Showing 36001 words to 39000 words out of 158722 words

Chapter 13 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

381

ni sauri nake budurwa nayi,Namiji? Spark ya tambaya,tace Kai nifa bana harkar takashi yawwa macece sunanta Beauty, a waya? a bangaren mata mana akanta zan iya fasa bango na kalleta,wannan ginin zaki iya fasawa? Naila tace wai me yasa ba a hada aure a gidan yari ne,ai da sai masu daurin rai da rai a dinga hadasu aure, uhm Spark ya furta kawai ya juya ya tafi abinsa Yana kamshi sosai, Naila susarta tayi sosai ta dawo dakinsu.

Malam Garzali yayi bacci cikin bacci ya fara mafarkin Jamilu suna zuba love Kuma a mace Jamilu yazo Masa ya Sha mafarkin dadi sun zuba love,cike da nishadi ya tashi da asuba ya Kalli Inda Jamilu ke kwanciya can karshen katon dakin Yana ta baccinsa hankali kwance yace ya Ilahi wannan ba mace bane kuwa dole nayi Istihara ko Allah zai nuna min gaskiya.

Washe gari yau ranar ziyara ce,yau Kuma Su Umma zasu zo wajen Naila,anyi girke girke masu rai da lafiya,Mohsin,Umma da Abba suka zo mata,Ana bude Maza Wanda aka zowa ana ta kiransu duk sun fito kamar me,Naila ba zato taji ance Jamilu yazo,tace nasan wannan Yan iskan ne zasu zo Wanda suka zo waccen karon tana fushi tana cika tana batsewa ta nufo wajen,Spark ta Gani shima an kira shi Yana waya ya fito sanye cikin 3qtr da tshirts arsh color sababbi yayi kyau sai kamshi yake Yana shining dake shi wajensu special ne,yana waya ya Kalli Jamilu ya canja kaya kanana girman kayan da yake sawa ne yake bashi dariya,amma yau ganin Jamilu yayi Yana ta fushi ba nishadi ba murna,haka ta fito ai sai ta hango Mohsin a tsaye Umma da Abba suna zaune ga kaya Nan a ledoji, ihun murna tayi ta fito da gudu tazo ta fada Jikin Mohsin tana murna tana dariya tace wow sai dariya Kuma tare da hawaye a fuskarta, Mohsin kankameta yayi Spark Yana satar kallonsu fuskar nan ba Rahma,.

Naila wajen Umma ta koma ta fada cinyarta tana murna,sai Abba ta mika Masa hannu ya riketa,shi ta fara durkusawa ta gaida shi ya amsa Yana murna Naila bata taba durkusa musu ba sai yau,Umma tace oh Nail....Naila da sauri tace Jamilu Karki manta cikin rada, Umma ya ta iya haka tayi shuru bata ce Jamilu ba bata ce Kuma Naila ba,Naila tace yawwa Umma ka Fadi Alkhairi ko kayi shuru,ya gida ya kowa da kowa ya su Hidaya shugabar masu hankali ta Kano state? Umma tace Hidaya din? Ai haka take nunawa ta fini hankali ita wayayya me hankali,Abba ya aikin? Abba yace Alhmdllh gashi nan kuwa naga ke har kiba ma kike yi,Naila ta sake gyara musu take yi Jamilu ku daina mantawa ta fada kasa kasa,Mohsin yace Hanan tace a gaishe ki,Hmm ka dai ari bakinta,bana amsawa indai itace,Mohsin yayi dariya yace ki yafe mata,wlh bazan yafe mata ba ni fa kawai ka fara neman aure,au kin fasa binciken a kaina ai sai ki bari a bincika ko canja ni akayi a asibiti muyi auren,Naila ta tuntsire da dariya tace lokacin ban waye ba yanzu na waye ato,Mohsin yace a Hakan? baka ga alama ba? Ni Gani nayi kin sake zama wata tsagera Yar kunyar ma da kike yi ta Fulani yanzu babu naga duk uban mazan Nan harkarki kike yi,Naila tace Dan ma baka San tsiyar da nake shukawa ba Yaya,Na zama Yar Yahoo fa wata nayiwa Yahoo zata siya min waya ta zaci namiji ne muke ta soyayya ta jikin bango,Suka yi dariya Umma tace Allah ya shiryaki,Suna hirar kuwa sai gashi an sake zuwa neman Jamilu Tantiriya,tace gani, Baban Beauty ne yace a Baki, Naila ta karbi ledar ta bude wayace hadaddiya Samsung sabuwa dal a kwali,harda kudi dubu goma a envelope, Naila tace Baban Babyna ya bani Yaya,Mohsin ya boye dariyarsa shi Kam Naila tafi karfinsa,duka Maza da matan ubansu suke ciki a wajen Naila, su Malam Garzali ne suka fito suma anzo wa kowa cikinsu,harda zuwa su gaisar da Iyayen Jamilu kowanne wai su a dole masu Aboki,.

