Showing 45001 words to 48000 words out of 150681 words
dake hannunsa ya jefawa Sayd Yana bude baki da mummunan sautin daya saka haukar Nicky tsayawa cak yace
"A rufeta a daki bayan wannan masu daukanta na zuwa"
Dawo da kallansa yayi kan Ammar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya miqa hannunsa ya kama hannun Jannah a gaban kowa ya jata ze bar gurin Ammar ya riqesa kai tsaye jikinsa na rawa yace
"And where d hell do you think are you going wit my wife?"
Wani irin mummunan sarawa kan AZIZ yayi ya juyo da idanuwansa jikinsa na tsananta rawa ya kalli Ammar din yana hadiye wani irin masifaffen ciwo da wutar data kama kirjinsa take wanda ya sake saka dukkanin masu aikin sake ja da baya
Mama ma da bata hayyacinta idonta na kan kofar fitowan Fatima sake samun kanta tayi da tsananin shakkar AZIZ wanda a yanzu take zargin ba daidai ba.
Kasa cewa komai yayi ya juya ya kalli Sayd
Nicky da sauri cikin tsananin baqin cikin da wutar dake ci kirjinta ta kwace daga madam Sisi tana cewa
"Eh matarsa ce aurenta...... Bata qarasa ba Sayd ya someta da allurar hannunsa ya nufi Ammar yana qwala Kiran securities dan shima Ammar din dole a rufesa kafin zuwan likitocin mahaukatan.
AZIZ na juyawa Mama tayi wuf ta fada dakinsu Jannah dan dubo Fatima sbd daidai lokacin saceta ne yanzu batasan tana dakin Dad ba tareda Dad din.
Jannah kuwa cikin tsananin fushi da ciwon da kirjinta ke mata ta fizge hannunta sedai kafin tayi wani motsin ya dauketa cak dinta yabi ta kofar da shi kadai ne me bi da ita.
Daqyar ya isa Sama da ita sbd yanayinsa dayake tsananta ya sakawa dakin key tareda zarewa yayi jifa dashi da karfin gaske Yana buga bango da hannunsa cikin wani irin tsananin fushi da wutar zuciya.
Baya taja sosai tana kallansa cikin wani irin yanayin tashin hankali sbd gabaki daya ciwonsa ya wuce yanda ta Sani,
Ciwon ya qarasa nisan da abin yayi Muni.
So take ta hanasa jiwa kansa raunin sbd yanda jini ke futa a hannunsa din Amma kuma ta kasa motsawa bare isa garesa sbd zuciyarta dake cikeda tsana har lokacin.
Ganin abin yayi tsananin gaske ya sakata isa gurinsa cikin daga sauti da nata fushin tace
"Ya isa,idan kashe kanka zakayi ka me yasa zakayi hakan a gabana?
Idan ka......
Wata irin tsawa me karfin gaske ya sakar mata Yana juyowa ya kamata da hannuwansa biyu ya girgiza da karfi yace
"Da auren nawa akanki wani yake kiranki matarsa?
Ina raye igiyoyin aurena uku suna raye kika bari wani ya kiraki matarsa?
Kin shirya zarar Dani ne bayan Wanda nake fama da ita?
Kinason maidani makashi ne??
Da wani irin mahaukacin sauti da kararsa ta fice ta me hankali da gabaki daya gidan saida ya amsa jikinsa na wata irin jijjiga yace
"Wayace ya kiraki da sunan matarsa"
Wani irin mummunan firgita tayi sbd tsananin tsoron yanayinsa da kaman ita zai fara kashewan.
Tsit gidan yayi kowa na sake shiga tausayinsa sbd alamu sun fara bayyana me gidan kansa ba lafiyayye bane a tsakanin jiya zuwa yau.
Juyawa yayi sbd wani irin tafasa da wutar dake ci jikinsa da zuciyarsa dake ingizasa ga maidata macensa a yanzu da tsakiyar ranar kowama ya huta Amma kuma a yanda yake zai iya mata illar da zatai Muni dan haka ya nufi toilet baya ko gani ya sakarwa Kansa ruwa yana zubewa qasa suna sauka a jikinsa.
Daqyar ta iya daukan key din dakin ta fice da sauri itama bata ganin gabanta sbd tsananin tashin hankali da firgicin maganganunsa ta nufi daki kai tsaye dan dauko takardar sakinta ta duba.
