Showing 132001 words to 135000 words out of 150681 words

Chapter 45 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9071

har magrib tukuna ta koma gurinsa.

Ana gama magrib dukkaninsu suka fito a Shirye zuwa zaadens Banda Falaq da fiddausi daga shi sai Mama sai Nicky da Jannah din wadda ita take ganin komawa gidane zatai.

Sayd na parking harabar ZADs jikin Nicky ya sake sanyi idanuwanta dake kumbure sosai tin jiya sbd kuka ta dago ta Kalli inda suka Taho din tana sake Jin hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata.

Jannah ma hankalin nata duk a tashe yake da yanda Dad zai karbeta ko Maheer Dan haka jikinta yayi mugun sanyi ga tashin hankalin abinda ya kawo LIMBAS din zaadens musamman ganin AZIZ daya sauya take ya dauke dukkanin rahamar fuskansa ya kame sosai sbd fuskantar lamarin da Kyau batareda tsayawa duba matsayin kowa ba zai bawa lamarin gaskiyansa.

Ganin yanayin AZIZ din ya saka kowa sake shiga taitayinsa suka nutsu ga Nicky ma sai kukan takeyi sosai sbd kunya da baqin cikin abinda zasu fada a gaban kowa da Kuma fargaban kada garban yayi denying din cikin a gaban kowa sbd Bata buqatan komai bayan koma yayane uban danta ya Yadda da nasa ne Dan tanason babynta ya tashi da sanin yanada uba bawai a rasa ma wa zaa Kira da sunan mahaifinsa ba,
Garba ya yadda da shine Daddyn babynta ya isheta komai zuciyarta ta gama samun nutsuwa ta karshe akan babynta da zata Haifa abinta.

Saleem ne ya fito da kansa harabar gidan ya tarbesu cikeda kulawa da sakewa kaman family sai Kuma Ammar dayake motarsa yana waya sbd dawowansa kenan bai shiga ciki ba.

Fitowa motar yayi yana kallansu d mamakin ganin familyn su duka ya miqawa AZIZ din hannu yana Masa sallama da barka da zuwa Shima AZIZ din miqa masa yayi suna gaisawa yana tambayansa Ummah sbd sanin shine danta a yanzu.

Kokarin nufar ciki sukeyi gabaki dayansu Ammar din ya Kalli Nicky wadda take cikin doguwar hijab Kanta a qasa baice komaiba mama ya gaida kafin Jannah ta gaidasa suna gaisawa aka barsu a baya suka biyo bayansu yana magana da Jannah din wadda ke tambayansa su Dad duka suna ciki.

Dariya yayi me nutsuwa yana cewa

"Zaune Kuwa a palo dukansu harda su modibbo gashi tin jiya kawu isiya akai Akai saiyace wai ina Jannah ne?"

Kallansa tayi zuciyarta na sake tsinkewa jikinta na sake mutuwa da kunyar da batasan ina zata saka Kanta ba sbd damuwa.

Saleem na shigo kamshin AZIZ LIMBA ya sako Kai palon take Dad ya dago yana kallan kofar hakama Maheer da Ummah dake kokarin zama tin safe a sanyaye take da Mummunan labarin da mama ta sanar Mata.

Modibbo dasu kawu duka suna palon ana Zaune gabaki daya fira sukeyi table din tsakiyan palon cikeda chops kala kala dasu snacks masu dadi da Ummah da fatma sukai sai fruits da sukai sanyi sosai da aka yanka a babban tray aka ajiye da fork da bowls.

Sanyin AC da qamshin shegun designer turarukan kowa ne suka bada wani combo suke tashi Dan haka hankali kwance da annashuwa kowa ke fira su kawu sai cika Baki akeyi dasu apples da chops ana bada zance.

Shigowan LIMBAs ya saka kowa kallansu ana musu barka da zuwa da mamakin ganinsu su dukan a Daren.

Su modibbo AZIZ ya gaida bayan ya gaida Dad da Ummah tukuna ya bawa Maheer hannu suka gaisa Maheer din na baasa gurin zama.

Jannah a bayan Ammar ta Dan boye tana kasa fitowa gabaki daya ta gaidasu muryanta na rawa
Dad da kwanan zaune yayi sbd sanin Bata gidan kallanta yayi yana son yin magana amma Jin idanuwa Ummah Kafe akansa ya sakasa hadiye maganarsa yana kasa juyowa ya Kalli Umman.

