Showing 39001 words to 42000 words out of 158722 words

Chapter 14 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

675

namansa, kwanciya yayi a Saman bed dinsa Yana ta sake saken rayuwarsa.

Naila kuwa tana zuwa dakinsu ta iske malaman sun hadu suna ta cin abincin da aka kawo musu duk cikinsu babu me binci da nama,daga shinkafa dafaduka sai shinkafa da wake,sai shinkafa da Miya da kifi sai Dan lemon su fanta,Jamilu Yana shiga suka ce Bismillah Malam Jamilu,Naila tace a'a kune malamai Kun taba ji nayi wa'azi a gidan Nan? Ba karantarwa ce ta kawoni ba kaddara ce wlh ba Wanda zan koyawa karatu ko na iya,Malam Sharu yace a daina biyewa rudun duniya Jamilu ka shigo makarantar mu, Naila tayi dariya sosai tace zan shugo,Naman ta ajiye musu tace gashi ta zube musu snacks da lemuka tace ga naku,suka yi ta mamaki Dan a jarabar Jamilu basuyi zaton zai kyauta ba,suka dauki yanka daya daya,Jamilu yace naku ne fa ku cinye wlh du ana tare taya zan cinye abu ni kadai,Malam sai murna da godiya yace Allahu Akbar.

Naila kuwa Beauty ta kwalawa kira akace ta tafi wanka tace idan tazo kuce yau bazan samu Daman Hira da ita ba naga sakon waya na gode,suka ce to za a fada mata,Malam Sharu yace Kai ni wannan Jamilu adduar ma taki Masa aiki Inda kasan shedan,Dan Indo ne ya shigo yace Jamilu Terror taho taho ga abinci, Naila ta mike ta bishi suka tafi,Scoler ya tare su a hanya yace Habibty na ajiye Maka Kazarka soyayya ce,Naila tace Rasssss dani Ina zuwa zanzo na karba,Sai da taje Wajen su Dan Indo da Goje ta karbo rabonta tace sai dare zata ci amma tana zuwa ta bawa su Malam Sharu sai murna suke yi,taje ta karbo kazar Scoler a soye ta sake kawowa su Malam Sharu,ana ta Bata abubuwa sai ta duba duk Wanda baida gata a gidan yarin ko ba a zo Masa ziyara ba sai taje ta bashi,har wasu take Gani tace wane baka bani nawa ba,sai an bata sai tazo ta nemi yaku bayi a ciki ta basu,Jamilu ya sake suna sai mutuncinsa ake gani,bayan tayi wanka da dare kaikayin gaba ya isheta tace gobe asibiti zanje inshaallah, ta shirya cikin sabon kayan da aka kawo mata suma manya falka falkan gaske, ta gyara tarkacen kayanta,suna fita Sallar Isha tayi sallarta da addua Allah ya rufa mata asiri kar a gano ta sannan Allah ya fitar da ita, yanda take sallarta idan sun fita jam'i haka tayi abarta,Allah kuma Yana ta rufa mata asiri har yau ba a kamata da mayafi tana sallah ba a haka ma sai ta nemi lungu a cikin dakin take yin sallah.

Malamai suna dawowa suka zauna zasu fara karatu yau sunci nama harda fara addua kafin a fara karatu suka ce yaron nan Jamilu idan sharri aka Masa Allah ka fitar da shi,Allah ka shiryi Jamilu,Allah Dan darajarka ka kubutar da Jamilu daga gidan nan,ka Kara daukaka shi suna cewa Ameen Ameen, Bismillah da Ayatulkhursiyyu,Naila dariya ta kamata ta danne ta zauna a kasa ta daga hannu sama itama tana cewa Ameen,Allah Gani ni Jamilu Allah kana kallona,Mummy ka tarwatsata,Mummy data min Sharri Allah ka tattaro bala'in duniya Dana lahira ka danna acan cikin Mummy, Allah kasa kullum cikinta ya kumbura,ka sata zawo,komai taci ciki ya kumbura,Ya Allah da zawo,da kashin jini,da amai da gudawa colera,ciwon zuciya, ciwon kafa,ya Allah da ciwon Kai,Dana mara,ciwon Sanyi irin naw,,,,tunawa tayi zata tona kanta tace Allah karka bari ta auru,Allah kasa tayi kwantai,ba ita ba samun bazawari,Allah Danta Ashraf da take ji dashi Allah kasa ayi Masa sharri irin nawa ya fado gidan Nan,Allah ka hadani da Ashraf Dan Mummy a Nan gidan yari,Allah basai na fita ba Allah a Nan gidan,Allah ka bani ikon cin ubansa,kar naji tsoro,kar ya min kwar jini,naci ubansa daidai yanda ya kamata.