A daidai wannan lokacin Mama ta isa dakin su Jannah din da kwalban da Nicky ta yadda bayan ta sume dan neman Ummah.
#MAMUH
#ZAADENS
#LIMBAS
07019691719
*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 26
*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
******************
Mama da hannuwanta ke tsananin rawa idanuwanta na rufewa ga kuka tsananin tsoro da fargaban dayake cike da kirjinta sbd Sanin bame hankali ce zata dosa da makami ba hakama kusan duka ahalin ita ganin takeyi kowama a gidan mahaukaci ne,
Shakkar haukar Umman takeyi sbd taga dukan gaske takeyi gata bata gama wartsakewa daga muguwar azaban datasha a hannun Ammar ba a Daren jiyan Amma bazata bari wannan damar ta wuce taba ta dauke Fatima tabar gidan da itaba sbd matiqar tana gidan batada zaman lafiyar zuciya data kwakwalwa dan itama kila zarewan zatai kaman Su Nicky ta ari hauka ba shiri dan haka gwara ta fiddata gidan tasan yanda zatai da ita bayan barin gidan da ita.
Hannuwanta har qara rawa sukeyi ta bude dakin su Jannah din tana shigowa kai tsaye sbd Sanin babu kowa a bangaren duk suna can.
Duba dakin tahau yi da idanuwanta a zare tana qarasa shigowa da tsoronta na ficewa.
Ummah bata dakin dan haka sake riqe makamin hannunta tayi dakyau tana nufar toilet din dakin.
Da karfi ta budesa tana soko kwalban ciki da karfi tin kafin ma taga waye a ciki sedai babu kowa a ciki.
Zufa ne ya fara gangaro mata ta juyo tana sake riqe makamin da kyau ta nufi dakin Dzad tana ayyanawa a zuciyarta tana dakinsa tareda tsinewa wannan masifaffen auren da a yanzu batama fatan ya mutu so takeyi suyita son junan ta samu suqi rabuwa su dauketa suyita tafiya ko zaa barta taji da 'danta ta dawo Kansa da zuciyarsa dake neman sauka daga inda ta dorasa.
Kokarin fitowa dakin takeyi kaman daga sama Umman ta bayyana gabanta ta fito daga dakin Dzad idanuwanta jajir kuka ne da tsananin tashin da ciwonta yayi suka saka kamanninta gabaki daya sauyawa.
Mummunan faduwa gaban Mama yayi zuciyarta na neman tsinkewa da ganin mummunan yanayin Fatiman dan haka taja da baya kadan tana dago fasashiyar kwalban hannunta tana nuna Maman da ita ta bude baki zuciyarta na bushewa tace
"Fatima kece kika zabi mu zama hakan tinda tin farko kinqi yadda ki bini kika zabi makasan 'yarki,
Kika zabi Wanda suka kashe Ummitah da karfi d yaji suka cire zuciyarta suka bawa tasu Yar Wadda kike yiwa tsananin son asara,
Kin zabi maqiyiyar ABDULAZIZ dina tinda kika zabi maqiyansa akansa,
Kin zabi Wanda suka wargaza rayuwar 'dana suka illata rayuwarsa illar da bazata barsa ba har abada,
Hakanne yasa bakida wani amfanin bayyana a rayuwarsa Fatima,
Ya dade da manta ki,
Ya rufe babinki
Nice uwa kuma mahaifiyarsa da bazai taba sauyani ba har abada,
Kinsan abubuwan dana fuskanta akansa tin yarinyartarsu shida Ummitah har zuwa yanzu?
Tayaya zaki dawo a lokacinda bazan iya baki shi ba,
Bazan taba iya rasa AZIZ LIMBA a matsayin Dana ni kadai ba,
JANNAH itace masifar gabaki daya rayuwar AZIZ Dina dan haka saina tabbatarda dga ke har ita babu Wanda har abada zai iya shiga tsakanina da.....
Kaman a mafarki taji anyi sama da ita an rafkawa tiles din gurin wnada ya daka idanuwanta da kanta juyewa tana kasa gane a mace take ko raye sbd azabar da tinda Allah ya halicceta tin haihuwa bata taba jinta ba irin yau.
