Showing 51001 words to 54000 words out of 158722 words
Chapter 18 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
kifinki ki zare Masa kaya,karki dugurguza shi a haka a hankali zaki zare kayar,
Gefe Kuma ga shinkafarki a tukunya Saman wuta tana chaf chaf chaf ta dakko dahuwa sai ki bude ki zuba kifin ki juya a hankali ki rufe ki barta turiri kawai ya wadatar idan kika sauke kika fara tsallake haba ai Kuma shike nan.
Batoola ta dinga dariya Abba yace ki gwada ki gani Ina dafawa matata idan shagwabarta ta motsa, kin san Kubra akwai Mulki bani da kamar Kubra duk duniya uwar yayana ba,duk wacce na aura sai ta yiwa Kubra biyayya zata zauna lafiya,Isa ya sake zungurar Hashimu akan yayi shuru amma Hashimu sai surutu an samu budurwa,Malam Isa sai cewa yayi su tashi su tafi suka mata sallama suka wuce,Batoola tace yo ai ni dama Wanda zan juya nake nema wannan sullutu ne sai dai Uwar gidansa Yana sonta da yawa dole na shiga da shirina wlh dole na kwace shi,Batoola bata San Umma da Mohsin ke yin komai a gidan ba, Abba baya tsinana komai amma har taci alwashinta.
Washe gari Umma da Abba suka ji Mohsin ya saki matarsa,Umma murna tayi amma Abba ba Wanda ya sani yaje da kansa gidan su Hanan ya dawo da ita gidan Mohsin,Mohsin Yana Shan shayi a Palo shi da Amal sai ganin Hanan yayi tare da Abba,yace Abba mene ne haka Dan Allah,gidanku Mohsin rufe min baki,na dawo da ita wlh tun wuri ka maidata dakinta idan ba haka ba zamu samu matsala da Kai kaji na fada Maka,komai ai hakuri akeyi,mu da ace bama hakuri zan zauna da uwarku ne,Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ya Maida Hanan sannan ya tafi,Hanan da Mohsin daga Nan Kuma suka dora gaba ba Wanda ke kula wani sai da dalili.
Bayan kwanaki Aikin da Spark ya kawo gidan yari ya kankama sosai ana ta aiki ba tsayawa,sannan kullum sai an zabi masu kananan laifi ya biya kudi an fitar da su,Jamilu ya buwayi kowa akan abokinsa ne ai yake aikin ruwa sai yaga dama zai saki wa mutane ruwan,cikin kankanin lokaci aka kusa gama ayyukan cikin Yan satikai, sai yabawa Spark akeyi,bangaren mata ma masu kananan laifi yasa aka fitar ciki harda Chikar Gayu domin rabonta ne ya rantse shekaru sunfi goma aka yanke mata amma aka zabo da ita,Chikar gayu sai kuka take tana murna Kuma tace wannan Spark din da ya fitar dani Allah ya biya shi da Aljanna,tabi kowa daki daki tana basu hakuri a yafe mata abinda tayiwa mutane,karshe wajen Beauty taje suna ta kuka suna Murna Beauty tace idan na fito Chikar gayu har gidanku zanzo,Chikar gayu tace shike nan yau za a girgiza kirji babu ni a Islamiyya,Dan Allah Beauty ki hada da nawa kiyi,Beauty tace Inshaallah chikar gayu duk abinda akeyi zan dinga hadawa da nawa da naki Ina yi, iskancina zan rubanya ya koma ninki biyu harda naki,Chikar gayu tace na gode zamu dinga waya ai daku dukkan ku,Sannan Dan Allah yau idan na tafi inji labari me dadi Ina so naji cewar lallai duwaiwai sunyi Injury,Beauty tace kamar da kasa yau zan cika alkawari,Chikar gayu tace duk gidan Nan Dake na yarda nasan ba karamar Tantiriya bac.