Su Malam Sharu suna addua sai suka tsaya kallon adduar Jamilu suna dariya Yana gama adduar suka ga ya mike yace na tafi wajen abokina mutumin kirki Ashe Yana da kirki duk gidan Nan babu me kirkinsa idan Kun ganshi ku dinga girmamashi wlh ga kudi ga kyau ga kirki iya kirki yau da shi muka samu ladar ciyayya ma yaci abincina naci nasa,Malam Garzali yaji wani mahaukacin kishi yace kaga Jamilu ka rabu da yaran masu kudi ka fiye rawar Kai ka kula ka tsare mutuncinka ato Ina baka shawara kar a Maka wayo kana yaro a lalataka Jamilu,Jamilu kayiwa kanka fada tam shike nan.
Naila tace a'a mutumin kirki ne wannan duk gidan Nan nafi kaunarsa,Wanda nake jira Allah ya hadani da shi Dan Mummy ne wallahi bala'i da masifa har sai na aro ta Ummata,rashin mutunci da tuggu kuwa shima sai na Nemo Kari sai na kusa halaka shi da sharrina,Malam Sharu yace wannan yaro Ashraf ya shiga uku har na fara tausayinsa mu kanmu da ba abinda ya hadamu ka buwaye mu bare shi,Naila ta fice abinta harda shafa turarenta sabo da Spark dan gayu ne.

Yana dawowa daga masallaci ya samu Jamilu ya shugo,yace Kai naci Dan tuwonka Yana Nan shine harda zuwa da wuri,Naila tace Ina laifi Dana jira akayi Sallah ma ko tuwonka ne? an kawo Maka ne daga gidanku? Spark uban isa da gadara yanzu kirki anjima rashin mutunci,yace gashi can dauki abinka,ya furta da gadara da kyar yake magana yana bata rai,Naila taji haushi tace koshi kayi shi yasa ka fada min haka taje ta dauki abincinta ta tattara da nasa gaba daya tayi waje,ya fito da sauri ya fisgota, shi mantawa yake Jamilu baida karfi,Naila sai gata ta zube a kasa har gwiwarta ta fashe,yace sorry, da sauri ya daga Jamilu yaji shi shafal ba nauyi,jikinsa wani shegen laushi haka,tsoro ya kama Spark yaja baya Yana kallon Jamilu,yace anya Jamilu bazan Maka tsirara ba kuwa na gani namiji ne ko mace,please muje ka tube wandonka,ni ba gay bane ba abinda zanji kawai so nake na tabbatar,Naila tace au ta haka ka bullo fyade zaka min dama ance yaran masu kudi Yan iska ne to duk gidan yarin Nan sai na fada musu Kai Gay ne,Spark ya zaro ido yace na janye maganata karka bata min Suna Ina respecting din kaina da kaina.

Naila tace to karka sake ce min haka yace never, muje zaka ci abincin? yace ni da zaka bar min abincin ma nafi son haka,Naila tace to muyi musaya Kaci nawa naci naka,yace good,ta koma ta shige ciki ya shiga shima Yana jinjina anya Jamilu ba mace bane,Haka yayi shuru ya zauna Yana kallon News,Naila ta dauki nasa snacks tana ci abinta cikin Jin dadi,shi kuwa baya cin tuwo ma a gida amma gidan yari tasa wai shine ke yin wayo akan a bar Masa tuwo,tsaki yaja yace akan tuwo da shinkafa duk mutuncina ya zube wai yau ni Spark nace wa wani katon zindiki sorry akan tuwo,bazan yafewa kaina ba yaja tuwon Yana fushi Yana cika Yana batsewa haka ya fara cinye tuwonsa Yana Santi,yace uhm Poor Umma da iya girki,maganarce ta fito fili Allah yasa Naila bata ji ba da ya gane kurensa akan iyayenta bata wasa.

