Showing 1 words to 3000 words out of 150681 words
*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 1
BismillahirRahmannir.
Kumar yanda hausawa ke fada qasar kabari bata kisa sedai ta binne binnannnniya,
Wahala,kunci,talauci,sauyin rayuwa da munin kaddara bai kashe Zaadens a rayuwar da suka samu kansu rana tsaka ba saima karfin imani dana zuciyar karban kowace irin kaddara datazo musu da hannu bibbiyu,
Rayuwa a kauye ta zuwar musu a tsananin da suke ganin kamar bazasu iyaba sbd rayuwa ce da babu ko a mafarki da suka taba jin labarinta bare tsintar kansu acikinta,
Rayuwa ce dataiwa tasu rayuwar nauyin da suke jin kamar bazasu kai koinaba zasu mace a cikinta,
Ammar da maheer sunfi kowa zarewa a cikinta musamman Ammar dayake jin kamar zai zare idan ya bude ido yaga a inda rayuwarsa take,
Bandaki kadai wani abu ne me girma dayake tsananin tsoro sbd ganin yakeyi kamar zai fada dashi,
Ranar farko da suka iso kauyen ya shiga Yana leqa masai/shadda da aka nuna masa anan zaiyi kashi tsutsotsi da kyankyason dayaga sunata yawo da motsi a cikin pool na kashi yanke jiki yayi ya some a jikin garba daya rakosa.
Cikeda mamaki da tsoro garba ya ciccibosa ya fito dashi waje yana kiran jamaa.
Su Dad da jannah ne suka iso da sauri tareda su modibbo hankali tashe kowa na tambayar lafiya.
Maheer bandakin ya nufa da sauri dan dubo abinda yaiwa rayuwar Ammar din barazana yana saka kai ya dawo Yana kasa shiga sbd jirin dayaji Yana dibansa na qaton ramin dayaga bakinsa a bude sbd shi baima leqa ba bare yasan meye shi ramin.
Ruwa masu sauyin gaske garba ya zubawa Ammar yana cewa
"Modibbo nifa inaga gamo yayi a bandakin,Aljanu sunga jan bature duk da ance a hakan ya dafe sosai ko?"
Katsesa modibbo yayi da cewa
"Aikuwa dai da alamar gamon yayi,
Maza ku kawo qauri yanzu a turara musu su duka sbd tsari"
Kawu isiya na jin haka ya kalli garba yace Maza debo jar wuta,
Juyawa yayi shima yaje daki ya dauko wasu manyan jakar dinki na kyallen atampa da wani yadi yazo ya zaro wasu daurin mgani kamar na hayaqin bori ya cika hannu ya zuba a cikin wutar da garba ya kawo suka tura su Ammar din da Maheer Harma da Dad dasu jannah a daki suka ringa turarasu.
Ammar sake somewa yayi sbd tsananin azabar hayaqi dayaji yana shigar masa qwaqwalwa da lungs Harma da neman makancewa.
Maheer tare yakeyi Yana neman mutuwa shima baisan lokacinda ya cara zabga ihun azaba ba Yana neman hanyar fita baya ko gani amma garba ya dafesa yana cewa
"Tsari ne da maganin kowane qwaro zaman kauye saida magani a jikin ku"
Jannah dayake sun dan fara sabo da azabar rayuwa da hayaqin sunsha wuya sosai amma ba kamar su Ammar din ba,
Dad ba shiri aka fito dashi sbd mutuwar da sukaga zaiyi shi da Ummah da jannah amma Ammar da Maheer suna sumewa suna tashi haka suka dannesu saida suka tabbatarda ya shigesu sosai maganin tukuna.
Tsoro da tashin hankali me tsananin gaske Ammar ya samu kansa a ciki bayan dawowansa daidai sbd ganin mutanen yake kamar rayuwar dabbobi ba mutaneba sukeyi.
Maheer ma zawo ya ringa yi amma a bayan Gida a daji sbd baya iya shiga bandakin shima tsoron tsugunawa akai yakeyi amma dayake a prison sun iya tsugunawa cikin grasses kashi da fitsari so sun dan saba,
Shima Ammar dole dajin yake zuwa duk abinda yakeji amma se garba ya rakasa sbd tsoro yakeji koina a kauyen.