,Beauty tace haka nake nice nan yo ai mu duk wani iskanci a jininmu yake,a gidan Nan fa muka goge,Chikar gayu tace wayyo Wanda basa gidan yari sun shiga uku Gani nan na fito yau za a kwanto kura,Ina zuwa unguwar mu Me unguwar layinmu zan samu na shararawa Mari,Beauty tace harda sa hannunsa a shugowarki Nan karki ragawa uwar da ta haife shi ma,Chika tace harda kakarsa, ahaf a gidan yari fa na balaga,anan na fara irgen dangi,na fara period, Beauty ta mika mata hannu suka tafa sannan ta tambayi Chikar gayu tace wai Chikar Gayu da zaki fara Irgen dangin naki da wa kika fara irgawa? Chikar gayu tace shegen kaya kanin Babana da shi na fara nace Saminu number one sai na bangare daya ya fito bul,na zaci kurji ne yasin,suka saki shewa,tace na biyu sai me mitsitsi Ido kanwar babata Hasiya baturiya Ina irgata nace Hasiya sai Wanda ya fito sai ya koma,Hasiya ba sa'a amma Ina irga Kakata Dake ta Sha Madara ta gaji sai suka fito duka karo na biyu amma daya yafi Daya,nace baza ta sabu ba,na sake irgo kakana na wajen uba tsohon ance akwai kyauta duk da ya mutu abinka da jininsa sai ga dayan ya daidaita,daga Nan Kuma na fara irga kannena da sauran su Mariya,Zainab,furdausi, Mubarak, Ismail har dai suka wuce irgen dangi,yanzu Kuma Saurayi suke ta kira nace Dan ubanku miji dai, dariya duka matan keyi suna da mugun yawa matasa Yan mata.
Rayuwa babu ke Chikar gayu Lami ce,ai Inshaallah duk zaku fito Ina Nan zamuna waya yau a gadon bayan uwata zan kwana,Ma'aikaciyar ce tazo tace Chikar Gayu to fito an tattaro wasu duk masu kana nan laifi,Chikar gayu tace Banga Azima me kwana ba wando ba Dan Allah idan tazo duk da munyi sallama ku fada mata yau ta kwanta ba wando har da nawa ta hada ta kwanta, Sukace zata ji,Beauty sai kuka take tana tausayawa kansu su har yanzu ba labari,Hajiya Kaltume ta rako Chikar gayu tana murna domin itama ta kusa fita bata damu ba,Beauty sun rako su Chikar gayu har iya Inda suke da iyakar zuwa,Chikar gayu tana zuwa bakin kofa ta kwaso shoki tace sai na dawo naga waye Spark din nan na Masa godiya,bani da gata an daureni a laifin da ba nawa ba, Allah ya zama gatana na, shekaruna hudu a gidan yari, tana fitowa waje wajen masu aiki ta daga hannaye sama tace Alhmdllh na shaki iskar yanci.
Aka basu takardu suka yi signing sannan sauran duk suka fito suna Murna suna sauri Yan uwansu suna jiransu a bakin gate za a dauke su,amma Chikar Gayu ba Wanda ta fadawa wai mamaki zata bayar, ta ratso cikin ma'aikatan tana kwambo tana wani bubbudawa sai kace Soja tana gadara tace ko za a Maida ni ne eiyeee? ba wani shege da ya isa Allah ya fitar dani waye ya isa, E choke you? Ta tambayi wani Ma'aikaci yace akan me? tace ba Wanda ya isa,sai data tsaya ta kwaso shoki yafi a irga ta cashe ba kida tayi kida da baki ta taka rawa sosai tayi fitsararta suna kallonta,duk wani Dan iska suna kallonsa basa kula mutum,Rafeeq ne yayi parking da mota ya fito yazo wajen Spark tun a mota yaga an fitar da wasu Chikar gayu ta taho zata fice waje,da Gandroba a bayanta zaiyi waje da ita amma tana wani mamar mamar da duwawu a haka take tafiya,shi Kuma Rafeeq a motar kida yake ji me duka yace ah yarinya Kya yi rawa wannan masifar gida ka fito ai kayi abinda yafi rawa sai ya karo mata vol ya bude motar ya fito, Chikar gayu ta gama iskancinta ta Kalli Rafeeq ta Harare shi tace Kai dalla matsa da motarka zan wuce hanya tayi min kadan yau,tazo gaban masu gadi tace a bude min gate wajen shigowar mota,hanya yau ta min kadan,sun Sha kunu tace ko za a Maida ni ne? tabi ta kofar da mutane ke wucewa tace to nace tayi min kadan na kasa wucewa, basu kulata,sai da ta gama iya shegenta ta fice,tana fitowa tace wai wai ta Ina zan gane hanyar gidanmu ma haka ta shiga napep tace Me Napep fara zaga Kano Dani kafin ka kaini tasha na shiga motar Kaduna garin Gomna gidan ubana,yace a zaga Kano? tace da uwar kudina Kai karka min akuya.
