Showing 111001 words to 114000 words out of 150681 words

Chapter 38 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9065

na wahalan gaske.

Scanning sabo Dr yayi masa na cikinta yana kallan Arzikinsa Dr na Masa bayanin dayake saka duniyarsa gabaki dayanta sanyaya da nutsuwan data Fi Masa komai na kyallin duniya.

Sake riqe hannunta yayi cikin nasa bayan angama komai nurses din da Dr sun fice ya zubawa fuskanta datai fayau idanuwansa yana kallanta kaman zai dauketa subar komai da kowa su tafi inda zata rayu a kwanciyan hankali itada babynsa su renesa babu hayaniyan komai da kowa.

Hannunta dake hannunsa yakai bakinsa yayi kissing cikin sanyi da tsananin kauna yana lumshe ido yanajin hankalinsa na kwanciya kawai ba ruwansa da tashin hankalin da kowa yake ciki.

Sayd da Fatma ne suka shigo suka nema guri suna zaunawa Dan taruwa a jinyar matar oga.

Shiru Shiru kowa na cikin nasa kalan damuwa da ciwon xuciya har akai Asuba tukuna dukkaninsu suka fita sallah,

Da LIMBA din dasu Maheer a masallaci daya sukai sallah amma Allah ba saka sun ga juna ba Dan haka suna gamawa kowannensu ya koma inda yake sai a lokacin Ummah da Garba suka ringa neman su Jannah wadda daga baya sukai tinanin sun koma gida da Fatma Dan haka suka ci gaba da zaman fargaba.

Sai guraren 8 na safe Dad ya farka dukkaninsu sukai private dakin da aka maidasa suna godewa Allah ganin shi ya tashi sauransu Ammar a yanzu Wanda dukkanin adduarsu ta koma kansa kacokam.

Dad tinda ya tashin baice komaiba Shiru yayi radadin zuciyarsa na sake qaruwa kowace daqiqa har lokacin yana kasa yadda da masifar datake kokarin fado musu wai cikin haihuwan 'dan mutum a jikin Jannah,
Ta ina?
Ta Yaya?
Ba abu ne me yiyuba Dan yasan wacece Jannah bazata taba aikata barna ba Dan ba tarbiyanta bace,
Ba hali ko dabiun Banza datake dashi ko daya tin tana qanqanuwanta bare yanzu,

Jannah ko saurayi batada shi Bata kula kowa,shi kansa Ammar da zaayi musu auren bata wani sakewa sosai dashi a yanzu kaman baya sbd LIMBA daya cire mata dukkanin shaawan yin aure ko soyayyar datai a baya sbd abinda yai mata Dan haka tayaya Jannah zata dauki ciki ita kadai ba miji ba komai?

Shi kwata kwata bai yadda da ciki a jikin Jannah ba labari ne da zancen da yake neman kashesa da ransa kawai amma yana buqatan tabbatarwa Dan Kuwa badai cikin mutum ba sedai na iska.

Sake nitso a Shiru da tinani yayi nauyi kirjinsa na tsananta a ransa yace

"Kodai ciwon Fatima da Ammar bai gama warkeba yake kokarin dawowa suke tinanin ciki a tattare da Jannah daga tana malaria tinda suna tsananin kaunarta kawai kwakwalwansu ta basu wannan tinanin??"

Numfashi ya sauke me zafi cikin mutuwan jiki da sanyi yana dagowa ya Kalli Ummah dake gefensa cikeda tausayinta da kaunarta me karfi Dan baya kaunar ciwonta ya dawo ko kadan amma ga alaman Hakan nan Dan haka hannunsa ya Dora akan nata yana kasa cewa komai radadin zuciyarsa na karuwa sosai da qunci.

Umman ma cikeda kulawa da kauna ta dafa hannunsa daya Dora akan nata daya tana dagowa ta kallesa tace

"Dad ka dena saurin saka magana a ranka sbd gudun samun shock irin Hakan baida amfani komai tsananin lamari da muninsa sai an kwantar da hankali ake iya magancesa a warwaresa,
Ammar yana kwance muna fatan tashinsa sai Kuma kaima ka saka mu cikin wani tashin hankalin Dan Allah ka cire komai a ranka Allah zai kawo mafita da sauki tareda maslahan komai na damuwan da mike ciki"

Shiru Dad din yayi yana gyada kai kawai kafin ya dago ya kalleta yana Dan kokarin dawo da nutsuwansa yace

"Yaya Ammar din??

