Showing 105001 words to 108000 words out of 158722 words
Chapter 36 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
jama'a Dan Allah ga kudi na dauki nauyi a Kai waccen asibitin mahaukata,Rass da Kwass fa ta haukace Baby,Ni na taba ganin kishi haka.
Umma ce ta gaji taje ta fisgo Hannun Hanan ta fito da ita tace baki da hankali ne,Allah ya isa duk munafukan surukan da suka zuga aka min kishiya ai munafunci ne,surukai su dinga munafunci suna zuga dansu Yana aure sabo da an tsaneka wallahi Allah ya isa,su an barsu sun zageni sun zagi iyayena sai ni yanzu sabo da Ina rawa za'a hanani ta fisge hannunta ta fice daga wurin dinner din gaba daya sai gida.
Can ta iske da ginta tsirari tana zage zage tace wallahi sai nayiwa amaryar duka za a kawota ne,sai na cinnawa gida wuta idan na tare,suma dangin sai wani bata hakuri suke suna Kara zugata a nutse.
Bayan an gama Dinner Spark yayi hanyar Hotel da Naila ta fashe Masa da kuka tace nice babba a gidanmu mace komai Dani ake shawara Idan Umma suka ji ni wlh bazan je ba ka sauke ni,Spark yace ko Abba bazai ce min komai ba wlh Dan na daukeki nifa ba abinda zan miki nayi alkawari sai an kawoki gidana,Naila tace aje wajen Abban indai ya yarda zanje,Ta Manda Abba Dolo ne.
Suna zuwa suka same shi a kofar gidan Yana jiran Naila zai mata kaca kaca,dama yace yau sai yayiwa Naila kaca kaca a gidan da fada, yace naji abinda kuka yiwa Hanan a wajen party ke Naila ki kiyayeni ke Naila ki dinga saukakawa ranki ato magana ta gaskiya, shike nan fadan wai ya gama,Spark yace Abba nima Kara na kawo, akan nace ta rakani unguwa wai baza taje ba, Abba yace ke Naila ki kiyayi fushin ubangiji,kibi mijinki sau da kafa da kika dawo gida mu me zaki yi mana? Banda ku cika mu da surutu da kawaye,Naila tace Abba fa hotel yace hotel fa tana hawaye,Abba yace Yar banza ni da Kubra zata kaini Hotel dinma ai San barka,so nake na samu kudi nima na dauki Kubra muje picnic.
Spark kasa rike dariyarsa yayi,Naila tace Abba Umma fa sai ta sake haihuwa wlh,Spark ya sake shekewa da dariya yace Dole dai a yara a samu DNA na gado ko Yaya ne Naila itama doluwarce,Abba yace ki daina ja da ikon Allah,da ba a haihuwar za a haifeku ne,gashi muna ta yawa a arewa sai cinye zabe muke na shugaban kasa,namu ne suke ta mulki,Abba da suke cin zaben ai wuya muke Sha munfi kowa Shan wahala,Abba yace ba abinda ya dameni da haihuwar Kubra,Allah in ya bamu muna so wani ma Yana kuka yake bashi da yaro.
Naila ce ta tsorata Abba tace Yan hisba kame suke yi yanzu a hotel,Abba yace yo Karuwa na dauka da za a kama mutum,jiya naji wa'azi ance a dinga fita da mace yawo idan matarka ce,yanzu ance za a tafi dake kinki kina karyata malamai kamar marar Ilimi,Abba kawayena su Rayya fa, in banda hirar shanu me suka iya,Naila yaja gefe Yana mata kus Kus wai nasiha yace baki da hankali ke bakya koyi da uwarki,a gaban suruki kike jayayya da ubanki wallahi watarana idan kuka yi fada zai miki gori namiji ba Dan goyo bane,inja ki ja a gabansa Yana kallonki a marar tarbiyya,ki wuce ki tafi idan Kuma baza ki je ba wallah baza ki kwana a gidana ba sai dai ki kwana a waje ko ki tafi masallaci,Naila juyawa tayi tana fushi ta shiga mota,Spark da gulma sai da ya tabbatar Naila sai ta je, yace Abba a hakura tunda bata so da an barta.