Naila tace ance ku masu kudi Kun San juna watarana Kuna haduwa a wajen da sai me kudi ke zuwa,idan a Abuja kake Dan Allah kasan wani Ashraf babarsa dai wacce ta Raine shi Mummy ake ce mata duk family dinsu sojoji ne yawanci,ance ai shegen Ashraf din nata ya fara aikin soja ya bar aikin ya koma business sabo da shi bakin Dan iska ne,ance ai matsiyacin ya tara kudi,naji danginsu kowa sai yace Ashraf,baka sanshi ba? Tunda Spark yake bai taba dariya irin ta yau ba,ya dinga dariya a ransa yace Allah ya taimakeni ban fadawa Jamilu ni bane Alhmdllh da Ashraf ya sanni,Allah yasa bai San nasan shi Mummy tayiwa sharri ba,Naila ta tsaya tana kallonsa Yana ta dariya

Tace ka sanshi dan iskan algungumin? Spark yace ai abokina nane, Alhmdllh ta mikawa Spark hannu tace mu gaisa ya mika hannu suka gaisa yaji wani shegen shock duk jikinsa ya dauki vibration,itama Naila haka taji da sauri ya janye hannunsa yayi wani Sanyi itama haka,tunawa yayi namiji ne da sauri ya girgiza kansa ya dawo daidai,tace zaka min hanyar ganinsa idan Allah yasa na fita daga Nan gidan, Kai wannan dan nata sai na Masa akuya,wlh sai na huce a kansa Dan iska matsiyaci,mutumin banza Allah yasa ya talauce ga mijinta ya mutu ta rasa ko suturar sawa inshaallah sai na taimaka Masa da shi da ita,jahilan banza jahilan wofi, Spark yaji ana ta Masa mummunar addua shi ba da laifi ba yace Kai Jamilu addua akewa mutum kace Allah ya shirya Ashraf.

Naila tace wlh bazan ce ba sai dai na tsine Masa na sake tambade Masa albarka mutumin banza wa ya sani ma ko a turai din Mata yake bibiya Yana can Yana sheka iskanci da mata,shi baiyi aure yayi ibadar Allah ba ya zama Dan kwararo shine turai shine kudu Lagos wajen mata,Dan Bariki, Mayen mata,Ashraf yayi dariya kamar cikinsa zai ciwo yace wait Jamilu kazafi fa kake Masa ba wani kazafi ai mun sani yaran masu kudi me suka sani in banda lalata mata Yana can ya zama Dan aci kullum sai kace Ronaldo kullum aci kwallo haka ya Maida mata,zai gane kurensa Ina Nan Ina addua Allah ya hadani da shi sai na kwankwatse Masa Hallare, Spark yayi dariya kamar ba gobe,Naila tace wallahi tun a waya zaka hadani da shi na fara rage zafi da zagi na fara rage hanya kafin mu hadu,Ba fa shi ya maka laifi ba Jamilu,Naila tace nima ai ba Ummata ce tayiwa mummy laifi ba ta kare akan Dan Umma to nima akan Danta zan kare.....

