Showing 138001 words to 141000 words out of 150681 words

Chapter 47 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9068

suka dawo gida sbd lafiyayyan reception da akai na masu abin duniya securities tako ina daga can AZIZ Kai tsaye gida ya koma shi Kuwa Sayd airport ya wuce yana ajiye AZIZ din gida yaje daukan Baba Al'hassan daya iso ayau din.

Tinda aka dawo daurin auren anata Dan sake taya juna murna su mama sunwa su Dad da modibbo Allah ya Sanya alkhair hakama Modibbo ya kira Fatma sun mata nasiha sosai suka Dora da maganar Garba Shima sukai fadan daya saka jikinsa sake sanyi kafin suka hakura tareda rungumar komai suka Barwa Allah.

Fatma sama ta koma Bata bari sun hadu da Maheer din ba sbd tasan dai Yana gidan tinda kowa ya dawo.

Sai magrib su Mama suka tafi gida gabaki dayansu Banda Falaq data maqalewa Jannah dole suka barta.

Da daddare kowa a gajiye yake Dan haka abincin Daren ma kusan kowa daban yaci sbd wasu a daki aka Kai musu wasu Kuma sun fito dining din koda 9 zuwa 10 na dare tayi kowa ya shige sbd neman hutawa.


Sai washe gari dukkanin suka hade a dining kowa gajiyansa ta sakesa.

Fatman ce dai kaman yanda ta saba sedai wannan Karan tana Jin nauyi yana hawa Kanta yana mata yawa ita ta saka aka shirya dining din yanda ya kamata ta qarasa gyara komai ta koma tayo wanka ta sauko a Shirye ciki riga da skirt na lace me laushi na hayaniya ta sake komawa kitchen ta hado Turkish tea da kusan kowa yana Sha ta nufo dining din lokacin kowa ya iso suna zaune.

Jin tayi jikinta na neman sanyi amma dai a daure ta qaraso tana ajiyewa ta gaida Dad cikeda nutsuwa da girmamawa kaman yanda suka saba.

Amsawa yayi cikeda kulawa yana sake jinta ta zama cikakkiyar yarsa yanzu data zama tasu har abada tinda ta riga ta zama matar Maheer dinsa.

Maheer din dake zaune sanyeda milk tsadaddiyar yadi me laushi daya Masa Kyau ta kalla cikin sanyi da mutuwan jiki tace

"Ina kwana Yaya Maheer"

Dagowa yayi daga wayarsa dayake kokarin ajiyewa ya zuba mata idanuwansa yana kallanta ita Kuma ta sauke kai ahankali tana Dan wasa da farcenta dayasha gyara jiyan yayi fes yana Dan shining.

Bude Baki yayi ya amsa a natse yana dan rage kallansa akanta,

Ammar ta gaida kafin Muhammad tukuna Saleem Wanda ya dago Dan amsawa fararen idanuwansa suka sauka akan Falaq dake tafe tareda Jannah sanye da riga da wandon Bvlgari da babu inda suka kama jikinta sunmata Kyau sosai sbd yarintarta ta fito sosai qaramar silk Louis Vuitton scarf ne a Kanta itama shi ta kalla ganin yanda yake kallanta ta juyar da idanuwanta tana bude Baki ba sauti tace

"Falaq Aziz ta fasa"

Wani mayen murmushi ya sauke yana Dan sauke kansa sbd kada kowa yaga halinda yake ciki ya Dan dago ya sake Kallanta ta sake juyar Masa da ido tana lafewa gefen Jannah.

Kansa yaji yana neman zarewa sbd Jin kaman ya janyota gabansa yayita kallan cute eyes dinta da bakinta me fadan ta fasa din.

Ganin murmushinsa dake sanyaya zuciyarta tin ba yanzu ba ya sakata sake boyayyar murmushi tana zaunawa gefen Jannah bayan ta gaida kowa cikin sanyi da yar shagwaban data taso a cikinta.

Breakfast din suka fara idanuwansa duk motsinta suna Kanta harma ta gaji cikin narkewa tace

"Saleem pls ka dena mana"

Da sauri kowa ya Kalli Saleem din Wanda ya Dan ware idanuwansa akanta yana kasa kallan kowa dake masa kallan mamaki.

Itama da maganar ta fita bakinta ba shiri saurin kallan kowa tayi tana cewa

"Sorry"

Jannah ce ta kalleta qasa qasa tace

"Me ya Miki?

Ruwa ta dauka tanasha fries din bakinta ya wuce tace

"Ze cinye wa daddy ni da ido ne"

Saleem daya ji abinda ta fada rintse idanuwansa yayi yana sake tausayawa kana da yarinyar Falaq da koyaushe yake fama da ita.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 79

Suna gama breakfast din kowa ya bar dining Fatma Kuma ta koma kitchen Dan rage wani aikin,

Jannah gurin Dad dinta ta tafi tareda brothers dinta suka shige Palonsa suna tattaunawa sbd tafiyan da Maheer zaiyi wani business deal kwanakin gwara ya tafi da fatma kawai wadda tana dawowa zata fara karatunta.