Abba yace a'a kuje kuje tafi da ita ai ba a biyewa mata haka suke da yanga ai idan bata yi haka ba ai bata cika mace ba yaro,ai macen kenan,Spark yayi godiya Yace Abba Allah ya Kara sutura,Abba yace Alhmdllh sutura Kam Ina da ita ma ta isheni haka, Spark yayi dariya a ransa yace wlh Abba Ina ga bokaye ba mutum suka sawa mamansa a ciki ba kawai aka haifo shi.
Naila mota ta shiga tana hawaye tace ko Kaka bamu gaisa ba da shi,Gani yayi bilhakki take Masa kukan,yace ai ke dama ba a abin arziki Dake,yace driver juya ka kaita gida kar ace satota nayi ,fushi yayi,Naila ta kalleshi kadan tayi shuru ya Maidata gida,ko sallama bai mata ba yasa driver ya ja mota suka Kara gaba,Yana mota sai cewa yake hmmm ya ja Kwafa yace yarinyar nan zata gane kurenta bari a kawota.
Naila bata samu Abba a waje ba tayi sauri ta shige dakin da suke zaune da su Rayya,suma an dawo dasu daga wajen Dinner har sun kwanta,Naila ta shugo tare da cire kayanta ta canja marasa nauyi ta sa Hijab ta wuce dakin da kaka yake tare da wasu dattijan,Yace Naila,tace na'am Kaka,yace shugo Maza ki karbi sakonki,Shiga tayi ya Bata magunguna yace ai duk kin San yanda ake amfani dasu,tace ae Kaka,yace to zauna mana,wuri ta samu gefe ta zauna ya fara mata nasiha sosai,Naila tana ji tana to.. to.. to.. ko Dan kuka babu,ya Dade Yana mata nasiha dattijan ma da suke daki daya, suka tayashi sannan yace idan an kaiki watarana sai kuzo min ziyara ko? Naila tace zamu zo Kaka,yace to gasu an dai kaya an nuna miki ko? Naila tace ae Kaka na gode duk ance ango yayi komai sai da ka kawo min kayan kitchen masu kyau harda tv plasma katuwa da fridge.
Yace ai sa na siyar muka tafi birni da goggo muka siyo miki na Yan birni,da ace ma ango baiyi komai ba ai ni zan miki kayan dakin,goggonki ta baki naki magungunan ko? Naila tace,yawwa wannan naki ne karki wasa dasu yanda tace ki Sha haka,Naila tace to tayi musu sallama ta tafi dakinsu tayi kwanciyarta.
Washe gari karfe 11am ne daurin aure,wanka duk suka yi ko wacce taci gayu,Umma Shadda ta saka maroon,Naila da kannensa duka shadda ce pink,Ango kuwa Fara ce Kal ta Sha aiki,Abba yau yasha kyau kamar ba shi ba,Shadda Gezna Mohsin ya Dinka Masa Arsh,gidan Amarya aka dunguma daurin aure, Baban Amarya yayi gayya masu kudi ne kawai suke zuwa,11:30am aka daura auren Beauty Nawwara da Angonta Mohsin Hashim kan sadaki dubu Hamsim.
Hanan tana Jin labarin tace ai bata yi tsada ba wlh,dubu Hamsim duk kudin Ubanta Sadakin yarsa dubu Hamsim ai sai a saka mata million Daya Muji,kawayen Hanan da danginta suka ce munje gidan surukanki wlh ana ta Shan lemuka mu lemo an kawo mana kadan har ya kare,wlh karki yarda kije a karo mana namu ko da bala'i.
Hanan gidan ta tafi lokacin an dawo daga daurin aure ansha pics da Amarya Ango yazo gida Yana ta dauka da Yan uwa,Abba ana yin pics ya fita sallamar masu zuwa Masa Allah sanya Alkhairi,Hanan tasan babu me saurarenta sai Abba wajensa taje sanye cikin Leshi taci takalmi da jaka,tayi kyau matuka,Abba Yana Ganinta yasan matsala ce wajenta ya nufa kar ta kunyata shi a cikin mutane,tana zuwa ba gaisuwa ba komai Abba lemo nazo a karo mana namu kadan aka bamu ni da kawayena sabo da ni ba'a kaunata sai ta fashe da kuka.
