Showing 27001 words to 30000 words out of 158722 words
Chapter 10 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
Tk yace a macen ma full option,ance jikinsa laushi kamar me,muje mu taba Muji,Muler da Tk suka taso da niyyar taba hannun Jamilu su ji,sai kuwa Dan Indo yaji wani uban kishi ya make hannun Muler yace wlh kana taba Jamilu sai na rushe Maka hakora,sun san DanIndo sai suka koma Inda suka taso,Naila a ranta taji dadi Sam DanIndo ya tsaya mata ba Wanda ke kawo mata wasan shirme sabo da suna ganin abokin Dan Indo ne.
Naila ta juya ta Kalli Dan Indo tace Ina baka labari abokina,yace Ina jinka,ai Ina fada Maka ni idan nazo waje shedan ya kan bace yace oga tazo har gisuwa yake kawo min ida na shirga wata tsiyar,badan gidan yari ba da yanzu na kashe auren Yaya na, amma kisan Kai bada ni ba,Dan Indo ya furta mene a cikin kisa ai kawai Wanda yayi akuya kawai ka caccaka Masa wuka,ai ni billahillazi da me zarto nake amfani cewar wani me suna Baballe da ya tsomo musu baki, shi da yake babban Dattijo ne ma,ya kunna sigari yace maganin shege sai Dan Banza Tantiriya Jamilu,ai karka sake a kawo ma raini ko a gidanku ne,Naila tana Jin halin kowa iri iri.
Tunda tazo gidan yari Dan ragowar tsoronta ya gudu, Uban Dawa yana wajen yace ni ka san daga Ina tsiyata ta fara? Maza nakewa fyade,in ketawa Namiji haddinsa ba komai bane duk girman gardi nayi niyyar lashe Masa Timber karya yake ko ubansa waye,Baki suka hada suka yi wata shaharriyar shewa da ihu harda,suna da masifar yawa a wajen sun hada uwar daba,wani da ake kira da Goje yace ke Tantiriya wanne tsiya kika yi a kasar Nan ta alfahari? Wacce kai da kanka Jamilu idan ka tuna kake jinjinawa kanka? Naila tace Ni Jamilu nine wanda na saka Budurcina a caca tun farkon fara Daudu nawohoho suka furta kamar Wanda suke shuka abin arziki haka suke hirarsu,
Fitsara da rashin mutunci a cikinsu ba a magana,akwai Yan iskan da su tsirara ma sukeyi watarana a ciki uban kowa ya gansu,duk wani sabon me laifi da aka kawo shi gidan yari Wala mace ko namiji tofa kowa sai yaji labarin an kawo sabo, sai Kuma an San waye,duk iskancin mutum akwai Wanda ya ninka shi sau dari a ciki,suna zaune Naila taja DanIndo da Goje wanda suka fi mutunci tace kwana nan zan bace a gidan nan,Goje yace ta wacce hanya Tantiriya? Naila tace ta bangaren Mata zan koma nayi shigar mata,dariya suka saki,tace wlh da gaske nake,ta bangaren Mata Anfi samun damar guduwa idan ta kama,daga part din Mata sai bayan Daji Kunga kuwa sai fecewa,Goje yace ai kuwa kana haurawa zaki karairaye, ka Kalli uban katangar gidan,tunaninka katangar banza ce,a banza zaka ga kartai sun kasa tserewa, gashi yanzu an Kara kwalabe da wayoyin shocking kana tabawa sai mutuwa,Naila tace bazan yarda daku ba,to munji yanzu ta ya zaka shiga bangaren matan har ka zauna ba a ganeka ba,Bari zaku gani bari yayana yazo zai kawo min kayan Mata ku gani.
Bikin Spark an saka rana an saka bikin a kurkusa, babu bata lokaci Mummy ta matsa Masa ba yanda ya iya,sai masifa yake yi,yau gidan su Asmau yaje har gaban iyayenta ya musu warning yace idan kuka aura min yarku ba ruwana da Yar uwa ce zan iya kashe ta nine ajalinta gwara ma ku janye ato ba abinda zai hadani da ita ya fada ne Dan ya tsorata su a fasa auren,yaci gaba da furta me zanci da yarku bana sonta ko dole ne ana so dole ne Dan kawai Kuna Yan uwana sai ku takura min.
