Showing 81001 words to 84000 words out of 150681 words
Dzad ce ba da Aurensa akanta sedai ta sanar masa duk abinda Danta ya yanke akan aurenta shi zatabi dan hakane ma ya maidata sama dauketa daga bangarensu.
Suna gama cin abinci magani aka sake bawa Jannah Tasha suka dan zauna fira sama sama itama ta daure ta zauna har kusan after 9 kafin ta miqe ta koma daki Fatma na bayanta tana dan waskewa da hana a gane tafiyan Jannah din daya sauya.
Suna isa daki ta tube ta nufi toilet daqyar ta sake iya shiga ruwan zafi da kanta ta hawayen azaba tagama tayi wanka ta fito jikinta a tsananin sanyaye.
Zaunawa take kokarin yi fiddausi ta shigo dakin ta sanar da ita dr taxo zata sake dubata.
Faduwa gabanta yayi sbd tsoron kada wani a cikinsu Maheer yaji tinda ba amfanin zuwan likita da dare dubata.
Rigar bacci Fatma ta dauko mata me dan kauri mara tsayi ta bata ta saka ta sako dogon hijab tana cewa suje can batason dr din ta shigo Nan.
Daqyar ta isa dakinsu fiddausi acan Dr din ta dubata falaq bata dakin tana gurin Ummah dataje sake dubowa.
Suna fitowa daga dakin Nicky ta fito daga dakinta idanuwanta da suka fada sosai cikin kwana biyu akan Jannah din tana kallanta zuciyarta na jin kaman ta kamota ta rataye a bene ta mutu,
Jannah da bata lura da ita ba gaba daya tana kokarin sauka aka bude dakin Ummah AZIZ ya fito.
Fiddausi juyawa tayi Dr kuma daman ta sauka,
Idanuwansa akan Jannah din Yana kallanta ya nufota Yana isowa ya kama hannunta ahankali yakai bakinsa yayi kissing ahankali Yana saka hannu goshinta ya taba yaji Yana cewa
"Kina jin sauki??
Ko a sauya wasu doctors din?
Ya kikeji yanzu?
Akwai sauran zazzabi da ciwon haryanxu ne??
Girgiza kai tayi tana dagowa ta kallesa a narke.
Hancinta yakai bakinsa ahankali yaji kissing Yana daukanta cak dan sauka da ita sbd bazata iyaba ya Sani.
Suna barin gurin Nicky ta silale qasa a inda take tana dora hannu akai ta kurma ihun daya rikita gabaki daya gidan kowa ya fara fitowa hankali tashe ita kuma take wani irin Amai yazo mata bayan ihun.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 47
Sake yunquro mata amai me karfi yayi ta miqe da sauri kafafunta na rawa ta nufi dakinta tana isa toilet ko qarasa isa inda zatai aman bataiba ya kufce mata ta zube gurin a qasa tana fesawa da karfin gaske jikintsa na rawa.
Firdausi da falaq ne suka fito cikin tsoron ihunta kafin Ummah itama sbd fargaban idan ba wani abin ya samu wani ba,
Madam sisi ma dake palon qasa tana wani aikin da gudu tayo saman tana rawar jikin jin ihun uwar dakinta.
AZIZ daya haye nasa saman da jannah a jikinsa ko jin ihun sosai beyiba bare ko yaji a yanzu daya saba da haukar kowa a gidan baya daga hankalinsa.
Madam sisi ce tabi Nicky dakin da sauri tana nufar toilet ta shiga jin irin yunqurin amai datake me karfi da nishi.
Kamata tayi cikin kulawa ta nufi ruwa da ita ta kunna mata tana wanke jikinta da fuskarta kafin ta daga idanuwanta da sukai jajir ta a wahalce tace
"Kiban towel kawai nayi wanka"
Da sauri sisi ta dauko mata ta bata tana juyawa ta fice.
Wanka tayi da ruwan dumi sossi sbd yanda taji zazzaɓi na rufeta sosai ga kuma ciwon rai da baqin cikin dayake lullube da ita.
Tana fitowa kaya masu kauri ta saka tana hayewa gado sbd zazzaɓi.
Firdausi da falaq dake bayanta lafe ne suka shigo dan dubata jin sisi tace ba lafiya ga mama me kulawa da ita babu wanda ya sake ganinta ta kuma dakatar da kowa shiga dakinta dan kuwa ko Ummah har yanzu basu haɗu sun fuskanci juna ba.
Tsabar baqin ciki da ciwo ko motsawa Nicky din bataiba bare tanka gaisuwansu haka suka gaji suka fice.