Abba yace karki bata mana shagali ke wai bakya son zaman lafiya ne,Lemo carton nawa aka Kai miki sabo da Allah,ai yayi mana kadan ni dama nasan an tsaneni ba a kaunata,Mohsin ya daina so na yaga wacce ta fini kyau,Abba yace ai kema ba mummuna bane ki kwantar da hankalinki Hanan bazai wulakantaki ba,karki ga Amarya ta fiku kyau ki tsorata, duk mun San Amaryar nan tana da kyau amma kar wannan ya dameki,
Abba yace kin San Kubra baza ta Kara miki ba domin an baku da yawa, sabo da korafinki fa abinci da lemo da ruwa da kaina na ebar miki nasa aka Kai miki,jama'ar taki nawa ce? ko Kasuwar singa kika tara ne,Hanan tace ba komai to amma wlh sai an Kara min ko na shiga ciki ayi wacce za ayi dani,kawai sabo da an rainani sai a dinga nuna min kiri kiri ba a kaunata,Abba yace ko kinje Kubra baza ta Kara miki ba,cikin gudunmuwarsa yace lemon duk carton daya nawa ne? tace dubu daya da wani Abu da manya Kuma ya kusa dubu biyu,dubu biyar ya zaro ya mika mata yace gashi jeki ku siya,kudin ta karbe ta juya ta tafi a Hakan ma korafi take yayi kadan.
Tana zuwa suka hau shewa da kawaye tace ai wallahi sai da aka bani kudina chass, ai basu gaji da ganin tashin hankali ba wlh baza su huta ba indai nice har sai an gaji an saki Amaryar.
Ganin Hanan da haka zata kori Amarya.
Spark kuwa ba zuciya akan Naila duk da yaji haushinta jiya amma Allah Allah yake yazo ya ganta,gidan suka shiga tare da su Rafeeq suka gaida iyaye tare da yi musu Allah sanya Alkhairi,Naila dai sai pics suke da Mohsin my love yau an zama ango yau za a kawo Maka Amarya fa,Mohsin Yana dariya yace yau zan karbi sabon kaya,ta dafa kafadarsa suna ta surutu,Spark ya kalleta yace da nine ai da tuni ta fara korafi,Mohsin yace kema nan da 3days ai za a kaiki,Naila tace ae mana munyi anko,tana ganin Spark tace takawarka Lafiya na Naila,anyi fushin anyi fushin zuciya amma zuciyar ta kasa hakura da ni,ya zaka yi da Jamilu,dariya yayi ba shiri,da ya shugo yace bazai kulata ba sai ya nuna mata fushi yake da ita amma gashi ta sashi dariya a banza.
Rafeeq Yana ta kallo dama abinda ya kawo shi kenan,Su Dije suna ganin Rafeeq sun zaci irin Spark ne,shima Spark din basu San sabo da Naila ya saurare su ba,Kanin mijin Tantiriya ga kanin mijin Tantiriya, Rafeeq ya wani bata rai wai kar wata ma ta so shi,ya tsani mace tace tana sonsa shi,Spark yace Kai kawayen mu ne na kauye wlh karka Raina mana kawaye zan karbe jarin Dana baka,Rafeeq dariya yayi kadan yace ai Kai yanzu Yaya sai an Maka uzuri,gaishe da su suka yi,Rafeeq ya Kalli Rayya Dake ta kallonsu tace wannan shi dai Yana da da talatu ne fura,ta nuna Rafeeq,Spark murmushi ya saki,to naga Yana ta wani yanga kamar mace,Rafeeq ya daure fuska tam, Spark shi Naila ta dauke Masa hankali tazo tana Masa rada kayi kyau ko Jin abinda Rayya kewa Rafeeq baya yi.
Rafeeq kuwa Naila ya tambaya yaushe za ayi walimar ne taku? Naila tace 3pm to 5pm sai a wuce Kai amarya,Kamal yace na taba Jin walima mata da Maza a hade,Rafeeq yace haka tafi dadi.
