Showing 12001 words to 15000 words out of 150681 words

Chapter 5 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9099

kawai ana rufe second gate kuma sukasan sun bar qasarsu a yanzu duniyar Familyn 4&4 suke ciki tsundum wadda babu komai a cikinta tukuna sai daular duniya da wata irin shiru da nutsuwa tareda kwanciyar hankali me sanyi da tsafta da suka ji suna samu.

Garba da Fatma da tinda Allah ya halicce su basu taba gani ko jin labarin irin wannan gidan ba da kusan komai nasa kashe musu ido yake hankalinsu mummunan tashi yayi sedai tsoron securities dake zagaye da gidan da bindigogi ya sakasu hadiye tsoronsa a cikinsu Wanda hakan ya ringa juya musu ciki.

Jannah da jikinta har lokacin yake a mace da sunan mansion din daya tinatar da ita rana mafi girma da muni rayuwarta itama hadiye radadin zuciyarta tayi tana jin wani irin ciwo a zuciya da kirjinta.

Ammar da bayan Jannah shi kadai ne ya riqe date din aurenta da LIMBA fes a cikin Kansa sbd shima bayan ranar rasuwar mahaifiyarsa ranar itace rana mafi muni da girman da bazai taba mantawaba a rayuwarsa sbd a wannan date dinne Jannah ta auri waninsa wanda a ranar zuciyarsa ta mutu a kirjinsa mutuwar da har yau bata farfado ba har sai ranar daya auri Jannah ta zama mallakinsa sbd baisan wane irin girman so yakewa Jannah Zad ba.

Dad da Maheer kuwa ajiyan zuciya suka sauke atare cikeda samun nutsuwan zuciya da ruhi sbd sunzo inda zasuyi aiki da karfi da lafiyarsu sbd Jannah da Ummah su samu rayuwar jin dadi da kwanciyar hankali sbd anan tsaro da kariyar da Jannah da Ummah zasu samu ko a nasu mansion dinne iyakacinsa kenan sbd ko qara da hayaniyar waje ko kadan baka jiyowa duk da wata irin anguwa ce da kusan tsaro da tsari tareda rashin hayaniyarta zai tabbatar maka da sai Wanda yakai iya kaiwa yake zaune a cikinta.

Hannun Ummah dayake hannun Dad ya sake riqeta da kyau Yana kallanta cikin kulawa zaiyi magana Chief ta maaikatan gidan ta fito babbar mace da ita Amma ba sosai ba hakama da gani batada sakin fuska ko sakewa ta qaraso tana kallansu daya bayan daya ta tsayar da idanuwanta akan Jannah Wadda take tinanin kamar ta taba ganinta sedai kuma ta kasa tinano inane dan haka ta gyara tsayuwa tareda bude baki ta amsa gaisuwarsu ta ciro wayarta daga aljihun kayan jikinta ta bude sakon da tin jiya aka turo mata na ayyukan da aka riga aka rabawa kowannensu tana sake karantawa tana fadawa kowa gurin aikinsa tana rakasu gurin daya bayan daya har aka kammala kafin ta sake kallansu tace

"Familyn gidan gabaki daya basa qasar amma suna gap da dawowa dan haka kafin dawowansu kuyi iya kokarin tabbatarda Kun sabu da aikinku babu matsalar komai sbd kwata kwata a tsarin ahalin gidan basason matsala ko hayaniyar matsalar,

Akwai me gidan kwata kwata Wanda bama lallai zaku taba ganinsa ba so ba amfanin ku sansa sbd baya lokacin kowa a duniya idan Yana gida bayan na 'yarsa Guda daya tak Wadda itace kusan zuciyar gidan sai ku kiyaye,

Sai mahaifiyarsa da qaninsa sai kuma matar da zai aura inshallah itama kuna buqatan kiyayewa sosai sbd kwata kwata bata son kuskure koman qanqantarsa hakama kusan itace take juya iko a kaf maaikatan gidan sai kuma Yar uwar mahaifiyar matarsa wadda itace tamkar uwa kokuma ace yaya ga 'yarsa dan haka ina sake fada muku da murya me kauri akan ku kula sosai kusan abinda ya kawoku,

Baa fita koina 24/7 kuna cikin 4&4 hakama duk me magana ko wani abin daban ya dameni da zancen.