Maheer ne ya basa amsa da cewa

"Sun gama basa taimakon gaggawa dayake buqata Shima ana jiran farfadowansa ne kowane lokacin"

Ajiyan xuciya me Dan sanyi Dad din yayi yana sake bude Baki yace

"Ina Jannah?

Kai tsaye Muhammad dake kokarin gyarawa Dad din pillow din dayake kokarin jingina daya tashi zaune yace

"Sun koma gida ita da fatma"

Shiru ne ya sake ratsa gurin kafin Maheer da kama Dad din zuwa toilet Dan alwala Ummah Kuma sake gyara Masa shimfidar gadon me Dan wali sosai tayi tana cewa

"Muhammad ka tabbata sun koma gidan ai ko??

"Insha Allah Ummah suna gida"


******Acan sai da gari yayi haske Jannah ta farka lokacin daga ita sai AZIZ din a dakin yana hannunsa da nata yana sarqe cikin lafiyayyan bargon da aka rufeta dashi Wanda sayd ne yaje ya kawosa sabo fil daga gida tin tsakar Daren.

Zubawa juna idanuwa sukai tana kallansa a sanyaye sbd har yanzu tashin hankalin Soyayyansa a rayuwanta bai qare ba sbd a yanzu da akasan tana dauke da cikin da bazata iya fadan nasa bane sbd kada a zubar mata da cikin wani babban qalubale da tashin hankali ne a rayuwanta data babynta da tinda ya bayyana sun sani tsananin son abinta takeyi sbd AZIZ LIMBA dinta ne ubansa,shine yabata kyautarsa datafi komai a rayuwanta yanzu,
Zata so ta haife Dan AZIZ LIMBA dake cikinta sbd sake basa farin cikin dazaifi komai na rayuwansa.

Shi kansa AZIZ din bazata iya fada Masa tana dauke da cikinsa ba sbd tashin hankalin yawa zaiyi idan yasan akwai ciki a jikinta kuma yaga familynta na kokarin daukan mataki akan laifin datai bazai kyaleba fitinar ahalin biyu tashi zatai ayita yi bayan saukinta da son zama abu daya datake fatan musu tsakanin LIMBAS da ZAADENS Dan haka Sai tagama karban hukuncinta sun karbi cikinta tukuna zata iya sanar dasu mahaifin cikin nata Shima ta sanar dashi.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 65

*_ZUZEAM VENTURES_*
Best kayan Mata
08144015291
*NEW ALERT*
*END OF DISCUSSION PACKAGE*
~25k~ promo 12k
Barka da Sallah promo pack
1. Tabajen kankana da fruit
  (Mai saukar da niima nan take ta kara miki dadi na musamman keda oga sai kunyi kukan dadi ranar )
2. ⁠gumbar chakwala dadi
(Hmm yar uwa daga jin wannan kema kinsani basai anbaki labariba wannan hadin na zallar dadi ne da ciko da gaba)
3. Turare kyauta dole
  (Wannan turaren na amsar kyauta ne ina masu fama da miji mai mako wanda ba a cin kudinshi Ga shi da abun amma ba a ci to yar uwa matsalarki tazo karshe da izin Allah Sai kinci abunshi ina yan kasuwa duk kina amfani da wannan turaren sai Kinga budi da izinin Allah)
4. Zumar bata gaban kishiya yar asali
( wannan zumar Ga mata wanda kishiya ta shiga gabansu mijinki baki gane kanshi ya fifita yar uwarki akanki baya son mu’a mala dake ko wadda mijinta ke biye biye yar uwa kukanki yazo karshe duk kikayi amfani da ita duk machen da yayi sex da ita zaijita salab kamar dusa don haka aji tsoron Allah banda wanda suke zaune lfy da kishiyoyinsu)
5. End of discussion powder
( wannan garin karshen zance kenan hajiya oga ya taba miki kukan agwagwa ko mussoshi 😁to ranar duk da kika sha wannan hadin garin hajiya sabbatu sai kin rufe mishi  baki ihu da kururuwa ba sauki kuma garin wata 7 yake ajiki yana aiki )

Hajiya karki bari wannan promo ya wuceki 25k ne promo saboda sallah 12k kacal

TikTok: Zuzeam.ventures5
Instagram: Zuzeam_ventures
WhatsApp: 08144015291

***********
"Hi Aslm alaikum Mrs LIMBA" shine abinda ya bude bakinsa cikin laushin murya da nutsuwa me sanyi ya furta can qasan maqoshinsa yana kallanta kafin yakai bakinsa yayi kissing hancinta yana Dan goga mata nasa hancin kan nata ya dago yana kallanta.