Amina Madam sisi ta aiko ta gyara toilet din ta wankesa tas ta qara gyara dakin ta kunna qamshi ta kashe mata wuta ta fice tana jan kofar dakin sbd baccin wuya na take daya dauke Nicky din.
Kowa dakinsa ya sake komawa fatma data kasa zaune ta kasa tsaye sbd tsoro da fargaban azo neman jannah da bata nan fitowa tayi tana kokarin waskewa cikin su Maheer ana dan fira sama sama.
Dad ne daya kalli fatma yace
"Ina jannah?
Ko har tayi bacci ne?
Murmushin karfin hali fatma tayi tana kallan kofar dakinsu tace
"Tana gurin Ummah amma yanzu ma nake cewa Bara naje na Kirita mu shige"
Numfashi me dumi ya sauke yana dan shiga nazari kafin yace
"Eh dare yayi kije ki kirata taxo ta kwanta tunda ba lafiya ne da itaba bai kamata tana kaiwa irin wannan lokacin can cikin gidan ba ki fada mata ta kiyaye daga yau."
Gyada Kai Fatma tayi tana cewa
"Insha Allah"
Barin gurin tayi nufi daki ta saka qaramar hijab akan doguwar rigar jikinta ta nufi hnyar da zata kaita can bangaren.
Tana fita Ammar da yayi shiru baice komaiba ajiyan zuciya ya sauke sbd zuciyarsa dake jin kaman ya rasa Jannah ko a wannan Karan sbd gabaki daya Soyayyar datake masa bata auratayyar dasuke fatan hadawa bane,
Soyayyar datai masa a baya kafin zuwan LIMBA rayuwarsu ko a idanuwanta da kuma yanda take muamalantarsa daban take da komai na Jannah din yanzu,
Yana tsananin son Jannah Wanda ya Sani itace jarabawarsa ta biyu Amma a yanzu Yana jin tamkar Soyayyar ta zama tamkar qunci a rayuwarsa da kodai ya hakura kokuma yayi gaggawar mallakanta ya samu cikar buri na biyu bayan na samun Uwar da rayuwarsa ke buqata.
Maheer ma baice komaiba sbd tinda tafiya zasuyi kuma suna tafiya zaa daura auren bama buqatan maimaita zance.
Fatma na isa dakin Ummah Jannah bata can dan haka ta wuce dakin su suma harsun kwanta bata Nan.
Kasa komawa tayi ta sauko ta zauna palon qasan su Falaq din tareda zaunawa ta rafka tagumi tana adduar Allah ya kawo ko Sayd ne ta dan sanar dashi Wadda aka aikota nema.
****Yana isa Sama da ita tin a palonsa ta Zame daga jikinsa tana sauka kan kafafunta ta dan dago batareda ta kalli idanuwansa ba ta bude baki a cikin sanyi tace
"Ba tsayawa zanyi ba su Dad zasu nemeni"
Hannunta ya kama Yana kallan bakinta da yayi maganar,
dumi jikinta yake dashi sosai sbd yanayin lafiyarta Dan haka dumin dayaji a tafin hannunta ya sakasa kai hannunsa a wuyanta ya Masa wata shafa yana gangarawa ahankali har bayan wuyanta dumin na ratsa tafin hannunsa zuwa jikinsa daya karban dumin a cikin sanyi yanajin kaman nutsuwarsa na ninkuwa.
Kashe mata jiki yake sake yi da dumama jikin da yanda yake shafa asalin fatar wuyanta zuwa bayanta Dan haka ahankali ta ta Dan yi baya kadan tana juya Masa baya ta bude baki zatai magana ya rungumeta ta baya ahankali yana bude bakinsa a kan fatar kunnenta cikin Wani irin sanyi da laushin sauti me nutsuwa yace
"Abinda nakeji a xuciyana yanada yawan da kaman xuciyan ma can't take it Jannah zad"
Bata iya cewa komaiba ta Dan fara zame jikinta.
Kasa barinta yai ya sake rungumeta da hannuwansa ta bayan da Kyau yana Dan sake ajiyan zuciya me dumi a fatan gefen fuskanta kafin ya sake taba jikinta yana jin dumin jikin ya yace
"Yaya jikin?
Ya kike ji?
Akwai inda yake da sauran damuwan ciwo ne?
Kinajin fever,pain or anything daya danganci rashin jin daidai?