Baban Asmau kuwa masifar son 'ya'ya ne da shi,sai abinda yaransa suka ga dama shi suke yi ba a yiwa yaransa fada bare ace ba a sonsu,shi indai kana son yaronsa to ka gama da shi,tunda ya fuskanci Spark baya kaunar yarsa shike nan ya tsani Spark yake mugun Jin haushinsa,sabo da yaga iyakarsa shi yasa ya dage ayi aurensa da yarsa ko tsawa idan yayi yarsa ya sa a ransa sai ya daure shi,sai yayi amfani da mukaminsa da hanya da kudinsa yaga karshen Spark a duniya, Suna jin Spark ya gama masifarsa ya fice ya bar gidan tare da shiga motocinsa suka bar gidan,Baban Asmau yace ni Kuma bari naga karyarsa bari a dawo da bikin nan da sati daya idan ya isa ya mata ko tsawa ya gani ni Kuma ba rangwame wallahi sai ya kare rayuwarsa a gidan yari Kuma bazan ma barshi a gidan yarin Abuja ba kar ma suje suyi cin hanci,l,Lagos zansa a batar da shi,ni dama bana son yaron nan tunda ya taba kwace min wata Kwangila da gomnati ta bani.
Kawai Baban Asmau sabo da shima babban Soja ne sai yace a dawo da bikin sati daya,Spark sai labari yaji wai an dawo da bikinsa sati daya,a fusace ya tafi gidan Mummy, shi yayi driving shi daya yana shiga ya samu Mummy a palonta tana takaba amma Dan masifa sai tayi bikin kamar ba me takaba ba har lallenta take yi, ya durkusa a kasa a gabanta,haka kawai ya fashe da kukan karya,yana hawaye yace wlh bana sonta Dan Allah karku aura min ita,bazan iya rayuwa da ita ba,ni bata min ba,Mummy ko kissing nata bazan iya ba bakinta ya min girma sai ta hadiye min bakina Kinga nawa Mummy ya turowa Mummy karamin bakinsa,yace ki tuna na Asmau kamar kofar ShopRite ya sake fashewa da kukan karya tare da Dora kansa a cinyar Mummy,a boye Kuma Dariya yake, Dariya Mummy tayi ta rike hannayen Spark tace yau Spark da hawaye akan mace,yace wlh bana son ganinta ko a hanya bare ace zan aureta,ni Spark ace za a min auren dole wlh bazan shiga gidan ba ko an kaita gidana.
Mummy tace ka makara ka koyi sonta wlh yau saura kwana shida zaka ganta a gidanka,mikewa yayi Yana cika Yana batsewa hakarsa bata cimma ruwa ba,sai ya koma spark dinsa ya daure fuska Yana kunkuni ya fice cikin fushi dama kukan karya yayi ko za a tausaya Masa sai gashi ba nasara.
Spark Yana ta bincikensa akan Case din Naila ya zaiyi ya fitar da Jamilu a gidan yari ga matsalar aurensa,kamar wasa biki yazo ranar Friday za a daura Kuma a ranar za a Kai amarya ba wani biki za ayi ba sabo da Mummy tana takaba,Spark har ya hakura ma yace Allah yasa haka shine Mafi alkhairi ya zaiyi.
Ana gobe daurin aure tare suke da Kamal suna Hira, Spark yace na kyale yarinyar Nan sabo da son da take min,taci darajar Sona da take yi amma fa bazan ko hada room da ita ba wlh har ta gaji tace na sake ta shine kawai adalcin da zan iya,ni zan hada jiki ne da wacce zuciyata ke so wacce ta kwanta min a rai wacce bana kyankyami, Kamal zamuga wace Yar sa'ar Nan Yar gidan waye idan Kuma Asmau ce zata sace zuciyar to,Spark yace hmmm ya Kalli Kamal yace zaka Gani inshaallah,ai Asmau bazan taba sonta ba,ni ba abinda ta min kawai Allah bai sa min ko digon sonta ba,hasali ma a duniya ba wacce na tsana irinta.