Bata iya cewa komaiba sai bakinta data bude kadan tace

"Meyasa kazo?
Su Dad zasu sake shiga fushi pls ka tafi banason kuyi wani damuwan fushi Kai da Dad"

Murmushi me sanyi ya sakar mata yana tayar da ita Zaune ahankali ya kama kafafunta ya sauko dasu qasa ya tayar da ita tsaye duka a natse kaman Wanda take cikin tsananin ciwo yace

"Muje ki fara tsarkake kanki da sallah tukuna"

Toile din dayake dakin kaman na tsadaddiyar hotel sbd tsari da kyansa ya shige da ita ya rufo kofar daidai nan Fatma da Sayd da fiddausi sai Falaq suka shigo dakin daga gida dauke da breakfast masu lafiya baske kusan uku da abubuwan buqatan Jannah din.

Da kansa ya taimaka mata tayi wankan tsarkin da bataiba tin jiyan sbd tashin hankalin da aka shiga tin acan ciki yace fiddausi ta kawo hand dryer da aka kawo da ita sbd yace a kawo da itan.

Da kansa ya busar mata da Kanta a toilet din kafin ta sauya kaya da kayan da Fatma tazo mata dashi tukuna ta fito tayi sallah shi Kuma Saida ya sauya nasa kayan Shima ya fito sbd wancan sun jiqe shikuma sayd daman baya wasa da komai na AZIZ a Shirye yake da kowane yanayin dazai kama Dan haka tin a cikin dare ya kawo kayan AZIZ din kusan kala uku sbd da safe koda babu abinda ya samu kayansa may b qamshin asibiti zaisa kayansa su ishesa ya buqaci sauya wasu.

Ko daya fito ta gama sallah da haka ya dago a sanyaye ta kallesa tana son cewa gurinsu Dad zata amma ganin duka wanda suke dakin basusan abinda yake faduwa ba yasata yin Shiru tana miqewa.

Breakfast akaso tayi ta kasa Sam gurin familynta take son zuwa dole ya hakura ya kyaleta.

Dukkaninsu suka isa dakin da Dad yake tana janyewa daga gefensa sosai ta koma gefe daya itada Fatma kaman tafiyarsu baa tare take ba musamman kallan da Maheer ke mata dad kuwa ko kallan inda take din baiyiba tukuna.

Ummah ce ta miqa mata hannu tana zaunar da ita gefenta Shima AZIZ din a dayan gefen Umman ya zauna yana kallan Dad bayan ya gaisa dasu Maheer kadaran kadaha ba sakewa ba Kuma basarwa.

Dad din ya yiwa ya jiki batareda yasan meya samesa ba amma dai kaman yanda sayd ma da baiji farkon draman data saka suman Dad dinba yace Masa shock ne na kasa dauka daukan halinda Ammar yake ciki ya sanyasa zubewa.

Ummah cikeda kulawa da kauna me sanyi take amsa gaisuwansa tana tambayarsa Mama.

Falaq ce ta amsa da cewa tana gida dayake tana zaune maqale da Jannah itama.

Dukkaninsu sunwa Dad fatan samun lafiya dashi da Ammar Kuma sun Dan jima kafin AZIZ da ahalinsa suka fice zuwa gida yana riqe da hannun yarsa dataso abarta gurin Jannah amma bazai iya Hakan ba sbd yasan suna cikin tashin hankali da damuwan Ammar ba zata gane kan Jannah dinba Sam ta bari kawai sai sun dawo gida.

Su AZIZ din na ficewa ummah ce tai karfin halin saka kowa yin breakfast akan dole na lafiyayyan abincin da aka kawo din Wanda daman dasu da Jannah da basuma San a asibiti ta kwana ba aka kawowa.

Sama sama kowa yaci abincin suka gama me gyara dakin ta shigo ta sake gyarawa tsaf ta daidaita ac ta sake cike dakin da kamshi ne sanyi ta fice tana sake musu fatan Allah ya karo lafiya.

Shiru dakin ya dauka kafin Dad ya dago ya kalli Jannah wadda ta rakube gefe Kanta a qasa ta kasa hada ido da Dad din bare Maheer.

Numfashi ya sauke me zafi yana bawa zafin kirjinsa damar ficewa ya bude Baki yana kallanta yace

"Jannah?"

Dagowa tayi ahankali ta kallesa cikin mutuwan jiki tace

"Naam Dad"

"Jannah me yake damunki?
Wane ciwo ne yake damunki kiketa sauyawa koyaushe?
Menene gaskiyan abinda nake ji sbd kwata kwata na kasa yadda da maganar da ni banason furtata da bakina"

Shiru Jannah tayi tana kasa cewa komai gabanta na faduwa zufa na keto mata tako ina sbd batasan tayaya zata iya bude Baki ta furtawa mahaifinta cikina a jikinta ba bayan sunsan batada auren kowa akanta.

