Showing 6001 words to 9000 words out of 150681 words
ba koda na manyan shaguna ne haka ko supermarket ganin sukeyi gwara shi akan aikin gadin.
Washe gari tinda sassafe suka sake Aron kudi a gurinsu modibbo suka wuce.
Tinda suka tafi Jannah ta maida hankalinta ta duqufa a gurin adduar Allah ya zabar musu abinda yafi zaman alkhairi koda aikin gadin ne sbd ta jima da ajiye matsayinta na princess Jannah Zad koina ne indai zata zauna ta rayu da familynta cikin kwanciyar hankali batada damuwar komai.
Kwanansu Dad goma sha shida suka dawo babu Hasken komai a tafiyar sbd duk inda suke saka ran samun wata mafitar babu,
Aiki harna tsaron shaguna da wasu guraren sun nema basu samuba gashi duk bashin da suka laftawa kansu ya qare ba aikin.
Bayan dawowansu su kawu suka sake bude wuta akan a basu kudinsu har abin yakai anfara samun matsala da damuwa sbd tini abin ya koma hadda gori da fade.
Dad ne ya samu su Kawun a Karo na ba adadi cikin nutsuwa ya sake rokonsu akan su qara musu lokaci.
Budar bakin Garba dake tsaye cewa yayi
"Baba ni idan zaka yadda inason Jannah a bani aurenta na bada dukiyar aure se abiya bashin da dukiyar Harma ayi canji"
Wani Amai ne me karfin gaske ya kubcewa Ammar dayake bayan Dad tsaya jin maganar Garba kamar saukar Mummunan qarnin kifin daya kwana cikin ruwan jini.
Maheer ma dagowa yayi yana yiwa Garban wani mummunan kallan baqin ciki me tsananin gaske.
Dad su kawun ya kalla yaga babu Wanda ya shiga mamakin zancen da alamar sun dan da maganar dan haka take yaji gabaki daya kauyen ya fita ransa fit sbd gwara mai aikin gadi daya nakasta rayuwar Hasken idaniyarsa.
Bude baki modibbo yayi yace
"Daman ta isa harta wuce aure kuma kila sbd itane basason aikin gadin sbd bazasu iya barinta ba hakama bazasu iya barin taje aikatau ba dan haka gwara AUREN nima na amince dashi"
Kawu Jibo ma kai tsaye yace ya amince shima.
Dad kuwa idanuwansa ne sukai jajir ya saukesu akan su Kawun sbd ya gama fahimtar toxartasu kawai suke son yi sbd suna rabe a gurinsu dan haka gwara ma su tattara din su qara gaban,
Bude baki yayi zaiyi magana Ammar da idanuwansa sukai jajir hannuwansa na rawa sbd wani irin azababben kishin dayaji Yana neman kashesa take ya riga Dad cewa
"Dad pls mubar nan koda a aikin gadin ne zan iya mutuwa idan naci gaba da zama anan"
Maheer ma kai tsaye ya amince da hakan Wanda shima Dad ya gwammace su tattara su tafi gurin aikin tinda zasu zauna gabaki dayansu guri daya cikin aminci.
#MAMUH
#BEST LOVE STORY
#AZIZ AY LIMBA
#ZAADENS
#JANNAH LIMBA
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 5
Da mamaki dukkaninsu kawu suka kallesu kawu isiya Yana cewa
"Au dukiyar aurence bazaku iya biyan bashi da ita ba kokuwa aurar da ita dinne baku tashi ba?"
Kawu Jibo ne ya qarasa dora masa zancen da cewa
"Kokuma Garba dinne bazasu iya bawa Yar gwal din ba kuma ba"
Da mamaki kawu isiya ya kalli Dad yace
"Aa wane su su fada hakan tinda a yanzu babu binda akafi karfin Garba dashi tinda shine yake da abinda basada shi a yanzu"
Daqyar Ammar yaji bugun zuciyarsa na dawowa daidai ya juya gefen Garba zai kallesa ya fasa sbd zuciyarsa zata iya bugawa kokuma zai iya shaqesa ya rabasa da duniya gabaki daya dan haka su kawun ya kalla yana kokarin dedeta numfashinsa yace
"Kawu kwata kwata fadar auren ne ma a tsakaninsu tamkar mugun sabo me zunubi ne sbd ko mun rasa komai a duniya Jannah tana nan a matsayinta na na sarauniyar Zaadens kuma darajarta ta wuce rayukanmu duka,
Duka wannan gwagwarmayar da aikin da muke nema sbd ita da Ummah ne kadai,
Duka abinda zamu nema mu samu harma mike son sake gina kanmu sbd mu basu rayuwar jin dadi d kwanciyar hankali ne kawai bawai munayi ne dan kanmu ba,
Hakama Jannah tamkar matar aure ce sbd ni Ammar Zad nine mijinta dan haka sunan matata ma ya fita a jerin hada sunanta da sunan wasu"
Maheer da Dad dake cewa yayi shiru baiyiba saida yakar karshe jikinsu mutuwa yayi da jin haryanxu Ammar Yana kan bakarsa ta auren Jannah wanda a yanzu kam zasu iya fuskantar komai dan aura masa ita ta yanda zasu rayu a guri daya dukkaninsu a duk inda rayuwa zata kaisu suna tare.