Dad ma na acikin tsaka me wuya da rayuwar daya samu kansa a ciki me tsanani da wuya amma ganin Jannah ta jure ta rungumi kaddara ta saba ita datake mace kuma yarinya gashi tfara shiga damuwa da ganin yanayin da suke shiga na samun kansu a inda rayuwa zata qara musu tsanani dan haka ya rungumi jarumta ya karbi kaddarar sabuwar rayuwar da suka samu a kauyen Wanda zai sun dangana sun rungumi rayuwar sun karbeta zasuji dadinta da kuma samun nutsuwar da suka rasa ta shekarun da suka wuce dan haka ya nutsu ya shirya rayuwa a kauyen har lokacinda Allah zai kawo musu wata rayuwar kokuma har karshen rayuwarsa.
Maheer ma a hakan dole ya dangana ya amshi rayuwar duk da akwai abubuwan da bazasu iya adapting nasu da wuri ba se ahankali kamar bandakinsu har yanzu tsoro sukeji basa iya shiga,
Hakama cimarsu da sauran yanda suke gudanar da rayuwar ko zasu saba sai ahankali,
Ammar ma sbd kwanciyar hankalin Jannah yayi kokari sosai ya fara karban rayuwar kauyen Ammar ko fitsari baya iya zuwa se tareda garba wanda ya zama kamar bodyguard dinsa kuma abokinsa hakama abokin fadansa sbd kullum sai sunyi fada amma koina Ammar baya iya motsawa yaje seda garba sbd garba akwai karfi da jarumta kuma baida tsoro ko kadan dan haka ko sunyi fada Ammar yayita zaginsa da turanci haka zai koma ya nemesa su shirya dole tinda baida yanda zaiyi.
Maheer ya ari jarumta da gabacin da ko yaushe shine yake dauka a Zaadens ya fara bin su kawu daji gidan shanunsu masu tarin yawa garke Guda da ake harkar fidda nono dasu manshanu da madara da taki dai sauransu harma da kulawa da shanun da kuma kasuwancin abincin dabbobi da sukeyi na hada harawa.
Fara binsu yayi Yana shiga aikin kamar sauran yaran dake aiki yana dan samo yan kudin da zasu riqa ciyar da kansu sbd Jannah ce har yanzu me dan sanaar dake suke dan ci baa maganar sha sbd sunyi kwanaki biyu a kauyen cikin azabar kishirwa karfin suka fara shan ruwan kauyen sbd direct daga kogi ake debosu,
Da farko sunyi fama da yawan ciki da yanayi na rashin kyan ruwan kafin cimarsu kafin ahankali cikinsu da jikinsu suka saba,
Fara fitar Maheer aikin wahala da nema ya dan sake kawo sauki da sassauci a rayuwarsu sbd su modibbo tini suka gama hidimar kwana biyu dasu suka dena kowa tasa ta fisshesa.
Tinda Maheer ya fara fuskantar aikin karfi da wahala ya sake jajircewa gurin neman abinda zai hana rayuwarsu shiga kunci da takura a rayuwar kauyen cikin rufin asiri,
Ammar ya kasa sabawa yanda ya kamata duk yanda yaso kokartawa kawai dai shima Yana jurewa Yana bin garba da abokansa nasu ayyukan daji sedai ya bige da mangwaro yake debowa shi yake siyarwa a kofar gida duk da mangwaron ma baya iya hawa ya debo sedai su garba dinne suke debo masa kuma su tayasa siyarwar sbd suna kaunarsa da tausayinsa duk da Yana shan wuya a hannunsu sbd tsoronsa suke sake rikitar dashi shikuma dole ko yaushe Yana biye dasu yana zagi da turanci.
***Rayuwa taja musu a kauyen wanda lokaci ma yaja Wanda ya saka abubuwa da yawa faruwa ciki harda sake samun tsananin hadin kai da sabuwar kauna me karfi a tsakanin Zaadens,
Hakama a cikin manyan alamarin da suka faru shine AUREN DZAD DA UMMAH da aka daura akan kauna da shakuwa da kusancin da suka samu me tsanani a tsakaninsu duka da Umman data maye gurbi na uwa da aka rasa a Zaadens din,
Kaunar me girma da tsaftar dake tsakanin Umma da Jannah yasaka ta shafi duka ahalinta Musamman Ammar da kusan shima kaunar uwa da kulawan uwa yake tsananin so da buqata tin Yana qanqani shiyasa Mimi ta kasance ta maye ta cike masa wannan gurbin shiyasa rashinta kusan yafi tabasa akan kowa sai kumaa yanzu da Ummah take cike masa wannan gurbin ahankali sbd kaunarta da kulawanta Kansa kamar Miminsa.
