Showing 6001 words to 9000 words out of 158722 words
Chapter 3 - Tantiriya A Gidan Yari Book1 Hausa Novel Complete
ware kanta gefe,sannan namiji Bata bari ya riketa sai idan Bata sani ba,Hakan ya tabbatarwa da kowa ta shahara a harkar Daudu.
Naila tana noma ta Kalli wani Dan saurayi matashi kamar sa'anta ne amma ya fita girma da komai namiji da mace ba daya bane ko a halitta, suna Shiri dashi Amjad, tace Amjad ban taba ganin mace ba tunda nazo gashi har na kusa sati,oh ashe kallon mata ma Rahma ne,dariya Amjad yayi yace wlh ai in ba a Yan uwanki mace ta zo Miki ziyara ba baza kiga mace ba,Kai da kake Dandaudu Ina ruwanka da mata,Tantiriya tace to ai munfi Jin dadin rayuwa cikin mata sune muke kama, Allah sai dai irinku Maza haba shi yasa naga maza suna ta Neman junansu.
Ni a dangina ma bamu da mazaje Samari sai wani Dan banzan kanina me tafiyar tolo tolo sai uwata sai ubana, Wanda zai iya zuwar min Yaya Mohsin ne,kaga Ina da saurayi Kuma nasan zaizo, Amjad Baki ya tabe tace Dan uwanka ne fa namiji,Jamilu yace kamar ka sani yanda nake son Gambo beauty sai baza ayi ba ta furta da sugar Yan Daudu,Amjad ya sheke da dariya yace kunyi asara wlh.
Amjad ya sake cewa hala kai Hariji ne ne ko kana sex tun a gida? Yo mu yai muna layin gidan Kashi cewar Naila.
Naila a ranta tace a gidan Nan nasan ma cuta ta kamani ta ciwon sanyi sabo da kazanta wlh har kaikayi nake ji a gabana tabbas na kamu da ciwon sanyi.
Wani shahararren Dandaudu ne da ake kira da Skoler yazo wajen Tantiriya Yana rangwada yace Kawas ya kamata na fada miki kiyi taka tsantsan da toilet mu mata muna kamuwa da ciwon sanyi in kinji gaba na kaikayi sai kiyi magana zasu kaiki asibiti a baki magani ahayye ya tallafe kirji ya zaci da gaske Naila Jamilu ce,suna ta hirarsu har kusan dare sannan suka hau layin karben abincin dare abincin Dan kadan gashi ba Dadi,masu kudi suna ta siyen abinda suke so,a hakan ma Idan wani yafi karfinka ya samu ya masgeka ua kwace ya hade du ya cinye.
Naila tana layi aka zubo mata Miya da Katon sandararren tuwon masara,ta Kalli abincin ta bata fuska tace Kai masu girki kuji tsoron Allah Miya kamar yawun kaza haka gomnati tace kuyi? Wani Ma'aikacin cikin fursunonin yazo zai kwade Tantiriya Naila da duka sai yaji ya wani shiga ransa sai ya koma yayi mukus ya juya, amma Naila harda tana Allah ya Isa wlh ma'aikatan har sun gaji da Halin Jamilu Tantiriya duk abinda akace kar yayi sai yayi, duk mugunta iri iri Amma bata jin magana,rashin kunyar ta da taurin kanta kullum karuwa yake sabo da basa taba dukanta kowa jinta yake a rai tunaninsu ma namiji ne.
Washe gari da yamma yau ta samu tayi wanka Dan Indo ne Ara mata sabulu ta fito gabanta Yana ta mata kaikayi cutar sanyi ta kamata,ta rasa Inda zata sa kanta gashi ba abin ta fada ba a gano ta,Dama kayan Dan Ido ta Ara ta barma a jikinta a wanke suke,ta wanke nata tas ta shanya su,kayanta suna bushewa ta koma toilet ta shirya ta Saka abinta, yau fes take sai kaikayin da gabanta ke mata na hauka cikin dakinsu ta shiga Wanda yake da malamai a ciki,gado ma Babu na kirki wasu duk a kasa suke kwanciya ko shimfida babu a masu kwanciya a gado har Tantiriya Jamilu,,ta Ari bargon malam Sharu tace bani da lafiya bani aro ta kwanta ta lullube jikinta da shi a ciki ta samu ta tattale kafa ta hau sosa gabanta ba ji ba gani,a hankali kasa kasa tana cewa a bani cokali wannan susar sai da cokali.