Bayan sun tafi zuwa karfe uku Rafeeq harda canja Jallabiya da carbi a hannu na tafiya walima,Spark ya dinga dariya yace ai Kai ka fi Angon ma,idan iskancin Nan kake sha'awa kayi mana kaima,wannan masifar son mata haka Kuma kace Kai kar wacce ta soka,Rafeeq yace ai ni Yaya nafi so na kallesu daga nesa sunfi birgeni,3pm mutane suka cika a Inda aka kama za ayi wa'azi,Misam maye sai da yazo,Rafeeq ya ganshi yace Misam kana birgeni Kai kawai mata kaji dadinka,baka da control ba komai,zanci uwarka wlh sa'anka ne ni,kaima idan kana so ka fara mana sai son mata a baki da Ido, Malama ce ta shugo.
Bata fi Naila ba Yar kyakyawa da ita me Dan haske amma ba can ba,ta Sha hijab har kasa,idonta tar a kan kowa,Spark baki ya tabe yace wannan ce zata min wa'azi naji Allah bazan batawa kaina time ba ya mike ya fice, dake a ciki bangaren mata daban na Maza ma daban.
Matan su Naila duk an Sha Abaya,Maza yawanci da jallabiya,Amarya da Ango ana zaune a high table anyi shigar larabawa ta Amarya da Ango.
Malama Speaker ta dauka suka hada Ido da Misam ya kashe mata Ido daya tayi sauri ta dauke kanta dama shi da Rafeeq duk suna gaba gaba,Kuskure Malama ta sake yi na kallon Misam ya daga mata gira tare da kashe mata Ido,ya radawa Rafeeq na samu Daya yanzu Malama,Rafeeq yace cikin rada ga Chikar Gayu nan ta shugo,Misam ya basar sai bayan Dan seconds ya kalleta,Chika ta kalle shi suka hada Ido gwalo ta Masa ta zaro harshe,dariya yayi ya sake kallonta ta turo kirji gaba tayi girgiza kadan,dariya yayi a boye yace ta sake yi wai,kanta ta dauke,yace Ina Amaryar Yaya Spark ne? ,Rafeeq yace gata can mana ai wannan tafi karfin kanka sai dai Spark na sallama mata,gata can a gaba Inda Chika take.
Malama ce tayi gyaran Murya tare da sallama,sannan ta bude da adduoi,Misam Allahu Akbar ya furta sai da kowa yaji,Malama Ikhram ta gaji da iskanci su Misam magana daya tayi sai sunyi Kabbara,sun gama Raina mata hankali,Misam tayiwa magana siiiiii....siiiiii...hey ..hey....siiiiii,dagowa yayi daga danna wayar da yake suka hada Ido, fito tayi Masa ta nuna kofa da bakinta wai ya fita,Malama da fito,ko kulata baiyi ba yaci gaba da danna wayarsa,Mohsin ya radawa Amarya su Spark duk gasu da Kamala kyawawan gaske gasu da aji sai iskanci fal ciki,Beauty tace naga alama kuma kamar basu suke yi ba,sai su Fadi Abu su fuske,su Rafeeq basa saurarar Malama waya suke dannawa amma ko ya tayi magana sai sunyi Kabbara Allahu Akbar.
Malama tana Jan Aya da hadisi tana wa'azinta sosai da sosai,ta Fadi mene ma auren gaba daya,da sharudan Dake ciki,sannan ta dawo kan yanda ake zaman Aure,ake tattalin me gida da kula da shi,tazo tana koyawa Amarya yanda ake tarairayar miji dama duk irin malaman Nan fitsara sukeyi su fake da wa'azi,da Allah Amarya ayi dinkunan zaman Palo Banda zuwa a dinga manne jiki a gidan miji,ki dinga saukaka Masa yanda zai cire su cikin sauki,Rafeeq kasa kasa yace wannan fadakarwa ce me kyau dole na dakko malamar Nan har Abuja ta koyawa su Mima rayuwa,akan kula da yara da musu tarbiyya,Misam yace maulidi zamu ce zamu hada sai mu dakkota.
