Showing 78001 words to 81000 words out of 150681 words

Chapter 27 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9061

hasken uwa ne kadai yake buqata ya yaye masa shi,

A rayuwarsa Yana tsananin so da kaunar uwa a tattaredashi wadda tin yana qarami Allah ya karbe masa wannan rahamar ta samun Uwa.

Ya rasa mahaifiyarsa,ya rasa Mimi a yanzu daya hango hasken samun wata uwar Ashe baida rabon fita duhun rayuwarsa.

AZIZ ne ya kasa juyawa ya kalli su Zaadens din da dukkaninsu kansu yayi qasa suna kasa kallan Umman da kuma jin tsananin nauyi da kunyar kallan datake musu sbd ta tabbata ita dasu kauna ta yanke sbd sune makasan 'yarta bata tabama taba samun damar saninta a matsayin Yarta ba sbd ta haifeta ta rasa hankalin ganeta hakama ta rabu da ita batareda hankali ba ayau data samu hankalinta babu Ummitah a duniya sedai zuciyarta dake bugawa a duniyar.

Ammar a Karo na farko a rayuwarsa ya samu Kansa cikin matsanancin kunya me girman gaske ta wani dan Adam,

A Karan farko yaji wani irin dana Sanin abinda yayi me tsananin gaske,

A Karan farko yaji ya tsani kansa da tinaninsa da iliminsa na likitanci tareda tsanar daular daya taso a cikinta Wadda ta sakasa bacewa a cikin batan da yayi,

A Karan farko dayaji Soyayyar Jannah na sanyi a zuciyarsa sbd itace sanadin batansa da gurbacewan zuciyarsa ya zama makashin Matar da ayau yakewa tsananin so na uwa kuma yake tsananin buqata,

Ciwo da quncin dayake hangowa a idanuwan Umman na rashin Ummitah tana kallansa ya saka dukkanin duniyar fita Kansa dan kuwa se yanzu ya gane kaddarar da suke ciki a yanzu ta haqqin Rai ce da rayukan da suka dauka da hannuwansu,

Babu ran da suka dauka wanda jininda bai bata hannuwansu ba wanda quncin da ahalinsu suke ciki kila bazai wanke ba har abada.

Wasu hawaye masu tsananin zafi da quncin zuciya ne ya ciko idanuwansa dukkanin jikinsa da jininsa suna wani mummunan sanyi.

Dukkaninsu idanuwansu jajir sukai suna jin zuciyarsu na fidda radadin samun kansu a matsayin hannun Riga da Umma Fatima sbd idan har da gaske suna sonta da kaunarta zasu barta da Wanda hankalinta ya zabar mata wato danta sedai kuma babu maganar sakin aurenta ga Dad har abada sbd abu ne da bazai taba iyawa sedai idan yabar duniy.

Daga kafa Ammar yayi idanuwansa na lumshewa hannuwansa na wani irin fara rawa ahankali Kansa na daukan yanayinsa gadan gadan sbd wannan Karan shi Kansa baya fatan ya warke daga haukarsa idan ta tashi yana fatan ya dawwama cikinta har mutuwarsa sbd ya huta daga quncin dayake ciki.

Juyawa yayi Yana barin gurin...

"AMMAR" shine kalman daya fito daga bakin ummah cikin wata irin sanyi da nutsuwa tareda tsananin kaunar data sakawa zuciyarta bayan tayi yaqi da zuciyarta akan korar duk wani ciwo da baqin cikin daya gabata Wanda yake mummunan kaddara da dukkaninsu.

Dukkaninsu idanuwansu dagowa sukai suna sauka akan Umman wadda idanuwanta suke jajir wani azababben ciwo takeji a kirjinta datake dannewa sbd tanason karban kaddarar Allah da hannu bibbiyu akan dukkanin abinda ya tsaro musu na hadesu guri daya duk da muguwar kaddarar daya kamata ta tarwatsasu har abada Amma Allah bai rabasu ba.

AZIZ dago idanuwansa yayi ahankali ya sauke akan Umman cikeda mamaki da wani irin sanyi Yana kallanta kafin ya gangara da idanuwansa ya tsayar akan hannunta daya data zare daga nasa tabar dayan cikin nasa ta miqawa Ammar data ambata Wanda ya tsaya cak tareda kasa juyowa sai data sake ambatar sunansa ahankali muryanta na rawa cikin karfin hali.

Juyowa yayi ahankali idanuwansa na sauka akan hannun data miqo masa cikeda kulawa da kauna irin ta Uwa....