Naila tana susarta tace yau Bado Yana cin ubansa da Susa,a fili Ashe ta furta Dariya su Malam suka yi sun zaci iskancin Yan Daudu ne kawai,Malam Jilani yace mene Bado? Naila tace gaban mata, ku baku ga yayi kama da Bado ba? Bado wannan Abar da take fitowa a cikin ruwa,Idan baku San Bado ba kuje kuyi bincike,malamai sai kunya ta lullube su,Malam Sharu yace Dan Allah ka koma cikin Yan uwanka Dandaudu Bai kamata kazo cikinmu ba muna malamai.
Rafeeq gida ya shugo cikin takunsa na yana kamshi yayi Sallama a gidan ShimaA wannan gidan da gani kaga gidan me hanu da shuni gidane na gasken gaske komai na more rayuwa akwai duk da gidan da iyayen Rafeeq suke yafi kyau sosai Amma wannan ma ba baya ba,ga motoci nan hadaddu masu tsada daban daban,Rafeeq yana shiga katafaren Palon gidan wata matashiya ce baza ta wuce 50yrs ba da kuruciyarta kyakyawa son kowa kin Wanda ya rasa ga kyan Kira da diri,tana ganin Rafeeq ta saki murmushi tare da amsa sallamarsa,kallonta yayi ya zauna a hankali yace Aunty barka da hutawa,Wacce ya Kira da tace Dana ya aiki ya Kuma school kana garin shine sai yau zaka zo min? Sai da ya dauki lokaci sannan yace kiyi hakuri Aunty Exam muke yi ne,kin San indai lafiya ai zanzo ko? tace na sani to ya school? normal Aunty,bari na kawo maka abinci,me kika dafa ne? Hmmm zai wuce tuwo ne da kyar fa ma ya bari nayi tuwon, kasan komai dai yau ma ko kudin cefane bai bayar ba,ayi mutum kamar talaka Wanda bai gaji arziki ba,Hawaye ne ya zubo mata tace Ina so ko Yaya ne ya so ni ya kyautata min amma Hakan ya gagara sai ma kuntata min da yake kana gani dai, Aunty wai waye naji ance an kaishi prison akan gidan su Spark? Hankalin Aunty ya dawo kan Rafeeq, tace wani Dandaudu ne marar Imani ya kashe shi,daga kawoshi gidan mutane,Aunty ta kwashe labari ta fadawa Rafeeq,Rafeeq yace Allah ya kyauta shi kam a ransa bai yarda ba Sam, yana da ja akan kisan domin yasan tsakanin Mummy da Mijinta irin zaman da suke, tace sunansa ma wai Jamilu Hashim.
Rafeeq yace hmm kawai sannan yace kina da kudi kuwa? tace da kyar ma na samu na siyan kayan Miya Sweetheart, Rafeeq ya mike tare da zaro kudi dubu goma yace kiyi hakuri da wannan kin San Yan Makaranta,ta Mika hannu Zata karba kenan me gidan ya shugo sanye cikin wata peach shadda Yar gaske yana sheki yana kamshi Shima ba wani babba bane,Rafeeq yace Sannu da zuwa wani kallon banza yayiwa Rafeeq yana daure fuska yace bana hanaka bata kudi ba,iyalina ko naka bana son shishigi,wato kana nuna min ban iya ruko ba ko?to baza ta karba ba jeka da kudinka,kafa dameni Karka bari na hanaka zuwa gidan nan,Ina daga maka kafa baka gani, Rafeeq kudinsa ya karba ya Kalli Aunty a sace suka hada Ido ya faki Ido ya tura mata kudin a kasan kujera tana kallo ya ajiye ya fice abinsa,Wanda ta Kira da Abban Na'eem da Na'eema ya fara yayyafa mata ruwan masifa yace wlh ki kiyayeni Rumaisa Ruma ki kiyaye ni banza shashasha,wato tona min asiri kike sabo da kin raini Rafeeq gani kike kamar ke kika haife shi karki manta Dan Yar uwarki ne,Yar uwar taki ma da bata son kike shiga sabgar danta in Banda masifa ma kina juya bakya haihuwa ki hakura da rike Dan wani mana yaja tsaki,tace kayi hakuri abincin fa? Bana ci ya juya ya wuce part dinsa fuuuuuu dama ya Riga yaci nama me rai da lafiya a wani joint me tsada a koshe yake abinsa.