Dukkaninsu ahankali suka sani suka fahimci ciwon Ummah Wanda sukai accepting dinta ahakan cikeda zuciya daya da kauna me girma tareda cike ahalin Zaaden da ita ayanzu datake uwa gaba daya a Zaadens dan haka ahalinsu a yanzu y dawo biyar a maimakon su hudu,
Sabuwar kauna me karfi da shakuwa me girma ce take sake gudana a tsakaninsu wanda Ammar yake sake dagewa gurin takurawa modibbo akan aiki dayakeso ya samo musu a birni shi dayake yawan zuwa binnin kuma ya dan San mutane,
Yanda yake tsananin son su samu aikin da Maheer da Jannah da Ummah zasu dena aikin azaba a kauyen yasa ko aikin gadi ko ban ruwa ko wanki da guga ne binni yanason su samu dan haka kullum modibbo ya dawo binni seya samesa da maganar aikinsu,
Ta bangaren modibbon shi Kansa yanason ya samo musu aiki me kyau koda bana office ba Kona gadin ne a manyan guri tinda sunada ilimi me girma d yawan gaske dan haka zaa samu kudi me tsoka dasu dan haka ya dage sosai Musamman dayaga da gaske sunason aikin kowane iri ne dan haka yakeson y samo musu aiki a guri daya.
Maheer ma dayaji ana neman aikin duqufa ya sake yi da nema sbd su samu abinda zasu dan samu gurin zama acan binnin idan ta kama.
#MAMUH
#THE STORY BEGINS
#BEST LOVE
#BEST ROMANCE
#LIMBAS
#ZAADENS
#NEW LIFE
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 2
Ammar tin Yana jira modibbo na zuwa neman musu aikin harya kasa hakura qagara ta saka ya fara bin modibbon birnin da kansa sbd a riqa sanin girma da zurfin ilimin dasuke dashi Wanda Banda mummunan kaddarar shigowan AZIZ LIMBA rayuwarsu da babu kamfanin daya isa su kallesama da irin ilimin da suke dashi bare dan haka dole yanzu tinda suna son koma wane aikin ne ya danne ya ringa biyo modibbon dan sugarwa kansu hakama a yanda yake gani ya kuma San iliminsu duk inda aka daukesu aiki ai a babban matsayi zaa daukesu sbd ansan samun masu irin iliminsu da experience dinsu akan aiki a banza irin haka ai bama abune me yiyuwaba dan haka yasani da gudu zaa ringa jin dadin samunsu a aiki.
Zuwansu na farko da zasuyi kallansa modibbo yayi kai tsaye kafin ya gangaro da idanuwansa kan kafafunsa da suke a tsaye kamar raken da aka ciro bata gama riquwa ba kafin yace
"Nifa idan naje kafuwana sune motata yawo nakeyi dasu me nisan gaske yanda kasan mashin din da babu burki haka suke,
Zaka iya?"
Kallansa Ammar yayi kafin ya dan hadiye yawun bakinsa daya bushe sbd ya dauka ma maganar kudi modibbon zai masa sbd yanda kasan mayu haka suke akan kudi,
Jin maganar tafiyar qasa kamar zararru a cikin rana ya sakasa hadiye yawun kafin ya bude baki kai tsaye cikin jarumta da qwallafa rai da yayi yace
"Eh zan iya indai yawon neman aiki ne ko abuja tas zamu zagaye zan iya amma zaka siya mana abinci da ruwa me kyau inace ko?"
Kawu isiya dayake zaune gefen modibbo Yana sauraronsu dago qananun idanuwansa da suke a matse kamar na yan Japanese yayi ya kalli Ammar din kafin ya tsayar da idanunsa akan wuyansa daya balain ramewa yayi tsayi kamar mariqar lema yace
"Kafin aje har ayi maganar abinci kanada kudin motar tafiyar ma tukuna Ammaru?"