Gurin fatma Jannah ta koma suka silale daga palon zuwa sama suka bar palon sunason magana kala kala a tsakaninsu.

Masu aiki ne suka sake kawo Karin chops da fruits suna yiwa AZIZ LIMBA barka da zuwa suka fice.

Rashin sabo da jituwan dake tsakanin ahalin biyu ya saka kusan zaman kowa wani iri yake jinsa Saida Saleem ya gabatarwa AZIZ su modibbo a matsayin iyayen Muhammad da Fatma.

Sake gaisawa sukai suma suna sake masa barka da zuwa,

A natse AZIZ din ya Kalli Dad Wanda yake satar kallan Ummah data hanasa tashi ya tafi da idanuwanta sbd yanda sukai dashi ta sanar Masa daga ranar da Jannah ta baro AZIZ to ita zata koma ta kula da 'danta itama.

Tinda ta fada Hakan ya kasa cewa komai akan dauke Jannah da AZIZ din yayi da anyi maganar Jannah sedai ya sauke ajiyan xuciya ya kasa maganar komai Dan haka ko yanzu din tinda suka shigo yake sauke ajiyan xuciya ta hadiye magana akai akai.

Cikin nutsuwa Kai tsaye AZIZ din ya bude Baki yana kallan Dad yace

"Magana ce me mahimmanci ta kawo mu wadda naji dadin daya kasance ma iyayen Muhammad din suna gari"

Kawu isiya na Jin Hakan ya hadiye apple din bakinsa dayake cike yana kallan AZIZ LIMBA din farin ciki na mamaye zuciyarsa sbd Jin maganar Garba ce me mahimmanci zaayi.

Su modibbo ma da suka kasa sabawa da sunan dakatawa sukai dukansu suna Maida hankali akan AZIZ din.

Shima Dad Shiru yayi yana sauraron AZIZ din sbd ganin yanda yayi maganar a kame da bawa maganar mahimmanci sosai.

Tsit palon yayi daidai nan Muhammad din ya fito daga hanyar dakinsa ya gamo Wani class da Ammar ya sakasa a online na koyan karatu Wanda yau suka jima basu gama ba.

Sanye yake da Gucci wears black da sukai Masa Kyau da black agogo a hannunsa.

Kallansa AZIZ yayi da idanuwansa da suke a tsananin kame Wanda Hakan ya saka kowa zubawa Muhammad din ido hadda Nicky din data dago jajayen idanuwanta tana kallansa sbd Sam ita ko kamanninsa bazata fada sosai ba tinda bama abinda yake hadasu kowa hanyarsa daban sbd matsayinsu daba daya ba.

Ganin ana kallansa ya sakasa qarasowa ahankali yana sauke idanuwansa akan Nicky wadda sai a lokacin ya lura da ita Kuma rabonsa dashi da ita su hadu face to face haka tin bayan faruwan mummunan kaddarar tsakaninsu Dan haka ya zuba mata idanuwansa yana kallanta cikeda damuwa da Jin wani irin ciwon laifin da suka taru suka aikatawa ubangiji.
#MAMUH
07019691719


Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman


Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 76

Takardu sayd ya qaraso ya ajiyewa Dad gabansa cikin girmamawa yana komawa inda yake zaune kusa da Saleem kowa na sake nutsuwa da shiga tinani da shakka,

Su modibbo Kuwa ganin takardu aka ajiye Kuma ance Muhammad take zuciyoyinsu suka sake cikewa da tsananin farin ciki da zaquwa suna kallan juna qasa qasa da maganar Ido a tsakaninsu bakinsu na kasa dena motsin Dan danne farin cikinsu.

Daukan takardun Dad yayi yana kokarin budewa AZIZ Kai tsaye ya katse Shirun da cewa

"Aysha Nicky na dauke da cikin wata biyar Wanda Kuma tace Muhammd ne Ubansa Wanda shine ya.......

Wani mugun yunqurin tasowan apple din da ba gama isa qasan cikinsa bane ya tasowa Kawu isiya yana dafe kirjinsa da karfi yana Maida abinda yake ji shine ya katse zancen AZIZ din Wanda ya Maida kallansa Kai tsaye kan Garba yana qarasawa da yanke zancen da cewa

"Ciki ne a jikinta Wanda nakeson jin shin kasan da Hakan?