Su Naila ana gobe ranar ziyara dukkansu murna suke musamman Wanda Suke da tabbaci za a zo musu daga gida,ita kuwa Naila bata murna domin Iyayenta Basu yarda da ita ba shi yasa suka ce ba ita ba su Kuma babu Wanda zaizo wajenta ko an kaita can,tasan halin Ummanta ,Amma haka suke ta tsafta suna gyara jikinsu kar azo a gansu cikin kazanta,Naila tana Kallonsu ta zuba tagumi a inda ta idar da Sallar la'asar Sallar ma a boye take yinta,a haka ma da ya ta shugo da Karamin mayafin a cikin wandonta a boye,duk Allah ya tsallakar da ita ba a kamata ba,Addua take Allah ya rufa mata asiri kar a tarfa ta,sai ta bari an fita makaranta take buya tana yi ba nutsuwa sabo da tsoro, kullum itace karshen fita school tace ya Allah karka bari a kamani ko a ganta da mayafi kowa yasan iskancin Yandaudu sunyi Imanin baza a kawo musu Mace gidan ba shi yasa duk suka amince Dandaudu ne,Allah yasa ma basu kamata ba har yanzu,kullum addua take kar a kamata har ta fice a gidan,kullum cikin faduwar gaba take.
Wani Wanda ake kira da Skoler Dandaudu baki har kunne ya samu Dandaudu me kyau kamar mace,wajen Naila ya karaso Yana rangwada ya furta budurwata ke wai baza kiyi wankin ba? Ai ko sabulu sai na Ara Miki ki wanke kayanki, ga wando da t-shirt Dina ki Saka,Naila tace ni ai ba Wanda zaizo min wa nake da shi Babana da Ummata sunce baza su zo min ba,nafi sa rai ma da Yaya Mohsin amma nasan halin Ummanmu ko zan mutu baza su kawo min ziyara ba,Dandaudu Skoler yace iyyee ke ki bari Dan Manzo, ai shike nan amma baki sani ba ko sun huce, kinyi fa sati daya da zuwa nan Jamilu ki samu dai kiyi tsafta ga farcenki nan sunyi Zako Zako haba Jamilu ta ,gashinka buzu buzu,ga kaya sunyi dirty gashi kina fama da susar Bado abin ai yayi yawa,sai yanzu Naila ta tuna hannunta na gabanta da sauri ta cire,Skoler yace ahhh karki ji kunyata ai daya muke nima macece irinka sosa abinki kafin Nan gaba ki aminta Dani na dinga lashe pole din naka,Ahhh ranar akwai harka ahayye chass Chass heyyyyy nanaye, fito dan Allah Jamilu Baby mu wuce.
Hannun Naila ya rike ta fisge da sauri,ya saki da mamaki yace ahhhh wannan laushi kamar auduka, billahillazi kinji za ayi bantan bala'i Dani a kanki Yar uwa,I love you Jamilu,Dan Allah ni dai Jamila zan dinga kiranki please
Naila ta Kalli Skoler tana hawayen karya gwanin ban tausayi tace nifa ba a sani sannan ba a hanani Iyayena ma hakuri suke Dani shi yasa ma da akace na kashe wani suka yarda kije kawai zanyi tunani akan soyayyar, Skoler yayi tafi tare da bugar cinya Yana fari yace shike nan Ina jira tawan ,Naila tace ba gwara ma na mutu na huta ba,gwara kazantar cuta ta kashe ni, zuciyata ta buga kawai na huta,ba na Jin magana ni yawwa ba a sani sannan ba a hanani,Suna jinsu kowa ya rabu da su,Shi kuwa Skoler ya dage lallashin budurwarsa yake Jamilu,tana ta shagwaba ,gajiya yayi ya zaro dubu daya yace ungo Baby je ki Sha lemon kwalaba ki sanyaya makoshinki,Naila taji wani dadi ta karbe tace thanks ,yace wow yimin fari Jamilu na,Naila tayi Masa fari da Ido,Kirji Skoler ya dafe yana karairaya yace zan suma bar ni haka, shi a dole ya samu budurwa namiji irinsa Dandaudu.