Chikar gayu tace wannan gaskiya ne ke Beauty kinji dai a saki a Palo su Sha iska,Malama tace ashe Kuna ganewa Alhmdllh Alhmdllh,ba ruwanki da kishiya kiyi ta kanki Amarya,me gida idan ya dawo yasha aiki ya gaji ya kamata ki tayashi cire kaya,idan ya hada zufa ki tanaji handkerchief dinki me kamshi ki goge masa gumi,sannan ki tarbe shi da ruwa me Sanyi,ko wani dan zobo haka me Sanyi,Maza suna son girmamawa,karki zo ki wani tsaya Masa kerere kamar namiji,da karairaya da kissa cike da girmamawa zaki bashi zobonki me Sanyi,idan ta kama ma ki bashi a baki,Maza suna son kulawa,Rafeeq yace haka muke Malama musamman ni,Malama ta Harare shi.
Tace shimfidar aure Amarya, Chikar gayu tace a tafawa Malama anzo Inda muke jira a bata darasi,Naila tace bari na bude kunne Malama nima Amarya ce anzo Inda muka fi wayo,yeeeee suka saki shewa mata.
Kamal yace ni dai wajen Nan Ina da mutuncina bazan iya zama ba ya tashi ya fice,Misam yace mu mun zubar da namu wlh sai naji komai,Maza matasa duk sun zuba kunne,wani har cewa yake Malama mu ba a zo kan Maza ba,tace zanzo ne ku saurareni.
Sanda ta fara bayanin kwanciyar aure Mohsin kunya ce ta lullube shi,Rafeeq yace ni dai na kamu da son Malama ta San harkar irinta nake so,Misam yace idan ka aureta zaka Sha dadi ko Mai ta iya,yace musamman idan aka fada bedroom.
Naila kuwa cewa take an gode Malama Allah ya biya da Aljanna Munji mun dauka zamu yi,Rafeeq yace Kai nima na tashi daga wajen Nan kar a rainani Chikar gayu sai raini take kawo min,Misam yace dani za a kare sai an rufe addua da Dani,Rafeeq ma ya tashi ya fece,Maza duk masu Yar kunya arcewa suka yi,Mohsin ya gaji shima badan dole ba Ina zai zauna sai dai su Tantiriya irin wajen sune,da kyar ya daure aka gama wa'azin Nan,Misam ana shafa addua yace har an gama gaskiya anyi sauri,Malama ta gasa Masa harara.
Suna fitowa aka Maida Amarya gidan Ubanta dangi aka mata nasiha sosai Daddy ma sai da yayi nasiha sosai,yace wlh idan naji watarana ko da wasa kin Masa gori na bashi gida da jari ko wani Abu ko kika yiwa kishiya gori wallahi Beauty sai Kinga fushina,na fada miki banza son gori a rayuwa,kayiwa mutum Abu tsakani da Allah mace tazo tana yiwa miji gori shi yasa Maza basa son zama a gidan mace ko gidan Baban mace,badan ke na bashi wani Abu ba,karki sake naji gori ko kiyuwa kishiya gori,Beauty tace to ko kuka itama sabo da sun Saba da gidan yari akan aure Kuma wanne kuka zasu yi,yayi mata fada Sosai sannan ya sata a mota da kansa,ga Yan uwa da kawaye,Naila har da ita a Yan Kai amarya suna gefe suna yiwa Amarya rada,Beauty tace karku damu fa ni kishiya Bata gabana,bana tsoron kishiya, gidan ta tarar sai na bata littafina dictionary na duk wani iskanci sai ta haddace shi tsaf.
Hanan Kuma daga ita sai Yan uwanta a Palo suna zaune suna jiran Amarya,Hanan tace a yau ana watsawa zan mata dukan tsiya wallahi,yau sai na daki banza,Kuma ba uwar da zai iya yi min,ai nasan lagonsa ko me nayi Ina bude Masa Nono sai Kiga yayi mukus,sabo da haka yau ma haka zanyi baza kuji komai ba,shi da nono ai Inda kisan asiri.
Dariya suka yi da shewa,suna habaici habaice tun kafin Amarya tazo.
Naila suna mota tace babu fa wata Amana da zamu bawa Hanan,kawai a wuce da ita part dinta,Chika tace Amanar Beauty ita ta isa ma mu Bata Amana har wani a fara Kai mata Amarya ita din banza,Beauty tace muna