Sake shaqurota Ummah tayi ta daga jikin bango ta sake bugata da qasa wanda ya saka wani rikitaccen ihun neman agaji fitowa bakinta jikinta na tsananin rawa sbd dukan rabata da duniya Ummah takeyi idanuwanta a rufe cikin rashin hankali da haukarta daya tashi tuburan sbd sunan ABDULAZIZ da Ummitah dayaketa juya kanta Yana sake haukatar da kwakwalwanta sbd tabbas sunayen sunzo mata a daidai sune sunayen dake mata yawo akai koyaushe ciwonta ya tashi.
Mama balain dataji Yana neman rabata da duniya ya sakata bude baki tana ihu ba shiri sbd hadiye azabar takeyi da farko tana hana kanta ihu sbd kada azo a samesu zancen yaje gaban AZIZ.
Jin Ummah zata rabata da sassan jikinta da duniyar ma gabaki daya ba shiri ta fara ihun neman ceto.
Koda Dzad dake toilet ya juyo ihun da sauri y fito
Ya duba dakin bega Ummah daya bari tana bacci ba da sauri ya saka kayansa ya nufi kofa cikin tsananin tashin hankali.
Maheer ma da tsananin gudu ya baro Ammar dayake kokarin taimkawa ya dawo daidai a dakinsu ya fito.
Mama suka gani a hannun Ummah tayi mata wani irin jina jina dan haka da tsananin gudu sukai kansu Dad ya janye Ummah Yana qanqameta jikinsa da karfi Yana rungume kanta zuciyarsa na bugawa da karfi idanuwansa na jajir sbd ganin gabaki daya ciwonta ya qarasa rikicewa.... tsananin tausayinta ne ya saka idanuwansa tsananta ja ya kalli Maheer yace
"Ka miqata inda zasu bata taimakon gaggawa"
Daki Dad yayi da Umman ita kuma Mama cikin tsananin azaba Maheer ya fito da ita sedai ko nisa basuyiba Madam Sisi tagansu ta qaraso jikinta na wata irin rawa tana neman buga ihun jawo hankalin maigidan yaga abinda ya samu mahaifiyarsa.
Cikin tsananin azaba mama ta hanata ihu tana cewa karta sanar da kowa idanma tayi nauyi tace a stairs ta fado.
Da sauri da mamaki Madam Sisi ta bude baki zatai magana Maman ta yanke jiki ta fadi daidai suna isa palon qasa dan haka dole Madam Sisin ta fito da gudu tana neman Sayd Wanda tini yakai Nicky dakinta aka rufe.
Falaq da fiddausi ne suka fito jin hayaniyar madam Sisi suka tarar da Maman a zube qasa harda jini a fuska da jikinta.
Madam Sisi data dawo jiki na rawa tace stairs Mama ta fado.
Fiddausi na jin hakan ta qarasa gurinta da sauri hakama Falaq.
Daki akai da Maman tareda Kiran likita Falaq ta hana a sanar da daddynta sbd Yana tareda Jannah Wadda a daidai lokacin ne gidan ya dauki ihun tsawarsa data saka kowa sake yin tsit Yana magana da Jannah.
Ko da Jannah ta baro palonsa bata ganin gabanta maganganunsa ne ke neman juyar mata da kai sbd tasan har abada ta gama zama Matar AZIZ LIMBA dan haka bama zai yiyiba abinda kwakwalwansa take basa yana fada.
Zaadens da Garba da suka San abinda ya faru na dukan da Ummah taiwa Mama da kuma yanda jikinta ya rikicen fuskewa sukai kaman ba abinda ya faru basu fadaba kuma basu nuna ba,
Ummah na daki tareda Dad Yana sake kokarin ganin ta dawo daidai ko yaya ne,
Hakama Ammar Maheer sun samu ya koma daidai sedai a cikin kwakwalwansa da zuciyarsa babu sauki ko sassauci ko kadan dan kuwa a wannan Karan idan ya rasa Jannah baisan abinda zai zamaba dan gwara ya mutu yabar duniya da hakan ya faru dashi.
Ko da Jannah ta iso babu kowa duka kowa Yana dakinsa dan haka kai tsaye dakinsu ta shiga ta nufi wardrobe dinta hannuwanta na wata irin rawa idanuwanta na qafewa da rikitaccen tashin hankali sbd bata fatan ko kadan taga komai bayan rubutaccen saki na mutuwar aurenta da AZIZ LIMBA.
Kayan cikin wardrobe din tafara janyowa tana wurgi dasu tsakiyar dakin idanuwanta na sake qafewa jajir...
