Showing 147001 words to 150000 words out of 158722 words

Chapter 50 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

404

a motar sabon saurayinki, har horn na miki na haske ku da fitila,Wahida tace tace Body no be Zuba Rock,Naila ta kalla Dan ta cusa mata haushi tace tunda Spark ya daina romancing Dina na shiga garari.

Naila tace lie lie wlh ko da bama tare baki isa ya tabaki ba bare Yana so na tun lokacin me zai ci da ke,idan ma ya tabaki kince da,to yanzu fa? Ko kallonki zaiyi ma,sai dai hakuri yarinya kafin na fito ma sai da na Sha madarar Nido ya Sha juice,Malama Ikhram ta zagayo ta fito daga mota tana Jin zance ta karbe tace juice dinma me bubbugowa a lokacin,a tabaka ya fito wannan sai ikon Allah waye ya isa ya kirkiri wannan,mazajen babansu ne yayi ruwan,ke baki da kunya a gaban mazan kike wani body no be Zuba Rock duk yan iska ne mu,a gidan yari muka yi degree ki shiga hankalinki,Chika tace na so,bana so ma nayi magana sabo zan iya Marinta a wajen,ke Spark ne zai taba ki,Naila tace ke badan Ina da aji ba yanzu kin isa ki min magana,to yanzu ni bana harka da Yan mata nafi karfinku,da masu karbar Hallare nake yi kullum sune dai dai ni.

Malama tayi ciki tuni tana duba agogonta,tana shiga kowa Yana jira yaga babbar mace Malama sai aka ga Yar budurwa yarinya,Mima tsaki ta ja tace yanzu wannan ce malamar, Kai amma Rafeeq kawai Yan iskan yara suka taramu a Nan,Mummy da Yan uwa sai kallon juna suke suna tabe baki,gaba daya abin ya sire musu Yar cikinsu,Mummy ranta ya baci ta tsurawa Rafeeq Ido kamar tace a dawo mata da kudinta data biya aka dakko Malama har kyauta tayi Masa,Baseeru Kusa kuwa shi a matse yake sosai baya son wa'azin shi burinsa a Kai Amarya
Naila ta shiga ta zauna,Wahida ta zauna a kusa da ita tana Jan tsaki tana jefar da magana,talakawa anyi clean anzo Abuja,Naila tana jinta ko kallonta Bata yi ba.
Rafeeq da matasa duk sun zauna,Malama ta karbi Speaker,anyi tsit ana jiranta,yace dan Allah Mata su ware gefe daya Maza ma haka,ba Wanda yayi motsi,Rafeeq tayiwa Dan kiranta da ta Saba siii siii hey....ya juyo ya kalleta tace saita musu zama wa'azi muka zo ba Party ba,fito ta yiwa Chika tace tashi Chika ki ware min mata,Chika ta mike duk girman matan wajen da masu kudi tace a tashi a ware,Maza kuyi chan,itama ta samu saitin Misam tayi Masa fito tace Maza ku kama kanku,Rafeeq yace mu ga kugunmu ga na mata,Kamal yazo wajen Yana ta dariya yace yau sai bari naji wa'azin nan me za ace.
Malama taga duk sunki tashi tace zan tafi wlh na fasa,Rafeeq yace karku jawo mana masifa Malama zata tafi ku tashi ku koma can shi Kuma yaki tashi ya samu wata ya makale a kusa da ita.
Mima ce tace ke dalla bama son iyayi kiyi abinki a haka duk Yayanmu ne Nan sabo da haka ko wani kika ga ya rungume wata to Yar uwarsa ce,Ikhram tace abomination....haramun ne,Amarya wani takaici ya isheta,Chika tace Malama fara aikinki idan sunji ruwansu.
Taro ta bude da addua sannan tace tana wata kalkala kamar zata yi amai sabo da larabci Alhmdllh wato ainihin naga Amaryar ma babba ce haka angon ma ba laifi,Allah ya Bada zaman Lafiya,Mummy tace Ameen,Rafeeq ya fara boye dariya ganin Angon idonsa yayi ja sai kallon Mummy yake kamar zai cinyeta ko kunya baya ji sai kace ya samu tv,text ya turawa Misam yace Kalli Ango dan Allah.
Misam Yana karantawa ya Kalli Kalli Ango Bai San sanda dariya ta kwace Masa ba,su Arham duk suna zaune mata San nan kowa yazo gasu da shegen yawa.