Washe gari bayan mata an gama zuwa ziyararsu sannan aka bude maza suma aka dinga zuwa musu suna ta murna yau sun samu abincin gida suna ta ci amma banda Naila ko kare bai zo wajenta ba ko ma fitowa bata yi ba sabo da sai Wanda aka zo wajensu suke fita,kusan kowanne anzo masa suka dinga dawowa da sabulai da omo,rezo,shaver da tarkace daban daban amma banda Naila me kaya kala Daya,ana koya musu Karatun addini Dana boko a ciki,ga sana'ar hannu iri iri,Itadai Naila sakar hannu ake koya mata a ciki da Saka kayan sanyi,Sai filin wasa Idan sunyi niyya,Naila ranar wasa tana can daki bata zuwa,duk sanda ta tuna iyayenta da Yan gidansu Kuma taci kuka ta koshi,hankalinta bai sake tashi ba sai da ziyara tazo taga kusan kowanne kato anzo masa banda ita,a Hakan ma su Dan lIndo da Yan Daudu ne suke taimakonta da sabulu da omo gashi wani satin zata fara period ta rasa Ina zata samu pad duk da sanyi ya kamata bata San ko zaizo ba ko bazai zo ba oho.
Dare na yayi sauro kamar zai cinyesu sauraye ne na hauka kamar yayi gomnati bata dauki mataki ba Yana zubawa mutane cuta,Naila sai Susa take ga cizon sauro gashi yanzu duk tunani da bakin ciki ya hanata ma yin tsaftar ba sosai ba,gashi ba wuta ma bare su samu suga haske ba kullum ake kunna musu inji ba,cikin duhun daren kowanne a kwance yake, kasa kasa take jin maza Yan gay suna numfashi suna ihunsu na Dadi ga wasu Kuma suna biyawa kansu da kansu bukata,Ko wanne daki haka suke yi Idan dare yayi,Yan Iskan karshe sai kalaman banza sukeyi suna ihu da Nishin Dadi,duk sanda Naila taji Hakan hankalinta tashi yake taji a duniya bata bukatar komai face Namiji,macece me bukata amma yau dake ciwon sanyin nata yayi nisa bata ji sosai ba ta mike sum sum ta koma dakin malamai Inda yafi mata mutunci, su na kirki ne basu aikata alfasha baccinta tayi a can.
Kafin sati biyu farcenta sunyi mugun Zako Zako duk ta fita a hayyacinta ta rame tayi duhu duk haskenta amma sai da ya ragu,ana gobe Ziyara Rafeeq da abokinsa Islam a Kano suka kwana a hotel kowanne da dakinsa,washe gari da safe bayan sunci lafiyayyen Kari ,Islam ya fito shirye cikin hadaddiyar Shaddarsa me kyau sea blue Dinkin Yan gayu na Yan zamani yana kamshi ya Saka hula kalar kayan yayi knocking dakin Rafeeq yayi yana tsaye yana fesa turaruka shi sanye yake cikin kana nan kaya masu mugun kyau na Yan gayu Riga me dogon hannu me tafe da hula bata da nauyi Sam sannan ya sauke hular a bayansa,da wandonsa fari cif cif shi ya tsuke, gashinsa ya gyara bai wani sharce ba sabo da an wani murmude sumar ne gata da yawa an kwashe bayan keyar duka ba gashi sai kadan,gefe da gafe ma an kwashe anyi wani irin gyara wajen yayi shape sosai daga tsakiya zuwa gaba sai tarin sumar me shegen tsayi an murmurdeta a tsaitsaye gyaran fuskar ya fito ras gashi da sajensa me kyau kadan sai gemunsa dan chass da shi Wanda ya kawata farar fuskarsa,abunka da me kyau gashi yana da Dan haskensa baza ace Masa baki ko wankan tarwada ba Kuma hasken ba me yawa ba,mutum gashi da cikar zati da kyan sura kana ganinsa kasan