Gidan Baban Asmau tuni sunyi hakuri suna ta uzurinsu an daure Spark,Amma Maman Asmau wato marikiyarta itakam Yar uwar Maman su Spark ce itama kanwarsu ce,abin Yana damunta bata ji dadin kulle Spark ba ai shima danta ne,a dalilin haka gashi Mima ta daina shiga harkarta bare Mummy kamar ba Yan uwa ba gaba suke da ita,Kanwar Asmau wace ake kira da Safna itama zata kai 26yrs ta gama degree har aiki tanayi a asibiti,itace kadai tafi kowa damuwa a gidan ta shiga wani hali,tunda aka kashe Asmau take ta faman ramewa tana damuwa sosai watarana ma sai ta kulle daki tayi ta faman kuka,kowa yasan yanda suka Shaku da Asmau kamar me kullum suna tare dakinsu daya,har addua ake mata sabo da yanda ta fice a hayyacinta,aikin ma ta daina zuwa ba irin lallabata da ba ayi ba taki hakuri,ta samu babansu tace wlh Abbu Spark bazai kashe Asmau ba,kawai furuci yayi a dai dai kaddara ta fada Masa,Dan Allah kasa a sake shi idan yaso tunda ana so lallai sai an hadin zumunci ni me zai Hana na maye gurbin Asmau ko da ace baya so na nima zanyi hakuri na zauna dashi sabo da na cikawa Asmau Yar uwata burinta,Ni a maye gurbin Asmau Dani,Abbu ya Kifa mata Mari ya sake Kifa mata Mari yayi ball da ita yace har abada bani ba hada alaka da Spark Kuma bazai taba fitowa ba,mahaukaciya wacce Bata kishin Yar uwarta Dabba wacce bata San me take ba get out,ta mike Zumbur ta fice tana sharbar kuka tace Allah kaga niyyata ta alkhairi ce amma Abbu yaki ta fada dakin Mahaifiyarsu Tana kuka Mama kinga Abbu ne akan nace ya saki Spark ni a maye gurbin Asmau dani shine ya mareni ya min duka, Mama tace maganinki kenan ai na hanaki zancen,nifa so nake na taimaki Spark a fitar dashi,Mama tace duk da bani na haifi Asmau ba wlh ko ba a kulle Spark ba bazai aureki ba kema,wannan yaron bashi da ta Ido shi yasa nake baya baya da shi,kina dai gani Yan uwana sun san Asmau bani na haifeta ba amma gaba suke dani,abin ya kwabe da yawa kiyi hakuri.



Sharhi Dan Allah



Free page

Accnt no
0175487861

Katin MTN
08061929616


Yan Niger
+22790795939






AsmaBaffa
[12/8/2023, 6:56 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI


26-30


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE
GARE KI❤️
AIDA MAMAN TASNIM