Maheer ne ya dago jajayen idanuwansa da tin jiya yake Jin kaman zai makance sbd ja da radadin da suke Masa ya kalleta ya bude bakinsa Dan Shima so yake yaji ya tabbatarda gaskiyanta bai gama yadda da maganar wai ciki ne a jikintaba Dan bama abu bane me yiyuwaba yace

"Tambayarki akai kikai shiru"

Sake Dan ja baya tayi tana sake matsewa gefen Ummah hawaye masu zafi na cikowa idanuwanta suna fara gangarowa take ran Maheer daya matsu su fita wannan banzan tinani Da maganar cikin sbd tana kashesa yace

"Magana zakiyi ko kukan Banza ne anan an tambayeki abu kinayi kaman munafuka"

Ummah ce ta karbi zancen da cewa

"Ya isa Maheer abi a hankali mana ai zatai magana dole"

Dawo da kallanta kan Jannah dake kuka sosai qasa qasa tayi ta dafata tana kokarin kwantar da murya sbd kada ta sake daga hankalin Jannah din tace

"Ummijan,menene gaskiyan ciwon dayake damunki fada mun naji kinji sbd kowa hankalinsa ya kwanta,
Ki duba kiga halinda Ammar yake ciki sbd Hakan,ki Kalli Dad ma yanda ya kusa shiga mummunan hali duka sbd Hakan mu kanmu kwana mukai cikin zullimi da rudanin xuciya duka sbd Hakan Dan haka fada mana gaskia kowa ya samu nutsuwa,

Kinga ni bazan taba yadda da wannan zancen ba sbd ina shadan Ummijan Dina,
Dad ma Sam bai yadda ba sbd yasan wace yarsa,
Ko Maheer ma ransa yana sake baci ne sbd kin kasa cewa komai so muke ki bude Baki kice ba Hakan bane shikenan fa"

Wani sabon kuka Jannah ta sake Wanda ya saka tsikar jikin Dad da Maheer tashi,
Dad din ya hadiye wasu yawun wahala yana neman sarkewa sbd alamu na neman tabbata akwai abinda yake faruwa da Jannah din Dan haka ya bude Baki zaiyi magana Jannah din ta sake fasa kuka tana cewa

"Dad kayi hakuri ka yafemun Dan Allah......

Wani lafiyayyan mari Maheer ya dauketa dashi Wanda tinda take rayuwarta baa taba marinta ba Dan haka ta gigice tana riqe Ummah da karfi sbd jinsa cikin kunnuwanta da Kanta suna Wani dauke wuta ta fasa wani sabon kukan jikinta koina yana rawa ta sake bude Baki zatai magana Maheer yayo Kanta Ummah ta riqesa tana cewa

"Ka bari tayi magana tukuna"

"Ummah hakuri take hadawa ba tambayar da ake mata zata amsa ba" Maheer ya fada yana jin kaman zuciyarsa zata buga.

Fatma data miqe tsaye jikinta na tsananin rawa sbd tsoro kasa kallan Maheer din tayi yana yi bayan ummah itama sai a lokacin Maheer ma ya lura da yanayinta ya tsayar da kallansa kanta yace

"Fatma fito kizo nan"

Cikin sauri muryanta na rawa tana sake boyewa bayan ummah tace

"Yaya Maheer banyi komaiba bansan komaiba babu ma abinda yake damunta inji likita"

"Nace ki fito kizo Nan Fatma"

Hawaye itama ta fara masu gudu tana cewa

"Yaya Maheer dan Allah kayi hakuri sharrin shedan ne"

Da sauri dukkaninsu suka kalleta xuciyoyinsu na tsinkewa Dad ya sake hade wasu wahalallun yawu

Muhammad ma Matsowa yayi yana fizgo Fatman daga bayan Ummah da karfi ya turata gaban Maheer din zatai baya Muhammad ya riqeta yana daka mata tsawar data sakata tsayawa jikinta na Dan rawa tana kallan Maheer idanuwanta har lokacin suna hawaye.

Maheer da jikinsa ya fara mutuwa da maganar Fatman yace

"Fatma kikace sharrin shedan ne?
Ta ina shedan din ya biyo zaki mana bayani sbd kinsan komai"

Dad daya kasa hakuri da riqe tashin hankali bude Baki yayi yace

"Maheer ku kaita gurin likita yanzu Nan ya duba mana ita a gabanku kaida Fatima a kashe wannan zancen yayi nauyi"

Jannah na Jin Hakan ta sake sunkuyar dakai tana sabbin hawaye.