Kasa motsawa yayi ya durqushe a gurin tareda fasa wani irin kuka me tsananin tsima zuciya jikinsa na rawa Yana fidda kukan dayake maqale a zuciyarsa na shekara da shekaru sbd mahaifiyarsa data haifesa a ranar da zata barsa duniya haka ta ambace ta miqa masa hannun dabai kama ba kenan dan kafin ya iso ranta ya fice hannunta ya sake.

Kuka yakeyi sosai Yana jin tsanar rayuwarsa gabaki daya sbd bazai iya dagowa ya kalli Ummah ba Wadda take miqa masa hannu a matsayin 'da.

Irin kukan dayake ne ya saka gabaki daya gidan yin tsit gashin jikin Zaadens gabaki daya Yana miqewa sbd kuka ne da Ammar bai taba yi ba,
Kukane yakeyi na tsananin kadaicin dayake jin rayuwarsa a ciki ba uwa ba uba ba madafa ba jannar daya qwallafawa rayuwarsa harya zama mugun Abu akanta.

Ahankali Ummah da hannunta yayi sanyi ta sake hannunta Wanda Maheer yayi saurin isowa ya tallafe idanuwansa jajir ya bude bakinsa dake rawa ya ambaci sunan Ammar Wanda yake wata irin jijjiga jikinsa na rawa Yana kuka.

AZIZ da yayi mutuwar xaune kasa dauke idanuwansa yayi daga kan mahaifiyarsa dake amsar Wanda ya bude kirjin yarta ya rabata da rayuwar a matsayin 'da da hannunta...

Wani irin ja idanuwansa sukai tsananin kaunar mahaifiyarsa na yagalgala zuciyarsa data kasa yafe komai Amma ita batareda ma tasan waye Ammar Zad ba take amsarsa,

Baisan ciwo da tsananin radadin da zataji ba idan ta san waye Ammar din,
Yaya zata karbesa?
Yaya zuciyarta zata iya daukan hakan?
Zai iya kallanta ya fada mata?
Zai iya bari ta dandani quncin da har abada bazai wanke daga zuciyarta ba,

Tsakiyar idanuwanta ya kalla ya hango kauna da shakuwa datakewa Ammar din Wanda take kalla idanuwanta na sake ja da hawaye a cikinsu take yaji wani irin nauyi akansa kaman Yana sauka sbd ranar farko daya hadu da mahaifiyarsa Yana karban tarbiyan da ya kasa samu ko bawa kansa akan rama sharri da alkhairi.

Juyawa yayi ya kalli Zaadens din dukkaninsu idanuwansa jajir kafin ya dawo da kallansa kan Umman Yana tattara maganar Kisan Ummitah da dukkanin Wanda yake cikinta ya rufeta a ransa har abada sbd bazai taba dandanawa mahaifiyarsa baqin ciki da quncin daya rayu a cikinsa ba,

Bazai iya dandana mata radadin da Zaadens suka dandana masa,

Bazai dandana mata radadi akan mutanen datakewa kallan ahalinta na biyu ba sbd irin kulawa da kaunar da suka nuna mata duk da baisan tayaya suka hadu ba hakama tayaya suka kula da ita Amma dai yasan sun kula sun kaunaceta a lokacinda batada kowa batada hankali bakuma tareda sunsan ita wacece ba.

Miqewa yayi ahankali tsaye Yana juyawa ummansa ta kama hannunsa tareda hanasa tafiya tana kallan Ammar har lokacin.

Da rarrafe kaman almajirin dayake tsananin hali Ammar ya iso har gaban Umman yana kasa miqa hannu ya kama na Umman ya kasa dagowa ya kalleta ya daga kai ya kalli AZIZ LIMBA Wanda ya idanuwansa sukai jajir sedai babu kiyayya ko daya a cikinsu sbd ayau ya zabi nutsuwar zuciyan mahaifiyarsa akan komai,

Daga yau a gurinsa maganar Kisan Ummitah ta tafi har abada a bakinsa insha Allah sbd dukansu masu laifi ne me tsananin girma a gareta,

Idan su sun raba Ummitah da duniya dan raya 'yarsu shi kuma ya kamu da tsananin son wadda aka kashe Yar uwarsa dan rayata da har yake jin zai iya sake bata tasa rayuwar dan ta rayu dan haka shima lefinsa me girma ne a gurin Umman.

Kallansa Ammar yakeyi da dukkaninsu suna jiran ya sanarwa Umma sune suka rabata da Ummitah,
Sune suka kashe Ummitah,
Sune suka raba Ummitah da duniya dan raya tasu Yar dake raye a yanzu Amma ya kasa juyowa ya kallesu bare Umman sbd dukkaninsu sun kasa kallanta.