Bataji bata gani kayan ciki kawai take fitarwa tana jefarwa,
Acan qasan kayanta rigarda ta bayyana wadda envelope din yake nade a cikinta.
Hannuwanta dake tsananta rawa takai da sauri ta fizgo rigar tana budewa bugun zuciyarta na tsananta.
Bayyanar envelope din ya sakata jefar da rigar tana budewa da wani irin rawa da dukkanin jikinta keyi.
Kasa budewa tayi dan haka ta saka karfi ta yagasa gabaki daya..
Takardu uku ne suka zube qasa daga ciki Wanda ta zubawa idanuwa tana kafesu da wani irin kallon da takardan saman itace ta bayyanar mata da ticket ce...
Sarewa qafafunta sukai ta zube qasa da karfi tana jin dukkanin jikinta na daukan wani irin zafi da zazzabi me karfin gaske.
Kasa saka hannuwanta tayi akan takardun sbd yanda zuciyarta ke wani irin juyawa tana kamuwa da ciwo me tsananin gaske.
Daqyar ta iya miqa hannuwanta suna rawa ta dauki takardun duka ukun tana fara bude ta farko Wadda ta sakata damqe takardun da karfi tana qasara zubewa zaune qasa gabaki daya.
Sabon ticket ne aka siya da sunansa da komai na tafiya a wancan ranar da limbas suka bar qasar.
Kafe ticket din tayi da idanuwanta tana kasa kyaftawa zuciyarta na tsananta ciwo da wani irin yanayin dake saka idanuwanta fara cikowa da hawaye masu tsananin ciwo.
Ta biyun ta dago ta bude ahankali Wadda rubutunsa ne a tsare cikinta na kalmomin da basu wuce biyar ba.
"KINYI NASARA AKAN AZIZ LIMBA DA DUK ABINDA YAKE ZUCIYA DA RAYUWARSA,
FATIMA DA FATIMA SUNE RAYUWAR AZIZ LIMBA IDAN ZAN MUTU DA KAUNARSU TO ZAN MUTU NE DA SON WADDA ITACE ASALIN ZUCIYAR,
AUREN AZIZ LIMBA AKANKI MUTUWARSA CE KADAI ZATA RABA WANNAN AUREN"
Rintse idanuwanta tayi hawayen dake cikinsu masu tsananin zafi suka gangaro tana fasa wani irin kukan da babu sauti tana kasa bude takardar karshen hannuwanta na damqe takardun hannunta da karfi suna nadewa.
Kuka takeyi sosai wanda daqyar ta iya dago takardar karshen ta bude...
Address ne na gidansa da qasar dayake na ticket da aka siya mata sai a qasa da aka rubuta.
Zan jira zuwanki a duk lokacinda zuciyarki ta aminta Dani na Miki alkawarin wannan"
Rintse idanuwanta tayi tana cusa kanta cikin kafafunta kukanta na sake tsananta sbd wannan envelope Yana kokarin maidata inda rayuwa take tsawon shekaru biyu da suka wuce,
Tayaya a lokaci daya komai yake neman juyewa ya komar da ita kaddarar da bata fatan komawa?
Tayaya auren data jima da wankesa ta kakkabe a zuciya da rayuwarta zai dawo mata,
Ta gama cirewa da yafe AZIZ LIMBA a rayuwarta,
Da Ammar Zad ta shirya ta yadda fara rayiwa sbd gyara kuskurenta ta baya Amma tayaya ma zata iya kallan ahalinta data cewa aurenta da AZIZ ya rabu kuma a yanzu da suka gama karban sabuwar rayuwa da wanke komai na baya tace musu auren da dukkaninsu sukafi kaunar mutuwa dashi tace Yana Nan?
Dago jajayen idanuwanta tayi tana kallan takardun hannunta wasu hawaye suka sake gangaro mata na wani yanayin me karfi dake fitowa can qasan zuciyarta tana dannewa ta bude baki tace
"Nima ban karbi auren Nan ba bazan karbi duk wannan zancen ba har abada anrufe babin AZIZ LIMBA rayuwata dan haka babu wani sauran abinda ya rage musu bayan rabuwa da juna batareda ma kowa a ahalinsu yasan da akwai aurenba har yanzu.