Tsit palon ya dauka babu Wanda ya motsa kaman babu me rai a cikinsa Saida Mama ta ringa kallansu daya bayan daya tana ganin yanda kowannensu ya dauke wuta.

Kuka me cin Rai Nicky tafasa ahankali Jin kowa yayi Shiru damuwanta na sake tsananta da quncinta,

Mama ce ta dafata tana rarrashinta AZIZ Kuwa baya buqatan sake maimaitawa su gama shock dinsu su fito sai kowa ya maimaitawa kansa zancen.

Garba da yayi mummunan mutuwan tsaye yana kasa dauke idanuwansa daka kan Nicky wadda kukanta ke sake ratsa kowa palon Jin yayi jiri ya debesa ahankali ya zaunar qasa da karfi jajir idanuwansa sukai kirjinsa na cikewa da tsananin sabuwar baqin ciki da ciwon wannan mummunan kaddarar daya dauka sirrin rayuwansu ne da har abada basa fatan maimaitawa ko kansu ne bare wani yaji bai dena tubarwa Allah ba haryanzu sai Kuma kwatsam Allah ya ninka musu wannan jarabawan kaddara,
Cikinsa aka dauka Bata hanyar aureba ta hanya mafi muni da baqin ciki,
Me zasu fadawa yaron ko yarinyar idan ta girma?
Da wane idon zai iya kallan abinda zaa Haifa?
Wasu hawayen tsananin baqin ciki da sabuwar danasani ne suka gangaro idanuwansa dake rintsewa ahankali yana yin qasa da kansa cikeda kunya da baqin ciki mara misali.

Dad na ganin yanayin Muhammad din shock dinsa ya sakesa ya bude takardun hannunsa da sauri yana karantawa illai Kuwa takardun asibitin ayshan ne Dan watannin cikin tareda cikakkiyar lafiyansa.

Rawa hannunsa ya fara ya dago da sauri ya sake Kallan garban Wanda zuwa lokacin hawayen baqin cikinsa sun tsananta kansa na qasa yana kasa dagowa.

Maheer ne ya dauka takardun ya duba Shima yana bawa Ammar muryansa na rawa yace

"Duba mana likita da sauri"

Ammar da Shima mugun mamaki da tashin hankalin yake ciki karba yayi yana budewa yafara karantawa yana koro musu bayanin komai a bayyane.

Take kowa ya Maida kallansa kan Garba Wanda jikinsa ke rawa sosai yana Jin tsanar kansa gabaki daya.

Numfashi modibbo ya sauke lokacinda Dad da kowa suka dawo da kallansu kan su modibbon dake Kallan kowa da kalar tausayi sbd Sam basuma kawowa kansu Garba dai nasu ake magana akansa ba Dan haka kallan da aka juyo hankali tashe ana musu ne ya saka modibbon sauke numfashi yana kallan Dad da idanuwansa sukai jajir da tausayawa yace

"Allah sarki waye wannan ake magana ne akansa?
Akwai aure ne tsakaninsu Hakan ta faru?

AZIZ da baida lokacin batawa akan lamarin Kai tsaye ya kalli modibbon da mamaki kafin ya Kalli su Dad da suka kasa cewa komai kirjin kowannensu cikeda radadi da nauyi ya Maida kallansa kan modibbon ya bude Baki yace

"Garba dai gashinan a gefe shi ake magana yayiwa kanwata ciki batareda aure ba sedai bansaniba ko auren sukai ba sanin kowa gashinan nima amsa nake nema daga bakinsa"

Modibbo kallan Garba yayi ya dawo da kallansa kan AZIZ yace

"Wannan Garba din kake magana dai?

AZIZ din bai iya bada amsaba sbd zuciyarsa dayake iya kokarinsa gurin dannewa sbd girmamasu sedai mama ce takarbi zancen da cewa

"Gashinan ai tambayansa zakuyi duka yai mana bayani mu fita a duhu sbd ita dai yarinyar ta fada Wanda yayi cikin shikuma yanzu nasa bayanin muke jira asan abin yi tinda dai wanna mummunan kaddarar ta riga ta faru haihuwa ake magana yanzu datake matsowa........

"A ina haihuwan zata matso?" Modibbo ya katse Maman Shima ransa na fara baci da wannan mugun alkabain da ake kokarin binsu dashi wai haihuwan shege a gidansu.

