Showing 114001 words to 117000 words out of 150681 words

Chapter 39 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9062

bata gaban kishiya yar asali
( wannan zumar Ga mata wanda kishiya ta shiga gabansu mijinki baki gane kanshi ya fifita yar uwarki akanki baya son mu’a mala dake ko wadda mijinta ke biye biye yar uwa kukanki yazo karshe duk kikayi amfani da ita duk machen da yayi sex da ita zaijita salab kamar dusa don haka aji tsoron Allah banda wanda suke zaune lfy da kishiyoyinsu)
5. End of discussion powder
( wannan garin karshen zance kenan hajiya oga ya taba miki kukan agwagwa ko mussoshi 😁to ranar duk da kika sha wannan hadin garin hajiya sabbatu sai kin rufe mishi  baki ihu da kururuwa ba sauki kuma garin wata 7 yake ajiki yana aiki )

Hajiya karki bari wannan promo ya wuceki 25k ne promo saboda sallah 12k kacal

TikTok: Zuzeam.ventures5
Instagram: Zuzeam_ventures
WhatsApp: 08144015291

*********
Nurse ce taxo ta sanar dasu Ammar ya farka Dan haka miqewa sukai dukkaninsu suka fice zuwa gurinsa har lokacin zufane ke jiqa rigarsa sosai yana Jin kaman jininsa na hawa yana qara hawa.

Maheer Kuwa rasa tinanin yi yayi sbd dai ta gama tabbata ciki ne a jikin Jannah yanzu Kuma tana sake Shirin tabbata cikin na AZIZ LIMBA ne ko me?

To tin sunada aure a baya aka samu cikin ya boye ya kwanta se yanzu yake bayyana ko me sbd baiga ta inda AZIZ din zai iya lalata musu 'ya ba harda ciki,
To yaushe ma akai Hakan?
Suna ina ne su harya samu kebewa da ita bayan sun kasa sun tsare sun Hana haduwansu bare alakarsu.

Idan cikinta wata uku ne ai a lokacin tana kauye kenan.....

Wani numfashi me zafin gaske ya sauke yana Jin yana buqatan karya kafafun Jannah da Fatma din kafin yaji komai Dan Kuwa wlh sai anfada Masa tayaya ma zaace AZIZ LIMBA ne uban 'dan cikin Jannah.

Dakin Ammar din suka iso Dad na tinanin da Maheer ke yi suna shiga suka watsar da tinaninsu suna qarasawa gurin Ammar din da sauri Wanda yake zaune Shiru ya zabge yayi fayau a Dare daya kaman ba Shiba,

Ummah ya zubawa idanuwansa wadda ta iso gurinsa tana zaunawa gefensa ya ciro hannunsa ahankali cikin rashin kuzari ya miqa mata ta kama cikeda kauna da kulawa tana Jin idanuwanta na cikowa da hawayen tausayinsa,

Shi kansa cikowa idanuwansa da sukai jajir sukai yana Jin inama kowa zai hakura ya bar Masa Umman ya tafi ya Gina sabuwar rayuwa daga shi sai ita sbd ya gaji da komai a yanzu Kam hutu da nutsuwan ruhi na kwanakin da suka rage Masa yake nema.

Dad da Maheer zuba Masa idanuwa sukai cikeda tsananin kulawa da kauna me karfi suna Jin jikinsu na sanyi da yanda ya kasa kallan ko daya daga cikinsu idanuwansa na bayyanar da gajiya da gazawa da rayuwan gabaki dayanta.

Dad ne ya qarasa yana zaunawa dayan gefen Ammar din ya dafasa a natse yana bude Baki yace

"Ammar Yaya jikin?
Ka bamu tsoro da halinda ka shiga,Allah ya karemu daga sake ganin irin wannan mummunan yanayin"

Cikin sanyin da ya saka jikin kowa sanyi da mutuwa Ammar din ya bude Baki a natse da qaramin sauti yace

"Amin" daga amin din bai sake cewa komai kaman yanda kowa ma yayi Shiru ya kasa cewa komai Saida Shirun yayi yawa Maheer Shima ya matso yana Masa sannu yana kallan fatma yace

"Hada Masa abinda zaici kafin yayi brush da sallah."

Miqewa Fatma tayi da sauri tana komawa dakin da Dad yake ta dauko basket na abincin da aka ajiye sbd Ammar din.

Maheer Kuwa shine ya kama Ammar din Wanda baida karfi sosai sbd karfin nasa bai dawo ba suka shige toilet.

