Showing 57001 words to 60000 words out of 158722 words

Chapter 20 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

709

ne? Suka ce ae baka ga ana ta yanka shanu ba a gidan nan zamu ci dadi, kazo kaima a baka sura ka karanta,Jamilu yace idan dai Yan Mandiri sunzo masu kida zan shiga na chashe sabo da haka ba wani gardi da zaiji Muryata ni Jamilu Tantiriya,Malam Sharu yace Allah ya shiryeka Kai sai dai sai abin shagala ka iya,Jamilu yace sosai ma kuwa ranar akwai dukan kirji inyi rawa itace zata kaini,Malam Jilani ya furta Allah ya shiryeka ka daina harkar Daudu kana bin Maza Yan uwanka, kaima idan kana so mu dan samu waje mu kebe malam,Malam Sharu yace ai gwara mu mutu,Dariya Jamilu yayi harda shewa irin ta Yan Daudu.

Ranar maulidi tun yamma aka fara Maulidi a gidan, Naila bata je ba amma ana saka Mandiri ta tafi wajen,Maza an samu rana sai shagali akeyi suna ta tikar rawa,wurin Spark ta koma yaji sauki suka je asibiti aka bashi magunguna bayan an tabbatar malaria ce, bai fi kwana uku ba ya warke,lokacin Beauty ma ana shirin barin gidan yari domin Daddy dinta ya shiga ya fita shekarar ta biyar a gidan yari, sai yanzu Allah yayi,shi yasa take ta neman Jamilunta ta fada Masa,amma bata same shi ba sai yau,Jamilu Yana daga wayar yace tuba nake gimbiya sarautar mata,kaina bisa wuya,Spark Yana zaune Yana jinta kawai shi bai so yaji Naila da wani ko wata, fushi ya fara ya kwanta kawai Yana jinsu Beauty tace Allah fa yayi nima nan da kwana uku zan fita an gama komai,Jamilu ya furta wow,tace murna nakeyi zanzo Maka ziyara na ganka,Naila tace na miki murna Baby Allah ya samu a danshinku, Beauty tace Ameen .

Naila a ranta tace ni yaushe zan fita ne? Kawai sai hankalinta ya tashi, Spark kuma ana ta kiransa a waya a fada masa labari me dadi yaki dagawa gashi har an fara zama a kotu,Mama zama daya ganin asirinta ya tonu kawai ta Fadi gaskiya bata Musa ba,Yan uwanta da suke uwa daya uba daya da Kuma Wanda ma uba suka hada suna ta jimami har kuka suke ta faman yi,ba kamar Mima da Mummy,Mummy harda refefe baki tace kinyi asara Kaltume,me ke damun mu ne? Mu yanzu mata sabo da son zuciya mune zaluntar yaran kishiya,shi yaro ma me yayi Maka,yaro Amana ne, uwarsa bata gida ko ta mutu sai mata su zauna sabo da son Kai su dinga zaluntar yaran kishiya,wasu su nakasa yaro ko yarinya,wasu Kuma suyi ta gana musu azaba wannan zalunci ne Kuma Allah bazai bar mutum ba,wasu har da kisan Kai a kashe Dan kishiya,kishi hauka ne,kishiyar ma da ta mutu amma baza a hakura ba sai kishin ya koma kan yaranta,yanzu mene ribarki Kaltume dan kin kashe Yar kishiya sabo da ta auri Spark wato yarki kike so ya aura sabo da yana da kudi,tirr da hali irin naki Kaltume,ganin ke kika raineta har ta girma na zaci ta zama Yar uwa,na zaci mun zama daya da Asmau,yarinya tana mutuntamu,Kai Kaltume kuma kin yarda Dan Yar uwarki uwa daya uba daya yayi life in prison,to Allah ya Toni asirinki,Mummy ana ta kallonta a mutuniyar arziki ana cewa gaskiya ne,su kuwa sauran magana ma ta gagara.