Spark ne ya fito Rafeeq yace yanzu naga wata Yar iskar yarinya Yaya an saketa wannan Yar ta gama kangarewa kaga yanda take girgiza tab,Spark yayi dariya yace nima Jamilu Yana ciki ya buwayeni,kasan matsalar namiji ne wlh sonshi nake? Rafeeq ya bude baki,Spark yace hmm bala'in ma da nake gudu idan yazo ko Hira muke yi sai na mike kamar me, Kuma Karin bayani idan banganshi ba bana iya bacci,Rafeeq yace again dai? yace baza ka gane ba Kuma idan ya rike hannuna dadi nake ji,Kai komai yayi birgeni yake wallahi, idan na ganshi da wani sai kishi kamar zan mutu sabo da kishi,Kai ko 'ya mace ban taba sonta haka ba a rayuwa,gashi kullum so nake na kaurace Masa ko zan samu sauki amma bazan iya ba akansa zan iya batawa da kowa,Kuma bana gudun abin kunya,Rafeeq yace Ina girman naka yaya? Kai da kake respecting kanka? Jamilu ya ruguza komai,Kai In Kai Maka karshen zanci sai abinda jamilu yace shi nake yi yanzu,idan yace yi kaza haka zanyi, Yaya Ina masifar taka? Ta gudu babu girman Kai babu duk Jamilu ya sauke min shi, Kai ni yanzu ma na sake fahimtar rayuwa na nutsu,yanzu idan na fito kowa zaiga na nutsu masifar da take afka min tayi yawa.
Yanzu Rafeeq yayanka zai zama Dandaudu me son namiji Dan uwansa Ina tsoro kar na mutu a kaini yankin annabi Lut, Rafeeq yace Allah ya tsare inshaallah zamuyi ta addua Allah ya rabaka da Jamilu, Jamilu ya zama annoba,Spark yace ku samu malamai ku basu sadaka a tayani da addua Jamilu nake so namiji,da zai aure ni murna zanyi,yanda zan biya Sadakinsa ko mace Bata isa takai Jamilu tsada ba a wajena,Rafeeq abin yafi karfinsa ya bude baki,yace Yaya ka daina fadar haka yace gani kuke wasa nake abin Nan wlh bro bana wasa bane da gaske nake son Jamilu Kuma tsakani da Allah amma Jamilu Sam yaki ya yarda Dani Ina sonsa Idan yazo ma na fada Masa sai ya dinga dariya wai wasa ne.
Rafeeq yace abin Nan sai an dage da addua fa, Spark yace shine mafita,wata hirar suka shiga sun gama ya karbi sakonsa ya koma ciki Rafeeq ya tafi.
Spark Yana komawa ciki ya fara dingishin karya yana furta wash,da Jamilu suka hadu zata tafi kallon ball a filin wasa,tana ganin Spark taji wani Sanyi a ranta ta karaso Inda yake tace me ya sameka? Yace daga asibiti nake kafata ce take ciwo Likita yace naje ayi mata ruwan zafi sannan a mata tausa,Jamilu ya rude yace muje bari na karbo ruwan zafi,Spark yaji dadi yace Ina jira kazo ka tafi dani,Naila ta fyalla da gudu taje ta karbo ruwan zafi a cup tazo ta rike hannun Spark tace muje sannu,Yana dingisawa tana cewa sannu, suna zuwa Palo ta zaunar da shi a Palo Saman kujera tasa karamin towel dinsa a ruwan zafin sannan ta zauna a kasa sosai taja kafar tare da dorata a cinyarta, ta Dan dage kafar wandon,farar kafarsa tana shining ta bayyana,tace Nan? Yana wani numfarfashi yace ae nan wash zafi,wayyo zafi,Naila ta Kalli fuskarsa yanda yake yatsina tace Dan Allah kayi shuru haka haba sai kace ka samu Badon mace kana ta wani ihu wai Kai ajebo, dariya ya boye ba shiri, tace Allah ai Kaine ka bari ka adana ihunka sai kayi amarya sai kayi abinka ko Mimanka da Daddynku bazai hanaka ba,Spark yace Allah? Naila tace ai birgesu ma zakayi suce ashe dansu gwarzo ne, yace to Allah ya kaimu tace Ameen.
