Showing 135001 words to 138000 words out of 150681 words

Chapter 46 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9058

shaida"
#MAMUH
07019691719

*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 77
Alhamdulillah

It’s Official! MG’s Beauty Lounge Opens Monday, 2nd June 2025 – Just in Time for Sallah!

Ladies of Kaduna, are you ready to shine this Sallah?
Your new beauty destination MG’s Beauty Lounge is opening with elegance, class, and all the pampering you deserve!

Here’s what awaits you at MG’s Beauty Lounge:

Beautiful Hair Styling & Braiding

Glamorous Makeup for Sallah

Relaxing Pedicure & Foot Spa

Natural Skincare Products & Full Kits

Fresh Henna Designs

Fragrance Oils, Humra, Incense & More

Bridal & Special Occasion Packages


We don’t just offer services — we offer an experience of royalty.
Come wash your feet, get styled, henna your hands, and glow with elegance—all under one beautiful roof.

Address: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, Behind Indomie House, near Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Bookings & Enquiries:
WhatsApp: 08062991549
Call: 09016108092 / 08064532391

Come See the Difference. Come Feel the Magic. Come Be a Queen.
Follow us on IG & TikTok: @MGsBeautyLounge



Maheer da sauri ya kalli Dad da modibbo a lokaci daya yana rasa wa zai tsayar da idanuwansa akansa cikin su biyun itama fatma silalewa tayi a jikin bango tana kaiwa qasa kukanta na tsananta sbd ba auren takeso ba kwata kwata hakama Maheer din ba saar aurenta bane bayan tsananin taxarar shekaru yafita komai bama zai taba karbanta a matsayin matarsa ba sedai matar cinne.

Numfashi me zafi Saleem ya sauke a sanyaye yana kallan Maheer Wanda ya zame ya zauna kan kujera idanuwansa na sauyawa zuwa Ja sbd auren macen daya girma sosai nesa sosai baya cikin tsarinsa yafison macen data qosa shekarunta suka tafi kusan daidai na nasa hakama kallan Jannah yakewa Fatma.

Saleem tausayin Maheer din yaji amma Kuma dukkaninsu a gurinsu babu baqin ciki ko asara ko abin damuwa Dan wani a cikinsu ya auri Fatma sbd takai macen da kowane namiji zaiso bayan rashin ilimin boko Wanda a yanda ta wanke din yanxu sai anfada ma ake sani sosai,

Shi a nasa bangaren babu maganar auren kowace mace a duniyarsa sai wadda zuciyarsa keyi tsananin so me karfi,zurfi da tsafta danma Allah yasa Bata gurin da kallansa da kawai akai a lissafin zabawa fatma Miji daya Sha rigimar da zata hanasa sukunin Watan gabaki dayansa.

Ammar Kuwa zubawa su modibbo idanuwansa yayi yana Jin mamakin tayaya bayan ance zaayi auren suce sai anyi yanzu bayan auren taruwa a rufawa juna asiri ne ba abin gaggawa ba Dan haka Matsowa yayi gaban su modibbon zaiyi magana Dad ya riqe hannunsa yana juyowa ya kallesa da idanuwansa da suke ja na duka wannan tashin hankalin da masifun dasuke neman warwarewa ya Maida kallansa kan kawu ya fara kallansa kafin ya Maida kallansa kan modibbon ya bude Baki yace

"Ba damuwa zaku sheda Hakan, gobe jumaa ce a daura auren bayan sallar jumaa a yanke masa sadakin Fatman"

Shiru sukai dukkaninsu kawu jibo na Jin zuciyarsa na tsallen farin cikin samawa Fatma tata mafitar har abada din me Kyau yana Kuma Jin shakkar yanda Maheer zai karbeta ko ya qi daukanta matsayin mata,
A dayan bangaren Kuma idan ya duba halinda Garba yake ciki sai yanajin gwara su tattara yaransu su tafi dasu amma Kuma a yanda yake satar kallan AZIZ LIMBA dake zaune yasan ko su da suka Haifa garban babu inda zai bari su tafi dashi sbd cikin dake jikin kanwarsa Sam ba fuskan da zai dauka abarta da babyn ita kadai.

Modibbo ma kusan tinanin da jibon keyi shi yakeyi amma Kuma yasani a ransa a bayyane zaadens bazasu taba cutatar da yayansu ba Tinda gashinan sun kula musu dasu tamkar nasu Wanda Hakan ne ma yanzu ya saka suke kokarin auren Fatman Dan Hana a tafi da ita a mata auren kauye da Wanda bataso.