Kotu zaman ta dage zuwa sati biyu sannan ta nemi a kawo mata Spark tare da ci gaba da tsare Mama, Mummy harda cewa alkali sati biyu yayi yawa Dan Allah a fito min da Dana dama na gama takaba ni Kam Alhmdllh,alkali ya kalleta yace to da kika gama takabar aurensa zaki yi kema? Dana ne fa yanlabai,yace ai naji kince kin gama takaba a fito miki da shi,zata yi magana alkali ya dakatar da Mummy da ta damu kowa a ciki da surutu.

Abba bayan ya dawo daga zance komai sai da ya kwashe ya fadawa Umma amma yaki fada mata zai mata anko,Yana runfar kayan miyansa Mohsin yazo wajen,bayan ya gaisar da Abba,Abba yace yau ba aiki ne? Yace ae,to madalla dama Batoola ce za ayi mata anko suna da biki ka kawo dubu goma a Kai mata ko kakai mata da kanka,Mohsin yace Abba kasan wata yayi nisa sannan kasuwar ma Bata tafiya yanzu ga me gidan nawa yayi tafiya,Kuma ma daga zuwa sai ace za ayi mata anko har na dubu goma,zagina zaka yi Mohsin? yace haba Abba ni na isa,to kaje ko rance ka samo ka kai mata kaji na fada Maka, Mohsin ba yanda ya iya yace ni na jawa kaina dana hada shi da Fatima.

Naila ce ta kira Mohsin lokacin daya shiga gidan wajen Umma, Mohsin yace na manta ban fada miki ba Abba fa zai kara aure sis,Naila tace na shiga uku kishiya zai wa Umma? Kuma kuka yarda? ya za ayi da shi shi yasa muka yanke hukunci cewar a samo me hankali a aura Masa kar ya kwaso mana jaraba,Naila tace Ina wani me hankali a kishiya,yanzu ma zuwan farko har tace ayi mata anko na dubu goma Kuma yace ni zan biya gashi ni yanzu ma dubu daya ma bani da ita cewar Mohsin,abincin gidana ya kare na su Umman ma ya kare,Naila tace ku rike auren Nan Sweetheart sai Allah yayi na fito ni nasan tuggun da zan hadawa Batoola da kanta ta fasa,sabo da Allah dame zamu ji ana fama da shi da gida, zai Kuma karo mana wani masifar salon tana zuwa ta haifo wasu yaran,Kai Yaya me yasa zaka yiwa Umma haka,duk da tana yiwa Abba masifa amma ai tana kokari tun Kuna yara itace cinku da shanku ta Sha wahala kullum a teaching Dan a rufawa Kai asiri amma kuce yayi wani aure da me za aji, magana ta Allah a nan baka yi tunani ba,ni bana goyon baya wlh kuma ko an aurota na dawo sai ta bar gidan nan kaji na rantse.

Mohsin yace gashi yanzu ashe kaina na nemowa aure ban sani ba,Naila tace yanzu baka da Sisi Yaya? Yace ae sai kayan kyau da wanka? dariya yayi tace Allah gwara ayoka mummuna a baka kudi,turo accnt number Yaya kaga kudin Daddy din Beauty ya bani ban kashe ba Kuma na samu wasu a wajen Spark Yana yawan bani kudi,ko bai bani bama sai nace ya bani rabona,yanzu sai da na Tara 50k,Banda kudin da su Dan Indo ke bani duk Tarawa nake yi,yace ke da zan kawo miki ni zaki bawa kina gidan yari,Naila tace Malam ka karba, ni I can survive macece ana so na a gidan Ina samu ba laifi,mene amfaninsu idan ban baka ba,Mohsin yace to Naila ai naji kunya,idan zaka karba ka karba ni da Kai akwai kunya ne Hallare ma ta kama ganin taka zanyi tsaf,zanci ubanki Naila tam,dariya tayi tace ka turo accnt karka bata min lokaci,ba a dade ba ya turo accnt,a cikin gidan yari suna da komai nasu sai taje Wajen masu POS ta tura Masa 50k din cass sannan ta koma dakinsu na malamai.