Dama baiso ya tafi yawo yafi so suyi ta zama tare, haka ta Kai har dare a wajensa tana faman jinya ya hana Jamilu sukuni da wayyo wayyo kafa,dare yayi yace bazai tafi ba,Naila Allah yasa tana period Bata sallah period dinta na biyu kenan a gidan yari, zai kwanta ya damu Jamilu muje mu kwanta,Jamilu Ido ya raina fata,yace Ni zan kwana a Palo, Spark yace dalla bro wai mene haka muna abokai me zai faru ne wai, Naila tana gudu kar ya ganeta haka ta bishi bedroom, ya kwanta a gefe daya,Naila sai zare Ido take yi tana faman zaga gadon tana Jin tsoro tana addua a ranta tace Allah ka kawo min mafita kwanciya da namiji a gado daya babu aure taya zan iya,ta dinga zaga gadon,Spark tashi yayi ya sawa kofar key,Naila kamar zata yi kuka,yace nifa nafi son wajen su Malam Jilani yau Ina da daukan karatu, yace Jamilu wai mene haka sai kace mace wai,Naila da sauri tace ka daina ce min mace tam ta lallaba ta hau can gefe karshen gadon tana furta wayyooo a hankali yanda bazai ji ba, ta kwanta dai tayi shuru tana karanta wasikar Jaki,Shima Spark Yana kwance ya wani baje daga shi sai gajeren wando,Naila kasa kallonsa tayi da kyar take iya hadiyar yawu,yawun bakinta ma ya kafe,Spark Yana kallon Jamilu duk abinda yake yi, ranar Naila kasa bacci tayi,idan Spark ya farka zai lalubeta yaji sai yaga idonta a bude tarrr sai ya koma ya kwanta,
Sai 3am yayi tunanin tayi bacci ya tashi a hankali zai duba ya taba yaji sai Muryar Jamilu yaji yace kaima ka kasa baccin ne? Da sauri ya koma ya kwanta Yana Jin haushi yaki bacci,ranar a haka suka kwana ba Wanda ya runtsa.
Washe gari ta riga shi tashi baccinsa yayi lokacin ita Kuma ta gyara ko Ina fes ta siyo musu tea ta gama kawo komai,ya fito shirye yayi wankansa cikin jallabiya fara me tsada, Naila taga wani kiba yake karawa da kyau sabo da baya fita ko Ina, tace mu karya nima wanka zanyi ka Ara min kayanka na saka wai duk Dan ta fitar da shi daga zargin da yake mata,yace to da sauri wai irin zai kalli jikin Jamilu, tunaninsa jikinta zai nuna a kayansa,sai lokacin tace Good morning,yace whats Good about the morning? Yaja tea dinsa suna Sha,tace ya naga kafa har ta warke? Ya manta ma jiya yace kafa na ciwo,yace Ina tashi naji ta warke.
Sai da suka karya sannan Naila ta shiga toilet dinsa yau ma bata wanke wajen boobs dinta ba ta bar mannewar da tayi bayan ta gama ta shirya ta fito da kayan jikinta,yace kace na ara Maka kaya? Jamilu yace barshi kawai na fasa, Spark tun Yana so ya gane ma har ya gaji ya hakura.