Dan Indo shima yazo ya gaida su Umma,Scoler da Goje ma suka zo suka kwashi gaisuwa,Scoler Yana wata karairaya ya Kalli Mohsin yace da alama wannan shine yayan namu,Naila tace shine Darling dina nane,Scoler yace ah wallahi shar Darling Mohsin barka da isowa na Dade Ina so mu gaisa da babban Yaya ashe zaka zo yau Darling,sabo da Allah bakwa kyauta mana ba kunki zuwar mana ziyara,to yanzun ma Kun kyauta ai idan zaku tafi zan yi mi'ara koma baya inzo muyi sallama yayi girgiza Yana shanye hannu yayi gaba.

Umma ta rike baki tace yau Ina kallon ikon Allah, Mohsin kuwa Spark yake kallo sai yaga kamar ya sanshi, Umma sai yanzu ta kula da Spark tace Kai waccen fa kaiii amma waccen Dan me kudi ne wannan irin kyau haka ko ziyara ya zowa wani ne? Naila tace ai abokina nane shi aka zowa Ziyara,Yana zaune tare da Kamal da Sadeeq kaninsa sai Naila taga kamar gulmarta suke yi.

Lokacin Kamal yake cewa ka tambayi kuwa Jamilu Hashim din ai Yana ciki shima,Saddiq ya nuna Naila yace gashi can ma wlh wannan amma ni mamaki nake ace namiji ne,Kamal yace namiji ne mana ai akwai masu kama da mata, Spark yace dama wai shine Jamilun da Mummy ta daure? Kamal yace shine kuwa ka taimaka Masa Dan Allah,Spark baki ya tabe yace waccen ai shahararren Dan duniya ne wlh ban taba ganin Tantiri irinsa ba,Saddiq yayi dariya yace muma da muka je kotu mun Sha kallo wallahi a gaban mutane da alkali ya dinga tijara,baka gani ma'aikatan gidan ma sun sallama Masa.

Spark yace Jamilu yafi karfina ta ya zan taimaka Masa duk gidan nan ba Wanda ya kaishi suna baka gani ba sai zuwa gaida iyayensa akeyi ba,ka dai daure cewar Kamal,Saddiq yace nima wlh Yana birgeni ba a taba namijin da nagani yake birgeni ba irinsa, Naila tana gani tace waccen gulma ta suke,Mai gulma Dan wuta ta furta yanda zasu ji ta,tace duk mai gulma ba shi ba Rahmar Allah

Spark ya kalleta suka hada Ido ambola ya mata,ya zageta da hannu,Naila tace niiii ...ta nuna kanta ya daga mata Kai, Kai ta jinjina tana murmushi tace zaka shugo ne,Kamal yayi dariya yace kaji yace zaka shugo,Spark yace baida karfi ko kadan bigeni yayi rannan fa ya Fadi a kasa,suka yi dariya.
Naila kuwa abincin aka ce a bude a gani sabo da tsaro kowa ya kawo abinci sai ya dandana kafin na gidan yarin ya ci,Umma duk ta dandana,Sannan Naila tace yau akwai party wlh ta zaro yankan nama daya kato ta lunkuma a bakinta tana ci tana kallon ma'aikatan nasu tace Dan bakin ciki sai dai ya mutu wlh Allah,nama munfi bayin gomnati ci,muna bautar Allah suna bautar Gomnati,Umma tace kiyi shuru Dan Allah mu fita lafiya..suna haka sai ga Hanan tazo itama tsabar sa Ido wai taga yanda Naila ta rame tayi dukun dukun tayi duhu sai kuwa ta hangota Shar da ita,a haka ta karaso tana Jin haushi.