Afusace kawu isiya yace
"Dzad kana kallan danka Yana mana rashin kunya Yana nuna mana kunfi karfin hada zuria damu ko?
Waton Kun rayu a cikin arzikinmu idanuwanku sun bude yanzu kunada maganganun fada,
Ita Jannah din Banda farar fata da turancin banza sai sanyin jiki mara amfani kullum mace kamar amaryar Aljanu itace zaace tafi karfin auren danmu?
Maganar ta sosa zuciyar Dad da duka Zaadens din sosai sbd har abada Jannah a zuciyar Dad babu wani abu daya kaita daraja a gurinsa kaf kuwa a duniyarsa wanda yasan hakan shine babbar jarabawarsa sbd ko a yanzu da baida komai idan ya kalli Allah bai rabasa da abinda yafi so a duniyarsa fiyeda komaiba saiyaji shi baima shiga jarabawar komaiba,
Sai kuma Ummah a yanzu da haka kawai yake jinta itama a tsakiyar ransa saima yanajin kamar auren kuruciya ne yayi sbd a baya dukiya da daula tareda yawan yawon kasashe dayake bai samu time sosai ya bawa Mimi ba dukda irin son da itama yake mata me karfi Musamman da ciwon Jannah ya bayyana suka fara gwagwarmayar neman lafiyarta gabaki daya bai sake samun nutsuwan rayuwa data sukunin zama da Mimin ba yanda ya kamata har saida Jannah ta samu zuciyarsa Ummitah Limba,
dan haka a yanzu da Ummah take rayuwar aure dashi tamkar yarinya karama sbd yanayinta yasaka rana tsaka Allah ya sakata a tsakiyar zuciyarsa itama dan haka a rayuwa yanzu bayan Jannah Ummah ce mutum ta biyu da zai jure komai munin kaddara akansu sbd haka kuma bazai iya daukan kowane cin mutunci akansu ba.
Kawu Jibo bazai iya doguwar hayaniya ba sbd baqin ciki da bacon rai daya gama rufesa yace
"Kai isiya kanada karfin batawa ne akan wannan lamarin ne ai amma ga abu a bayyane kai tsaye idan bazaa bawa Garba auren Jannah ba a bamu kudinmu a yanzu a take idan yaso su aura mata sarkin larabawa mugani dan babu ubanda talauci baya sakawa ciwon hauka tinda ai suna da ma me haukar ai"
Miqewa tsaye Dad yayi batareda yace komaiba ya juya yabar gurin sbd yanda zuciyarsa tayi mugun daukan zafi hakama bayajin yanada energy din batawa gurin magana dasu kawun sbd kwata kwata yaji ya tsani cigaba da zama da iyalinsa a cikinsu.
Maheer ne ya kallesu tareda tattaro gabaki daya kudin dayake jikinsa ya ajiye gabansu ya bude baki cikin danne daci da baqin cikin dayake ransa yace
"Sauran kudinku din inshallah bazaa a kwanaki biyu zamu hada muku"
Kawu Jibo ne ya rufe ido yace
"Wlh tallahi kwandala kai ko sisi idan babu a kudina ni bazan karba ba"
Kawu isiya kuwa daukan kudin yayi ya kirga a nasa dubu Tara ne babu dan haka ya dunqule kudin ya saka aljihunsa yana cewa
"Na biyo dubu tara kuma nima wlh kwana biyu na bayar a hadomim dubuta Tara cif a ban idan ba hakan ba har birnin tarayyar zan samu mutum ba abinda ya damen"
Maheer bai iya cewa komaiba ya juya yabi bayan su Dad da suka wuce.
