Showing 84001 words to 87000 words out of 150681 words
Wanda ya riga ya wuce ban ajiyesa a Raina ba sbd babu lefin da uwa zatai 'danta yayi fushi da ita matiqar yana neman rahama,
Mama baki haifeni ba amma har abada ke uwata ce da kinada naki matsayin da kika taka na uwa da ko mahaifiyata data haifeni bazata taba taka wannan matsayinba na daban sbd itama nata matsayin daban yake da babu Wanda zai taba iya hawansa sbd itace ta haifen,
Girmanki da matsayinki na uwar AZIZ LIMBA mama bazai taba sauyawaba har abada kaman yanda itama nata matsayin na wadda ta haifesa bazata taba sauyawaba,
Kinada mahimmanci a rayuwata sbd zamtowanki uwa hakama ummah nada mahimmancin sbd zamanta mahaifiya,
A gurina har gobe ke uwa ce mama da babu kamarta a rayuwar AZIZ LIMBA da Ummitah limba Dan haka mama ki wanke zuciyarki daga duk Wani tinanin da ba daidai bane akan 'danki sbd ban sauya ba bazan taba sauya miki ba."
Kuka mama keyi sosai sbd kunyar Kanta da kunyar AZIZ din sbd yama takaita maganar komai bayason a tada kowane zance,
Bata dauka AZIZ zai dauki lamarin da sauki ba sbd sanin mahimmancin Fatima a gurinsa hakama bata dauka zai sake duba ko kallanta a matsayin uwa ba.
Baice komaiba ya sake maimaita Mata tafiyarsa tareda tabbacin sayd zai saka kudi acct nata kaman yanda aka saba hakama zaa bar cash Nera da dollar akan duk abinda zai taso.
Bai yi tinanin bawa ummah komaiba sbd mama ce ta saba riqe gidan kuma itace har gobe zataci gaba da riqewa idan baya nan Dan haka taji Wani sabon kuka ya taho mata sbd duk kunya baqin halinta AZIZ ya gama tila mata shi yabarta da mugun abinda duk yake cikin ranta.
Yana ficewa Ummah yaje ya sanarwa itama kuma su Jannah na dakin amma ko juyowa batai ba bare ta kallesa harya gama ya fice yana waya.
Ummah itama tanason magana da mama amma ta kasa zuwa sbd ta Bata daman saukowa da dawowa daidai kafin su fuskanci juna Dan haka ta sake daga mata kafa.
Da yamma Jannah saukowa tayi da ummah suka tafi palonsu sbd ganin su Ammar.
Suna shigowa Ummah akan dzad idanuwanta suka fara sauka yana zaune Shima jin Ammar ya ambaceta ya sakasa dagowa yana zuba mata idanuwansa.
Qarasowa sukai suka zauna palon Maheer na gaidata cikeda farin ciki da kulawa yana tambayarta jikinta.
Amsawa tayi tana kallan Ammar daya dawo kusa da ita farin cikinsa a bayyane yana gaidata.
Shafa kansa tayi tana amsawa tareda tambayarsa yanayinsa tana sake tinanar dashi addua datace ya yawaita.
Dad ta Dan dago Wanda ya Kafeta da ido ta bude baki a natse tace
"Dad ina wuni?
Ajiyan xuciya ya sauke yana amsawa a natse tareda tambayarta jikinta ta amsa tana Dan Maida kallanta kan Ammar suna magana cikeda kulawa.
Fira sukeyi sosai hankali kwance suna jin farin cikinsu da familyn na sake cika har dare anan tayi har ishai kafin Jannah ta Rakata suka koma.
Tana saukowa daga saman lokacin karfe 9:37 na dare,
A palon qasa tana sako kai Shima yana sako kai sai a lokacin suka dawo gida.
Sayd gaidata yayi yana wucewa gaba sbd basu guri ganin irin kallan da AZIZ din yake mata.
Hanyar palonsu ta nufa da sauri tana qin bari sayd ya qarasa wucewa sbd zai iya riqeta.
Ko taku hudu bataiba AZIZ din ya riqota da hannuwansa biyu yana dagata sama ta baya ta fara yar qaramar dariya mara sauti tana cewa
"AZIZ LIMBA"
Ajiyeta yai yana juyo da ita zaiyi magana ta rigasa da cewa
"AZIZ pls"
Lips dinta yai kissing kafin ya sauke ajiyan xuciya yana zagaye cikinta da hannuwansa yace
"Zanyi tafiya gobe"
Kallansa tayi tana cewa
"Allah ya kaika lafiya ya dawo dakai lfy"
Murmushi yayi yakai fuskansa ya hada da nata ya goga hancinsu guri daya yace amin yana Dan lasan lips dinta.