Karasowa tayi tana Bata rai su Umma kawai ta gaisar ta Kalli Naila tace Yaya wahalar gidan yarin? Naila tace hmm wahala tana wajen Wanda suke cikinta ni Kinga wahala a jikina ne?rayuwa kenan cewar Hanan,Naila tace yo dama life haka take mana cikin biyu zaka yi Daya ko kaji jiki ko kaji dadi,ke ba gashi ba ai son ranki ki auri me kudi to ga Yaya Nan dai sai rufin asiri kina kallo matan masu kudi suna shanawa ke kuwa fa? Kina son daura atamfa super ba hali sai dai chigambi karama Naila ta furta tana kallon atamface chigambi a Jikin Hanan,taci gaba da cewa to Kinga rayuwa haka take kina cin shinkafa da wake wata tana cin Shinkafa da Miya har da nama da kayan lambu,Umma tace gaskiya ne ke kika ja ma kanki Kuma wlh bazan hanata ba.

Hanan baki ta tabe,Naila ta sake dakko nama tasa a baki tare da girgiza Kai tace wash....dadi my Enemies are crying,har mafarkin kukan makiyana nayi jiya na hango su suna ta kuka ashe yau abin zai faru hhhhh tayi dariya tace ahhhh Makiyana suna fama,Yaya ya kamata fa ka hanzarta ka Nemo mace ka Kara aure mun gaji da shinkafa da ake ta ci kamata yayi a nemo taliya da Miya, Umma tace to ya isa haka ai kin rama duk tsiya wajenki ta zo,Naila tace sa Ido dai tazo taga ya na koma Kuma taga ba haka ba,mutum ba a shiga harkarsa ya dinga takurawa wani shi yasa tuntuni nace na saketa ni,wlh Bata gabana Sam na gama da shafinta a haka ma darajar Darling take ci,Inama ace Yaya ba Dan uwana bane ta dole zan shiga gidan wlh muyi kishi ni bana so ma a saketa sai nasa tayi zaman bakin ciki a haka zata kare rayuwarta.

Abba Yana jinsu yace Naila ba a hanaki ki ji ko bakiji me Umma tace ba, nayi shuru to naga bakin Umma shine yayi sanadin zuwana Nan gidan,sai da tace kar na siyar da magani bada yawunta ba amma naki jin maganar uwata sai gashi na fado gidan yari Dan Allah ku yafe min daga yau sai abinda kuka ce zanyi ba ruwana,Hanan mikewa tayi taja tsaki ta fice tayi tafiyarta gida,Mohsin yaji haushin tsakin da Hanan tayi a gaban iyayensa bayan itace da tsokana hasali ma bata fada Masa zata zo ba,ransa ya baci matuka abinda take Masa duk Inda taga dama sai ta fita ba tare data fada Masa ba.

Hirarsu suka ci gaba da yi Naila tace Abba ya kasuwa ashe an koma kasuwa,yace kasuwa Alhmdllh Ina can Ina ta yin araha,ai kowa araha nake Masa, Naila dariya ta kamata wai Yana can Yana ta Araha,Naila tace Abba kace duk masu abincin siyarwan nan na layin...kafin ta karasa yace duk a wajena suke siyen kayan Miya,zawarawa da matan aure harda Yan mata layi suke min ni kuwa inyi ta musu araha,Umma ta kalle shi tare da galla Masa harara,tace kamar Wanda yayi abin arziki bayan duk dakko kayan Miya sai an cika Masa kudin jarin ya karye,Naila tayi dariya tace Abba Debora me yin Sakwara itama nan take zuwa? Yace ae rannan ma kyauta na bata,Harira kuwa me shinkafa da Miya jiya tace min tunda ta fara siyan kayan miya wajena miyarta yawanta ya karu, tace riba take ci sosai shi yasa kullum a wajena take siya,Mohsin yayi dariya a boye Dan kuwa Su Harira sune suke cutar Abbansu Yana basu da yawa watarana ma shi yasa idan Yana free sai yaje ya zauna a wajen sannan ake cin Riba ko a tura Hidaya ta zauna ta siyar shi Kuma ya koma gida ya kwanta abinsa ko ya taya Umma girki.