Kawu jibo da duk zufa ta gama jiqasa kansa na neman kuncewa gyara zama yayi yana kallan Nicky yace

"Itace wannan me cikin?

"Itace" ummah ta bada amsa jiki a mace cikeda tausayin Nicky da garban Wanda har lokacin ya kasa motsawa hawaye yakeyi sosai.

"Qare mata Kallo kawu jibo ya hau yi haka Shima kawo isiya tinda akai maganar ya Kafe Nicky da idanuwansa ba ko kyaftawa Saida kawu jibo yace

"Jamaa wannan fa baturiya ce nake gani a gabana,
Itace tayiwa Garba cikin kokuwa shine yayi mata sbd nasan dai wlh wannan Garba bazai tinkareta ba sbd tafi karfinsa ko a ido matsayinsu bama dayaba,

Kawu isiya daya rasa abin fada kawai kuka sukaji ya fasa yana kasa cewa komai sai girgiza Kai yakeyi yana nuna Nicky yana nuna Garba saiya sake fasa kuka yana girgiza Kai hannuwansa na rawa.

Kalaman kawu jibo suka Sanya Nicky fasa sabon kuka ahankali tana Jin tsanar Kanta da Jin inama ta tafiyarta tin kafin kowa yasan da cikin taje wani gurin ta haife abinta ta renesa.

AZIZ ma kalaman sun sosa ransa ya dago idanuwansa jajir zaiyi magana Mai zafin gaske Mama ta hanasa ta hanyar dafa hannunsa tana kallan Dad Wanda su shine Wanda zasu iya fuskanta kansa a qasa idanuwansa jajir Shima tace

"Dzad kaine Wanda muka xo gurinsa Kuma muke fatar samun kyakkyawan fahimtar fuskantar wannan matsalar wadda badan darajar ku dinba da babu abinda zai hanamu daukan mataki sbd mune da mace mune aka Fi cutatarwa Dan haka muna neman Jin magana me karfi daga gareka kafin komai"

Dad da kirjinsa ma yaji yana ciwo sbd baqin cikin dayake neman kashesa na Yara daga wannan se wannan,

Ya gama fitowa shock din cikin Jannah yanzu Kuma a kawo Masa wani cikin shikenan jikokin zaadens dinma sirki zaa samu.

Cikin fushi da tsananin bacin Rai da baqin ciki Dad din ya Kalli garba yace

"Muhammad zakai magana ne kokuwa baqin cikin kake jira yayi ajalin daya a cikin ni dasu modibbo?
Meye muke ji yanzu da kunnuwanmu?
Meye tsakaninka da Ayshan?
Akwai muamalan data saka ake ambatarka da uban cikinta kokuwa ba haka bane kayi gaggawan bude Baki kayi magana"

Shiru kowa ya sake yi cikin zaquwa ana jiran amsarsa wadda yana bude Baki kawu isiya ya dakata da kukansa yana jiran amsar da zata fito daga bakin garban Wanda muryansa cikeda baqin ciki mai tsanani da kunyar Allah yace

"Muamala ta shiga tsakanina da ita bisaga kaddara Dan haka Bazan iya musa cewan ba Nine uban cikin ba,
Amma wlh tallahi kaddara ce da haryanxu ina neman tuba da gafara a gurin ubangiji.......


Wani salati me karfin gaske modibbo ya sake yana kallan Garba jikinsa na rawa hakama muryansa yace

"Garba soyayya kukeyi ne ko dole tayi Maka?kokuwa kudi ta baka??

Wasu hawaye masu tsananin ciwo ne suka sake gangarowa Nicky sbd tasan zai fada itace tai Masa dole Wanda Hakan zai qarasa zubar da martabarta ta har abada a idon kowa harma da abinda zata haifa sbd zaa goranta Masa wata ran uwarsa tayiwa ubansa Dole koma ace ta nemesa ko Masa fyade ma.

