBaffa
[12/11/2023, 9:27 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI
41-45
END OF FREE PAGE
1,2,3 duka 300
Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger
+22790795939
OFFICIAL
BY
ASMABAFFA
SADAUKARWA GA
AIDA MAMAN TASNIM
Page naki me Maida book Dina audio jinjina
Gare ki Auntyna
HAUWA S ZAIRIA
MASU AUDIO BAN YARDA A JUYA MIN NOVEL ZUWA AUDIO BA
Dandaudu washer ne ya shugo da gudu cikin su Dan Indo da takardar Jamilu a hannunsa yace me nake gani haka? Su Dan Indo sunyi jugum jugum,suka ce da gaske ne,yace yanzu naje dakin su Malam Sharu na duba kayan Jamilu,ya daga pant din Jamilu na mata yace na rabauta da wannan ni wlh Ina so tunda macece ta saka wannan gwaurantaka da me tayi kama ashe wasu