Naila tace Inama Ina Nan Abba yanda kake son hutun Nan na karba na dinga siyar Maka kaje ka kwanta ka huta kawai tunda burinka kenan,Abba yace da kuwa na zama Dan Madara,Umma tayi dariya tace a ranta yazo dai ya dameni ba uwar da ya iya sai jaraba shi dai yaji dadi a rayuwarsa.

Suna surutunsu Naila tace ma'aikata ga nama Bismillah Kunga month yayi nisa ba albashi bare a ci a gida,yanzu da za aje shaguna duk list din Yan bashi idan aka dakko ma'aikatan gomnati ne a ciki,dariya suke yi kawai, sabo da suma ma'aikatan wasu duk lallaba Yan gidan yarin suke suna wasa da wasu,Wanda yayi rashin mutunci idan ya sake mutum Yana gidan yari zai bada umarni a bishi har gida a kashe shi,shi yasa sai da taka tsantsan, dariya suke yi indai Jamilu yazo waje sun ga ta kansu da bakaken magana.

Spark ya gama da su Kamal zasu tafi yace Mummy yaushe zata zo? Wai sai ta gama takaba tukun, yace Alright my regard to her ace na gode,suka tafi shi Kuma ya taho zai wuce ciki Naila ta riko rigarsa ya tsaya tare da Juyowa tace abokina ga iyayena da yayana My love,duk wulakancinsa sai tayi mamaki ganin ya rusuna ya gaida da Umma sosai,Ya gaida Abba da mutuntuwa sosai harda kakalo murmushi,Sannan ya mikawa Mohsin hannu yace sannu da zuwa Yaya,Mohsin zasu yi sa'anni da Spark suka gaisa,yace kaima kaddara ta fada Maka to Allah ya kubutar da ku,yace Ameen da ledar take away a hannunsa,muma lokaci yayi tafiya zamuyi an fara Maida mutane ciki,Spark yace yeah ai matan ciki za a fito dasu suma,Naila tace ai naso ganin Beauty amma ba dama, Spark ya faki Ido ya gallawa Jamilu harara.

Mohsin yace to Jamilu ku shiga ciki zamu wuce,Naila ta mike tare da daukan ledojinta, tace a gaida su Aslam da Hidaya,tayiwa Mohsin rada ka tabbatar yau baka bawa Yar iskar matakar ka ba Hallare,Kaine baka da garanti a rayuwa ayi mutum ba hakuri,wlh idan na fito sai na kashe Hallare ta daina komai kowa ya huta,dariya yayi yace munje wajen Kaka Affa,mun fada Masa halin da kike ciki Yana ta kuka wlh,Har maganin gargajiya ya bani shi yasa yanzu Hanan bata so nace ta tafi gidansu,Baki Naila ta rufe da hannu tana dariya tace Yaya kaima ka zama Tantiri,Umma tace Dan Allah Kai muje sai za a tafi zaku fara kus kus, Naila tace Umma ya bin kangon wajen masu gini? Umma tace na daina yanzu bana so na koma neman warin taba sigari,Abba yace Dan Allah muje sun fa daga mana kafa Kalli yanda ake Maida wasu ciki.

Sallama suka yi Naila ta tafi ciki tuni Spark yayi nisa har jiri yake yi na yunwa gashi daga nesa su Kamal suke basu taho Masa da abinci me nauyi ba,Yana komawa ciki ya tsaya Yana jiran Jamilu,Naila ta shugo da kayanta Niki Niki,wai wayo zai mata yace Jamilu zo muje part Dina muyi ciyayye kasan akwai Lada cin abinci da Yan uwa,ana so ko makwafta da abokai ka dinga fitowa da abinci kuna ci tare.
Naila tace Allah sarki ai shi yasa mutanen da suka fimu zumunci da kaunar juna to za a hadu a ci abinci tare muje,yayi mata wayo dake macece.