Dagowa Ammar yayi ya bude baki cikin mummunan yanayin quncin dayake cin rayuwarsa Yana neman sassauci da sautin daya saka kowa sake kasa motsi yace

"Ni me laifin da babu yafiya ne a gareki da bazan taba zama 'dan ki ba sbd na riga na zama makashin daya rabaki abinda kikafi so a duniya,

Ni makashin Ummitah ne da har abada bazan taba goge hakan ba a tarihinki da nawa ba,

Yau itace rana mafi baqin cikin danai Dana Sanin gani,

Ummah bazan taba zamowa 'da a gurinki ba,
Nayiwa kaina mummunan tabon da zai bini hr abada,

Ciwo da radadin rashin uwa n Sani bansan ciwo da radadin rasa 'da ba sai a yanzu danake ganinki a cikin ciwon rashin 'yar da nine na rabata da.....

Kasa qarasawa yayi Yana wani irin kukan da yake fitowa daga kirjinsa Yana dafe kirjinsa.

Duk yanda Umman taso riqe kanta kasawa tayi sbd dalla dalla Ammar ya fara bayyana mata girman laifinsa Danasani da quncinsa me tsanani a bayyane take ta fasa wani irin kuka me tsananin tsima zuciya tana qanqame AZIZ LIMBA da Shima sai ayanzu yake jin yanda Ummitansa ta rabu da ranta idanuwansa sukai jajir Yana qanqame mahaifiyarsa dake kuka kaman ranta zai fita jikinta na mutuwa.

Dzad da kafafunsa suka kasa daukansa durkushewa qasa yayi ahankali Yana zamewa zaune bakin kofar dakin cikin tsananin kunyar Kansa da tarbiyan daya Dora zuriarsa akai na tsananin son zuciya da tsananin son kai idan ba kansu ba basusan kowa ba hakama balain da masifa idan ya wuce kansu basu damu yahau kan kowaba.
#MAMUH
#LIMZAD
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 46

Basuda kunya da baqin cikin tareda magirmamiyar Dana Sani akan abinda zuriarsu ta aikata sai gurin ubangiji da suketa neman yafiya a gurinsa sai ayau da suka samu kansu a cikinta akan Ummah Wadda Allah ya dasa kaunarta me girma da tsafta a zuciyarsu gabaki daya sbd ta shigo rayuwarsu a daidai lokacinda basuda kowa,kowa gudunsu yakeyi yana tir dasu,
A lokacin da suke cikin tsananin buqatar uwa a cikinsu hakama ta kaunace su tamkar jininta duk da batada cikakkiyar hankali kaunar datai musu me tsafta da girma ce dan haka ita din itace ta zama mutum ta farko da suka saukewa kansu qasa cikeda kunya da sarewa ga dukkanin hukuncin da zata dauka akansu zasu karba.

Maheer ma qasa ya zube a gaban Umman dake kuka sosai har lokacin tana sake qanqame 'danta.

Falaq da duk hankalinta ya tashi da ganin wannan masifun da jin asalin yanda mahaifiyarta ta rasu jikinta rawa ya dauka na tsananin tsoro da rikicewa.

Sayd ne ya iso gurinta da sauri Yana rungumeta jikinsa Yana qanqameta sbd a Karan farko da suma shida ita suka samu Kansu da tsananin kadaicin da junansu kawai suke dashi.

Fiddausi ma kuka takeyi sosai daga palo hakama fatma sbd duk me Imani yaji yanda Ummitah ta rasu daga bakin Wanda sukai aikin sai ya shiga sabon tashin hankali da kuka.

Saida Umma takai idanuwanta basa gani kafin ta dago ta kalli Ammar dasu Dad da kuka sukeyi da idanuwansu me karfi da tsananin baqin ciki ta share hawayen da suka gangaro mata ahankali ta daga hannunta dake rawa sosai ta dafa Ammar wanda ayau jin yake mutuwa yake tsananin so sbd ya huta kawai.

Dagowa yayi ta sake miqa masa hannu Wanda yayi saurin kamawa hannuwansa da dukkanin jikinsa na rawa yanason magana Yama kasa ya kifa Kansa a kafafunta Yana fasa sabon kukan samun sassaucin da bai taba tsammani ba daga rayuwarsa.