Girgiza kai tayi tana bude baki tace
"No kawai dai inason komawa na huta ne"
Kasa sakinta yayi tsawon mintina yana shakar qamshinta da karban dumin jikinta cikin nasa a tsayen da suke rungume cikin jikinsa kafin ya sake ta yana kama hannunta yayi kissing ahankali kafin ya dauketa cak ya fito da ita tareda saukowa da ita har qasa ya nufi palonsu da ita tayi saurin zillewa ahankali ta sauka qasa tana dagowa ta Dan kallesa idanuwanta na Dan laushi ta murya mara karfi da hayaniya tace
"Dad or Maheer koma Ammar zasu iya dukana suka ganni a Hakan,
Just go back daga nan ya isa pls"
Yanda tayi maganar fargabanta na bayana ya sakasa zubawa fuskanta ido yana mamakin tsoronta,
Sbd itane yake da bayason sakawa tashin hankali da fadan family dinta ya saka yake biye mata yana mata yanda takeso tareda Bata time datace yayi alkwarin zai Bata harsai ta samu lokacinda ya kamata ta sanar dasu komai da kanta sbd idan ya fada da Kansa ko kawai sukaji daga sama ba qaramin tashin hankali zaayiba Dan bazasu yadda ba dauka zasuyi kawai ya fada ne Dan haka ne yake dannewa Dan yi mata yanda takeso din.
Ganin yanda ya ko motsawa beyiba ya zuba mata ido ne ya sakata kama hannunsa ahankali ta juya dashi tana jansa kaman karamin yaro shikuma yana binta.
Wani qaramin waiting area ne ya rabasu da palon can cikin dama Dan haka anan ta tsaya tareda sakin hannunsa ta kallesa idanuwanta na Dan yin kalan sanyi da laushi tace
"Pls AZIZ LIMBA"
Juyawa tayi zata wuce tabarsa a gurin ya riqo hannunta daya tareda dawowa da ita baya ta fado jikinsa ahankali ta baya ya juyo fuskanta cikin nutsuwa ya Kalli lips dinta ya hadiye wasu mayun yawun da tana Kallo suka wuce maqoshinsa ahankali sbd yanda Adams apple dinsa ya motsa ta moqoshin.
Idanuwanta ta dago cikin slow ta Kalli fuskansa sedai baima bari tace komaiba ya Dora bakinsa akan lips din nata ya lashesu cikin sanyi da nutsuwa ya sake hadiye yawun daya lashi lips din kafin ya zira harshensa me dumi da kamshi ahankali cikin bakinta ya fara tsotsa a natse yana zagaye qugunta da hannuwansa cikin salon kulawa da mannota jikinsa yana lumshe fararen idanuwansa ahankali.
Tsoro da fargaba ce ya fara shigarta sbd tina me zai iya faruwa idan ta bari yaci gaba da kuma tsoron inda suke tsayen Wani zai iya zuwa ya gansu.
Zamewa taso yi ahankali sedai motsawanta ya basa daman manne kirjinsa da nata yana sake lumshe ido yana zuqan bakinta cikin wata irin salon nutsuwa Dan wata irin deep kiss yake Bata.
Rawa kafafunta suka fara yi suna kasa daukanta ta sake a gurin ya qarasa tarota jikinsa gabaki daya yana dagata sama ya Dora kan console dake gurin yana bude kafafunta ya tsaya tsakiyarsu batareda ya sake bakinta ba har lokacin.
Ta qasan rigarta ya sako hannunsa daya yana shafa tin daga kafarta ahankali cikin Wani irin salon daya sakata qanqame kansa tana sauke numfashi me karfi daya kufce mata Wanda ya saka nutsuwarsa sake sauka yabi cinyarta da shafa yana yin sama da hannun har zuwa sama cikinta Wanda yayiwa mararta shafar data sakata yin baya ya samu damar sake sama da hannunsa yana shafa saman lace bra din datake jikinta.
Jin irin yanda komai yake Kara daukan zafi ya sakata Dan zamewa tana ciko idanuwanta da hawaye ta bude baki tace
"AZIZ"
yanda take ambatar sunansa a ko yaushe da Wani irin sanyi da nutsuwa yake sake kashesa amma sanin Batama warke ba kwata kwata ya sakasa rungumeta kawai ya kyaleta sukai mintina ahakan yana samun nutsuwarsa a jikinta kafin ya saukar da ita qasa ya gyara mata rigarta yana sake Rakata har kofar palon kafin ta shige shikuma ya juya.
Tana isa tsakiyar palon Maheer na fitowa yana waya zai kawowa Dad wayar.
Daga dad din har Maheer juyawa sukai suna kallan hanyar data shigo ahankali.
Garba sake zaune tareda Dad miqewa yayi yana kallan hanyar Shima sbd tinanin AZIZ LIMBA ne zai shigo.
Ganin yanda suke kallan bayanta ya saka gabanta Dan faduwa ta dakata tareda juyawa ahankali ta Kalli bayanta taga babu kowa.