Tafiya tayi suka bita zuwa can bayan mansion din Wanda acan akai bangaren masu aiki anyi tazara tsakaninsu da bangaren masu gidan hakama bangaren masu aikin me girma da tsari sosai wanda shi kansa bangaren masu aikin kamar qaton gidan wani me kudin sosai sbd hatta ac dasu fridge akwai da lafiyayyun dakuna da gadaje da beddings da komai me tsari da daula.

Ajiyan zuciya Ammar ya ringa jerowa Yana hamdala a cikin ransa sbd Allah ya kaddari ya dawo cikin rayuwar jin dadin dasuka rasa hakama a yanzu zai samu nutsuwa da kwanciyar hankalin aikin wahalar ma kowane irine.

Bangaren maza daban hakama na mata amma akwai kofar baya data hadesu dan haka hankalinsu ya sake kwanciya hakama gurin cin abincinsu daya dan haka sai ya zamana kamar palo ne da dakuna tamkar dai sun kama selfcon.

Dakin Jannah da Fatma da Ummah daya da gadajen kwanciyar mutum daddaya Guda uku sai kowa nasa daban sai rug carpet me tsananin laushi da kyau da haske sai mirror da AC da wardrobe itama kowa tasa daban da toilet dinsu a cikin dakin dashima yake irin na masu hali sosai.

Suma dakin su Maheer hakanne sedai su gado uku ne dan haka aka bawa Dad daki daban shi kadai shima komai aciki dan haka dukkaninsu suka samu nutsuwar da suka dade basu samu ba daga nan Madam Sisi ta juya tabarsu zuwa nata dakin dayake daga baya babban daki ne ita kadai dayafi nasu duka tsari.

Kayansu suka ajiye kowannensu ya zauna Yana sauke numfashi kafin Jannah ta kama hannun Ummah zuwa toilet ta nuna mata yanda zatai amfani da komai kafin ta barota tayi abinda zatai tayo alwala ta fito.

Fatma ce ta shiga bayan fitowan Umman itama Jannah ta sa fahimtar da ita komai tayo alwala ta fito kafin Jannah din ta shiga karshe.

Sallah sukai dukkaninsu suna idarwa wayar dake dakin ta hau ringing Jannah ta miqe ahankali ta isa ta miqa hannu ta dauka a natse tace

"Yes ma'am?"

Madam Sisi ce kai tsaye tace su fito su tafi kitchen.

Cikin sanyi da nutsuwa Jannah din tace "ok"

Ajiye wayar tayi jikinta na mutuwa dan batasan ta yanda zasu ringa aiki a karkashin mutanen da batasan yanda zasu ringa treating nata da familynta ba.

Gurin Dad Jannah takai Ummah har dakinsa kafin ita da Fatma suka wuce zuwa lafiyayyan kitchen din da acan ne zasu ringa aiki kafin masu gidan su dawo su koma aiki acan na cikin mansion din na masu gidan.

Koda suka isa akwai wata me aikin da suka gani dazu tanata aikin abinci dan haka kai tsaye suka saka hannu tana sake musu bayanin aikin suna yi.

Duk da aikin gas ne kuma a tsararren kitchen amma sbd abincin mutane da yawa ne hakanan sukaji sun aikatu sbd ana gama na rana aka Dora na dare ba bata lokaci kuma lafiyayyan abinci akeyi Wanda yake cikeda lafiyayyun kayan abinci.

Sai bayan ishai suka baro kitchen din sbd duka kayan abincin da akai aiki dasu saida aka wanke aka maida kitchen din kamar baayi aikin komaiba.

Jannah bata iya cin abincinta na dareba sbd cikinta daya cunkushe da yanayin kamshin abincin da kuma na rana da bai gama narke mata ba datake ji.

Suna isowa daki wanka tayi da sabulun dove da shine aka raba musu kowa anbasa set na kayan wanka da sabulu isashen da zai karshen wata hakama toothbrushes da toothpaste masu kyau da tsada duka an raba musu da body oils masu kyau da body sprays da qarin kaya kala bibbiyu sbd baa bari kazo da wasu tarkacen kaya.

Tana fitowa wankan sallah tayi ko Mai bata iya Shafawaba ta zame ta kwanta.

Ummah dataga yanda gajiya take bayyane qarara a tattare da ita zaunawa tayi kusa da ita tana cewa

"Ummijan kin gaji ko?