AZIZ ta kama da hannunta daya ta bude bakinta cikin muryanta data shaqe sbd kuka tace

"Dukkanin abinda sukai tsakaninsu ne da ubangijinsu na yafe sbd halaccin kaunar dake tsakanina dasu Wadda ta ginu batareda hankali na ba suma ta ginar musu batareda Sanin ni wacece ba sukai sbd Allah da bawa rayuwata kariya"

Wani nauyi me girman gaske dayake danne da kirjin AZIZ ne yaji Yana saukar masa ya zubawa Umman ido Yana ayyanawa a ransa duk duniya babu uwa mahaifiya kaman tasa.

Numfashi ya sauke me sanyi ahankali tareda lumshe idanuwansa ya bude Yana juyawa ya kalli Falaq wadda take a rude ya miqa mata hannunsa ta kama da sauri ya juya ya fice da ita Yana rungumota jikinsa sbd ya sake samun nutsuwan zuciya data ruhi dayake fatan daga yanzu rayuwarsa ta koma daidai kaman kowa.

Sayd ne yabi bayansa shima jiki a mace fiddausi ma miqewa tayi tabi bayansu suka bar bangaren gabaki daya.

Mama da ta koma dakinta ta zube qasa tana wani irin kukan da baida magani jin tayi gabaki daya ta tsani rayuwar da duk wanda yake cikinta,

Jin takeyi inama zata iya dawo da baya ta goge dukkanin wani tarihin dayake tsakani Zaadens da AZIZ me kyau da mara kyau sbd su koma rayuwarsu wadda daga ita sai AZIZ dasu Sayd inda take uwa kuma mahaifiyarsa ita kadai,..inda ita kadai duniya ta Sani a mahaifiyarsa Wadda ta haifesa wadda take iko dashi Wadda bai hada da komaiba hakama maganarta batada ta biyu a gurinsa,

Shin yanzu menene matsayin datake dashi a rayuwarsa da duniyarsa?

Waye duniya zata kira da sunan mahaifiyarsa ita ko Fatima?

Menene matsayin da zata taka a rayuwarsa da familyn LIMBAs gabaki daya?

Dafe kirjinta tayi sbd tsananin suyar dayake mata tana jin kaman ta cinnawa kanta da gidan wuta gabaki daya su mutu lokaci daya kowa ya rasa kowa ya huta.

Zaadens aka bari da Umma Wadda ta kasa dagowa ta kalli Dad kaman yanda shima ya kasa dagowa ya kalleta tsananin sonta,tausayi da kunyarta yake.

Fatma gurin Jannah dake baccin azaba da gajiya har lokacin ta koma ta zauna tana zubawa Jannah ido sbd tinanin zuciyar dake bugawa a zuciyarta ba tata bace zuciyar dashe ce.

Shiru gidan yayi bayan kowa ya koma dakinsa dan samun dawowa nutsuwa da hankalinsa.

Abincin rana da aka kammala Amina da madam Sisi ne suka jera a dining kuma suka taho Nan palon su Zaadens ma aka jere nasu a dining aka sake gyara koina aka kunna AC dasu kamshi me nutsuwa gidan ya sake daukan shiru da nutsuwa.

Babu wanda ya fito cin abinci sai kusan 3 na rana tukuna suka fito daya bayan daya banda Jannah data kasa fitowa sbd Sabon gashin da Fatma tayi mata bata iya tafiya daidai tsoro takeji na familynta zasu iya ganewa.

A daki Fatma ta kawo mata abincinta fiddausi ma taxo ta kawo mata lafiyayyan pepper turkey da warm milk taci Tasha madaran sosai ta Sha magani.

Kaya ne kaya Guda da Sayd ya taho da motar wani designer boutique aka kawo kayan sakawarsu da suka kone aka jere mata a wardrobe hakama a dakunan mazan suma duk wata suturar buqata da abin amfani angama jere musu shi duk da sun gama yanke shawarar tafiya idan komai ya dan sake lafawa sbd bazasu cigaba da zama a gidan ba ba dalilin zamansu ko daya gwara su tafi.

Doguwar riga mara nauyi har qasa sedai qaramin hannu ne da ita na vest me shegiyar tsada amma zaka dauka abar banza ce ta saka da taimakon Fatma bayan ta gama cin abinci ta miqe cikin rashin kuzari ta zira slippers din Versace din da Fiddausi ta ajiye mata gabanta ta nufi kofa da mayafin original jersey akanta data rife jikinta dashi ta nufi dakin Ummah fiddausi na tareda ita.

Suna kama hanyar dakin fiddausi tace

"Anmaida Ummah sama tana can"

Kallan fiddausi da idanuwanta masu nauyi tayi da har lokacin basu koma daidai ba tace

"Umman??

Yes muje can din"

Palon daze kaisu saman suka nufa suka hau ahankali cikin sanyi dan bata iya motsawa sosai da karfi.