Asmau kuwa Banda murna ba abinda takeyi,itakam shagali take matukar zata zauna gida daya da spark to rayuwa ta mata dadi ko da bazai kulata.
Washe gari Friday daurin auren Spark dukkan Yan uwa da abokan arziki sun hallara har abokinsa Kamal duk sun dauki wanka amma ba ango yace bazai je ba wlh,mahaifinsa da Mima mahaifiyarsu sunyi iya yinsu yaki zuwa,haka aka daura aure ba ango,shi Yana Office ma aikinsa yake ya kashe waya kar ma ayi Masa Allah sanya Alkhairi,haushi yake ji in akace Allah sanya Alkhairi, zuwa Yamma aka Kai Masa Amarya sai kace dole,amarya anci gayu an hade,har aka watse ango bai zo ba,shuru shuru haka Amarya ta mike tayi alwala tare da gabatar da sallah sannan tayi Shirin bacci ta kwanta abinta,Nawwar a ranar a Office dinsa ya kwana ma bai je gidan ba.
Asmau kuwa bayan ta kwanta bacci, sai da safe dangin Amarya suka zo zasu mata sallama zasu tafi garinsu amma sallamar duniya a palon ba a bude ba,har suka gaji tare da shiga ciki suka zauna a Palo nan ma shuru shuru,suka fara duba bedroom dinta sai kuwa suka hangota a kwance ta Kalli sama idonta a kafe,da sauri suka isa kanta suna tabata shuru har ta sandare ta kame, Dake akwai dattijai a ciki suka tabbatar ta rasu,wuyanta ga shatin igiya Nan da alama igiya aka sa tare da shake mata wuya har ta mutu,sai kuka da kuka suna cewa dama angon yace sai ya kasheta to kuwa da gaske ya kasheta shike nan sai bige bigen waya azo ango ya kashe Amarya ya gudu baya gidan ma.
Hankalin kowa ya sake tashi a family gaba daya,iyayen Spark kowa suka tattaro sai katafaren gidan Spark, Kamal ma da gudu yazo gidan,iyayen Asmau kuka suke suna cewa wallahi baza mu yarda ba,mahaifiyar Asmau ta fada kan gawa tana kuka tace Asmau...Asmau na....wayyo ya kashe min Yata bai San zafin haihuwa ba, Mummy da gudu ta shugo gidan tana wallahi Dana bazai yi kisa ba ban yarda ba karya ne sharri ne ta Fadi a kasa tana kururuwa,Mummy a duniya tana son spark ko uwar data haife shi baza ta fada mata son Spark ba,kamar ranta haka yake,tace wallahi da nasan haka zaku ce bazan daure gindin Spark ya auri Asmau ba.
Mutane ba Wanda ya yarda da Mummy duba da halin Spark da Kuma furucinsa Kuma an San baya karya shi yasa har iyayensa na gaskiya suka yarda, Baban spark shima Soja ne ya Kalli Baban Asmau yace kuyi bincike ku dauki mataki akan Ashraf ya girbi abinda ya shuka,Mima uwa to fa uwa ce amma Mummy ta fita son Spark itama tace idan an tabbatar shine a hukunta shi, sai kuka take tana cewa tabbas yara haihuwarsu jarabawa ce,mu iyaye muna ganin jarabawa akan yaran da muka haifa, Rafeeq zuwa yayi shima Yana ta al'ajabi amma bai yarda Spark zaiyi haka ba sabo da yasan halin Spark.
Baban Asmau dama kadan yake jira yasa aka Kai gawa asibiti duk wani gwaje gwaje anyiwa gawa amma komai normal bata ci wata guba ba da wire ko igiya aka shaketa har ta mutu,Spark aka shiga nema lungu da sako babu Wanda yayi zaton Yana Office,sai da Yan sanda suka dangana da Building dinsa,gashi Baban Asmau ya musu alkawarin mahaukatan kudade na mamaki shi yasa suka dage.
Suna shiga ciki ko Ina a bude yake sabo da ma'aikatansa duk sun zo aiki,har Office dinsa suka shiga sai kallon tsaruwar office din suke,akwai Palo a ciki suka karasa a Nan suka same shi Yana ta bacci hankalinsa kwance kasancewar jiya baiyi bacci da wuri ba Yana ta aiki.