Koda Dad ya shiga gidan kai tsaye Jannah da Ummah dake zaune suna nade kayansu na wanki da Maheer ya wanke musu ya kalla fuskokinsu cikeda kwanciyar hankali da farin cikin kasancewa tareda ahalinsu.
Ajiyan zuciya ya sauke me zafi Yana rintse idanuwansa yana rokon Allah yayi masa arzikinda zai dawwamanar da farin ciki da kwanciyar hankali a wainnan fuskoki da zuciyar tasu.
Jannah ce tafara dagowa da fararen idanuwanta ta kalli Dad din kafin ta kalli Ammar daya shige dakinsu Yana dafe da kirjinsa dake masa wani irin nauyi sbd ambatar auren Jannah din kadai ya dawo masa da tinanin da ko a lahira yana fatar kada Allah ya hadasa da LIMBA,
LIMBA shine sunan da har abada harya bar duniy baya fatan ya sake ji bare tinawa,
Yana kullum yanda yake rokon Allah kada ya sake hadasu da ko me sunan AZIZ bare Limba baya rokon Allah yayi musu mafita kamar hakan,
Bazai iya sake rasa Jannah ba akowane hali dan hakama kawai a yanzu yake jin zuciyarsa ta bushe qamas gwara yaje aikin security din suje inda zasuyi rayuwa a natse ba barazana ko gori bare kauyanci da dabbancin da akeson kawo masa wai jannarsa da auren wani.
Tasowa Jannah tayi ta nufo Dad dinta ta kama hannunsa ahankali cikin kulawa tace
"Dad,akwai damuwa ne?
Kallanta yayi ahankali tareda sake damke hannunta ahankali cikin nasa yana jin kamar ya maidata cikinsa ta dena fuskantar kowace irin matsala,
Wai yau Princess dinsa ce a cikin wannan rayuwar bayan wani qaton banza ya mayar masa ita bazawara.
Rufe idanuwansa yayi ya bude yanajin radadin tinawa da Wanda ya maidata bazawarar kirjinsa na nauyin da haryanzu bai manta yanda azabarsa take ba sbd a rubuce a kaddarance AZIZ LIMBA shine kaddarar ZAADENS da har abadan abada komai nisa da yawan da zuriar Zaadens zasuyi bazasu manta ko goge wannan tarihin daya riga ya kafu ba.
Ahankali Dad din ya sake sauke idanuwansa da sukai sanyi akan fuskan Jannah Wanda fuskanta take bayyanarda a kowane hali zata iya rayuwa indai dasu ne duk da akwai ciwo da kunci me zurfin gaske a zuciyarta datake rufewa zata kuma cigaba da rufesa ta ringa hadiye quncin da radadin ita kamar yanda takeyi duk tsawon wannan lokacin batareda ta taba barin ansan asalin menene ciwon dayake cintaba a yanzu harya fara taba lafiyar zuciyartaba.
Cikin kunyar yarsa daya kasa bawa rayuwar data kamace ta yakega ya sake kalleta cikin sanyi ya bude baki yace
"Jannah kiyi hakuri na gaza a matsayina na uba....
Rungumesa tayi ahankali tana hanasa karasa maganar sbd itace ta kasa a matsayinta na 'ya sbd itace ta bude musu kofar duk wannan abinda yake faruwa dasu wanda kuma haryanzu take cikin mummunan kaddarar data kasa fizguwa daga zuciyarta dan haka itace take jin ta kasamtowa Yar halak ga iyaye da yan uwanta.
Dad sake mutuwa jikinsa yaci gaba da cewa
"Kome zai daidaita inshallah amma ayanzu muna buqtaan barin nan zuwa wani gurin wanda zamuyi aiki a karkashin wasu Wanda ina jin nauyi da kunyarki akan hakan Jan"
Girgiza kai tayi ahankali tana dagowa ta kallesa idanuwanta na cikowa da hawaye tace
"Dad Jannah ta dade da karban rayuwar da duk taxo gabanta matiqar bata sabon Allah bace,
Nayi aiki a karkashin wasu,
Nayi aikin gidan abinci nida Ummah,
Munyi aikin wanke wanke sbd mu tsayu da kafafunmu da tsira da mutuncinmu harmu samu haduwa daku dan qarasa rayuwa cikin amince dan haka Dad indai ina tareda ku babu aiki da wahalar da bazan iya jurewa ba,
Dad duk inda zaku tafi zamu iya jure koman wuya dan rayuwa tareda ku nida Ummah dan haka Dad har abada ka sani baka taba kasawaba a matsayin ubana ba,
Babu uba irinka a rayuwata kaine uban dayafi kowane uba a duniya,
You are my one and only hero
And you'll forever be,I love you Dad."