Nicky wadda ta fito kitchen ta ciyo bread da butter ta koshi tana ganinsu Bata tsaya komaiba zuciya ta dibeta tayi palon su Dad tana zuwa ta kamo hannun Maheer sbd tinanin Ammar ne idonta ya rife tayo palon dashi.
Suna zuwa bude kofar Maheer da karfi ya saka Jannah yin baya da sauri daidai Maheer din na shigowa ya taddasu tsaye.
Bai Kalli AZIZ ba sbd zuciyarsa dake tafarfasa da Jannah din.
Hannunta kawai ya kama ya jata har dakinsu.
Kallan Fatma yai yace
"Ki shirya muku komai gobe tinda safe zaku wuce kauye."
Gyada kai tayi tana cewa "to"
A cikin Daren aka gama musu komai na tafiya gari na wayewa tinda safe taje tayi bankwana dasu Falaq batareda ta sanar musu tafiya zatai ba sbd su Dad da suka hanata sedai abinda Bata saniba Fatma ta fadawa fiddausi.
Babu Wanda ya sani ko tashi karfe 8 na safe akai musu bolt tazo ta daukesu zuwa Tasha.
Suna wucewa dukkanin su Dad suka sauke ajiyan xuciya suna jin kaman an zare musu qayar tashin hankali sbd yanzu sun nesanta Jannah da AZIZ LIMBA.
Ko mitina 8 basuyi da barin anguwan ba black Royce Royce din 4&4 Tasha gabansu cikin nutsuwa.
Sayd ne ya buqaci da driver yayi parking.
Yana parking AZIZ LIMBA ne ya fito daga motan a natse cikin black Fendis da shade na Versace a fuskansa dake fidda wata nutsuwa da hasken kwarjini.
Kai tsaye motar ya iso ya bude mata tareda kamo hannunta ya kamota daga ciki yabar motar batareda yace komaiba.
Sayd ne ya sallami me motar Fatma ta fito da kayansu suka koma motar take suka bar gurin yana kallan time na agogon hannunsa sbd jirgin Lagos zasu bi.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 49
Fatma dake zaune gaban motar gefen sayd kasa dogon motsi tayi zuciyarta na harbawa dan Bata dauka zai iya kaisu Tasha da kansa ba.
Jannah Kuwa kallansa ta juyo gabaki daya gefensa tanayi tareda zare hannunta cikin nasa ta Kalli Sayd da Fatma tayi Dan qasa da murya tace
"Me kakeyi AZIZ LIMBA?
Kasan ina zamu tafi ne?
Juyowa yai a natse a kame ya kalleta yana hana kansa fushi da ita ya bude baki yace
"Duk inda zakije inaga idan kowa bai saniba ke kinsan dole ne sanar dani right??
Shiru ta Dan yi kafin ta kallesa tana bude baki tace
"Dad ne ya bada umarnin tafiya na and ka sani I can't say no or bada kowane irin excuse na qin tafiyan"
Dauke kallansa yai daga kanta yana sake dago hannunsa ahankali ya Kalli time a jikin agogon dayake daure a hannunsa kaman bazai tanka ba ya bude baki yace
"Buqatan Dad din daman ki bar 4&4 ne kuma gashi kin bari"
"AZIZ" ta ambaci sunansa ahankali tana kallan hanyar da suke dauka sbd tasan ba hanyar park bane.
Juyowa yayi ya kalleta tsawon seconds baice komaiba ya kama hannunta cikin nasa ahankali ya sarqe yana cigaba da duba wayarsa.
Sake shiga tsoro da fargaba tayi ta zare hannunta tana kallan hanya tace
"AZIZ pls kayi magana mana,
Me yake faruwa ina zamu?
Fatma dake a darare tana jin maganar Jannah din wadda tayi da Dan sauti me karfi kadan juyowa tayi ta saci kallan Jannah gabanta na Dan sake faduwa sbd jin ba hanyar park suka nufa ba Dan ita batasan gari ko hanya ba.
Kai tsaye hanyar airport suka nufa Wanda a hanya Sayd ya kira kafin su isa an siya tickets dinsu Jannah din Dan haka suna isa aka iso aka dauki kayansu Banda nasu Jannah da aka bari a motan wadda aka karbeta aka wuce da ita.