Spark yayi baki su Kamal sunzo suna fada Masa labari me dadi,yayi farin ciki matuka sai dai Kuma mummunan labarin Mummy suna fada Masa ta bude cin duniya da tsinke har kana nan kaya take sawa ta tsuke kamar Yar arna ta fice,itace gidan Shan shisha da Kuma yawo da kawayen banza suna cinye mata kudi,kullum suna gidanta sun tare,gefe daya Kuma tunanin Jamilu yake ta ya zai bar gidan ya barta,yace ai ko an yanke hukunci ni ba yanzu zan fito ba,Banga ta tafiya yanzu ba,su Kamal suka bude baki,yace ae ni yanzu banyi niyyar fita ba yanzu dadin gidan nake ji nafi nishadi a nan,Su Kamal haka suka koma gida da mummunan labarin cewar Spark yace Bai shirya barin gidan yari ba shi yafi son can,an Kuma rasa dalili sai Rafeeq ne ya tuna yace ai wlh a uzura Masa ya bar gidan ana yanke hukunci sabo da namiji yake so,kowa bai gane ba Daddy yace kamar ya? Rafeeq yace Gay yake so ya fara wlh wani Dandaudu yake kauna,yace ma shi zai aura,Mima zumbur ta mike tare da furta Yana hauka ne wlh dole sai ya bar gidan nan ana yanke hukunci,Kun san dai halinsa baya Jin magana ku San yanda zakuyi wlh ya bar gidan.

Chikar Gayu sai da aka dan yawata da ita taga gari,tace to kaini tasha aka kaita tashar mota,motar Kaduna ta shiga har ta shiga ciki tace na fasa katsina zanje yes Katsina zani na fara zuwa wajen Uwata tukun na dawo naje Kaduna din gwara na fara cin uban me unguwar layinmu sannan naje gidan Ubana,fitowa tayi ta canja tasha ta hau motar Katsina suka ware birnin katsina, bayan awanni ta sauka a motar ta biya me napep yayi parking a kofar gidan me unguwar Layin,taci sa'a a waje ta ganshi,a gabansa ta tsaya,ya zaci fatalwa ce ya ja da baya Yana salati harda faduwa a kasa Yana Nuna Chikar Gayu da hannu, Chikar gayu tace nice ba Aljana bace Dan gyatumin ubanka,ai dama nace zan fito sharrin daka kulla min to na fito,Mikewa tsaye yayi yace karya kike gudowa kika yi Kuma sai na sake kiran police sun Maida ke,shegiya Yar iska haihuwar kwararo.

Ubanka aka Haifa a kwaroro cewar chika,me unguwa ya jawo sandarsa wai zai kwalawa Chikar gayu ya zaci a baya ne sanda tana karama, Chikar gayu taci kwalarsa dama gashi wani Dan figigi ta yanka Masa Mari,Mutane suka taru a wajen ana labari Chikar gayu ta dawo, Me unguwa ya dafe kumatunsa yace ni kika mara? tana rike da kwalar me unguwan ta lakace Masa hanci tace an mareka,baka ga na girma ba to na balaga dattijon banza, ta zaro Masa idanu tare da furta balaga ce ta jawo, na rika na tatira na tumbatsa, tayi fatali da rawaninsa ta shake shi sosai,mutane suka taho suna cewa dan Allah Chikar gayu sake shi kina mace a unguwar Nan kowa yasan ke saliha ce,Chikar gayu tace duk Wanda ya rabamu Allah ya isa,kar Wanda ya sake ya rabamu wlh duk Wanda ya rabamu iyalansa ma sun shiga uku,mutane suna ta mamaki, wani a ciki yace Chikar gayu da a baya ko yatsa aka sa mata baza ta iya cizawa ba ita dai barta da gayu.