Gyada kai Jannah tayi tana matsowa ta kwanta jikin Umman tana cewa

"Ummah koina ciwo yake mun"

Mai Umman ta miqa hannu ta dauko tana budewa tace

"Gobe zan tayaki sbd kada ki gaji irin haka,
Banason kina gajiya ke kadai kinji"

Man ta fara Shafa mata a kafafu tana Danna mata kafafun ahankali cikeda kulawa.

Lumshe idanuwa Jannah tayi tana jin dadin yanda Umman ke mata tausan tace

"Ummahna bazaki iyaba kuma nima banason kiyi aikin ki gaji irin hakan ki bari duk ranar dana gaji zance ki tayani kinji"

Shiru Umman tayi sbd bata yadda da hakan ba.

Fatma ma wanka tayi Tai sallah Amma sanin batada me bata irin wannan kulawan ya saka tana gama sallah ta hau gadonta ta kwanta take baccin samun lafiyayyar katifa da AC ya dauketa hadda wani irin gurnanin bacci kamar ba maceba.

Jannah ma a jikin Umman tayi bacci hakama itama Umman data kasa tadata a gurin bacci ya dauketa se dare sosai Jannah na farkowa ta tashi ta tada Umman suka hau gado ta rufe Umman kafin ta koma nata gadon ta kwanta take bacci me nauyi ya sake dauketa.


Washe gari Ammar da wuri ya tashi yayi sallah ya ringa yiwa Allah godia sbd rabonsa da baccin nutsuwa da kwanciyar hankali irin na yau tin ranar da AZIZ LIMBA ya bayyana rayuwarsu dan haka yau da wani irin nutsuwa da sanyin zuciya ya tashi ya kwana a cikin lafiyayyan guri da AC da bargo me kyau yayi wanka da ruwa me tsafta da dumi a cikin toilet mafi nutsuwa hakama da soap me kyau duk da kwata kwata ko kusa bai kai Wanda yake wanka dashi a baya ba sbd sabulun wankansa a baya kadai zai ciyar da wasu da yawa Amma dai a yanda rayuwa tayi dasu yanzu wannan dinma ai babban cigabansu ne wanka dashi dan haka wankan tsafta yayi yai brush da lallausan brush yana sake godewa Allah kafin ya fito aikinsa.

Kusan hakanne ya faru da kowannensu dan kuwa sunyi tashin nutsuwa yau kowa fuskansa bayyane da kwanciyar hankali suka fito ayyukansu.

Dad da Maheer ne securities din second gate dan haka uniform dinsu suka saka suka isa bakin aiki.

Garba kuma wankin bangunan gidan dana motoci da sharan harabar gidan tin daga first gate har second shakuwa Ammar duk wata flower da grass dayake gidan shine me kulawa dasu tareda harkar ruwa shima tin daga gate din farko harna biyun.

Breakfast aka kaiwa kowa wanda su Jannah ne sukai aikin Fatma ce tayi kaiwa kowa harfa securities na can babban gate.

Ummah baya yadda ba saida ta biyosu kitchen dan haka aikin yankan su albasa da bude Maggi ne kawai suke bata.

A kitchen suka wuni se yamma suka kammala komai aka kaiwa kowa nasa sukai wanka da sallah suka zauna hutawa.

Da dare gabaki dayansu sukaci abinci a tare a palon dayake nasu hankali kwance suna firarsu kowa na fadar yanda yafara ji akan aikinsa suna dariyan juna sbd sun ringa sun karbi wannan sabuwar rayuwar kuma.
#MAMUH
#LOVE
#4&4BEST LOVE
#AY LIMBA
#HOT LOVE
#BOSS GOING CRAZY FOR.......
#JANNAH ZAD
#FALAQ LIMBA
#ZAADENS


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899
*_KALBIM_*
Mamuhgee


Book 2
Chapter 8


Washe gari ma hakance ta kasance sosai kowa ya maida hankalinsa akan aikinsa duk da dukkaninsu babu Wanda bai fara fuskantar rashin sabo da aikinba Musamman Ammar da aikinsa yake da wuya sosai shida Garba kullum sai sunyi aikinsu ko akwai datti ko babu dan haka Maheer ganin yanda Ammar ke shan wahala sosai duk da baiyi complain ba sbd ya qwallafa rai Sosai akan zaiyi aiki dansu tsayu da kansu bazasu dawwama a cikin wannan bautarba dan haka ya fara tayasa sosai sbd su nasu aikin gadi ne kawai tinda babu masu isowa second gate se masu gidan dan haka babu wani aiki su kam sai masu gidan sun dawo tukuna nasu aikin ya fara tinda a bakin gate din ma kila zasu riqa kwana sbd koyaushe masu gidan zasu fita ko dawowa.