Kawu isiya Kuwa ko magana da tinanin komai baya iyayi sai kallan Nicky da Garba yana sake tsiyayo hawayen ina zai saka ransa da jika bature, Garba ya gama da rayuwansa.

Kai tsaye modibbo ya Kuwa yanke sadakin yana kallan Maheer Wanda Dad ya kalla Dan haka ya taso a hankali ya Kalli modibbon ya bude Baki yayi godiya ya Kalli su kawun suma yayi musu godiya yana koma gefe kansa na sarawa.

Ammar gurin Maheer din ya koma Shima kansa na sarawa sbd yana Jin damuwan da Dan uwansa yake ciki.

Kaman daga sama suka tsinci muryan AZIZ data sakasu duka sake dawo da kallansu da hankalinsa gabaki daya akansa ba shakka ko kwana bare lankwasa kowane zance yace

"Zan karbi muhammd a yanda yake sbd inganta rayuwarsa dan tsayuwa da kansa ya kula da 'dansa Idan an Haifa da matarsa wadda tana haihuwa zaa daura musu aure,

Muhammd zaiyi karatu ya Gina kansa da kansa ban yadda kowa tsaya Masa ba sbd dole yasan nauyin daya dorawa kansa daga shi har itama dole zata auri Muhammad din Tinda ta iya Daukan cikinsa zata iya zaman aure dashi Dan haka Muhammad zai dawo karkashin Sayd.......

Da sauri dukkaninsu suka kallesa kawu isiya a rikice yace

"Bayan wannan barnar Kuma da girmanka Garba zaa karbeka riqo??

Modibbo ma cewa yayi

"Kai baka bamu macen ba munyi renan cikin zaaka ce a baka zabgegen namiji yaje ranan cikin??
To wlh akan wannan muna Nan sai an haife cikin"

Dad ma da Dan mamaki da kame fuska yace

"Inganta rayuwar Muhammad ko da babu wannan nauyin daya hau kansa ko da akwai duka akan zaadens ya rataya sbd shi namu ne Kuma sunan zaadens yake amfani dashi a yanzu Dan haka babu buqatan zamowa karkashin wani zamu dauki nauyinta Dana babyn tin daga yanzu har lokacin da zata haihu"

AZIZ da daman Hakan yakeson ji daga bakinsu Kuma yasan yana Sanya zasu banzatar da Nicky ne Dan haka sbd ya sake sakasu a zancen sosai yace

"Bayan ta haihu zan dauki nauyin komai na aurensu tin daga gidan da zasu zauna a duk kasar da sukeson har.......

Maheer ne dayake cikin nasa juyayin ya katse AZIZ din da hanasa qarasawa yace

"Wannan ma duka nauyin mu ne zamu dauka tin daga yanzu har daurin auren da duk abinda Aysha da babyn zasu buqata zamu dauki nauyin inganta rayuwarsu gabaki daya sbd babynta Zaaden ne"

Ajiyan xuciya AZIZ LIMBA ya sauke yana miqewa tsaye fuskansa a sake yana sake tsananin kamewansa ya Kalli Dad da Maheer dasu modibbo dake zare idanuwa jajir suna jiran ta baci Dan suma a Shirye suke da zuwa kauye su kawo dukkanin dukiyar shanunsu Dan tsira da martabar iyalinsu zasu bada komai da dukiya me yawa a basu Nicky su reneta da cikinta akan su bada Garba ya tafi LIMBAs renan ciki sbd kawai AZIZ LIMBA din yafi zaadens arziki da power.

Kallan Nicky da idanuwanta sukai jajir suka kumbura har fuskanta yayi Mama ta tayar da ita ya tsayar da ita gefensa yana kallanta cikeda kulawa yace

"Babynki ya samu identity dinsa tin kafin yazo duniya,
Kina dauke da baby Zad ne Dan haka kuka ya qare tubarwa Allah zakiyi ta yi yanzu kina neman gafarar laifin da kuka aikata har Allah ya saukeki lfy"

Ajiyan xuciya ta sauke tana dagowa ta kallesa sosai da idanuwanta kafin ta bude Baki cikin tsananin sanyi tace

"Thank you LIMBA"

Murmushi me Kyau ya sakar mata yana sake kwantar mata da hankali da idanuwansa batareda yace komaiba.