Brush da wanka Ammar din yayi da ruwan zafi masu zafi jikinsa ya sake karfinsa ya Dan dawo ya goge jikinsa da towel din da aka kawo Masa tareda kaya tin daga gida ya saka riga da wando mara tsayi ya fito yayi sallah duka a natse ya koma bakin gadonsa ya zauna sai a lokacin ya dago ya zubawa Jannah idanuwansa yana kallanta batareda yace komaiba,

Jannah da tinda ta shigo ta kasa kallan Ammar din kunya da takaicin Kanta take ji data basa hope a karo na biyu bayan zuciyarta Bata cire Wanda shine yake cikeda ita ba gashi yanzu sun sake dawowa inda suka bari a baya ciwonsa zai iya tashin da zai sauya rayuwansa gabaki daya.

Dad da Maheer tsoronsu ciwon Ammar din dazai tashi daya sake tabbatarda da gaske cikin ne a jikin Jannah,

Abinda basu sani ba Ammar din ya riga yama San waye uban cikin sbd ya ga Hakan da idanuwansa da baya buqatan Jannah ta bude Baki ta fada waye me cikin,

Ajiyan xuciya me sanyi Ammar din ya sauke yana dauke idanuwansa daga kan Jannah din ya koma baya ahankali ya kwanta yana rufe idanuwansa Ummah ta rufe Masa jikinsa tana Hana kowa damunsa sbd babu abinda yakeso a yanzu kaman Shirun.

Haka sukai jigum jigum Shiru babu me abin fada zuciyoyi babu dadi Daci da ciwon Rai zalla tako ina.

Jannah ce ta zame tafice dakin ta koma waje ta zauna tana dafe goshinta sbd Kanta dake neman bugawa sbd a dakin Shiru kawai kowa yayi amma itace duka sanadin bacin Rai da quncin kowa tin farko haryanzu da ake cikin wannan halin.


Haka suka wuni a asibitin babu wani magana me Kyau dake shiga tsakanin junansu gabaki daya sbd Ammar kwata kwata bayason magana baya son rabar kowa bayason kallan kowa zuciyarsa tayi sakayau bayajin nauyin ko ciwon komai haka yake jinsa kaman sabon mutum din da aka Halitta ayau din,

Baya ganin laifi ko Jin zafin kowa kawai kansa ne yake gani Mai laifin daya kasa bawa zuciyarsa da rayuwansa damar samun sukuni da nutsuwan data kamacesa tin farko bayan rasa mahaifiyarsa,

Ya bari kunci ya mamayesa ya bawa duhu daman gauraye rayuwansa dayake ganin babu hasken dazai haskakesa saina Jannah da ahalinsa,
Ya rasa kowane irin hope na rayuwa da kwanciyan hankali da nutsuwansa ya kwallafasu akan macen da Bata taba Masa kallan masoyin daya sadaukar da kansa gaba daya akanta ba kallan Dan uwan da bazata taba iya zaman aure dashi ba take Masa gashi a karo na biyu ta sake zabar waninsa akansa Wanda a yanzu Kam komai ya qare yazo karshe take dukkanin abinda yake zuciyarsa yaji yana narkewa yana sauka daga kirjinsa Wanda a yanzu yake jinsa empty sbd Jannah ta riga ta zama macen AZIZ LIMBA Wanda ya gama mallakanta cikakkiyarta mace,

A yanzu Jannah Zad macen waninsa ce,
Jannah Zad a yanzu uwa zata zama wadda daga yanzu data dauki cikin wani ya gama samun iyakarsa da har abada ya tsaya anan bazai taba wucewaba sbd bawa rayuwansa daman samun sukuni da farin cikin daya rasa,

Ya sani haqqin Rai ne ke bibiyansa Wanda yake fatan zai samu nutsuwa ta hanyar yadda da Hakan sbd samun warwarewan damuwa da quncinsa daga ubangijinsa Dan haka Ayau shi Ammar Zad ya hakura da dukkanin rayuwansa ta baya ya shafeta ya rungumi kaddararsa zai bawa kansa damar Dora sabuwar rayuwan daya kamata ya Dora tin a baya.