#MAMUH
#ZADENS
#LIMBAS
#LOVE PSYCHOs
#CRZY LOVERS
#MAMA
#NEW LIMB*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 27
*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
https://chat.whatsapp.com/IexiuY21PP75lt4yoJtNsK
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
************
Miqewa tayi ta sake share fuskanta ta tattara takardun tareda daukan envelope din ta hada dashi ta juya ta nufi kofa ta fice idanuwanta a rufe bataji bata ganin komai bayan sabuwar takardar karshen auren AZIZ LIMBA.
Ko data iso palon qasa babu kowa sai Sayd da zai wuce da likita zuwa zamansu Mama ko kallansa bataiba shima hanya ya bata sbd ganin yanayinta Musamman da idanuwansa suka sauka akan takardun dake hannunta take ya fahimci abinda zai faru dan haka cikin sauri ya wuce da likitan sama dan ya duba mama ya gama ya fice.
Yanda take hawa stairs din idanuwanta a rife ya saka har faduwa takeyi amma bata tsaya ba sai data Isa kai tsyae kuma ta bude kofar palon ta shiga.
Baya palon dan haka bacin rai da tsananin baqin ciki bai barta jiran komaiba ta isa kofar bedroom dinsa ta bude kai tsaye.
Zaune yake a couch har lokacin fama yake da kansa jin yake kaman ya fasa ihun dazai rusa gidan gabaki daya,
Jin yakeyi wata irin wuta na balbala a zuciya da jinin jikinsa,
Idan har wani zai iya sake ambatar 4&4 da sunan matarsa a gabansa babu abinda zai iya hanasa zama makashi...
Dago jajayen idanuwansa da suka sakata dauke idanuwanta akansa tana qarasowa gurinsa...
Rintse idanuwansa yayi sbd indai a daidai wannan lokacin aka cigaba da wannan hayaniyar zai iya rasa control na Kansa dan haka qin dagowa yayi ya kalleta yana sake rufe idanuwansa ya bude.
Takardun hannunta ta zubar masa a gabansa tana bude baki da sautin dayake bayyanarda fushi da kuka ciwon abinda zata fada dake zuciyarta tace
"Ni Jannah Zad bazan taba iya zama matarka ba,
Ayau a Karo na biyu na sake zabar rabuwa dakai,
Wancan Karan I choose my family wannan Karan kuma I will choose Amm......
Qarar glass din table din gabansa da yayiwa wani mahaukacin duka ne ya sakata rintse idanuwanta idanuwanta da karfi ya hanata karasa zancenta.
Qarfin karar har palon da dukkaninsu Falaq da Sayd suke said sukaji kowannensu yayi qasa da kansa babu me iya cewa komai bare motsawa Musamman Falaq da idanuwanta suka ciko da hawaye sbd komai na rayuwar gidan d daddynta sun rikice a qanqanin lokaci amma dai idan har zai shirya da Jannah komai da zai faru me sauki.
Miqewa tsaye yayi tareda fizgota da hannuwansa biyu da karfi zuwa jikinsa wanda ya saka rauninta fiddo jini tana rintse idanuwanta cikin karfin halin hana kanta sanyi ta bude idanuwan ta sauke akan fuskansa datai jajir idanuwansa da babu abinda yake cikinsu bayan wata irin fitinar wutar kishin dake neman kashesa ya bayyanarda haukansa gabaki daya zuwa level din karshe.
Ita ya saukawar idanuwan Ya zubawa Yana rasa abinda zai mata,
Wata irin azababbiyar Soyayyar da yakejin zatai ajalinsa ke ci da wuta a kirji da zuciyarsa,
A cikin kwakwalwansa wani irin jijjiga da yamutsi yakeji duk akan Jannah Zad Wadda duka wannan masifar da balain dayake ji bai taba jinsu akan rashin Fatima da Fatima ba Amma a yanzu Yama rasa wace masifar da baya iya controlling ne yake ji...
Ruwa ne take gani suna cika idanuwansa Yana kasa cewa komai jin yake kawai Yana zarewa dan haka ya janyota jikinsa ba zato ya qanqameta ahankali Yana rintse idanuwansa ko zai samu sassaucin abinda yake ji sbd azaba ma yake ji yanzu wanda Tai masa yawan da bazai iya riqewa ba..
Qwacewa ta fara yi tana fizgewa sbd itama azabar take ji a kirjinta da azabarta take mata yawa.
Duk yanda taso qwacewa kasawa tayi dan haka ta fasa masa kuka me karfi tsawon lokaci har takai karfinta ya qare ta bude