Rafeeq ya sake turo message yace Allah yasa Mummy tana period yau,Misam yace a'a ai itama so takeyi kaga katon bahon data siyo da naje jiya a toilet dinta na ganshi wai tsumi takeyi tana zama a ciki,Rafeeq Yana duba waya Yana dariya yace ai dole sai da liki ta dinga Dan like wajen, Malam Ikhram wa'azinta ta fara sosai kowa Yana jinta gaskiya take fada Sosai game da aure da abinda Allah yace,da Kuma duk wani sharudan zaman Aure,ta jawo Aya da hadisi ta fassara,har ta gangaro yanda ake tarairayar miji,Rafeeq wayarsa ya Maida Aljihu ya nutsu,duk mazan nan suna Jin ance wai ake kula da miji ne? Kun San komai Yana tafiya da zamani,karki kice wai ke tun daurin dankwalin zamanin Da can da kika iya shi zaki yi a yanzu,Inaaaaaa Sam Hajiya an barki a baya,Zamani zaki shiga kema duk abinda zamani yazo da shi da haka ake tafiya.

Idan sabon daurin dankwali ya shugo to kar abarki a baya waje cikarawa me gida shi,haka sabon dinki,da yawa ana siya mana sutura me tsada amma sai ki dinga kallon ai kin girma kin tsufa kina da yara sai ki kaiwa tela ya miki dinki made in Da,wata shegen son kudi miji ya baki kudi kiyi dinki na Gani na fada sai ta rage ta bawa wata kawai tayi mata me araha marar kyau,ko bakiyi kwalliya ba Hajjaju matukar dinkin ya hadu wlh sai kinyi kyau a ciki shape dinki ya fita,amma kinje kin Masa dinki sai a hankali zaki ga sai a hankali.

Chika ce ta daga hannu tace Ina da tambaya Malama,Na'am wai ya akayi ne gashi Ina daukan wanka amma mijina baya yabawa Kuma Ina kokari nayi,Ikhram tace wankan Bai Kai wanka bane,ai indai kinji miji Bai yaba ba duk da ana samun Wanda ko zaki yi basu yabawa to amma Mafi yawa wankan da akeyi Bai Kai wanka,kiyi wanka kamar zaki je Dinner ki Gani karya yake wane shi sai ya yaba.

Sannan mace ta zauna ta lalata kanta wai har sai tayi aikin gomnati sannan zata siyi sabulu me kyau wlh baki hadu ba,in har kin hadu karya yake ya hanaki shi din banza,ke kike da idon gari ba,idan kina biyayya,kina hakuri,kina gyara kanki in and out wlh lungu da sako,tsabtar jiki,gida,sutura da komai sannan kina cikawa da daukan shegen wanka ki Gani ya isa ya hanaki kudin sabulun,sannan mu mata muna zubar da darajar mu da kima ta ya mace shi yasa muka fi samun matsala mu hausawa,girman Kai Yana cutar damu,kinyi laifi baza ki accepting ba,hakuri kinfi karfin kiba namiji,sannan ta rashin kulawa ta matanmu,kina fara yin yara sai gaba daya hankalinki ya koma kan yaran ki kyale mijin naki,komai an daina,Yar shagwabar ma babu,duk kin ballagazar da kanki.

Kishiya kaddara ce amma ana so idan anyiwa mace ta tabbatar cewa idan wata ta shugo ba abinda zata nuna mata,ba abinda zata yi Wanda ita bata riga tayiwa miji ba,amma Baki San bacin ran me gida ba naki San farin cikinsa ba,ko baya ganin abinda kike yi karki fasa kiyi iyakar iyawarki ko bayan ba ke sai yaga amfaninki,Kuma wani baya yabon mace a gaban idonta amma a bayan idonta Bata sani ba duk Inda ya zauna sai ya yabeta tana da wani matsayi a wajensa Wanda ita Bata sani ba just Kinga naya yabonki kin damu ko kin daina kulawa da shi Baki San Kuma a ransa bashi da kamaki.