Da yamma Ummah da fatma da Garba suka bar asibitin suka koma gida Wanda ummah dole tayiwa Jannah na zuwa gidan suna isa gidan Ummah Bata iya barin kowama yasan mugun tashin hankalin Da suke ciki ba na ciki a jikin Jannah sbd ganin sirrinsu ne da bai kamata kowama yaji ba ciki Kuwa hatta AZIZ dayake danta da Mama datake uwar AZIZ din Kuma aminiyarta sbd ita tama Fi Jin kunya da baqin cikin AZIZ da mama suji sbd mutuncin Jannah din dazai zube a idon tsohuwar sirikarta da shi AZIZ din tsohon mijinta suji cikin da baa San ina ya fito bane a jikinta Dan haka sukai Shiru babu Wanda yasan me yake faruwa a cikinsu.

AZIZ na gidan bai fita koina ba daman jiran dawowansu yake idan Bata dawoba yana niyar tafiya asibitin ya dawo da ita gida da kansa sbd ita tama Fi Ammar din da Dad buqatan hutu da nutsuwa suda suke kwance a gadon asibitin amma itace ya kamata a bawa dukkanin kulawa ba su ba.

A dakin Ummah tayi wanka tai sallan laasar tana idarwa fiddausi takawo mata fruits da abinci ta lallabata taci fatma taxo da maganin da AZIZ din ya Bata tin a asibitin Wanda na Jannah ne ta ringa tabbatarda Tasha akan lokaci.

Maganin Tasha tana gamawa ta kwanta a farkon gadon Ummah tana dan lumshe idanuwanta tareda Dan rage AC.

Ummah na kitchen tareda su fiddausi da Kanta takeson ayi aikin abincin da Ammar zaici sbd gabaki daya ya kasa cin komai baya iya cewa komai Shiru kawai yakeyi yana sauke ajiyan xuciya akai akai tace ya yawaita ambatar Allah zai samu nutsuwan xuciya Dan haka duk ya numfasa saiya ambaci Allah Dan haka yaji yana samun sukuni da nutsuwan xuciya ahankali ahankali Dan haka ya sake Jin baya buqatan yawan maganar Dan Hakan yana sakasa Jin yana sake dawowa daidai Wanda tin a shekarun baya ya kamata ace ya samu Hakan da kila baiyi batan da yayi ba a rayuwarsa.

Bude kofar dakin akai a hankali cikin nutsuwa tareda shigowa da sallamarsa me dadin sauraro ya rufe dakin qamshinta Dana AC daya gauraye dakin na shiga hancinsa take yasan tana dakin Umman Dan haka yakai idanuwansa bangaren lafiyayyan makeken gadon umman yana saukesu akanta.

Gurin Ummah yazo sanar da ita cikinsa dake jikin Jannah din sbd ta kula da ita a cikinsu Dad din da bacin Rai zai iya sakasu wani abinda zai taba lafiyan nasa arzikin sedai bai samu Umman ba yayi nasarar samun Jannah din data qi barin ya ganta tinda suka dawo kaman tasan neman zarewa yake rashin sanin halinda take ciki.

Qarasowa yayi har inda take din ya tsaya akanta yana zubawa kyakkyawan fuskanta nasa fararen idanuwan yana kallanta kaman ya dauketa ya tafi duniyar dazai rayu da ita su reni babynsu.

Jin tsayuwan mutum a Kanta ya sakata bude idanuwanta ahankali tana saukesu akan fuskansa tana kallansa a kasalance sbd Dan zazzabi da rashin karfin dayake tattare da ita na Kukan datake yi tin jiya da Kuma damuwan data ciketa me tsananin rashin sanin wane hali da matakin familynta zasu dauka akanta da Kuma damuwan halinda ta saka Ammar Wanda kila qarasa rasa kansa zaiyi duk da ya kasa cewa komai ko kallanta bai sake ba.

Durkusawa yayi ahankali gabanta yana miqa hannunsa na dama ya shafi fuskanta cikin wata irin sanyayyan kulawa da kauna me tsafta.

Rufe idanuwanta ahankali tayi tana budewa akansa wasu hawaye masu dumi suna gangaro mata na tausayin Kanta da babynta da ubansa baima San dashi ba,

Idan su Dad sukace cire mata cikin zaayi batasan tayaya zata iya sake kallan AZIZ dinba duk da bai San dashi ba kaman yanda Kuma batajin zata musawa su Dad din sbd sanyaya zuciyarsu data kuntata,

Wasu zafafan hawayen ne suka sake sauko mata sbd tana kaunar cikinta har cikin ranta tana Kuma tausayin AZIZ da ita Kanta.

Hawayenta AZIZ din ya miqa hannunsa ya shafo yana kalla zuciyarsa na sanyaya da damuwa ya saka hannuwansa biyu ya tada ita Zaune ya dauketa yana komawa kan sofa da ita ya zauna ya zaunar da ita akan cinyarsa ya fara share mata hawayen da tissue daya dauka a gefen sofan dasuka zauna kan qaramin side table.