Suna isa palon saman babu kowa duka suna dakinsu.

Dakin fiddausi da baida babancin komai Dana Falaq da Nicky Nan aka dawo da Umman bayan an sauya beddings sababbi masu laushi da tsada komai na fiddausi ta kwashe daga dakin ta koma dakin Falaq.

Suna isa fiddausi tayi knocking tareda bude kofar da sallama ta bawa Jannah guri ta wuce ahankali tana kafe idonta akan Umman dake kan sallaya ta idar da sallah tana addua idanuwanta a kumbure sosai itama alamar kukan data Sha.

Ahankali Jannah ta bude baki tace

"Ummah"

Juyowa Umman tayi tana kallan Jannan ta sauke numfashi me sanyi da ajiyar zuciya tana kokarin sake murmushin karfin halin daya kasa fita ta bude mata hannunta tana cewa

"UmmiJan"

Mantawa tayi da halinda take ciki ta isa da saurin gaske ta rungume Umman cikin tsananin farin ciki tana cewa

"Ummahna"

Farin cikin datake ciki kasa boyuwa yayi ta sake rungumeta tana murnanta afili.

Cikin nutsuwa da kulawa Umman ta dagota tana kallan fuskanta tace

"Bakida lafiya ne?
Meya sameki?

Shigowan AZIZ dakin qamshin na gauraye iskan dakin gabaki daya a natse sanyeda black blue Christian Dior wears da suka fiddo haskensa da kwanciyar hankalinsa sosai ya saka Umman dagowa ta kallesa cikeda kauna me sanyi tana jin babu kowane irin qunci da baqin ciki bare riqewa a zuciyarta sbd Allah ya raya mata AZIZ tagansa da idanuwanta ta hadu da abinta batareda tabar duniya ba,

Daman shi ta Sani shi ta Shaqu dashi,shine Danta kuma ubanta da guardian dinta a baya dan haka tana godewa Allah daya raya mata shi harya zama haka batareda qunci da tsanani sun rabata dashiba hr abada.

Jannah datasan shine sbd qamshinsa bata dago ba hakama bata juya ba Sedai numfashin data sauke ahankali jikinta na mutuwa sbd jin idanuwansa akanta.

Ummah dawo da kallanta kan Jannah din tayi tana sake cewa

"Meya same ki ne?
Menene ya dameki?

Zaunawa yayi ahankali Yana kallan Jannah din ya bude baki zai bawa Umma amsa Jannah tayi saurin bude baki tace

"Ummah zazzabi ne kawai Se ciwon baya kila sbd yawon danake ta yi ne jiyan"

Zuba mata ido Umma tayi ganin ta kasa dagowa ta kalleta.

Maida kallanta tayi kan AZIZ Wanda idanuwansa suke akan Jannah din yana mata kallo a natse sbd ta sauya duniyarsa gabaki daya.

"To kinsha magani kuwa?

Gyada Kai Jannah tayi tana dan kwantawa jikin Umman ahankali kafin ta dago ta kallesa da idanuwanta da suke a laushi har lokacin batada wani kuzari.

Kallan datai masa ya sakasa jin gashin jikinsa ya tashi ya zuba mata mayun idanuwansa yace

"Nan da awa daya Dr zata sake zuwa ta dubaki"

Bata basa amsaba ta fara magana da Umma ahankali tana fada mata ita batason ganin likitan.

Lallabata Umman tayi ta amince kafin ta miqe ta fice daga dakin dan basu guri suyi maganar dataga alaman zasuyi.

Tana fita suka fara magana me zurfi ta tsakanin uwa da da a natse sbd jin yanda kowannensu yayi rayuwa bayan rabuwa da juna.

Bai fito dakin Ummansa ba sai magrib Yana fitowa ya wuce masallaci tareda Sayd Wanda acan suka hade gabaki dayansu mazan gidan.

Tsakaninsa da Zaadens babu Wanda ya cewa kowa komai sbd babu Wanda yasan abinda zai fara cewa Amma dai sunsan suna kan burinsu da alkawarinsu na aurawa Ammar Jannah koda kuwa kowa ya aje makaman yaqinsa to wannan dai shi alkawarine da bazaa daga ba kuma ma da gaggawa yanzu sukeson yin hakan.

Da daddare Jannah ta daure ta fito cikin familynta suka ci abinci tare kowa yana kokarin bata kulawa sbd suma a yanzu sun samu jin wani nauyi me azaba ya sauka daga kirjinsu dan haka sun samu kwanciyar hankali tinda Umma bata gujesu ba bata kuma mance dasu ba kaman yanda bata manta ita din Matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login