Maza yawanci haka suke ba sai an fada miki ba amma ke Baki sani ba Ashe kece on top,ke Kuma kina Nan kina zage zage baya sonki yanzu ai kaza kaza a garin haka duk ki watsa kanki a wajensa,Sannan mace ita fa Yar kwalliya ce da gyara duk kyan mace idan ba gyara to aikin banza ne,bare yanzu an waye kayan gyaran jiki gasu Nan iri iri,ki gyara headquarter,amma kin zauna sai sanda zaki wanka zaki wanke Headquarter Hajiya baza ki haifi da me Ido ba,a kalla a wanke sau uku da ruwan zafi ga sabulan wanke Headquarter ne iri iri yanzu da masu tsada da masu Araha a samu a dinga siya.

Bakya wankewa bakya gyarawa Kuma kina jira mijinki ya Kai Baki Nan wajen mahaukacin inane shi,har su Mima suka kwashe da dariya,duk ga yaransu kowa baya Jin kunyar kowa ana magana haka,amma ba ga iyayen ba ga yaran nasu kowa yayi mirsisi,Rafeeq yau shi dai Shar da shi ana zancen abinda yake so,Kamal yace bari na tashi na fece an fara zuwa wajen da zai gagare mu ji.
Chika tace Malama da hammata a dinga gyarata,Malama tace yawwa a dinga aski akan lokaci,sabo da haka a Headquarter din ma ba kullum zaki dinga sakewa kina kwalkwal ba haba ba style ai ko Carlos Kya dinga yi watarana,Kamal tashi yayi yace naji rabona ni Kuma ai,Ikhram ana bayani har zaga wajen take,har tazo idan an samu ciki Nan ma ya ake kula da me gidan,har haihuwa,ana gama na haihuwa da yanda za a gyara jiki tace sai yanzu muzo tarbiyyar yara Kuma amma kafin lokacin yanzu Ina siyar da ingantattun maganin Mata sa me gida suma,su makale mata,duk akwai,da turaren musk na sawa a wajen ai Kun gane.
Naila ce ta daga hannu tace Ina da tambaya,tace Malama mace zata iya saka zuma a wajen wato idan za ayi abin Naila ta nuna da baki sai ya lashi honey,Malam tace babbar tambaya na gode miki wannan ma dai dai ne.

Mima kasa hada Ido tayi da yaranta sabo da dole sai da taji kunya,Naila a ranta tace duk Tsohuwar da bata ji kunyar yara da jikoki ta tashi ba muma surukai baza mu ji ba.
Mima so take yi ta siyi maganin Ikhram na mata amma ga yara,haka Maman Rafeeq,da sauran Yan uwan Mima sai Kus Kus suke yi ya za ayi su siya,Misam ne yaji suna ta faman Kus Kus,wannan ta taso ta radawa wannan,yace kan bala'i Kai Ashe harda tsofaffin basa hakura.
A waya ya turawa Rafeeq yace Uwar rainonka tana so tayi chaji,Yace zan siya mata ai shi mijin nata ma ba sonta yake ba sai dai a siya mata,Misam yace Kai banza ga Naila wlh ance Kakanta Yana Bada magani kaje ka samo mata ta Sha ita da mijin Wanda zai haukace mata itama maybe ta Gyaru,Rafeeq yace haka za ayi amma bana so ta haihu ni bana so ayi min Kani ko Kanwa su isheni kishi nake gwara ni kadai nayi shagwaba ta,Misam yayi dariya yace Allah ya shiryeka baka so ta samu nata itama.