Hannunsa ta riqe da nata tana kallansa jikinta a sanyaye zuciyarta na ingixata akan ta fada Masa abinda take dauke dashi amma tana shakkar fushin su Dad idan suka San ta fada Masa Dan haka ta zuba Masa ido tana sake tsiyayan hawayen damuwa.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 67

*_ZUZEAM VENTURES_*
Best kayan Mata
08144015291
*NEW ALERT*
*END OF DISCUSSION PACKAGE*
~25k~ promo 12k
Barka da Sallah promo pack
1. Tabajen kankana da fruit
(Mai saukar da niima nan take ta kara miki dadi na musamman keda oga sai kunyi kukan dadi ranar )
2. ⁠gumbar chakwala dadi
(Hmm yar uwa daga jin wannan kema kinsani basai anbaki labariba wannan hadin na zallar dadi ne da ciko da gaba)
3. Turare kyauta dole
(Wannan turaren na amsar kyauta ne ina masu fama da miji mai mako wanda ba a cin kudinshi Ga shi da abun amma ba a ci to yar uwa matsalarki tazo karshe da izin Allah Sai kinci abunshi ina yan kasuwa duk kina amfani da wannan turaren sai Kinga budi da izinin Allah)
4. Zumar bata gaban kishiya yar asali
( wannan zumar Ga mata wanda kishiya ta shiga gabansu mijinki baki gane kanshi ya fifita yar uwarki akanki baya son mu’a mala dake ko wadda mijinta ke biye biye yar uwa kukanki yazo karshe duk kikayi amfani da ita duk machen da yayi sex da ita zaijita salab kamar dusa don haka aji tsoron Allah banda wanda suke zaune lfy da kishiyoyinsu)
5. End of discussion powder
( wannan garin karshen zance kenan hajiya oga ya taba miki kukan agwagwa ko mussoshi 😁to ranar duk da kika sha wannan hadin garin hajiya sabbatu sai kin rufe mishi baki ihu da kururuwa ba sauki kuma garin wata 7 yake ajiki yana aiki )

Hajiya karki bari wannan promo ya wuceki 25k ne promo saboda sallah 12k kacal

TikTok: Zuzeam.ventures5
Instagram: Zuzeam_ventures
WhatsApp: 08144015291



***********
Fuskansa ya hade da tata yana goga hancinsa da nata yana kokarin rarrashinta ya bude Baki da wata irin sanyi yace

"Pls Jan bana iya ganin wannan hawayen naki"

Maganarta ta Santa kuka me sauti xuwar mata tana fadawa jikinsa gabaki daya tana Jin ita kamarma Rabasu zaayi.

Rungumeta yayi tsam jikinsa yana qanqameta yana Jin kaman ya tsaga jikinsa ya maidata ciki ya rife abarsa.

Kuka takeyi sosai tana fada Masa itace sanadin duka damuwa da quncin danginta..

Dago fuskanta yayi yana sake share mata hawaye yace

"Ba haka bane karki manta su kansu fada sukeyi kece farin ciki Kuma wadda suke alfaharin tsananin son dasuke Miki ne ya riqe ahalin zaadens har babu Wanda ya isa ya raba wannan kaunar,

Aurena da soyayyata akanki bazata taba raba tsakaninki da familynki ba sbd karfin kaunarku a tsakaninku ta wuce nan ni kaina na San Hakan,

Duk bacin Rai da abinda zai faru a tsakaninku bazasu taba tsana ko kyamatarkiba sbd kece zuciyarsu da suke jure komai na rayuwa da suka fuskanta akanta"

Zuba Masa ido tayi sbd Jin maganarsa na ratsata Dan ita Kanta kaunar datake musu ce ta saka take shakkar bayyanarda aurenta da AZIZ din haryanzu Wanda Shima sbd tsananin son dayake mata ne yabi umarnin yanda takeso na boye Hakan ya Bata lokacinda ta buqata isashe tinda dai bawai rabasa tayi da Kanta ba.

Ganin irin kallan datake Masa hawayenta na tsayawa ya sakasa saka tissue ya qarasa share mata hawayen yana kai bakinsa yayi kissing idonta ahankali kafin yayi na hancinta tukuna yayi na bakinta yana sake zagayeta da hannunsa daya.