Matse fuska yayi Yana qasa qasa da Murya a siqe da takaicin yanda kaf kauyen ake kiransa da Ammarun kamar wani sakarai yace
"God,Ths fools are killing me slowly"
Kawu isiya dayaji yayi magana besan meya fada ba sake maimaitawa yayi Yana zare hular shape din kwanon sha datake kansa ya ajiye gefe Yana cewa
"Idan bakada kudi ka wuce ka nema su Garba suna daji gurin qona gawayi ka shiga cikinsu kayi kunar ko hada saika samu na motar"
Modibbo ne ya katsesa da cewa
"Ni gobe zan wuce banda lokacin batawa na jiran har ayi kunan itace kwana biyu su zama gawayi a hada akai a siyar tukuna ayi tafiyar sedai ya jira wani jiqon idan zan sake komawa"
Qara matsowa Ammar yayi Yana dan kwantar da kai yace
"Modibbo idan ka tafi kilama saar a tafiyar yanzu take gwara dai ko yayane a tafi dani din zan nuna musu girman ilimin danake dashi da gudun gaske zasu daukesumu aiki fa,
Kuma a matsayin da muka taka na aiki da ilimi ana daukanmu aiki mu duka zakaga yanda kudi zai ringa shigowa kamar ba wani abu me girma ba so gwara dai a duba tafiyar,ko me kace kawu isiya?"
Gyara zama kawu isiya yayi Yana bawa Ammar din hankalinsa yace
"Bangane kudi zasu fara zuwa take ba,qaran hasken shi ilimin naku da atake zai ringa bada kudi"
Qaramin tsokin da basu jiba ya sake Yana bawa Kansa karfin gwiwan zaqewa yai musu bayanin da zai sakasu rudewa shidai ya samu su tayasu neman aikin duk da ba ilimin komai da suke dashi kansu a toshe yake kamar an narka kitse an rufe musu kan ya daskare amma kuma tinda sunada yan kudaden da zasu taimakesu gurin yawon neman aikin dole ya dorasu a kai tinda mayun kudi ne dan haka kamar wani tsohon fakirin malamin boko haka ya janyo dutsi ya zauna gabansu ya fara cewa
"Mun samu iliminmu ne bayan mun barar da dukiyar da zata gine kauyen nan da zagayensa gabaki daya kada kace ginin da kuka saba gani, infact mun saka kudin da zai siya qungiyar shanunku dubu a gurin neman ilimin...
Katsesa kawu isiya yayi da cewa
"Meye kuma kungiyar shanu?
Cikin takaicin da modibbo ya rasa na meye sbd kamar rena musu wayo Ammar din yakeyi da wannan karyar ya amsa tambayar kawu isiya da cewa
"Garken shanu yake nufi lusarin"
Zaro ido kawu isiya yayi Yana tashi zaune daidai ya kalli Ammar din ido waje yace
"Garken shanu dubu fa kace Ammaru"
"Yes sbd a cikin dukiyarmu kungiyar shanu dubu is nothing.....
Katsesa modibbo yayi da cewa
"Akace maka garken shanu ne ba kungiya ba ko?"
"Koma ya yake modibbo munada dukiya da abinda babu Wanda yasan iyakarsa da yawansa sai Allah sbd ko mu bamusan yawansa ba,
Dan haka yanzuma wuyarta dai mu samu aikin zamu Tara Harma fiyeda yawan na bayan kuma kunga wannan Karan daku a cikin duka alkhairin da zaa samu zamu ringa sammuku sosai..."
A tare kawu da modibbo suka kallesa kawu daya gama hawa da rikicewa akan zancen yace
"Sammuku??
Eh kawu kuma zaku lashi arziki sosai fa indai aka samu aikin nan"
Modibbo tsoki takaici ya sake yace
"Kai yanzu isiya sbd mutuwar zuciya da shegen kwadayin dayafi na Jibo zaka yadda da zancen a neman ilimi kawai an kashe dukiyar datai yawan garken shanu dubu,
Dubu fa,
Garken shanu dubu fa isiya"
Shiru kawu isiya yayi Yana jinjina maganar modibbo din kuma sbd kaf rayuwar fillo ma ganin yake akwai me garken shanu dubu kuwa to amma kuma kowa yasan su Zaadens din gadon wata irin dukiya sukai me yawan da shima modibbon Yana fada bai taba ganin irinta ba..
Miqewa kawun yayi da sauri ko takarmi babu kafarsa ya fada cikin gida ya kirawo kawu Jibo Yana cewa
"Jibo zo muje kaine me lissafi akan zumudin harkar duniya Ammaru yai bayani ka fada mana yaya zaayi dan dai nifa bazan yadda ayi arzikinnan sabo bada niba acikinsa dumu dumu"
Fitowa sukai tin kafin su qaraso bakin shimfidar tabarmar Jibo ya zare takarminsa ya qaraso yana kallan bakin Ammar daketa kokarin dora modibbo akan zancensa dayaga kamar baya shigarsa.