Hannun Jannah na riqe a cikin nasa idanuwanta sunyi jajir hawaye ne ke cikowa ya kuma kame fuskansa tsaf ya hanata magana.
Fatma da kallon koina ya dauki hankalinta mantawa tayi da yanayin da suke ciki tanata kallanta har suka shige.
Ba Bata lokaci suka gama komai suka shige jirgi jirginsu ya daga zuwa Lagos.
Tinda suka shiga jirgi Fatma ta dawo hayyacinta fargabanta ya dawo ta fara neman inda zata ga Jannah amma Bata gantaba sbd suna guri daban itada AZIZ sayd kawai take gani da sauran mutane a zaune Dan haka tayi zuru Shiru tana jiran tsammani.
Jirginsu na sauka Lagos lafiyayyan motan datazo daukansu tafara daukan hankalin Fatma ta fara shagala tin anan ta manta da komai tafara kallan duniyar da suka zo.
Jannah fuskanta a hade take sosai batace komaiba kaman yanda Shima baice komaiba.
Wani lafiyayyan underground lodge dinsa suka isa Wanda kai tsaye kofar da aka budewa Fatma ta shiga daban da wadda aka bude Masa ya shiga da Jannah wadda hannunta yake riqe cikin nasa har lokacin.
Securities da maikatansa ne suka fito dukkaninsu suka tarbesa da barka da zuwa cikeda girmamawa me tsanani da kiyayewa musamman ganinsa tareda macen da suka tabbatarda itace matarsa sbd bai taba fita da kowace macen ba bayan yarsa da mahaifiyarsa.
Suna shiga kai tsaye masu aiki suka fara fitowa suna Jere abinci kala kala a dining da drinks cutlerys da ake jerewa kaman mutum goma zasu ci abincin.
Wani babban lafiyayyan Palo me tsananin sanyi da qamshi suka fara isowa Wanda komai yake nasa milk da golden kafin suka wuce underground din acan lafiyayyan Palonsa yake dauke da qaton makeken master bedroom dinsa Da girmansa zai iya Daukan gado uku sbd girma,
Daga Palonsa har bedroom dinsa zuwa bathroom dinsa luxuries ne kawai ke magana tako ina sbd duniya da dukiyar dake cikinsu Wani daulan ne na musamman.
Fatma dakinta itama Palo ne lafiyayyan da Bata taba ganin irinsa ba da bedroom Wanda ya sakata jin kaman duniyarta tagama samuwa Dan haka kai tsaye toilet ta nufa ta fara sauke mararta ta fito ta fada kan gadon tana lumshe ido tana jin zuciyarta na cika da farin ciki.
Jannah Kuwa bai Wani zauna ba ya shirya ya fice meeting din da yake da shi yabarta zaune a Palo tanata quncin da damuwa.
Har karfe biyu da mintina tana zaune kafin ta miqe ta nufi bedroom din ta nufi bathroom tayo alwala ta fito ta duba gabas ta tada sallah.
Tana idarwa yunwa ta sakata fitowa har zuwa main Palon anan ta samu masu aiki biyu suna sake qamsasa palon ta kallesu kai tsaye ta tambayi inda Fatma take.
Har dakin Fatman aka kaita tana shiga da mamaki take kallanta kwance take tana bacci ac na ratsa cikin lafiyayyan gado.
Wayar Fatman ce take ringin a cikin jakar hannu datake gefen gadon ta isa gurin jakar gabanta na faduwa sbd tasan bazai wuce Dad, Maheer ko Ammar ba kokuma Garba.
Fatma ma ringin din wayar ne ya tadata baccin ta bude idanuwanta tana kallan Jannah kafin ta tashi da Dan sauri tana rarumo wayar ta Kalli sunan me Kiran.
Maheer ne,
Kallan Jannah tayi tace "ya Maheer ne"
Kasa amsar wayar Jannah tayi ta girgiza kai tana cewa
"Ki dauka tsoro nakeji"
Yankewa Kiran yayi ba Bata lokaci Wani Kiran ya Kuma shigowa.
Saida Fatma ta sauke numfashi ke karfi ta daidaita nutsuwarta kafin tadauka cikin nutsuwa tace
"Ya Maheer ina wuni"
"Lfy kalau,Yaya hanyar?
Kun isa Kuwa?
Yaya su modibbo?
"Lafiya kalau alhmdllh amma bamu isa ba an tsaya wani kauye ne sallah"
"Ok idan Kun isa ku kira dan mu sani tinda ba wutar Cajin wayar zaa samu ba a kauyen yanda ya kamata so idan munji dai Kun isa shikenan,
Ina Jan?