Kallansa tayi tana kokarin bude bakinta tayi magana ya Dora yatsarsa a akan lips dinta yana girgiza Kai a natse yace

"Kin gaji pls ki huta karki sake wahalan da kanki"

Hannunta takai akan nasa tana janyewa ta ce

"Idanma Ammar ya fada musu meyake faruwa pls kamun alkwarin baza Kai interfering ba"

"No,i can't make a promise da bazan iya cikawa ba"

Kallansa tayi tana ciko idanuwanta da hawayen da tasan zasu iya sakasa yadda zatai magana ya Dora bakinsa a kan nata yayi kissing nata sosai kafin ya saketa yana kallan fuskanta hannuwansa tallafe da fuskanta yace

"Bazan taba iya Miki alkwarin tsayawa nayi Shiru ina kallan ana min wasa da Arzikina na duniya ba"

Hawayen ta sake tsiyayowa yana share mata yana kissing idanuwanta da hancinta yana kokarin hanata wannan hawayen da duk ya damesa.

Kokarin sake kissing lips dinta yakeyi aka bude kofar dakin da suka manta da inda suke kwata kwata.

Saurin janyewa Jannah din tayi jikinta na tsananin rawa ta miqe da mugun sauri daga jikinsa tana komawa bakin gado da gudun gaske har tana bigewa ya miqe tsaye yana kallanta da mamaki yace

"Kibi a hankali fa"

Ummah data shiga mummunan shock da firgita duk rikicewa tayi tana qarasowa tareda yi kaman bataga komaiba sbd ta kasa ma gane me idanuwanta suka ganar mata.

Rawa hannuwanta ke yi ta qaraso tana amsa gaisuwan AZIZ batareda ta iya kallansa ba hakama Jannah din Dan haka kai tsaye toilet ta wuce tana shigewa bayan tayi Masa Saida safe alaman batason fitowa ta samesa a dakin.

Tana shigewa ya qaraso ya durkusa yana duba kafan Jannah din data bige tayi saurin janyewa tana cewa

"Ka tafi kada Ummah ta sake fitowa ta ganka"

Kamo fuskanta yayi bayan ya miqe ya Dan rankwafo yai kissing goshinta yayi mata sai da safe ya fice.

Bai wani jima da fita ba Ummah dake bathroom tana faman sakawa da warwarewa cikin fargaba da tashin hankali ta fito tana qarasowa ta zauna har lokacin ta kasa kallan Jannah wadda ta kwanta ta lafe Shiru kaman tana bacci itama sbd kunya da tata fargaban data rufeta na tsoro da fatan Ummah Bata gansu ba.

Shirin bacci Ummah ta miqe tayi tana Jin kamar zazzabi na neman kamata sbd Bata fatar wani sabon tashin hankali a tsakanin AZIZ dinta da Zaadens da suke ahalinta a yanzu.

Gama komai tayi Tazo ta zauna bakin gado tana kallan Jannah wadda yanda take numfashi da motsi ahankali ya tabbatar mata da idanuwanta biyu ba bacci takeyi ba.

Cikin nutsuwa da sanyi Umman ta bude Baki ta ambaci sunanta tace

"Ummijan tashi magana zanyi dake"

Jannah na Jin Hakan gabanta yayi mugun faduwa tana Jin zufa na kokarin yanko mata amma ta riga tasan Ummah bazata taba fushi me muni da ita ba Dan haka ta juyo ahankali tana tashi zaune daga kwancen ta sauke Kanta qasa tana kasa hada Ido da Umman tayi Shiru.

Umman ma Shiru ya fara yi tana nazarin maganarta kafin ta fuskanci Jannan da Kyau ta bude Baki a cikin nutsuwan da zata fahimceta dakyau tace

"Jannah nice na haifi ABDULAZIZ Dan haka bazan taba goge a cikina ya fitito ba sedai Kuma a yanzu ba nice uwarsa ba ba shine 'dana ba,

A yanzu kece tawa,kece 'yata dan haka ke nakeson ji daga gareki idan har na isa na Kai matsayin uwa a gurin ki Jannah inason sanin meyake faruwa tsakaninki da AZIZ,
Yaya akai kike dauke a ciki a jikinki?
Kuma na waye?
Ni duka banason ma furta wanna maganganun a bakina sbd Daci da nauyi sukemin Dan haka ki sanar Dani komai bana buqatan sake tambaya."

Numfashi me sanyi da mutuwan jiki Jannah ta sake a boye sbd daga karshe dai zata samu rage damuwan ranta Kuma daman batada Wanda zata iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login