Malama tana gama talla tasan dama yanzu baza su iya siya ba sabo da haka mata suke yi sai dai a sirri,ai kuwa ta dawo taci gaba da bayani akan tarbiyyantar da yara,tun daga farawa su Mima suka tabbatar sunyi kuskure tun farko,sannan su kansu sun San iyayen su basu basu tarbiyya ba,Malama Ikhram tace mu da kanmu iyaye muke raba kan yaranmu,kinki tsayawa yaranki su fahimci Allah da addinin Allah,ko Kuma sunyi karatun addinin ma amma duk abinda yaro zaiyi baza a Masa fada ba,a gaban uwa yaro Yana zagi na rashin mutunci baza a nuna Masa ba dai dai bane,a gaban iyaye yaro zai dinga rawa baza a nuna Masa kunya da cewa wannan ba Abune me kyau ba a'a wasu iyayen ma da yaran nasu suke rawa musamman mu iyaye mata,mune masu tarbiyyan yara mazajen sun fita nema sai ke sai yara,ya kamata mu San Amana Allah ya bamu,Yaro ko yarinya kaji suna wakokin batsa,magana ta batsa,ta banza ta fitsara amma baza a iya Masa fada ba bare a nuna Masa ba kyau,yaro zai zagi babba ko waye bazan a Masa magana ba,aje gidan wasu da yaro sai ka gane basu da tarbiyya komai suka samu lalatawa zasu yi uwa tana kallo baza tace ya bari ba.

Musamman masu kudi yaro bai San darajar komai ba zai iya fasa tv,ya lalata remote etc amma ko Harara yaro bai sani ba,yaranmu yanzu sun zama samari sun zama Yan mata amma sunga babba baza su iya gaida shi ba wasu ma kallon arziki baza suyi Masa ba,sannan wasu idan zasu gaida mutum komai girmansa Ina yini kafin ki amsa ma ta Kara gaba ke kika sani,Kuma wai abin mamaki a gaban iyaye,wasu ma kannen uwarsu ne,wasu yayyen Uba,ko Yan uwa,amma basu da darajar ma da zasu musu gaisuwa me kyau,yanzu haka akeyi ba talaka ba me kudi,wasu ma yaro sai ya dinga kwana a wani wajen basu sani ba,Yaronki Yana can ya kama hotel Yana da permanent room baki sani ba sabo da rashin kula da Amana.

Yarki kin barta tana ta Tara samari tunaninki farin jini ne kina tana Nan har sai an samu wani ya lalatata gashi ta samu na auren ance sai tayi karatu dole,wasu Kuma basu samu mijin auren ba amma an takura an hanasu sakewa karshe har sai sun zabo Wanda basa so sun aura haka,daga Nan Kuma sai Kiga yarinya da aurenta tana bin Maza,idan tana da Wanda take so ta koma suna aikata masha'a sabo da kowa Yana da taste ba a bari mace ta zabi Wanda ya kwanta mata kawai tayi aure,shi yasa zawara suka mana yawa,da yawa yan mata gasu Nan suna complain cewar sabo da basu da mijin aure iyaye da Yan uwa sun matsa musu lallai sai sun fitar da miji,gidan yayi musu zafi,har Yan uwa daina shiga suke yi karshe yarinya tace ita koma waye ya fito aura zata yi karshe ta auri Wanda Bata so,gashi aure ba abin wasa bane halin kowa sai ya fito mace ta auri Wanda take so ya aka kare bare Bata sonsa yaushe babu so zata zauna ya mata wani wulakancin dole yarki ta dawo bazawara.

Kina da Maza namiji ya samu wacce yake so take sonsa indai an yaba da tarbiyyarta mene ne,a'a mu yanzu masu kudi sai masu kudi talaka sai talaka,yarinya Abi a tsaneta idan an aurota gori ma ya isheta Yar talakawa,Naila tace gani nan a sa dani,duk matar da tayi sake yaranta suka taso ba tarbiyya karshe sai tayi kuka da Dana sani,a yawaita yiwa yara addua kullum ana sa musu albarka sannan a basu tarbiyya shine mafita,amma a zubawa yara Ido suna iskanci suna badala da Sunan wayewa wlh ba daidai bane,Kuma suna girma a haka gyara bazai yuwu ba sai dai addua,su Mummy dukkansu suka yi tsiiitttt kamar ruwa ya cinye su.