Rungumeta yayi Yana jin dukkanin kuncinsa na yayewa karfin gwiwa da zuciyar daya rasa suna dawo masa yanajin zai iya aikin dayafi security qanqanci sbd Jannarsa tinda tana tareda shi.
Hannu ya miqawa Ummah dake zaune tana kallansu hakanan jikinta na sanyi itama cikeda kauna yace mata
"Come"
Batasan me yace ba duk da dukansu suna kokarin mata turanci sbd yawanci idan suna tare turancin sukafi wa juna dan haka ta taso ahankali cikin farin ciki ta kama hannun daya Mika mata ya janyota ya hada da Jannah din ya rungumesu Yana sake samun nutsuwan zuciyarsa datake ciki da daci da qunci.
Ammar ne ya shiga dakinsu Jannah din ya hada musu kayansu itada Ummah guri daya Yana kokarin rufe jakar kayan idanuwansa suka sauka akan rigar data sakasa dakatawa Yana zuba idanuwansa akanta sbd rigar Maza ce hakama mazan se wanda yakeda duniya a hannunsa sbd designer ce ta asalin Balmain.
Hannunsa daya dan fara rawa kadan yakai akan rigar zuciyarsa na nauyi ya janyota ahankali daga qasan kayanta tin bai qarasa bude rigar ba qamshin daya doki hancinsa daga cikin rigar ne ya sakasa sakin rigar da sauri hannuwansa na wata irin rawa numfashinsa na sarkewa sbd sbd asalin qamshin Jannah ne na baya a jikin hade dana AY LIMBA Wanda shima bazai taba mantasa ba koda zai mutu ya dawo sbd qamshi ne daya zama gubar numfashin rayuwarsa gabaki daya.
Bugun zuciyarsa tsananta yayi tareda wani irin sarawan kai da rawar hannuwa Wanda yake nuni da ciwonsa daya kwanta fiyeda shekara Yana neman tashi tinda ba cikakkiyar lafiya ya samu ba daman.
Takarda ce idanuwansa suka hango masa a cikin rigar a boye Wanda ma envelope ne kalar milk da rubutun golden mw dubu daga can qasa Wanda kai tsaye yasan envelope din LIMBAs ne sbd kaf kamfaninsa haka rubutun yake milk envelope ko paper da golden a jiki uLIMBAS Wanda duk duniya babu wanda yasan me u din farkon take nufi bayan Sayd d mamansa sai yanzu ne duniya tasan Ummitah take nufi.
Nauyi kirjinsa yayi masa sosai yanason kai hannu ya dauki envelope din yaga abinda yake ciki sedai kuma yanda Kansa ke neman juyewa da bugawa tsabar wani irin kishin dayake jin kamar zai kashe basu bari ya iya motsawaba se rawa hannuwansa keyi har kafafunsa...
Jin qamshin LIMBA na gauraye dakin take yaji Yana suffocating da rarrafe ya isa kofa baya gani sosai ya fado tsakar gidan Yana Jan numfashinsa dayake neman daukewa.
#MAMUH
PLS AYI MUN AFUWA BAN NUTSU BANE WLH HARYANXU AMMA INSHALLAH DAGA YANXU POSTING YA KOMA DAIDAI DA YARDAR ALLAH.
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 6
Babu wanda ya lura da halin dayake ciki sbd shi Kansa ya hana a gane din kokarin boye halinda yake cikin yakeyi sbd barin ciwonsa ya tashi a wannan halinda suke ciki na rashin mafita kamar qara jefasu cikin masifane yakeyi,
Sedai kuma a dayan bangaren tsoro da tashin hankali me tsanani ne ya shigesa na ganin Jannah na tareda abinda ya shafi LIMBA Wanda Kansa da tinaninsa sun kasa tinano masa me hakan ke nufi.
Maheer ne ya shigo Yana sake kallan Jannah da Ummah dake jikin Dad cikeda kulawa ya musu bayanin zasu sauya gurin zama ne sbd rayuwa na cikeda qalubale Yana son duk abinda zasu fuskanta suyi hkr komai zai wuce hakama kome rayuwa taxo musu dashi zasu taru su fuskanceta gabaki dayansu sbd sunada junansu kamar yanda asalinsu Allah ya halicce su da kaunar junansu fiyeda komai.