Maman su Asmau ce ta zauna tare da yarta kanwar Asmau a daki suna kuskus tace Kinga wallahi ki rabu da zancen Spark din Nan idan ba so kike Daddy dinku ya gano Ina da sa hannu a kashe Asmau ba,Kinga ki rufa min asiri,nayi zaton Yar uwata ce zata ce a bawa Spark ya aura sai kawai tace Asmau sabo da Asmau tafi ki nunawa a fili tana son Spark,Yar kishiya ce fa Asmau, hauka nake na yarda wata banza can ta auri Spark yaro me kudi da arziki gaki Yar da na Haifa Dan uwanki wata banza can sabo da na riketa a dinga cewa ta zama kamar Yar uwa,wlh karki sake a gane, kin san million biyu na bayar aka kashe Asmau,Kanwar Asmau tace ni wlh Ina son Spark idan ba a fito da shi na aureshi ba nima mutuwa zanyi,ni Ina ruwana ni nace kisa a kashe Asmau ai gwara kiyi kokari ma a hana auren amma kisa aka kashe ta ni Ina ruwana kawai ki San yanda za ayi a fito da Spark na aure shi duk duniya Nafi kowa son Spark ato idan ba haka ba na tona miki asiri.
Daddyn su Asmau ne ya fado dakin yace ba sai kin tona mata asiri ba naji da kunne na,amma ku dai jininku kunyi asara,Kuma ba Yan arziki bane ku,uwarku tayi asarar haihuwa, Nan take hawaye ya zubo Masa yace Kun sa na kama yaro, na bata Masa suna ba hakkinsa,to ki sani zan fito da shi Nan da 3days ke Kuma zaki koma prison,ya durkushe a kasa Yana kuka Wiwi Yana furta wannan wacce irin masifa ce wannan,wannan mene haka,Mama sai diririce ta fara cewa tsaya Kaji yanda akayi,ka bari kaji mana,Nan take ya kira Yan sanda suka tafi da Mama ya fada musu komai Wanda sune suka kama Spark,yace a hada da kanwar Asmau a tafi da ita a Kai case din kotu zasu fi bayani da kyau,ya dauki waya ya kira dukkan manyan Spark yace gaskiya ta bayyana amma suje kotu zasu ga ko waye ya kashe Asmau,ba Wanda yasan waye ana dai ta jiran ranar zuwa kotu domin a ga waye yayi hakan.
Jamilu yau ya fito Yana kallon ball,wani ne ya bugo ball sosai tazo ta daki cikin Jamilu,Nan take ya Fadi kasa a sume hancinsa Yana jini,aka yi kan Jamilu babu bata lokaci Goje Yana wajen ya dauki Jamilu yaji ba nauyi shafal Yana mamaki ya wuce da shi asibiti,Spark bai sani ba sai Goje ne yace budurwarka fa ya sume yana asibiti,ko gama ji baiyi ba ya nufin asibitin,ya samu Likita Yana kan Jamilu Yana cewa yaki farfadowa Ina ta kokarin dai,Spark yazo kan Jamilu, Doctor yace bari naje Office na dakko kayan gwaji zan kirawo wasu doctors din, yi kokari ka cire Masa riga yafi Shan iska,Jamilu Yana sume bai sani ba,Spark ya cire uban rigar daya jibga, sai wata t-shirt a ciki itama ya daga zai cire sai yaga vest ta mata,da sauri ya janye rigar sama gaba daya sai yaga nonuwa an damesu da seletape da bandage,da sauri ya mayar ya rufe rigar,ya kama wandon Jamilu jean ya zuge zip din ya Buda yaga pant da pad alamar period take,ya sake jawo pad din yace har Jinin sai na tabbatar ya kalla,ya Kalli gaban Naila,yace Alhmdllh gashi nan kuwa,bari na Kalli kadan sai yayi sauri ya gyara mata komai ya zuge ya gyara komai Yana uwar murna yace wallahi wallahi na fada wannan mace ne, karya ne ace namiji ne haka,farin ciki ya isheshi ya sake kallon Naila,a hankali ya duka ya Dora bakinsa a Saman nata yayi kissing dinta,hayyacinta ta dawo a lokacin ta bude Ido Taga Spark bakinsa cikin nata Ido ta zaro ta hankade shi, yace sorry Jamilu kaki farfadowa ne shine nayi Maka na baki ko zaka