Har a ranta batasan tayaya zata auri Garba ba amma sbd tanason bawa bin umarnin na gaba da ita dama ko zataga sauyi da amfanin Hakan ga rayuwanta ya sakata kasa cewa komai akan maganar auren sbd ta jira haihuwanta ta gani ko zata iya idan Kuma taga bazata iyaba zata sanar da kowa ta bawa kowa hakuri ta tafiyanta da babynta tinda dai ubansa ya yadda dashi hakama iyayensa da familynsa sun yadda da babyn Dan haka ko a Hakan ita alhmdllh Allah ya mata rahama.

Sai a lokacin bayan komai ya natsa Ummah ta samu daman saka baki tana sake bawa kowa hakuri a lamarin tareda nusar da kowa ba abin damuwa bane tinda Allah ya kawo lamarin cikin bazata da tashin hankali Kuma gashi an nema mafita a cikin sauki da rufin asiri batareda kowa ya sani ba.

Mama Kuwa ganin yanda hankalin su modibbo ya tashi akan fatma da irin abinda suke gudu ya sake biyowa baya a cikin zuria ya saka itama nata hankalin taji ya Dan tashi sosai ya Kuma karkata akan nata ahalin da Bata fata amma kaddarar Bata wuce ta fada wa wani ba a gidan gashi yanzu tana ji tana gani AZIZ ya riga ya gama karban Nicky kwata kwata a matsayin kanwarsa Dan haka dole dai itama itace uwar Nicky din kenan gashi zata fara da tarbon jika na biyu bayan Falaq da babu aure sbd cikin Nicky yana gaban na Jannah.

Kai tsaya taji hankalinta yasake tashi Dan haka ta matsu su isa gida ta yanke nata hukuncin a nata Yayan.

Babu sauran gurin sake zama ko wata firar sbd babu Wanda ransa yake a cikin dadi kowa da nauyin kirji yake numfasawa Dan haka sallama LIMBAs sukaiwa Zaadens din suka fara kokarin tafiya.

Mama ce Kai tsaye ta Kalli Jannah tace

"Jannah mu tafi ai gobe zaki dawo daurin auren tinda auren aminiyarki ne da Kuma yayanki"

Kallan Mama Jannah dake rungume da Fatma tana tayata hawaye tayi tanajin gabanta na faduwa.

Sake magana Maman tayi Wanda ya saka Jannah kallan Dad Wanda ya hade fuska sosai ya saci kallan Ummah Shima wadda tama qi kallansa sbd kada ma wani ya gano ita yake Satan kalla.

Cikin sanyi Jannah ta bude Baki tace

"Mama Dan Allah a barni anan din"

Kallanta Mama tayi AZIZ dake gap da isa kofa a cikin kunnuwansa zancen ya sauka ya Dan lumshe idanuwansa tareda juyowa ya Kalli Mama a natsensa ba damuwan komai yace

"Mama mu tafi"

Mama kallan Ummah tayi tace

"Kinji yarki tace gidansu take so bari mu barta kafin a kwana biyu a gama hidimar bikin"

Murmushin karfin hali ummah ta sake tana cewa

"Aikuwa mun gode da Hakan ana gama hidimar inshallah kawota ma zaayi har gida"

Murmushi Mama tayi tana juyawa tabi baya AZIZ Wanda ya fice tini.

Suna ficewa Jannah taji jikinta yayi sanyi tana Jin kaman ta samesa ta duba idan ba fushi zai sake yi ba.

Ummah juyawa tayi tabar palon tana yiwa kowa Saida safe ta tafi da fatma da rarrashinta akan auren da gobe zai hau Kanta.

Kowama watsewa yayi ya nufi dakinsa Banda Garba Wanda sai da kowa yabarsa a palon kansa na qasa har lokacin idanuwansa sunyi jajir sbd Kukan da yayi Kuma har lokacin ma Jin radadin komai yakeyi yana tubarwa Allah jiki a mace.

Ammar ne ya dawo ya kamasa zuwa dakinsa suka zauna ya fara basa qwarin gwiwa yana sake Masa nasihar kaddara ce da jarabawan Allah ya bayyana laifin da sukai a boye sbd ya zama izina ga wainda suke tareda su da Kuma Allah ya riga ya qaddari akwai Rabon haihuwan a tsakaninsu Dan haka rungumar nauyin daya hau kansa da zuciya daya da Kuma kauna tinda dai jininsa Kuma Ayshan ma ta saduda shine mafita da abinda ya kamacesa.