Shi kansa Garba maganar ta ratsesa sbd fadar koma Yaya almarin yake baida amfani tinda kaddarar dai ta afku Kuma kowa yanzu yasani Dan haka dago idanuwansa da sukai jajir yayi ya sauke numfashi me zafi ya bude Baki yace

"Babu Wanda yayiwa wani dole a cikinmu akan raayin mu ne da Kuma zuwan kaddara"

Hakan daya fada ya saka gabaki daya kowa ya sake shiga bacin Rai da fushi take modibbo ya fara zufa yana neman iska,

Kawu isiya Kuwa kuka ya sake fasawa yana dafe kirjinsa yana cewa

"Innalillahi ina zan Kai garba da abinda Garba zai haifa?
Garba jika bature ba aure Wayyoni Allah na me nakeji nake gani"

Kawu isiya ma rikicewa yayi Nan take yace

"Inace maganar cikin Jannah aka fara ita Allah ya yayyafawa kaddararta rufin asiri da aurensu itada mijin
Yanzu Kuma Garba da haihuwa ba aure,ita binnin haka akeyi kowa haihuwa kota Yaya?
Ina Fatma wlh tazo gida zamu koma bazan barta ba auren shehun da batason wlh shi zaa mata asiri rufe Shima garban wlh auren zamu Masa tin kafin kowama yaji maganar daya debo mana"

Modibbo da jikinsa ke tsananin rawa cewa yayi

"Da gaske dai garba cikin haihuwan Dan mutum ne a jikin yarinyar Nan Kuma Kaine uban?
Garba zuwa kayi ka fara Raba mana zuria ba aure?
Garba wlh tallahi aure duka zamu muku kaida fatma Dan zamanku anan ya qare tinda kuka fara haife haife"

Fatma da suke can gefe da Jannah kuka ta fasa jikinta na rawa Muhammad dinma kuka yakeyi sosai shi da Nicky wadda yanda ya rufa asirin ta ya Kuma yadda da cikinsa take tausayinsa Dana Kanta ya sake sakata kuka Mai sanyi tana jiran duka hukuncin da AZIZ zai yanke ko zabar mata.

AZIZ kuwa rasa ma abin fada yayi sai dayaga su modibbo sun miqe hankalinsu duka a tashe da tsananin no ciki da dacin Rai suna cewa ayau din zasu koma da garban da fatma take Shima ya miqe yana cewa ai babu maganar tafiya da Garba sbd shine yayi barnar Kuma shine zai runguma Nicky da babynta Dan haka maganar aurensa da kowama Bata taso ba sedai Nicky wadda tanajin Hakan ta sake fasa Kuka tana rufe Kanta cikin kafafunta.

Dad ma cikin damuwa da tashin hankali yace maganar AZIZ din itace daidai babu maganar komai data wuce a hada Nicky da garban aure tinda since da yardarsu suka muamalaci juna,

Maheer Kuwa da Ammar fatma dake kuka suka miqe suna tare su kawun dake daka mata tsawar tayi gaggawar hado kayanta ta fito su tafi ayau yau dinnan.

Rikicewa gurin yayi Jannah ma gurin Dad taxo tana rokonsa Dan Allah su modibbo suyi hakuri kada a tafi da fatma.

Cikin tsananin fushi modibbo ya Kalli zaadens din daya bayan daya kafin ya tsaida idanuwansa akan Dad dake sake magiyar suyi hakuri Dan Allah kada a lalata rayuwan Fatman a bari tayi karatun da ake kokarin farawanta.

Cikin fushi da wani irin baqin ciki da bacin Rai modibbo yace

"Wallahi fatma aure zamu daura mata ida kuma kana ganin zaka iya cetan rayuwan tata Da kake ganin zamu lalata to ai kanada Yaya Maza daura mata aure da daya a cikinsu musan a matsayin da zamu barta anan din"

Juyowa Dad yayi ya Kalli Maheer kafin ya Kalli Ammar da Saleem yanajin baida baqin ciki ko kadan Dan wani a cikinsu ya auri Fatma Dan haka ya tsayar da idanuwansa akan saleem Wanda Hakan ya saka Saleem saurin miqewa tsaye yana girgiza Kai tsaye ya bude Baki yana kallan AZIZ LIMBA yace

"Banda ni sbd inada mata ta already"

Gabaki dayansu suka juyo suna kallansa Banda AZIZ daya matsu a gama wannan tashin hankalin ya fadi nasa tsayayyen raayin akan Muhammad da zai auri Nicky.

Maheer Dad ya kalla sbd yasan Ammar bai gama Shirin sake bawa wata macen dama ba a rayuwansa yace

"Zan daurewa Maheer fatma inshallah"

"A gobe muke son Hakan Dan tabbatarwa kafin mu wuce mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login