Spark yace a ransa Kai Jamilu ba wayo, suka shiga bangarensa sai da izininsa aka barta ta shiga ciki, palonsa suka zauna ta bude ledarta ta duba har kayan Maza an kawo mata harda pad a ciki a boye an sassaka a ljihun kayan pieces yanda baza a gani ba,tace ai sai Yaya Mohsin, harda hular Sanyi da hula p-cap yanda zata dinga rufe gashinta, da wani mayafin kamar na Maza tasan na sallah ne, ta samu kayan sawa har kala biyu ga vest ta mata me kalar ta Maza,haka boxers da panties dinta duk a boye Wanda mace na iya sawa haka namiji na iya sawa tasan aikin Mohsin ne.

Shi kuwa Spark Yana Ganinta ko ta kan kayan Bai bi ba kawai abincin yake so a bude yaci me gishiri da Maggi, Naila Jamilu ta bude abincinta na farko farfesun Naman rago Yana kamshi,Ga wata fried rice taji hadi,harda hadin salat daban da soyayyar kaza,gefe ga tuwon shinkafa miyar egusi, harda dambun nama da yawa daban,sai chinchin da meat pie, ga hadadden zobo Umma tayi da sanyinsa,Jamilu yace Kai gidan yari yayi ta wani bangaren,da a gidane yaushe za a kawo min wannan, da spoon na roba guda uku an zubo mata.

Spark sai kace abincinsa ya dauki Spoon yayi Bismillah ya ja kwanon Fried rice ya fara ci,yaji dadi yace mamanku Jamilu ta iya girki,Jamilu ma yasa spoon yace kaifa mamanku? yace tab Yan aiki suke girki ta manta yanda akeyi ba dadi nata, dariya ta kama Naila ta dinga kyalkyala dariya, Spark ya kalleta yaci gaba da cin abincinsa ba tare da ya kalleta ba yace Jamilu kasan kana kama da mace kuwa? Naila tace haka ake cewa ya na iya da halittar Allah,tunda nazo gidan Nan nake kallon kirjinka ko zanga Nono amma babu,Jamilu yace wato Ido kake sa min, fuska ya hade yayi shuru Yana cin abincinsa sai da ya cika cikinsa dam,tunda yazo gidan yarin sai yau ya koshi yaji dadin jikinsa, duk ya cinye shinkafar Naila kadan taci ya cinye mata,tuwon ta jawo zata ci ya kwace yace sai dare za a ci wannan, Jamilu ya tsaya Yana kallon ikon Allah yace ni da abincina zan fasa ciyayyen wlh kaji mutum,Yace baka isa ba sai mun dinga ciyayya daga yau Kaci abincina naci naka ya tura mata ledarsa yace gashi Nan cinye wannan ai dama ba aci nawa ba.

Naila ta bude ledarsa Taga tarin snacks da su yogurt,fresh milk da tarkace daban daban, ta zabi cake kato da yogurt taci ta koshi sannan tace kawo abincin na tafi da shi akwai Yan dakin mu,yace baza a basu ba kawai sai su cinye mana suma ai anzo musu Kai Jamilu bana son wannan Imanin naka,idan mutum ya fiye Imani baya iya taimakon wasu,Naila dariya ta kamata tace to kawo Naman a basu,yace ka basu farfesun mana mu sai mu ajiye soyayyen ko ya kace,Naila tace to Hakan yayi ta dauki farfesun da wasu cakes din da su lemuka Wanda aka kawowa Spark ta tafi da su dakinsu tana cewa sai dare zanzo muci tuwon yace to sai kazo,ka samo min Dan aiki a part dinku zai na min wanki da guga da shara zan dinga biyansa.

Naila tace gani aikin me nake ni indai zaka biyani zanyi,a ransa yaji Tausayin Jamilu Ashe shine Mummy dinsa ta yima sharri,amma bazan nuna nasan shi bane,wannan dalilin ne ma yasa har ya gaida iyayen Jamilu,baida burin yasa Jamilu aiki ya dinga wanke Masa kaya da shara a fili yace muguntar tayi yawa gashi ya yarda naci abincinsa wannan Jamilun akwai kirki,wai har Yan dakinsu zai bawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login