Maganganun Ammar sun sanyaya zuciyar Muhammad din sun Kuma sake bude idanuwansa akan babu abinda yanda ya iya bayan rungumar Ayshan da babynsa tinda dai har Allah ya sake taimakonsa iyayensa na nan akai Komai baida fargaban yanda zai fuskancesu a gaban da Dan gaban fatiha tindai da su akai Komai Dan haka yaji nauyin kirjinsa da damuwansa suna ragewa yana Jin kaman anzare Masa ciwon dayake kirjinsa na tin ranar da sukai abin shi da Ayshan yanzu tubarwa Allah kawai zasuci gaba da nema.
#MAMUH
07019691719


*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 78

Ummah har daki takai Fatma ta zaunar da ita ta fara rarrashinta tana nuna mata ba abin kuka bane sbd Maheer dai mijin da kowace mace zataso aurensa ne sbd yanada abubuwan so hakama rayuwarta zata inganta zatai karatu ta samu kwanciyan hankali da nutsuwa auren gida batareda taje koina ba a ciki wainda ta saba rayuwa a cikinsu tasan halaye da kyakkyawan maamalan datake tsakanin ahalin Dan haka ta dena kuka ta sakawa ranta Maheer shine mafi alkhairin da aketa jira ana fatan samu.

Jannah datake a sanyaye kasa cewa komai tayi sai sauraron Umman takeyi rabin hankalinta Kuma yana kan AZIZ dinta da batasan Wane halin suke cikiba ita dashi.

Ummah ma Bata nuna damuwan komaiba ta sake hadasu su biyun tai musu nasiha tana gamawa ta miqe ta fice tana komawa dakinta ta shige ta rufe.

Jannah ma sbd rashin dadin zuciya da son sake cirewa fatma fargaban auren da damuwa a dakin ta kwana tareda Fatma wadda Sam babu bacci a idanuwanta sallar ishai sukai suka kwanta Shiru ba me dogon motsi.


***LIMBAs Kuwa suna isa gida AZIZ ya sake maimaita maganar auren Aysha da Muhammad tareda kulawa da babynta batareda tina ta hanyar da aka samesa ba ya Kuma sake kwantar wa da Nicky hankali sbd ta sake da wannan ya gama magana kowa ya shige Nicky na Jin inama tin farko a matsayin Yayan ta dauki AZIZ LIMBA da yanzu Bata zo wannan matsayin na kaddarar datake ciki ba.

Mama Kuwa tana shigewa dakin bayan ta gama komai ta zauna bakin gado wayarta ta dauka ta bugawa baba Al'hassan waya sukai magana sosai ta sanar dashi duka abinda yake faruwa Dan haka take Shima yaji hankalinsa ya Dan tashi da lamarin Dan haka yace Shima yana Nan tafe su toshe hanyar faruwan ire Iren wainnan kaddarorin.

Wayan dashi ya saka zuciyar Maman samun sukuni Dan haka ta samu nutsuwa harma tayi bacci me nutsuwan tana fatar itama azo ayi me yiyuwa a tsakanin Sayd da Fiddausi kowama ya fidda abokin rayuwa suyi auren zaman ya isa hakanan ba aure.


Washe gari na wayewa Zaadens suka tashi da hidimar daurin auren da suke dashi a yau din Dan haka tin asuba Ammar da Saleem suke wayoyin hidimar sai Kuma gayyatar mutanensu na kusa masu mahimmanci wainda zasu samu daman halarta,

Muhammad duk da yana cikin wani halin Shima hakanan ya daure yashiga hidimar sbd auren kanwarsa ne da Dan uwansa Dan haka shine ma ya fita zuwa karbo kayan da Maheer din zaiyi amfani dasu wainda tin cikin dare Ammar ya zabesu.

Su modibbo sun kasa fitowa daga damuwansu kwata kwata Saida Dad ya sake zaunawa dasu shi da Ammar suka kwantar musu d hankali tareda rufe zancen maganar cikin Aysha da Garba akan babu me ji har acan kauye kada kowa yaji a bari ta haihu a daura musu auren kawai batareda kowa yasan ya sukai suka samu 'yayansu ba Dan haka suyi hkr su dauki kaddara tinda Allah ya kawo lamarin da sauri yaran zasu auri juna Kuma basa inda ake rayuwan saka Ido ko wani abin makamancin Hakan itama Fatma gashinan zaa yi Mata auren cikin amincin Allah da yardarsa.