Dawo da kallanta tayi kansu tana kasa qarasowa daf dasu ta bude baki tace
"Dad,Wani abu ya faru ne?
Kallanta Dad din yayi kafin yayi magana Maheer yace
"Qamshin AZIZ LIMBA ne yake biyowa bakiji bane ko me?
Ammar daya iso daidai maganar Maheer din Jannah din ya juya yana kalla wadda zuciyarta ke bugawa ta bude baki a cikin nutsuwa tana kokarin riqe nutsuwarta tace
"Banji ba kila kofan Dana bude ne na shigo"
Ammar Wanda kai tsaye qamshin yake shigar Masa hanci daga jikinta kuma yake jiyosa zuba mata idanuwansa yayi gabaki daya yana kalla itama juyowa tayi ta kallesa a sanyaye ta sauke kanta tana nufar daki sbd kada qamshin yaci gaba da tashi a jikinta.
#MAMUH
KUYI HKR YAU ASIBITI NAJE TIN SAFE WLH ACAN WAYANA TA MUTU BA CHARGE.
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 48
Tana shiga daki rufo kofar tayi tareda jingina jikin kofar tana sauke ajiyan xuciya tareda rife ido tana jin jikinta na sanyi da damuwan yanda familynta zasuyi idan suka San AZIZ LIMBA haryanzu mijinta ne.
Fatma da har ta kwanta jin shigowan Jannah din ya sakata bude idanuwanta tana tashi zaune sanye da riga da wandon bacci masu santsi ta Kalleta tana cewa
"Su Dad sun ga shigowanki?
Gyada kai Jannah tayi tana kasa magana sbd damuwan dataji duk ta rufeta akan familynta da Bata taba iya boyewa komaiba.
Toilet ta wuce ta Dan yi abinda zatai ta fito tayi Shirin bacci itama kawai ta kwanta gefen Fatman tana Daukan remote ta Dan rage AC sbd zazzabin da har lokacin tana Dan jinsa a jikinta.
Rife idanuwanta tayi tana adduan bacci idanuwanta a rife sbd baccin datake son ya dauketa tinani yabar kanta.
Fatma ma komawa tayi ta kwanta tana shigewa lallausan bargo ta rife rabin jikinta tana rife idanuwanta itama.
Washe gari da safe koda Fatma ta tashi an sake kawo sabbin masu aiki an kawo musu sbd kula da komai nasu Dan haka ko data fito sayd yace ta koma sun dena kowane irin aiki.
Dawowa tayi ta sake komawa baccinta hankali kwance daman Jannah har lokacin Bata farka ba sbd Batama da cikakkiyar lafiyan cewa zatai Wani aiki.
Kusan dukkaninsu babu Wanda ya tashi da wuri sbd anriga anyi replacing nasu da maikata sabbi tini Dan haka ko sun tashi babu abinda sukeyi.
Karfe 10 Jannah ta farka Dan haka toilet ta nufa ta yi brush da toothpaste me tsadan gaske a cikin dukkanin siyayyar da akai mata da familynta.
Wanka tayi ta fito daure da towel ta zauna gaban mirror ta Dan shafa mai kadan da body spray masu sanyi da tsada ta miqe ta saka kaya.
Doguwar riga ta saka mara nauyi sosai purple daidai nan Amina ta kawo mata breakfast dinta dakin Wanda fiddausi ce ta bada umarnin abinda zaayi mata a breakfast din.
Zaunawa tayi taci abincin kadan tana gamawa Dr ta iso dubata.
Fiddausi ce taxo ta sanar mata da zuwan likitan Dan haka ta miqe suka fice can dakinsu fiddausin aka Dubata likitar ta tabbatarda ta samu sauki yanda ya kamata basai ta sake zuwa ba.
Dr na tafiya ta fito tai dakin Ummah.
Tana shiga Umman na zaune tayi Shiru ba komai ba kowa.
Da kulawa ta isa gurinta tana Kwantawa jikinta cikeda kauna da shaquwa tace
"Ummah ina kwana?
Murmushi me sanyi da farin cikin ganinta umman tayi tana cewa
"Lafiya kalau,Yaya jikin naki?
Kinji sauki?
Yaya su Ammar Shima dai ya warware ko?
Nauyin tambayar taji daga bakin umman duk da bawai umman tasan komai bane Dan haka cikin Sanyi ta amsa tana dorawa da cewa
"Ammar duka munyi kewanki ummah"
Murmushi umman ta sake yi tana cewa
"Kewa kuma bayan muna gida daya"
Shigowan falaq ne tana isowa da sauri itama ta kwanta jikin Jannah tana cewa
"Good morning my Jan"
"Morning Falaq Aziz,kin tashi lfy?