Chikar Gayu tace to yanzu gartsa yatsan zanyi,mutum ya sa min yatsan a baki ya Gani idan ban gartsa Masa cizo ba kafira nake, koma na fille yatsan,Kuma wallahi fada bai mutu ba bari naje na huta zanzo har gida sai na hanaka Shan ruwa a layin Nan,bari naje naga dangi zan dawo a Yar dabata zanzo,Me Unguwa yace sai na daure ki,ta hankada shi tana haki tayi cikin gidan Me unguwa mata suna girkinsu a murhu sai kawai Ganin Chikar gayu suka yi ta daki tukunyar tayi foli foli da ita abincin Dake ciki ya juye a kasa,Mata da yara sai kowacce ta nufi dakinta ta rufe,Chikar gayu ta duba kajin gidan gonar me Unguwa da yawa a katon cage Yana kiwo ta bude su tare da Koro su waje tace duk ku fice Dan ubanku,sai Kaji suka yo waje tatatata suka yo waje suna kuka kuyat... kuyat...kut..kutt..kut,ta kwance akuyoyin me unguwa ta Koro su waje kofar gida suma,fitowa tayi ta ce zan dawo ne sai ka fada min abinda na Maka kayi min sharri zan dawo ne,gashi Nan kullum tsiya tsiya da kai kana cikin birni kana kiwon akuyoyi gidanka kamar na kauye, daga yanzu gaba ni da ku har yarana da jikokina da iyali na,Me unguwa Yana dafe da kumatu Inda yasha Mari yace sai naga bayanki,idan har Ina sallah to ni Kuma sai na nuna Maka banje gidan yari a banza ba,gidan yarin da kayi sanadin shigata to Kai na shigarwa,idan ba Kai asararre bane muna alaka da Kai ta jini amma Kaine munafuki ko,zaka ga tantirin iskanci me maiko.
gidansu ta nufa ana ta cewa ga Chikar Gayu ta fito ga Chikar gayu.

Bayan kwana uku Beauty ma Allah yayi tayi sallama da kowa itama,ranar da Beauty zata fita aka kawo wata budurwar,Beauty tace yanzu duk ba kuka kike ba sai nan gaba zaki fada,ki saki ranki ki tsula tsiyarki Yar nan duk Nan mu da kika ganmu tantirai ne,mu da kanmu mun san ta wani bangaren ba kyau bama ji gidan masu laifi ai gidan tatirarrun Yan iska ne,budurwar ta Kalli Beauty kawai tana Jin wani kunya,Beauty ta Dora hannu a Kai tare da furta Laaaaaaaa Kunga kunya take ji cewar Beauty,su Azima suka ce da sauranta lallai,ke a Nan ba kunya Dan ubanki wallahi ki warware ko kici duka a gidan nan ba a mana kunya yanzu kyaji jiki cewar Azima da wata dattijuwa Yar duniya.

A ranar da yamma Beauty ta fita taje Wajen signing,ma'aikatan suna tayata murna,Beauty baki yaki rufuwa kowa ta gani sai gaisuwa Ina Kwana,idan ya amsa ma sai tace Dan Allah mu sake gaisawa Kuma gaisuwar da wani Shoky take kwasota ta duka ta kwaso tace Ina Kwana ta watsawa mutum shokynta,dariya ta dinga basu, Daddynta da kansa yazo daukanta suna ta murna ta shiga hadaddiyar mota suka tafi gida.

Naila bata San Spark shima Yana Shirin fita ba sunyi muguwar shakuwa kullum suna tare, tare suke yin komai Kuma Bai nuna yasan ba mace bace, Ranar da za a tafi dashi kotu ranar ya samu Naila a part dinsa tana zaune tana Shan lemo da cake,ya fito cikin shirinsa ,a gefe ya zauna a kusa da ita yace Jamilu zanje kotu,gaskiya ta bayyana akan sharrin da aka min