Da wannan su modibbon suka samu sake zuciyoyinsu sbd daurin auren hakama Garba sun sauko Masa daga wutar da suka dauke Masa Dan ko gaisuwansa babu Wanda ya amsa a cikinsu

Maheer baida zabin daya wuce karban komai duk da Sam fatma dashi din baiga ta inda zasu fara bama amma kasancewan ko bai karba aurenbama baida lokaci ko ranar sake wani auren Dan haka ya barwa Allah zabi akan auren.

Ummah tinda ta tashi itama take wayoyi da mutanen da Mama ta hadata dasu da zasu Taho su gyara mata Fatman Dan haka itama busy take
Jannah Kuwa dole ta ajiye damuwanta gefe ta fara nuna farin cikinta da murnan auren Dan haka Bata gurin Fatma Bata gurin Maheer din Wanda nasa lamarin yasa yama manta Dana Jannah din da Bata kwana gida ba yanzu ta kansa yakeyi ta inda zai fara.

Kamar wasa sai gashi qaramar hidimar da basu shiryawa ba ta zama babba sbd yanda kowa yaketa hidimar auren daya kama ba shiri.

Koda aka tafi sallan jumaa su Mama dasu fiddausi da Falaq sun iso gidan harma dasu anty Maryam din alh saad duka sun iso sbd mama data gayyacesu daman suna son zuwa gaida Umman AZIZ LIMBA Dan haka sai gashi gidan ya Tara baqi masu aiki Kuwa aikin lafiyayyan abinci suketa yi na baqin gidan.

Gabaki daya mazan Zaadens din haka suka fara fitowa a Shirye daya bayan daya suna Jan lafiyayyun motocinsu suna ficewa zuwa daurin auren sai Maheer dinne ya fito karshe ya fice tareda Muhammad da shine zai tafi tareda shi cikin wata lafiyayyar farar Mercedes Benz S550 Muhammad ne ke Jan motar suka fice daman su Modibbo tini suka fice tareda Dad a motar Dad din driver ya jasu.

Lafiyayyan ready made lace Mai shegiyar tsada Ummah ta siya mata a acikin kudi masu yawan da aka ware na Shirin Fatman dama matan ZADs din gaba dayansu dan haka ko masu gyaran Kai da fata da fuska duka gida suka taho sukai mata komai Dan haka itama koda baqi suka iso angama shirinta tai Kyau simple ba hayaniya sai Dan glowing takeyi na gyaran da akai mata.

Jannah ma da Ummah duka dasu akai gyaran fuskan da skin din Dan haka kowannensu yayi kyansa yanda daukan ido musamman Jannah da cikin jikinta yake qarawa skin dinta Kyau.

Mama da Ummah suna dakin Ummah din suna maganarsu Maman na sanar da Ummah abinda suka tattauna da Baba Al'hassan itama ummah Naam tayi da shawarar tasu sbd gwara duka yaran a tattara ayi musu aure a huta da fargaban me zaije ya dawo Dan ita data tatace ma da har Falaq sai amata auren tinda uwarta ma ance iyakacinta Sha Biyar akai mata auren.

Mama data San zancen bama me isa gaban AZIZ bane dariya tayi tana cewa

"Ai idan kika anyi auren Falaq a yanzu ai bayan idon AZIZ ne zamuyi sa dan har gobe shiyasa baya Tina ko sunan dangin Mahaifinsa sbd auren da suka tilasta Akaiwa Ummitah da wannan shekarun.


*******Ana gama sallar jumaa aka daura auren MAHEER ZAD da FATMA JIBO ZAD Wanda mutane da yawa suka shaida anata taya murna da barin kudi wa maroqa kawai manyan mutane da manyan motoci ne keta ratsowa wasu na kokarin fita wasu na Pake anata gaggaisawa ai take su modibbo dasu kawun sukaji baqin cikinsu na yayewa suka hau farin cikin gaske anata sake gaisuwa da manyan mutane sosai.

AZIZ LIMBA ma ya halarci daurin auren Wanda ya saka tin ana yan media da maroqa suka ringa Kiransa a matsayin sirikin zaadens Wanda dole Dad ya ringa washe Baki yana farin ciki sbd yawancin manyan mutanen gasken da suka halarta mutanen LIMBAn ne dan haka a idanuwan mutane LIMBAs da Zaadens kusan ahali daya ne sbd sun zama dayan.

Ana gama daurin aure sai kusan yamma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login