Ummah Kuwa tana dakinta itada Falaq suna fira tana Dan hada kayanta ta dauki waya ta kira sayd Kai tsaye tace yazo ya dauketa zata zo Nan gida.

Acan LIMBAs Kuwa koda Umman ta kira suna tattaunawa ne akan maganar aure da baba Al'hassan ya Tarasu yayi musu gabaki dayansu hadda AZIZ daya kamata ace zuwa yanzu yana guri daya da iyalinsa bai kamata aceba sunada aure amma tana gidan iyayenta a zaune.

Jin Ummah na tafe ya saka baba Al'hassan din taqaitawa sbd idan taxo a sake zaman na ita sbd hankalinsa ya tashi kawai da wannan lamura tinda koshi AZIZ din me auren kwatsam kowa haka yaji cikin babu wani tarewa babu wani zance babuma Wanda yasan da sauran ran aurensa Dan haka Shima ai duk abin mamaki da fargaban ne Dan haka ya kame ya bada umarninsa me karfi na karshe akan kowa ya gabatarda abokin rayuwa ayi musu aure.

Sayd daya rasa ta inda zai fara bayani Shiru yayi har aka gama tukuna ya fice zuwa dauko Umman,

Itama fiddausi Shirun tayi tana kasa dagowa ta kalli baban Dan batada abin fada bare iya fadan waye suke tare dashi hakama itama tinda cikin Nicky ya bayyana na Muhammad ne take cikin tsoro da tsananin kame Kanta daga zuwa dakin Sayd tin suna Greece sbd Bata daukesa komaiba kaman yanda Shima be dauka komai dinba sbd turai data ratsasu daidai gwargwado.

Yanzu Sam bata zuwa ta dena zuwa sbd kaucewa kaddarar shedan Dan kila su Kam AZIZ Batama San hukuncin dazai musu ba.

Sayd na fita fiddausin ma ta miqe ta fita ta koma dakinta tana tinanin kada ace auren hadi zaa musu daban daban da wasu idan basu fada halinda suke ciki ba.

Ko da Sayd ya iso Falaq na hangosa ta window din saman ta sauko da sauri suka hade palon qasa daidai yana shigowa da sauri ta kama hannunsa tana cewa

"P badai daukana kazo ba?
Ni tareda Jan zan koma fa,
I love staying here..." ta qarasa fada tana kallan Saleem daya qaraso fuskanta da sanyayyan murmushi tana sake lafewa gefen papan nata.

Wani mayen Kallo Saleem din yayi mata yana jin tako ina yarinyar tai Masa illar da baya iya control na idanuwansa da xuciyansa idan tana guri.

Hannu ya miqawa sayd suna gaisawa cikeda sakewan datake tsakaninsu Dan wani irin shakuwa da sabo suna qarasawa ciki har lokacin tana maqale gefen Sayd din tana murmushinta.

Shakuwa ce da kulawan daya ringa bata a lokacin jinyarta da Kuma sacrifice dayayi akanta na Bata zuciyarsa wadda baa karba ba Kuma ya dage ya nace ya haukace Saida ya samo mata wadda take kirjinta ya saka soyayya shiga tsakaninsu wadda da farko dukkaninsu sun dauka shaquwa ce kawai da kulawan dayake mata me tsanani kafin daga baya daya fara zama busy suka fahimci suna cikin zuciyar juna,

Yayi kokari sosai gurin danne duk abinda yake ji a Kanta sbd taxarar shekarunsu me yawa da Kuma ganin tayi qanqanta amma Kuma shagwabanta da rashin wayonta ya saka zuciyarsa ta qarasa macewa akanta a hankali ahankali dole suka yadda da soyayyar da sukewa juna sedai ya sani zaman jiranta ne zaiyi har lokacinda zata gama duka karatunta.

A nata bangaren batasan komaiba bayan cewa Saleem Zad nata ne ita kadai,baida iKon kula kowace mace me shakaru da mara shekarun ita kadai take dashi Wanda Hakan ya saka sam Baya iya muamala da mata ko a gurin aikinsa irin sosai sbd kaucewa fitinarta da rigimarta wadda idan ta tashi Bata tina lokacinta baiyiba na irin wannan rigima take Masa sosai,

Daddynta da Sayd sunsan akwai shakuwa da kauna tsakaninsu sosai amma basusan da soyayyar data gigita musu yarinya ba bare kudirinta na batason dogon karatu saita fara auren Saleem Zad ya zama nata kafin ta qarasa karatun daga baya.