zai wahala ace ba ruwa biyu bane, yana bulbula kamshi ya fito,Islam ya Mika masa hannu suka tafa irin na Yan zamani yace let's go mun makara fa,suka fito a tare zuwa cikin motar Islam wacce ta sha wanka ta hadu suka saki kidan zamani tare da Jan motar, Rafeeq ke driving, da tambaya sannan suna duba location a waya map a haka suka Isa gidan yarin,Dan cin hanci Islam ya Mikawa masu tsaron gidan aka bude musu ana girmamasu aka basu shedar shiga ciki, suka yi parking sannan Wanda suka bawa cin hancin suka tambaya ya shiga da su har inda ake ganin Yan gidan yarin maza da aka zowa ziyara,suna ta fitowa gasu nan iri iri dattijai da Yan matasa ba kalar da Babu,Suna shiga suka fadi sunan Jamilu,Rafeeq yace Jamilu Hashim,akwai wani Ma'aikaci nan yake ya gane yace wani me kama da mata ko,ya bada Umarni aje Azo mata da Tantiriya Jamilu,Nan take Rafeeq da Islam suka Kalli juna mamaki ya kamasu,su gashi basu San waye bama Jamilu Tantiriya bare su tabbatar,gashi gidan yarin duk Wanda aka zowa ziyara a gaban kowa za ayi hira a gaban masu tsaro da sauran da ake zuwarwa ziyara suma suna ta hirar su ana jin na kowa.
Naila tana zaune ita kadai a dakinsu tayi tagumi aka zo akace Kai Jamilu fito Yan uwanka sunzo,ihu ta saki da murna tace nasan Yaya Mohsin ne,ni sanan Abba ma zai hakura ai nasan Umma ma dole zata huce,gaskiya Iyayena suna so na,gashi banyi tsafta ba haka ta fito tana uban sauri itama baki har kunne zata ga Umma,har ta fito inda ake ganin mutane Naila ta shiga zare Ido bata ga kowa nata Wanda ta sani ba,Amma kallo ya dauke mata Ido tace wai yaushe rabon da na ga mota kunga yau na hango motoci ta window,Mika tayi da hamma tace Allah mun gode maka da ka halicci Nasara ka Bawa bature ikon kera mota, ashe Kallonsu ma Rahma ne amma da kullum sai Maza kartai nake ta kallo Yan banza sai kayan wari,yau maza Kun shiga uku a wajena,ta fara zare Ido tana washe baki tace ga maza Yan gayu ba masu wari ba yau,maza mutanenmu,ana jinta ana ta dariya a wajen Banda masu tsaro duk dariyarsu sai dai suna gazawa suna danneta suke yi wai ba raini.
Kai baka ga Wanda ke jiranka bane wannan yaron baka ji wlh,Rafeeq Yana zaune yana ta danna waya ko kallon Naila baiyi ba Yana dai jin surutun kamar mace kamar namiji bai sani ba ko shine sai da Islam yace gashi fa yazo,sai lokacin Rafeeq ya dago a hankali ya Kalli Naila ya ganshi yaro ne ma matashi,da riga da wando manya na maza kayan dukun dukun wandon ma ya dan yage,Islam yasan Rafeeq bata musu lokaci zaiyi kawai shi yasa yayi magana yace kaine Jamilu?
Tace ae nine Tantiriya Jamilu mana,wajenka muka zo,ta dawo benchin da suke zaune ta zauna a gefen Rafeeq,kamar an tsira masa Allura haka ya tashi tsam ya tsaya a tsaye,cikin masu tsaron ne sunga kalar kudi harda sake mikawa Rafeeq kujera ta daban ya zauna shi daya tare da harde kafa Daya kan daya kamar yana Palon ubansa,ko kallon Naila baiyi ba,Islam ne yayi magana yace kaine Jamilu Hashim ko? tace ae a sanyaye ganin kyamar da Rafeeq ya mata,yace kaine ka je Abuja ka kashe me gidan ko? Naila