Jannah gyada masa kai tayi tana janyewa daga jikin Dad ta koma jikinsa tana sake jin kaunarsa kewan Saleem Zad na saka idanuwanta cikowa da hawaye masu tsananin ciwo da zafin da har abada bazata iya yafewa LIMBA ba idan har zuciyar Saleem bata kirjinsa tana bugawa.
Dad ma hakanan yaji kewan Saleem din ta rufesa yana fatan Allah yasa yana cikin rahama da hasken kabari.
Jannah ce ta wuce ciki lokacin tini Ammar ya rarrafa ya shige dakinsu shida Maheer yana kokarin dawo da kansa daidai.
Maheer ne ya shigo shima sedai lokacin Ammar din ya dawo daidai ya miqe yana sake hada sauran kayansu.
Jannah kuwa dukda taga kayansu a yamutse batai tinanin komaiba ta qarasa hada musu kayansu kafin ta fito ganin Ummah na gurin Dad har lokacin saita wuce can kuryar gidan gurin jamaar gidan dasuke shirinsu sosai su babu damuwar komai a tsakaninsu.
Acan cikin gida Jannah ta sanar dasu tafiya zasuyi amma bawai kwata kwata ba aiki ne suka samu dukkaninsu zasu tafi.
Damuwar sabo da sukai sosai da Jannah da Ummah da kuma yanda suke qaruwa sosai da Jannah akan abubuwa da yawa datake koya musu Musamman na tsaftace jiki dama tarbiya ya sake sakasu jin ciwon rabuwa da ita.
Fatma kuwa kusan tafi kowa shiga damuwa da tashin hankalin rabuwa da jannah sbd gabaki daya rayuwarta ta sauya sbd Jannah gashi tinda ta taso haka take ba qawaye ba sakewa harta auren qananun shekarun da akai mata ta fito ta dawo gida sai xuwan Jannah ne ya kawo walwala da sanin ciwon kai da zama mace a rayuwarta Wanda a yanzu ta zama macen da kusan yanda akeson Jannah hkaa ake sonta sbd daman itama tanada hasken asalin Fulani da jiki me kyau dan haryanxu data dade gida batai wani aurenba shekarunsu daidai da Jannah gashi duk da basu taba zaunawa sukai fira ko maganar aurensu da kowanne ya fito a cikinsa ba dukansu sun karanto boyayyan qunci da rufaffiyar damuwa a auren bayan.
Dan hakanne ma takejin shakuwa da nutsuwan datake samu da rayuwa a karkashin Jannah zata iya binta koina.
Se washe gari ne tafiyarsu sbd motocin fita daga kauyen tinda sassafe suke wucewa dan haka dole sai washe gari zasu wuce.
Dad bayason rabuwar damuwa dasu kawun dan haka da dare acan cikinsu yayi sallar magrib da ishai ya nutsu ya sake fahimtar dasu komai gameda rayuwarsa da iyalinsa da yanda rayuwarsu ta sauya ya dora da godiya sosai tareda basu hakuri tin daga cikin ransa ya kuma samu sun fahimcesa sun kuma sauko sbd kusan suma haka suke tsananin kaunar junansu su ukun duk da su dukan sunada tsananin son kudi amma kuma sam basa barin kudin na hadasu sbd basa iya barin komai ya shiga kaunar da sukewa junansu dan haka sun fahimcesa yanda ya kamata tinda kusan kaunar juna duk tsanani duk wuya basa taba iya son wani fiyeda nasu Kenan abin a zuriarsu yake.
Godia Dad ya sake musu sosai akan halacci da kaunar da sukai musu Musamman akan Jannah da suka riqe cikeda Amana da kauna da kulawa tsawon shekara Guda da basa nan da gurin zaman da suka basu.
Ammar da Maheer ya kira ya saka suma suka basu hakuri tareda godia
Su kawun suka yafe musu harma Garba da Ammar yaji ya tsana take sbd ya furta Yana son Jannah saida ya danne zuciyarsa yai masa godia sbd shine ya zama wanda ya tsaya masa ya basa kariya da kulawa harya iya rayuwa me tsayi a kauyen sbd badan Garba din ba da tini ya mutu da tsoro da tashin hankalin abubuwa da dama na kauyen.
Jannah ma taxo tayi godia cikeda girmamawa da kaunar datakewa su kawun sbd ita a gurinta sune bangon daya bata majingina a