Suna qarasowa tsakiyan palon suna zaunawa Ammar ma yana fitowa a Shirye zai fita wani gurin Dan haka hannu ya fara bawa sayd suka gaisa a Mutunce haryana tambayar Yaya jikin Aysha tukuna ya fice daga Palon yana daga wayarsa da ake kira.

Ammar na ficewa fatma da Jannah suka sauko suna gaisawa da Sayd din suna kokarin zama masu aiki suka sauko da akwatinan Ummah suna ficewa dasu harabar gidan.

Gabaki dayansu miqewa sukai suna kallan kayan kafin Ummah dake saukowa hankalinta kwance fuskanta a sake tana cewa

"Aa Falaq Baki shirya bane?
Bafa zama Sayd din zaiyiba tashi ki dauko kayanki muje"

Falaq cikeda mamaki tana kasa cewa komai ta miqe tana nufar sama.

Jannah Umman ta kalla itada Fatma da Saleem da sauri tace

"Ummah tafiya zakiyi ne?
Ina zaki bansan zakiyi tafiya ba"

Saleem ma kallanta yayi yace

"Ummah lafiya dai ko?

Fatma cikowa kawai idanuwanta sukai batason ummah tayi tafiya a yanzu datake buqatanta.

Murmushi umman tayi tana kallansu tace

"Tafiya zanyi amma bama nisa zanyi daku ba gida kawai zan koma"

Tana fadar Hakan ta Kalli Sayd dayake kallanta da mamaki tace

"Muje na shirya"

Miqewa yai yana yin gaba tabi bayansa.

Dad ne ya fito daidai lokacin yaga Umman na ficewa ya kallesu ya bi bayan Umman.

A kofa ya cimmata yana saurin riqo hannunta yana dawo da ita baya kadan.

Ganin hakan kowa yabar palon
Jannah data fahimci kaman tafiyarta ne Umman zatai take hawaye suka ciko idanuwanta tafara gangarowa dasu tana son magana bama tasan me zata fada ba.

Dad dayaji zufa na kokarin keto Masa kallan Umman yayi yana sake riqe hannunta cikin nasa yace

"Fatima ina zaki tafi da kaya haka?
Meya faru Kuma?
Ba duka na dena shiga lamarin yaran ba na barsu,
Gashi ma yanzu komai lafiya"

Numfashi Umman ta sauke ahankali tana dagowa ta kallesa cikin nutsuwa tace

"Haryanzu akwai damuwan auren Jannah da AZIZ dayake damunka,
Kai fa mahaifi ne,tayaya kana kallo yarinya da aurenta tana zaune gida ta zabi zaman gida akan gidan mijinta sbd kawai tasan abinda yake ranka,

Aure tsakanin LIMBAs da Zaadens dai bazai taba yiyuwaba Dan haka kowane auren ma a hakura dashi kawai idan zaka zo karban takardar 'yarka saika kawo Masa takardar uwarsa daga nan.."

Tana gama fadar Hakan ta juya zata wuce Dad ya share wani mugun zufan dayake tsiyayo Masa yana kallanta duk yama rikice cikin qasa qasa da murya kada Yara su jisu yace

"Fatima wane takarda ana Zaune kalau da girmanmu?
Dena fada ma kada Yara suji
Ni yaushe nace zanje karban takardar Jannah?wallahi tallahi bance ba Kuma bazance bama,
Yi hkr yanzu ki koma ciki sai miyi magana anjima kinji?"

Numfashi ta sake saukewa tana zare hannunta ta wuce gaba tana cewa

"Kowa ya riqe nasa ai haka kakeso ko?

Mota ta isa daman sayd ya bude mata tana isowa ta shige a rufe Dad na qarasowa ya tsaya yana Kallo Falaq ma ta iso ta shige sayd yaja motar suka bar gidan.

Suna barin harabar gidan Jannah dake sama tana Kallo ta silale qasa tana kuka.

Fatma ma tashi hankalinta yayi jikinta na sanyi ta zauna tana rafka tagumi.

Dad jiki a tsananin mace ya dawo ciki ya shige Palonsa yana Jin gidan na Masa wani irin empty yakuma San duka yaransa babu Wanda bazai shiga tsananin damuwan rashin Fatiman ba musamman Ammar Wanda itace kamar garkuwansa a yanzu.


Sayd da Falaq baby Wanda ya iya cewa komai a motan har suka isa gida aka shiga ciki da kayan Umman Wanda ya saka Mama mamaki amman batace komaiba sbd ganin kowa na nan,

A lafiyayyan bedroom din dake Palo daya da Mama aka Kai kayan Umman,

Koda AZIZ ya taho gaida Umman yana ganin kayan datazo dasu baice komaiba Shiru yayi kaman bai luraba sbd ya dena shiga tsakanin Umman da Zaadens.