Tashinsa suka yi sun san da kudi shi yasa ba raini suka tashe shi,a hankali ya bude idonsa ya kallesu da uban yawa a kansa sun zagaye shi,kallonsu ya sake yi yace lafiya? daya daga ciki yace matarka Asmau....kafin ya rufe Baki Spark yace Allah yasa ta mutu na huta da mayya,me ya faru? Sheda ta Kuma tabbata sai suka fito da sarka tare da furta You are under arrest, ana tuhumarka da kashe matarka,Idanuwa Spark ya zaro yace kisa Kuma ni? Yaushe ma na kwana a gidan? Mamaki ya kamashi,Asmau ce ta mutu? Su dai yanda suka ce zai raina musu hankali ne kawai suka sakala Masa sarka a hannaye yace ba sai Kun sa min sarka ba zan iya binku normal cire min chain,ba musu suka cire Masa.
Spark yana furta innalillahi wa innailayhirrajun yaci gaba da cewa ko a lahira Allah karka hadani da Asmau, ya Allah ka gafartawa Asmau ka yafe mata,Allah ka gafarta mata irin shiga hakkina da tayi ta aure ni bada izinina ba l,Allah na yafe mata ka yafe mata,kansa ya jinjina yace uhhmmmm su Asmau an matsa min lamba Allah ya yafe miki,Sadakin ma sai da Papa ya biya min,Allah ya miki Rahma uhmm rabo to..dama ance rabo Yana kisa,sai da nace a hakura rabon wata ne aka ki ji, Yana magana ya tattara documents dinsa da kudadensa da duk wani Abu nasa me amfani ya fito dasu tare da Yan sandan motocinsu sunfi biyar suna ta jiniya.
Manager dinsa ya mikawa yace ka kaiwa Mummy kace ta ajiye min ba Mima ba Mummy nace,yace angama sir,ya shiga mota yaransa masu aiki a karkashinsa suna kallo Yan sanda suka tafi dashi.
Yana can aka sallaci Asmau tare da kaita makwanci,Yana motar Yan sanda ya Kalli Inspector guda yace iceko takaba bata hau kaina ba? sabo da tsabar ya raina musu hankali,Kuma wulakanci Spark ne,Yana da kudi to ba uwar da suka iya Masa,dama duk jaraba akan talaka take karewa, Spark sai kallon raini yake musu,suna ta Shan wulakanci iri iri.
Inspector yace Kai nifa Inspector ne,Spark yace no Inspectataatatatataaaa,yaja wani tsaki Kuma ba uwar da suka iya yi,shuru ya musu fuskar nana hade, har suka kaishi tare da tsare shi,ko tambaya suka Masa baya basu amsa a mutunce,shine ya Kara basu haushi sosai.
Duk wasu bincike an fara yinsu akan Spark amma ba hujja shi ya kashe Asmau,Baban Asmau kudi yake dannawa Yan sanda akan a Masa duka to shima Spark Yana da kudi Kamal Yana kawo kudi dole basa iya dukansa ko farcensa basa iya tabawa gashi tsagera Yana da kwarjini,Inda Allah ya saukaka ma da wuri Baban Asmau ya Kai Kara kotu ta can Lagos,ana ta faman bincike yaga zasu bata Masa lokaci ya Maida karar Kaduna,Nan ma yaga Spark ya fishi hanya ana ta daga sharia gashi ma za a bada bailing Spark,tsoro yaji kar ya cale kasar waje,yasa aka sake tsare shi sosai aka Maida case kotun dake Kano state.
Yayi hakane Dan ma kar Ashraf ya bada cin hanci a sake shi,duka dangi ma sai labari suka ji ai an Maida shi kano.
Wani mugun azzalumin Alkali ya samu sannan da lauyoyi azzalumai, Spark Yana tsare ba dama yayi katabus,Mummy duk kulla kullarta Baban Asmau ya fita gashi babban Soja ga kudi kamar yayi, gashi namiji ya fita basira,iyayen Spark da danginsa sunki shiga cikin case din sabo da spark ba Wanda ya kyale shi yasa suka kyale shi.