Miqawa Jannah wayar tayi da sauri tana cewa "gata nan.
Da Dan sanyi Jannah tace
"Ya gida Yaya Dad da Ammar?
"Duk lfy kalau ki tabbatarda idan Kun isa Kun kira ok??
"Ok inshallah" tace tana kashe wayar sbd kada zancen tayi tsayi ya fahimci wani abin musamman background sound din inda suke din tinda yanada saurin fahimtar abu.
Fatma saukowa tayi ta nufi toilet da wuri tayo alwala ta fito Jannah ta nuna mata inda gabas yake ta tada sallah.
Tana gamawa masu aiki biyu suka shigo cikeda girmamawa suka tambaya anan zaa kawo abinci ko abarsa a dining.
A kawo Jannah din ta bada umarni tana kallan closet din dakin Fatman wanda kayan sakawa suke Jere a cikinsa dogayen riguna da jeans da shirts da kayan bacci masu wando da daguna komai a Jere.
Da mamaki ta miqe ta isa ta duba dakyau taga hadda undies Wanda ya tabbatar mata da kafin isowansu aka saka aka zo aka shirya musu wardrobe kenan.
Abinci aka kawo musu aka Jere a table dake tsakiyar dakin tareda ruwa da fresh juice na fruits da tissues suka fice.
Fatma abincinta tafara ci tana tambayar Jannah abubuwan data kasa amsawa sbd tinanin dayake cikin kanta tana cin abinci ahankali sbd yunwa itama take ji sosai.
Dukkanin daula da luxuries da suka tadda a gidan bai dagawa Jannah hankaliba sbd ta saba rayuwa a cikinsu,a cikinsu aka haifeta a ciki ta taso Dan haka haka duk wannan bai sakata wani kalle kalle ba,
Fargabanta idan akasan basa kauye duk da su modibbo babu me waya a cikinsu sai sun fito birni ne suke waya amma suna komawa basa waya sbd basuma siya wayar ba sbd ha wutar Caji ko gurin siyan katin wayar ma.
Ci sukai suka koshi aka zo aka fidda kayan aka ake gyare dakin tas kamshi ya Kuma fara tashi me sanyi da nutsuwa.
Fatma wanka tayo ta saka doguwan riga ta zauna Palo tana Kallo hankalinta kwance Dan ita jin takeyi gwara ma da basu koma kauyen ba sbd Allah ne kadai yasan ranar fitowansu daga kauyen da sun tafi ita dai indai AZIZ LIMBA zai dauki Jannah daga har gaba zata bisu batada matsala tinda akwai aure tsakaninsu Kuma suna tsananin son juna, duk matsalarsu Ya Maheer Allah zai kawo mafitar yanda zaa ji da ita.
Jannah da duk ta kasa sakewa sbd damuwa da shakka ganin yanda Fatma a lokaci daya ta sauya ta sake tana hutawanta ta ajiye fargaba a gefe ya sakata jin yar nutsuwa sbd ta dauka Fatman zata shiga tashin hankali da tsoro Wanda zai Sakata damuwa sbd akanta ne komai ya faru.
Har yamma suna palon da dakin Fatman yake Fatma na kallanta,
Maheer y sake kira Fatma badatada yanda zatai tace Masa sun isa lafiya suna gida,
An basa Jannah sunyi magana itama ta kasa cewa komai tadai saurara nasihar kula da kanta da sukai mata tareda dalilinsu na hanata waya sbd kada AZIZ ya samu damar damunta ko shiga rayuwarta ko shi ko yarsa.
Suna gama wayar Fatma ta kashe wayarta gabaki daya sbd tsoron yawan Kiran ya saka asan basa kauye Wanda ba iya su Dad zasu shiga masifarsu ba modibbo rataye su zeyi ya tsiyayar da jininsu.
Magrib akai Wanda sai a lokacin su sayd suka dawo gidan,
Kai tsaye AZIZ ya shige bai fito ba sai bayan kusan mintina hamsin,
Sanye da riga da wando ash rugbay ya fito sai slippers na Versace kamshinsa na tashi ahankali fuskansa fresh ba alaman gajiya ko kadan a tare dashi.
Har daki Jammy me aiki ta isa ta sanar da Jannah dining is ready.
Fatma na Jin Hakan ta buqaci a kawo mata nata daki.