Su Jannah ma ahankali da kwanaki suka fara tafiya suka saba da aikin Wanda a yanzu da suka fahimcesa suka ga kamar ya rage yawa sbd kusan sun rabawa kansu aikin ne sai kowannensu na dan samun lokacin hutawa dakyau.

Iya masu aiki da securities din gidan akewa abincin safe rana da dare shikenan ne kadai dan haka suka nutsu suka fahimci aikin sai ya dena wahalar dasu suka samu qarin nutsuwa.


Watan farko da aka basu albashi kowannensu kusan kasa gasgatawa sukai Amma duba irin mansion din da suke sai sukasan fiyeda hakanma koma waye me gidan zai iya dan ko yanda ake kashewa maaikatan gidan da securities kudi gurin ciyarwa da buqatu ma kadai kasan koma waye yakai kuma yanada ilimin da kusan ya wuce nasu sbd komai a waye ba cutatarwa.

Waya suka bawa Madam Sisi ta siyowa Dad dasu Maheer Jannah tace bata buqata.

Su Garba ma da fatma tin kafin su shigo aka bude musu acct dan haka suma direct kudinsu ke shigar musu su kuwa Zaadens gabaki daya a acct din Dad kudinsu ke shiga dan haka saving kawai zuka fara tinda babu abinda zasu buqata a yanzu bayan wayar dan haka ita kadai suka siya.


******Lokaci Yakuma tafiya ahankali ahankali har sun share kusan wata biyar a 4&4 mansion sun saba sun zama maaikatan da Madam Sisi da can kamfani ke alfahari dasu hakama zuwa wannan lokacin dukkaninsu wahalar ta riga tabi jikinsu sunma dena jinta aikinsu sukeyi hankali kwance da kwarewa.

A bangaren samun lafiya da sauyi na komai sun gama samu sbd gabaki dayansu babu Wanda bai sauya ba ya dawo hayyacinsa,

Sun samu sauyin fata me kyau sbd a tsawon watannin nan basu taba fita ba sai ranakun jumaa da ake barin su Maza maaikata zuwa sallar jumaa Amma bayan ita a lafiyayyan masallacin dake cikin mansion din dukkanin maaikatan gidan musulmai ke sallah dan haka basa cikin wata doguwar wahala,

AC da samun abubuwan amfani masu kyau ya sakasu farfadowa daga mutuwar tsayen d sukai,
Garba ma ya sauya sosai ya wanke ya zama dan birni,

Jannah batai jiki ba kamar yanda Fatma tayi jiki sosai gabaki daya ta cire ramar datazo da ita tayi haske abinta kamar ba Fatman kauye ba,

Jannah haskenta ne daya dan rage ya bayyana sosai sosai ta koma fresh dinta Amma sam batai wani jiki ba,

Ummah ma tayi haske ta sauya sosai itama sbd kulawan datake samu sosai yanzu a gurin Dad duk da tana aiki tareda su Jannah Amma suna tattalinta da tarairayanta sbd tsoro da gurin tayiwa kanta wani abu da wuqa da koyaushe take hannunta gurin aiki dan sam su Jannah basa barin ta kusanci inda gas yake.

Amina shine sunan dayar me aikin da ayanzu dukkaninsu akwai shakuwa ta aiki a tsakaninsu hakama ta bangaren Madam Sisi tafi jin Jannah kaf a cikinsu sbd iliminta dayake a bayyane dan komai nata a natse ba hayaniya ba gaggawa sai hakan ya saka tafi jinta takuma fin jin itace kadai wadda zata iya kai tsaye bawa ragamar kulawa da komai na Mai gidan ko yarsa sauran sedai suji da sauran ayyukan sbd nutsuwa da rashin hayaniyar Jannah din takai wani level da take ganinta kamar sarauniyar wani gidan masu kudi.


Lokacinda suka cike wata bakwai a lokacin ne jikin Ummah ya ringa rikice musu akai akai kuma da tsanani dan haka duk hankalinsu ya tashi suka shiga damuwa walwalansu ta rage kwata kwata gashi basuda yanda zasuyi haka suka ringa lallabawa sunason su sake Tara abinda suka Tara saisu fara nema mata lafiya.