Gaba Maheer da Ummah suka sakata har scanning room dake asibitin Maheer ya samu yayi yanda zaiyi yayi payment me tsada aka shiga dasu scanning din sbd babu card nata na asibitin yana gida.

Karan farko ana farawa likitar tace

"Masha Allah babyn is healthy inshallah"

Rufe ido Jannah tai da sauri hawaye na gangaro mata gefen ido sbd ganin yanda Maheer yayi mutuwan tsaye yana jiri ya dibesa yayi baya zai fadi ya dafa bango da sauri yana Jin kansa na juyawa.

Ummah ma Shiru tayi tana zubawa Jannah din ido cikeda matsanancin mamaki harma batasan sanda tace

"Doctor cikin mutane ne Kuwa?
Kodai wani abin ne me kama da ciki kika gani?

Murmushi doctor din tayi tana cewa

"No,ciki ne lafiyayye wata uku a jikinta yanzu harda kwanaki ai kaman nai mata wani scanning din kwanakin baya data zo"

Shiru sukai babu Wanda ya sake cewa komai har aka gama suka fito takardar na hannun Maheer daya mata wata irin damqar da idan kaza ce data mutu.

Suna isa dakin Dad daga Dad din har Muhammad suna tsaye Fatma na zaune gefe zuru itama.

Rufe dakin Maheer yayi yana kasa kallan Dad sbd sanin zancen zai sake tabasa.

Ummah ma cikeda tausayi da kulawa take kallan Dad din Wanda tin a yanayin yanda suke kallansa ya sare ya miqawa Maheer hannu ya karbi scan din ya bude yana dubawa.

Jiri ne me karfi ya dibesa ya zaunar da karfi bakin gado sukayo kansa da sauri suna ambatar sunansa ya rintse idanuwansa jikinsa na rawa ya sauke kai yana cewa

"Innalillahi wainna ilayhirajiun,
Jamaa wannan masifar Kuma daga ina?

Ummah data kasa magana itama ajiyan xuciya ta sauke cikin sanyi da nutsuwa tace

"Ummijan daga ina?
Garin Yaya Hakan ta faru?

Fatma Maheer ya zubawa ido yace

"Kece me bakin bamu amsa yanxu saiki mana bayani"

Garba Kuwa cikin zafi yace

"Itama ai kaita yakamata ayi a dubata sbd tare suke komai"

Kuka Fatma tafashe dashi tana cewa

"Wlh tallahi Banda komai a jikina itama akwai aure ne a tsakaninsu"

Salati muhammd ya dauka yana cewa

"Kenan dai kinsan komai din Fatma?

Maheer Kuwa wani zufa ne ya fara jiqasa ya Kalli Dad Shima Dad din shi ya kalla suka Maida kallansu akan Jannah a tare tashin hankalinsu na tsananta Ummah da Bata gane inda zancen ya dosa ba sai ta karba zancen da cewa

"Indai akwai aure a tsakani Kuma su modibbo dake kauyen sun sani ai da sauki a lamarin" a tinaninta acan kauye akai wani auren.

Dad da Maheer Kuwa babu Wanda ya sake cewa komai sbd tsoron ma Jin abinda zai buga xuciyoyinsu Kuma ga Ummah a zaune basason fada ko nuna bacin ran da zai sosa ranta Dan haka sukai Shiru zufa na jiqa kowannensu amma tabbas suna buqatan zama na musamman da Jannah kafin suyi bikin kusan binneta da ranta.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 66

*_ZUZEAM VENTURES_*
Best kayan Mata
08144015291
*NEW ALERT*
*END OF DISCUSSION PACKAGE*
~25k~ promo 12k
Barka da Sallah promo pack
1. Tabajen kankana da fruit
  (Mai saukar da niima nan take ta kara miki dadi na musamman keda oga sai kunyi kukan dadi ranar )
2. ⁠gumbar chakwala dadi
(Hmm yar uwa daga jin wannan kema kinsani basai anbaki labariba wannan hadin na zallar dadi ne da ciko da gaba)
3. Turare kyauta dole
  (Wannan turaren na amsar kyauta ne ina masu fama da miji mai mako wanda ba a cin kudinshi Ga shi da abun amma ba a ci to yar uwa matsalarki tazo karshe da izin Allah Sai kinci abunshi ina yan kasuwa duk kina amfani da wannan turaren sai Kinga budi da izinin Allah)
4. Zumar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login