Jannah dake son magana dashi daman fitowanta wanka kenan Dan haka shiryawa tayi ta saka Vneck doguwan riga har qasa me santsi ba nauyi a cikin kayan dakin Fatman ta fito a natse ta nufi dining din.
Tana isa dining room din bai riga ya iso ba babu kowa sbd sayd ma yace a jera Masa nasa a palon dakinsa sbd bawa megidansa daman cin abinci da iyalinsa.
Juyawa tayi kai tsaye zata bar dining room din daidai yana sako kai ta tsaya da sauri tana Dan yin baya da karfi sbd Bata dauka shi bane.
Riqota yayi a natse ganin yanda tayi bayan da karfi ya dawo da ita har tana Dan fadowa jikinsa ya kalleta da idanuwansa da sukai haske suna fiddo da asalin kyansa na kwarjininsa ya gyra mata tsayuwa a jikinsa hannunsa daya na zagaye da ita ya saka dayan hannun ya gyara mata wuyan rigarta gefe daya daya sauka sbd Dan fadin da wuyan ya mata ya bude baki a natse da yanayin da kusan ita kadai ce take ganinsa a cikinsa yace
"Saurin me kikeyi bayan ganinan tafe da kaina na karbi fadan naki"
Da Wani irin Kallo ta dago ta kallesa tana turesa zatai magana yace
"Ok ok naji ba ni kike nema ba Jannah zad"
Sake turesa tayi tana cewa
"Ni gida zan koma bazan iya batawa Dad rai ba,
Ransa zaiyi mummunan baci idan ya San ina tareda K....
Kasa qarasawa tayi tana qasa da ido,
Mannota jikinsa yai da Dan karfi yana murmushi yakai bakinsa yayi kissing hancinta a natse kafin yana murmushi yace
"Bazaa batawa Dad rai ba sbd zan kula Masa da princess dinsa fiyeda kowa"
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 50
Zamewa tayi tana cewa
"No AZIZ"
fuskansa ya rankwafa ahankali yakai bakinsa a kafadarta da wuyan rigarta ya sake sauka ya sauke mata kiss me sanyi tareda kuma hannunta ya jata zuwa dining ya zaunar da ita ya zauna Shima.
Jammy dake tsaye tin dazu a dining room din kanta a qasa tana jiran tai serving nasu matsowa tayi a natse kanta a qasa tafara serving na Jannah kafin tayi nasa ta juya ta fice.
Brown beef and veg spaghetti ce sai meat balls da burger bread da salad da Turkish tea me zafi sosai da aka hado Masa.
Abincin ya fara ci a natse yana kallanta yanda take cin abincin a hankali tareda meatballs.
Komai nata Daukan hankalinsa yakeyi yana Jin kaman ko a yanzu data gama zama macensa bai gamsu ba so yake ta kasance shi kadai ne yake da iKon ganinta ba kowa ba,
Tissue ya dauka ya goge bakinsa ahankali bayan ya gama cin abincin,
Zuba mata idanuwansa yayi yana Kallo a natse harta gama cin abincin ta dauki tissue itama ta goge baki taqi kallansa har lokacin sbd tanajin idanuwansa akanta.
Miqewa yai ya kama hannunta suka fice daga dining room din zuwa Palonsa.
Suna isa zaunawa yayi tareda zaunar da ita gefensa yana sake sarqe hannuwansu ya dauki wayarsa dake haske alaman kiran dake shigowa.
Falaq ce Dan haka ya dauka a natse yana cewa
"Barka da dare Ms Falaq Aziz"
Dariya Falaq din tayi me sanyi da farin cikin samun daddynta ya dawo daidai yanda take fata tana cewa
"Barkanka the great AZIZ LIMBA"
Murmushi yayi me sanyi yana cewa
"Yaya Ummanah da mamanah?
Yaya Dad din zaadens da kowa da kowa?
"Kowa lfy daddy amma ni dai nayi missing Jan"
Kallan Jannah din yayi wadda ta juyo ta kallesa da ido a bude sbd tinanin ya akai Falaq tasan suna tare.
Wani zancen ya kama Wanda Falaq din ta ringa Masa surutu da labari kala kala har tsawon lokacinda sallah ishai yayi Dan haka ya bawa Jannah wayar ya miqe ya fice.
Falaq na Jin Jannah tahau murna da labari kala kala ta sauka har qasa palon su Dad ta gaidasu Jannah na sauraronta ta Kuma jiyo muryansu take taji sanyi yar rufeta.
Fiddausi aka bawa wayar itama suka hau fira har yadawo suna wayar ya karba yai