Suna ji suna gani aka Masa sharrin kisa ta karfi tare da yanke Masa daurin rai da rai shima a gidan yari.
Spark yaga masifa ana kawo shi ciki gidan yari Naila ce ta fara ganinshi tace wow, sai data tsaya ta kare Masa kallo Yana wani gadara da kyar yake tafiya fuskar nan a hade ba mutunci dama ya lafiyar Kura bare tayi zawo, sai kallonsa akeyi sabo da kyansa da gadararsa ana ganinsa an San Dan gidan wani kusa ne a kasar, Naila ce ta fito tana tafiyar Yan daudunta tabi bayansa tana kiransa tace wannan zaka dace da Daudu,ni Kam nayi budurwa,ta fara kiransa da Asabe....Asabe....ko Tabawa ce ne? Tabawa...ahhh Ashe ba tsohuwa bace sannu ko sunanki Kamariyya? Jin Muryar mace sosai yayi mamaki ya juyo ba shiri,gashin kawai ya kalla yace a ransa Ashe Dan daudu ne,Naila ce ta katse Masa tunaninsa da cewa Kaiiii gaskiya kina kama da Lady Gaga, jar Uba I love you, shike nan ga suna na Yan gayu Iklima ai yafi?,ni sunana Dahara,wani takaici ya kama Spark,Sam shi ya tsani mutum dandaudu wani tsanar mutum yake yi,ga wannan gaba daya suffar mata gare shi, Naila kuwa ta jera dashi taci gaba da cewa,Sunana Dahara sunan ya samo asali ne tun Ina karama Allah ya sa min yin tsarki,kullum ni dai na dauki buta nayi in tsarki shine aka canja min Suna Dahara, Kuma fa Ummata sanda tana da cikina ance Bata iya rike fitsarinta shine kullum ta dauki buta shine ana haifo ni nima kullum da buta a hannuna dole aka gaji Dani aka sa min Dahara.
Look ni ba wani abu nake so ba,kawai abokina zaka zama sabo da ba karamin girma bane a ganni tare da Kai,kawai ma ace Ina Dating naka ai ni na zama kadara, duk Inda ya sa kafa Naila tana biye da shi,mutanen gidan sai daga mata hannu akeyi a matsayin Dandaudu ne kowa sai yace su Jamilu Terror anyi sabon kamu, Naila tace harka ce ta Uhmm humhum,hankalinta ta Maida wajen Spark tace to shike nan da sunanka zan na kiranka, ya sunan naka? Ko kulata baiyi ba, ganin Dandaudu y matso kusa da shi hannu yasa ya ture Jamilu,ai Naila rikicif sai gata wanwar a kasa, lebenta na kasa ya fashe kadan,Mamaki ya kama Spark namiji guda daga Dan ture shi yayi wannan uban faduwar haka,Bai San macece ba,a ransa yace wannan ya gama kashe kansa ya zama macen gaske,wait tsayawa yayi Yana tunani da yasa hannu a jikinsa yaji Laushi haka,wani sabon mamakin ya dira a zuciyarsa,kallon jamilu a kasa Yana goge bakinsa, haka ya wuce bangarensa na masu kudi wajensu daban dakinsa shi kadai harda tv da fridge harda kujeru sai dai rayuwa kawai a waje daya musamman ga namiji akwai wahala.
Naila tashi tayi da kyar ta goge jikinta tana dingishi ta koma dakin su Alaramma Jilani,samunsu tayi suna Hira ai suna Ganinta ta shiga gaba daya suka jawo Qur'anansu kowa ya bude ba shiri,dariya suke Bata.
Gefen bed ta zauna Malam Garzali ya dago Kai ya saci kallonta ai kuwa karaf suka hada Ido Naila ta kashe Masa ido daya,da sauri ya duka karatunta Yana yiwa sauran magana kasa kasa yace kaiiiiiii wallahi Ido yake kashe min Kuma ya birge ni,Malam Garzali shima yace nima haka zuciyata
Naila Hanata akayi shiga indai ba da izinin