Hakan ya saka Umman ta rage zuwa kitchen sosai sbd koyaushe cikin qunci take haka kawai,
Duk yanda Jannah tayi dan sakata walwala ko farin ciki bata iyawa sedai tayita binta da idanuwanta dake fidda zallan qunci dayake rufe da zuciyarta gashi bata iya furta abinda takeji bare suyi tinanin ta Tina wani abu na rayuwarta dan haka sedai suka koma lallabata,

Dad duk dubaru da rarrashi da kulawa babu Wadda baya mata sbd ta dawo Matarsa daya sani me saka zuciyarsa samun nutsuwa yayi Amma babu sauyi dan hakama ta koma gurinsa take kwana sbd acan dinne ma take samu tayi masa kuka sosai sai ta rage nauyin kirji tayi bacci wanda shi kadai magani da sassaucin datake samu.

Ana haka Chief din gidan gabaki daya shikuma yazo ya sanar da dawowan masu gidan dan haka a karon farko da aka bude musu asalin cikin mansion din suka shiga suka wuni suna aikin gyara.

Tin daga ranar kullum sune masu zuwa aikin gyara cikin gidan sbd akalla afi satika ana gyara koina kullum kafin dawowansu yanda gidan zaiyi kamar daman akwai mutane.

Sabbin masu aikin abinci aka kawo su biyu aka hadasu da aminah a kitchen ita da Fatma kuma aka dawo dasu bangaren masu gidan gabaki daya da aiki.

Babu komai na masu gidan sbd da alama yanzu ne zasu fara zama sabon gidan basu ma taba zuwansa ba se yanzu dan haka babu kowane irin abu daya shafesu bare ya nuna yanda suke sai idan sunzo tukuna.

Aikin ciki yanzu bame wahala bane kamar na kitchen dan haka hutun da suke samu yanzu ma yafi na bayan.


*************
SIDNEY

White Royce Royce ce ta sako kai a harabar gidan datake zagaye da fresh flowers masu kamshi da tsari da qamshinsu ke tashi ahankali yana gauraye harabar gidan.

Da kansa ya tuqo motar sbd daga airport yake yaje yayi sallama da wasu baqinsu da suka taho daga Cyprus sunyi sealing wani babban deal na sabbbin kamfanin daya bude na 4&4 tinda sassafe ya fita tin gari nada sauran duhu.

Sayd ne da tasa motar wata blk Lamborghini ta biyo bayan shigowanta LIMBA yayi parking can gefe daban ya fito yana kashe wayar dayake yi da baqin da shima tin safe ya fita sallama dasu ya nufo motar.

Waya LIMBAn ya tsaya amsawa a natse kafin ya kashe daidai Sayd n bude masa motar ya juyo fararen idanuwansa masu wani irin kwarjini da asalin kyau ya kalli Sayd din ya ziro kafafunsa ya fito yana zanye da sweatsets na Balmain milk da hular sanyi akansa data rufe lafiyayyan gashin gashin Kansa da kunnuwansa.

"Good morning Hamma" Sayd ya fada Yana kallan kyakkyawar fuskansa da haskensa yake qarawa kwarjininsa yawa.

Sake dagowa yayi ya kalli Sayd din sbd a duk lokacinda ya ambacesa da Hamma yanajin zolaya ne kokuma son tabasa.

Kallan da yayiwa Sayd dinne ya saka Sayd din sakin murmushi me kyau Yana kokarin sake magana LIMBAn ya a katsesa a natse da Murya me Kamala da wani irin class da cewa

"Arrangement din sun zama ready ne??

"Yes,komai anyi angama handing over dinma ya tafi smoothly,
Anjima 12 zaa qarasa bord meeting tareda chairmans din NIELS PUBLISHERS na duka branches din harda na Greece da China duka,

After that chairman na 4&4 Sidney Branch ya aiko da email na record da zaka duba daga nan sai time na haduwanka da doctors din Falaq Aziz after that kuma.....

Hannu ya dagawa Sayd din a natse Yace

"Daga nan kayi canceling sauran schedules din sbd daga asibiti zan dawo gida da Falaq Aziz da kaina"

"Yes" Sayd yace yana fiddo wayarsa dan cancelling sauran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login