Page naki ne
YAR LELEN ROYAL STAR



MASU AUDIO BAN YARDA A JUYA MIN NOVEL ZUWA AUDIO BA IZINI BA



*_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_*
*_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_*
*_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_*
*_dama wadanda zasu ganki ahanya?_*
*_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_*
*_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_*
*_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_*

```ARZUQLANA GALLERY```

*_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_*
```Laces
Atampha
Shadda
Abayas
Materials
Gyale
Takalma
Jaka
Kayan Kitchen
Bangles n jewelries```
*And many more*

```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO```

*_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_*

*_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_*

*_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_*


*_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_*
https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ




Spark suna zaune Yana faman Jin me Jamilu ke fada Yana ta Shan zagi a wajen Jamilu shi da Mummy, katseta yayi yace yanzu ka samo min me aikin? Naila tace gani wai zanyi indai zaka biyani,Kai ba karfi ba kace zaka yi,Ae zanyi haka Ina so,yace ba damuwa,Naila tace bari na tafi dare zaiyi,ka zauna a nan mana zan biya Maka kudin kwana mu zauna tare nima na huta zaman shuru,Naila tace a'a tafiya zanyi,Baki ya tabe tare da furta alright you can go,Naila tace aha sai da safe,ko kula Jamilu baiyi ba ya mike Yana taku dai dai ya shige bedroom dinsa,Naila ta juya ta fice.

Tana fita taga kartai sun hargitsa gidan suna ta fada ana kokarin rabasu,tsoro taji ta juyo da gudu tana haki ta shiga dukan kofar Spark kamar zata balleta domin shi ya sa key,wanka yake yi amma ihun Jamilu yaji Yana cewa abude wayyo,da sauri ya daura towel Dan guntu jikinsa duk kumfa ya bude kofar,ta fado ciki tana haki zata yi kuka tace fada akeyi saura kadan jifan dutse ya fasa min Ido,murmushi ya saki tare da furta shine Kuma abin kuka ko kunya baka ji sai kace mace yaja tsaki tare shigewa toilet abinsa,sai bayan ya gama wankansa sannan ya fito,jikinsa Naila ta saci kallonsa a ranta ta furta wow idonta ta dauke a kansa kar ya kamata taga bai son kallo, gashinsa yake gogewa da Karamin towel,Naila sai faman kallonsa take ta saki baki,kamar wata wawiya, Juyowa ya sake yi da sauri tayi kasa da kanta ta koma kallon kafafunsa masu kyau farare sanye cikin takalma slifas, gashinsa ya busar ya fara taje shi,Naila taga duk su lotion dinsa masu tsada da sauri ta Kalli skin dinta ita, tace shi yasa ni bana shining Dan hasken nawa ma sai guduwa yake,wai ni ya haka ne ai kuwa bai isa ba wlh duk da ya fini haske sai na kamo shi.

Juyowa yayi haka kawai yaji shi Sam a mace yake kallon Jamilu ya rasa dalili magana yayi a gadarance yace koma Palo zan shirya,Jamilu yayi murmushi Yana kallon Spark yace Ina namiji me zan gani a jikinka,ni ko towel dinka ka cire ba ruwana ba abinda zan Gani abinda kake dashi nima Ina da shi, Spark yace Allah? tace sosai fa,yace to a Kalli juna wallahi na yarda ka tube wandonka ni ma zan cire towel din, Naila a ranta tace wannan fa ya uzura min tsakani da Allah kar ya gane ni,a fili tace sai kace wasu yara,wato na ganeka so kake yi muyi wasan bayan murfin kofa na yara to bazan yi ba na girma ni,idan mace kake bukata ka San ya zaka yi ka samu wata ta bude Maka Garejinta ka shiga amma ni namiji ne,me yasa kuke zargin macece ni ta ya zan shugo Nan ba a gane ba Kuma,to a wajen Yan sanda ma daga ni sai gajeren wando da singlet,Inama kasan Mummy da nace ka tambayeta kaji ai ita ta ganni a haka,Spark yace na yarda to ka fiye surutu Kuma ka daina kallona.

Naila da sauri ta dauke kanta amma ta manta ta sake sakin baki tana kallon kyakyawar surar Spark, ta wani bude baki ta sake shi,a haka ya fara shafa mai Yana Juyowa again ya kama Jamilu,da sauri Naila ta mike zumbur tace na tafi,ko magana baiyi ba Yana jinta ta bude kofa ta fice, a tsorace take tafiya tana addua a bakinta har ta fada dakinsu Inda ta samu malaman sun fara bacci ma,tace an gaji da tilawar kenan,tazo ta kwanta tare da jawo sabuwar wayarta ta kunna tana Gani ta hadu a fili tace wannan tafi karfina kyan wayar Nan Yaya Mohsin wlh shine Dan gayu ni Ina gidan yari wa zan birge da waya Ina cikin wahala ai gara na rike Yar karamata burin kwaila, ta jona abarta a charge ta cika full sannan ta zare ta Maida cikin kwalin ta ajiye tace sai sunzo ziyara na bashi ita.

Bangaren mata a gidan yari Beauty kwance take a Saman gadonta tana ta faman tunanin Jamilu tana matukar kaunar Jamilu,Surarsa take kissimawa a ranta kawai ta hango Jamilu wani kyakyawan matashi hadadde me dauke da faffadan kirji, damatsansa wasu manya alamar Yana Gym,murmushi ta saki cike da shauki ta juya a Saman bed din tare da rungume wata teddy dinta da Maminsu ta kawo mata, ta sake juyawa tayi mika tare da sake kankame pillow tace wato Allah haka yake ikonsa idan yaga dama ba Inda bazai hadaka da mijinka ba,gashi nan shima sharri aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login