Amsawa Falaq tayi tana gaida ummah wadda tinda safe sun gaisa sakewa takeyi.
Fira suka fara saiga fiddausi itama tayi joining suka debewa ummah kewa sosai wadda mama dake dakinta tana jiyo hayaniyar fiddausi da Falaq din suna ambatar umman.
Ajiyan xuciya me zafi da karfi mama ta sake sakewa a karo na babu adadi tin shekaran jiya zuwa yau batareda lokaci yaja ba a cikin kwana hudu zuwa biyar abinda take ta yiwa fada da yaqi da tashin hankali ya faru ya tabbata,
Batareda anje koinaba Abinda take tsananin tsanar ya faru ya faru,
Bayyanar Fatima ga AZIZ ya take matsayi da sunanta na mahaifiyarsa,
Ta rasa AZIZ din sbd ya samu mahaifiyarsa,
Ta rasa dukkanin girmamawa da matsayinta a idanuwan duk Wanda yake gidan sbd anga mahaifiyarsa ta asali,
Bayyanar Fatima ya saka kowa a gidan sanin ba itace asalin uwarsa ba,
Kaman yanda kowa ya sani duniyama a qanqanin lokaci zatasan batada matsayin komai a gurinsa da rayuwarsa face uwar riqon kanwarsa data tayasa renan kanwarsa har rasuwarta,
Shikenan ta rasa matsayinta,
Girmanta,
Nasabarta,
Karfin ikonta da cikakkiyar damarta na matsayinta uwa mahaifiyar AZIZ AY LIMBA,
dukkanin yaqinta yafadi a Banza,
Batasan yaushe da kuma wane lokaci Allah ya saka mata tsananin kishin 'dan nata ba amma dai tasan tafara tsanar kowa ya rabesa ya Rabata da shine a lokacinda taga zai iya tsananin son Wani halittar bayan ummitah data rasu da Falaq sai ita,
Ta tsani kowa ya shigo rayuwarsa ne bayan data ga irin zafin son dayakewa Jannah Wanda bai fada ba amma taga Hakan,
Taga yanda zai iya bada ransa akan Jannah zad tinda har Ya iya karban zuciyar dan uwanta a lokacinda tasa yar take kokarin barin duniya ya zabi hakura ya rungumi gawar yarsa akan ya raba Dan uwan Jannah da zuciyarsa,
Ya zabi Daukan kaddara bayan ga zuciyar Wanda suka dauka ta mahaifiyar Falaq din a Banza an Masa tayi amma ya qare da inganda rayuwarsa.,
Idan zai iya Hakan akan Jannah to tabbas zai iya fifitata akan kowa da komai ita kuma Bata renesu ta zama uwarsa Dan ya zama na wata mace.
Hawayen baqin ciki me tsanani ne suka gangaro mata sbd ayau gashi tana gida daya da AZIZ din ya ajiyeta ya zabi mahaifiyarsa,
Kukan tsananin baqin ciki ta sake tana jin zuciyarta na mata ciwo sbd akan AZIZ da Ummitah ne Bata taba baqin ciki ko kukan rashin haihuwa ba musamman ummitah datake mata kallan itace uwar data haifeta.
Kuka takeyi sosai tana jin Wani irin zafi a zuciyarta Dan Kuwa tasan matiqar Fatima na nan AZIZ ya gama zama Dan ta Dan bazai taba zabarta yabar mahaifiyarsa ba.
Knocking kofar dakinta akai ahankali tareda budewa ya sako kai a natse cikin kamewa da nutsuwa.
Dagowa tayi ahankali tana goge hawayenta batareda barin ya gani ba duk da fuskanta ta gama nuna halinda take ciki.
Zaunawa yayi inda ya saba zama idan yazo gaidata ya Dan dago ahankali cikin nutsuwa da girmamawa ya gaidata.
Amsawa tayi da Dan sauri cikin sanyin ganinsa.
Cikin girmamawa yanda ya saba batareda ya dawo da komai bayaba yace
"Mama tafiya zanyi gobe inshallah ba buqatan komai ko?
Numfashi ta sauke me sanyi tareda dago kai ta kallesa idanuwanta akan qin kallanta da yayi ta bude baki da murya me cikeda damuwa tace
"AZIZ kana fushi dani ne?
Dagowa yayi ya kalleta cikin girmamawa da nutsuwa ya bude baki yace
"Mama ke uwata ce bazan taba fushi dake ba,
Abinda kikai kuskure ne