Zama sukai Jibo na jin yanda Ammar ke fadar dukiyar da sukai abaya wadda yawanta yafara zarar da tinanin Jibon ya kalli isiya yace
"Idan shawara zaku tsaya nidai ina ciki dumu dumu,
Ammaru Ni zan baka Aron kudin motar idan aka samu aikin mu ringa raba albashin."
Dukkaninsu tare suka kallesa cikeda mamaki da siqewa da takaicin yanda yayiwa kowa shigar sauri dga zuwansa,
Ammar da takaicinsu duka yakeji daurewa kawai yakeyi yana sake maida Kansa dan iska Yana musu bayanin dan su basa Aron kudin duk zaayi tafiyar harya samu aikin batareda sun gaji ba a siqe ya kalli kawu Jibon daidai Maheer ya kawo Yakuma ji abinda kawun ya fada Ammar ya kalli Maheer din cikin takaicin kawu Jibon yace
"Is he mad or just stupid?
Ajiyan zuciya Maheer yayi yana kasa cewa komai
Modibbo ya katse Gardamar kawu isiya da kawu Jibo da kallan Maheer Yana cewa
"Mahe kai kadai nake yadda da maganarka a ahalinku sbd kafi wannan me kama da rubabben kabejin zama mutumin arzikin daya San Kansa,
Fadamun gaskiya akan maganar neman aikinsu shin d gaske ne wannan dukiyar dayake fada kamar ta zamanin tarihin misra?"
Kallan Maheer Ammar yayi da sauri yana nuna masa ya taimaka masa ya qarasa dora masa su akan zancen sbd maganar gaskia sai sun qarasa mutuwa akan son abin duniyar dayake fada zaa samu su saki yan kudin da suke dashi a taru ayita neman aikin koda offer din aikin ta siyarwace su taru a siya din dai suga sun kama abin arziki sbd sukaci gaba da rayuwa a haka a cikin kauye da gwagwarmayar kauyen ba jimawa zasu tashi daga kamanninsu su koma kamar wainda aka haqo daga rami dan ko yanzu idan ya kalli wuyan Maheer daya koma kamar wuyan fanka hakama Dad gabaki daya rigar jikinsa kullum a kode kamar wani me tallan yalo ga Jannah da Ummah ma duk sunyi laushi kamar alayyahun daya kwana shi kuwa Kansa baama magana dan ya koma Ammarun da suke kiransa dashi tini dan haka ransa baci yake idan yana kallansu gwara kawai su nema aiki komai qanqantar albashinsa.
Numfashi Maheer ya sauke yana zaunawa gefen Ammar din yana kallan yanda su duka suka zuba masa ido da baki da hanci da komaima nasu suna jiran abinda zai fada
Gyara murya yayi shima ya fara jero bayani irin Wanda Ammar yaketa fesa musu harma da qari akan na Ammar din sbd yafi Ammar iya tsara zance take suka rude suka rikice gabaki kansu na neman zarewa da kuncewa.
Ammar ma zaro idanuwansa yayi akansu kawun Yana jiran jin amsarsu dashi dasu kamar zararru har gumin kuncewan lissafi suke fitarwa
Kawu Jibo da bayason sanya a harkan samu bude baki yayi zeyi magana modibbo ya taresa da cewa
"Ni zan dauki nauyin nemo aikin da dukiyata"
Da sauri kawu isiya yace
"Ai gwara dai a taru a hada kudin a tsakaninmu ayi neman aikin idan ta fashe kowa nada hannun jari a ciki kenan kawai"
Kawu Jibo da sauri ya share zufa Yana cewa
"Eh nima na yrda da hakan gwara kowa ya saka hannun jari a cikin neman aikin da neman kudin Ni hannu biyu zan saka ma"
Farin ciki ne ya mamaye Ammar da Maheer suka saki fuska Ammar na cewa
"Thank God sun hau zancen"
Rigima abin yaso zama saida Dad ya fito aka sake sabuwar shawara tukuna aka yadda akan kowa hannu daya zai saka na jarin da suke magana dan haka aka karshen magana.
Washe gari tinda safe modibbo da Maheer da Ammar sukai tafiyar cikeda zumudi.
Dad kuwa dole a ranar shine ya fita aikin da Maheer yakeyi sbd ya gaji da ganin Jannah