Naila zumbur ta mike tsaya tayi rau rau zata yi kuka,shima tsayen ya mike tare da rike hannayenta biyu ya bata labarin me Mama tayi, ya fada mata halin da ake ciki a nutse,ai Jamilu sai kuka sai kurruwa da burburwa,kasa ta sulale tayi zaman Yan bori tana tumami a kasa wayyo Allah na shiga uku kowa sai ficewa yake Yana barina,Ina zan sa kaina Beauty ta fita itama gashi kaima, hawaye rabe rabe a fuskarta sharkaf tana kuka harda shidewa tana furta way way way way ihihihihi wayyo zuciyata ta dafe kirjinta tana uban kuka,tausayi ta bawa Spark yace bance fa zan tafi na barka ba ka daina kuka,ya tasheta tsaye ta mike da kyar tana tangadi kamar Yar giya,rungumeta yayi a hankali a kirjinsa tana ta kuka Yana bubbuga bayanta a hankali,a nutse yasa hannayensa masu taushi tare da tallafo fuskarta ya shiga goge mata hawayenta amma wasu bulbulowa suke kawai, hannu biyu ta sa ta riko rigarsa gaban kirjinsa tayi baya da kanta tana rasgas uban kuka, yace amma da nasan haza zaka min bazan fada Maka ba,kayi shuru Jamilu,Naila tace sunana Naila ni ba namiji bane wlh, Spark ya kalleta sosai yayi dariya yace ai na sani tuntuni, kawai kallonki nake,tana shesheka ta furta yaushe ka sani a Ina? murmushi ya saki yace nasan kai mace ne ba tun yanzu ba sunanki ne kawai ban sani ba,Ashe sunanki Naila nice name,Naila duk a rude take tace na cire abinda nake daure kirjinta da shi taba kaji ni Macece,Spark yace ni da na kalla wai with my two Kworo Kworo eye,kallo fa nayi ni Kinga gani ya kori ji,ki bari na dawo zamuyi zancen,kici gaba da zama a jamilunki please kafin na fitar Dake,ai kace baza ka tafi ba,idan ban tafi ba taya zan fitar dake to? Naila ta sake fashewa da kuka,yace na fasa bazan tafi ba zan zauna,da kyar ya lallabata tayi shuru,idonta yayi jajir har ya fita tana hawaye.

Spark bayan an kaishi kotu da matakan tsaro a motar gidan yarin,Mima ya fara gani ya dauke kansa,Mummy ya gani wajenta ya tsaya ya gaisheta ta rungume shi tace Dana I miss you,ya furta me too,Rafeeq ya mikawa Hannu suka tafa da Kamal shima suka gaisa,bayan duk wani bincike kotu ta wanke Spark tas bashi da hannu a kisan Asmau sannan Mama Kuma an yanke mata hukuncin daurin rai da rai,tana ta kuka,yaranta suma sai kuka suke na bakin ciki,ana fitowa daga kotu wai Spark ya bisu su tafi,Spark yayiwa Wanda suka zo dashi Yana da abubuwan yi a ciki akwai kwangilar gyaran kofofi da zai musu shi lallai a Maida shi ciki sai ya gama zai fito,Har kudi ya basu tun a mota,Su Mummy suna kallo Spark yabi motar gidan yari suka koma ciki da shi, to da uwar kudinsa.

Naila tana palonsa ta zuba tagumi tana ta wani sabon hawayen Spark ya shugo yace au kukan kike yi dama? Naila tana kuka tace nidai ka zauna karka tafi,Spark yace Tantiriyata ke da na sanki da juriya,jajirtacciyar ce ke fa,kici gaba da fitowarki a Jamilunki karki sake a gano har na samu ki fita please,Naila tace to kawai yace ko ke fa,Baki murmushi ba? Harararsa tayi tana goge hawaye,da kafadarsa ya Dan biki tata kafadar kadan,kansa ya dora a kafadarta yana karewa fuskarta kallo,janye jikinta tayi da sauri ya koma zai kwanta a cinyarta ta mike ta canja kujera,dariya yayi yace ki dakko hijab dinki ki daina boye boyen sallah,kamar an dinke bakin Tantiriya,tunda Spark zai bar gidan shike nan Kuma ta rasa sukuni,Bata kazar kazar da surutu ko wani Abu,Su kansu a gidan yarin ana mamakin Jamilu ya daina walwala Sam,Yar dariyar da yake bawa mutane ya daina an rasa dalili,su Malam Sharu har tambayar Jamilu suka yi wai meke damunka ne Jamilu? Yace ba komai kawai,Su Dan Indo,Goje sunyi sunyi suji meke damun Terror Jamilu amma basu gano komai ba.

Bayan kwana biyu kullum Spark aikin lallashinta yake amma Jamilu ya daina walwala,yace idan baza ki dawo dai dai ba zan tafi wlh,Naila tace ai dama nasan zaka tafi din mene to ka tafi mana Dan Allah Kafi ruwa gudu,Spark yayi dariya yace shike nan, washe gari ranar Ziyara,ranar Beauty zata zo wajen Jamilu, Chikar gayu zata zo taga waye Spark da ya mata hanyar fita, Yaya Mohsin da Umma sunzo yau su biyu,Naila ta fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login