Malama tace wlh yara da kudi ku sani duk jarabawa ce kaddara ce,idan kin tafi dasu daidai kiji dadi idan aka samu aka si Kuma kiyi kuka da idonki,duk Wacce tayi aure kafin ta haihu ta sani aiki ne ja a gabanta matukar ta kusa aure ta shirya aure wata hanya ce ta producing 'ya'ya, yaro zakiyi producing,Producing Abu kuwa ana bukatar kayan aiki sosai,shine dole kiyi bincike kisan wa zaki aura,shima dole yayi bincike yasan wa zai aura sabo da abinda zaki producing ba Abu ne na wasa ba,tsatso na kirki ake nema sai ayi producing Abu ingantacce,ko a sahabbai ku bincika tarihi kuji kalar mataye da suka aura,haka ko matayen su ku bincika kuji mazajen su waye ya tsatson yake,sannan ku bincika yayansu da suka Haifa Kuma kuji Yaya suka taso su waye su sannan wanne tarbiyya suka basu me yayan suka zama a duniya,sun amfani duniya ko basu amfani duniya ba,amma mu munzo ba lissafi kawai kyau sura,kyau sura ita ake aure yanzu,daga an kaiki a bude Banana ki bude fanke ko gurasa faaaa sai yara yuuuu Kuma an barsu sakaka, yawwa a kiyaye a kula,ayi mana addua iyaye gamu Nan duk Yan banza ne muma,aka fara dariya,Arham yace harda ke Malama tace harda ni nima Nan kwalluwar kaina ce baka ji lafazi na bane,ai mu gyara muke yanda za a daidaitawa miji kayan harka.

Duk da wa'azin ya shigi kowa amma Ikhram sai ta dawo taci gaba da koya yanda ake kwanciyar aure,duk mazan Nan suka nutsu suna ji sai iskanci suke yi kamar ba su aka yiwa wa'azi ba,Mima tace gaskiya zan gyara nima yau Mijina Papan yara zai ga canji ya zama dole,har na manta da shagwa rabona da ita tun ina Amarya,yau kuwa ta dawo sabuwa.
Sai 7pm aka gama wa'azi sannan,Malama ta fito, tasan kan tsiya ana can ana Mandiri ana liki mata Kuma suna ta lallabawa waje wajen Malama suna siye maganin Mata,Mima da ta fito sai da ta Kalli gabas yamma kudu da arewa ta tabbatar ba Danta a kusa sannan ta siya,Rafeeq yana kallon ko wacce cikinsu Malama tana ta ciniki,Basu San ma ya fito ba ya rabe a bayan mota, sai da suka gama siya yaga Mamansa bata zo ba yasan zai wahala idan tana da kudi Kuma maganin yaji da tsada sosai na manya ne,Wajen Ikhram ya karasa yace yawwa maganin naki wanne mata suka fi siya yafi yi musu amfani? Ikhram ta nuna Masa kala hudu,ya Bata kudin sannan yace muje na nuna miki matar da zaki bawa a sirri karki kice ni na siya ko wani,kawai kice Dan Allah kece Maman Rafeeq? Idan tace ae kice school dinmu Daya Dake ki bata kice kyauta kika bata,Yanda yace haka Ikhram taje ta kira Maman tasa gefe ta mata bayani ai tasan Rafeeq ajinsu daya,ta bata tace gashi Mama kyauta na baki,Mama tace ayi haka? tace wlh ba komai suna da amfani,ta karba ta zuba a jaka tana ta godiya.

Ana tashi daga Walima dama an gama shirya komai da bangaren Amarya a gidan Daddy Beauty,Mummy ta gama kulle gidanta ta bar masu gadi kawai zasu dinga gyara mata shi kafin tasan abin yi,anci an Sha a wajen Walima kawai aka wuce Kai Amarya,duk Mummy ita kallon da take wa Chika ai kishiyarta ce sabo da Baseeru yace baya sonta yanzu Mummy yake so shi yasa ya ballagazar ita take abinda taga dama,sabo da Chika idan ta Kalli Mummy sai Harara tsakaninsu,a dinner ma haka tayi a wajen Walima haka,Mummy tace nasan kishi ne ya zakiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login