Har dare babu Wanda ya cewa ummah komai gameda dawowan nata itama batace komaiba haka suka sakewansu cikin walwala da farin cikin kasancewanta cikinsu.

Ammar na komawa gida a daren ya Samu Ummah Bata gida Dan haka kai tsaye LIMBAs din ya taho gurinta.

Yana zuwa har ciki aka shiga dashi bayan sun gaisa dasu AZIZ harma da baba Al'hassan Falaq ce takaisa har dakin Umman datake zaune tana waya da Jannah daketa rokonta ta dawo tana shashantar da ita.

Tana ganin Ammar din tai sallama da Jannah ta kashe wayar tana ajiyewa gefe tareda kallansa cikeda kauna da kulawa tana nuna Masa gurin zama.

Acan Zaadens tinda Ammar ya tafi suke fatan yadawo da Umman tinda sunsan tana ji dashi zata iya biyosa ta dawo Dan haka duka suke zaune a palo suna jiran dawowansu.


Sai dare sosai Ammar ya rabu da ummansa bayan sun tattauna sosai ya dawo gida,

Da mamakin rashin ganin Ummah suke kallansa Shima da mamakin ya kallesu yana basarwa yaci abincinsa ya shigewansa daki.

Haka kowa ya kwana jiki a mace washe gari kafin Maheer ya wuce office LIMBAs ya fara biyawa gurin Umman Shima yayi nasa rarrashi ya Dade sosai Shima kafin ya wuce office.

Kafin Kace me zaadens suka fara zarya a LIMBAs takai har dasu ake cin abinci wasu lokutan musamman Ammar Wanda babu ranar da baya zuwa gidan yakai dare sosai,
Maheer ma kullum saiya biyo kafin ya wuce office kokuma bayan ya dawo,

Saleem dayake kaman da gida shikam koyaushe ma zuwa yakeyi,
Muhammad ma tin yana Jin nauyin zuwa harya fara zuwa duba Aysha da cikinta da Kuma Umman.

Jannah da fatma ne kawai basu samu daman zuwa ba sbd Jannah na kunyar yanda zata zo gidan ta koma hakama shi kansa AZIZ din ya kawo idanuwansa ya saka mata bai nemeta ba bare ce mata Komai,
Itakuma fatma batasan yanda zata je gurin Maheer ta rokesa son zuwan bane shiyasa duk damuwa da kadaicin rashin Umman ya musu yawa suka koma abin tausayi a cikin gidan gashi su modibbo sun koma.


Dad ma da kwata kwata ummah Bata daukan wayarsa a cikin sati biyun take ciwon zuciya da damuwa suke neman Kaisa kwance Dan haka yau yana tashi Tara yaran yayi gabaki dayansu yayi zaman nasiha dasu yana Jin Sam bazai iya rayuwan ba Dan kadaici zai Masa illa da yaran duk da ba Yara bane amma zaman Umman yana sake bawa familyn farin ciki da jinsu a cike.

Da daddare kusan karfe goma Jannah harta fara Shirin bacci jiki a mace saiga Kiran Dad din a wayarta.

Hijab ta sako akan kayan baccinta ta sauko ta nufi Palonsa.

A tsaye yake ko data shiga Dan haka a Sanyaye ta qaraso tana gaidasa.

Amsawa yayi yana kasa kallanta yace

"Je ki hado kayanki yanzu ku fito muje"

Kallansa tayi da Dan sauri ya kalleta Kai tsaye yana cewa

"Kije"

Juyawa tayi ta fice cikeda mamaki me girma amma ba fuskan tambaya a gurinsa.

Dakinta taje ta kasa ma hada kayan sedai fatma da jikinta yake tsananin mace ne ta hada mata tana Jin kadaici tin yanzu yana mamayeta ba Ummah ba Jannah.

Saukowa sukai gidan tsit kowa na dakinsa Dad ya kama hannunta fatma Kuma takai mata kayanta har motan da Dad ya kira Muhammad ya Kaisa.

Fatma suna shigewa mota hawaye suka fara gangaro mata ta juya da Sauri tana komawa ciki sukuma suna ficewa Jannah ma hawayen takeyi.

Fitan motarsu Dad din ya saka Maheer fitowa sanyeda kayan baccin Frnsess masu santsi black da suka qarawa haskensa haske ya nufi kofar palon yana kallan time.

Fatma data shigo tana kuka mara sauti tana Jin gidan itama duk ya isheta Bata lura dashiba sbd hannuwanta dake fuskanta sai Jin tayi tai karo dashi da sauri ta janye hannuwanta hawayenta na gangarowa ta kallesa cikin sanyi da kuka tace yayi hakuri.

Kallan bakinta da yayi maganar da hawayenta dake gangarowa yai yana Jin tausayinta kafin ya bude Baki yace

"Waye ya fita?

"Dad ne da Jannah ya tafi kaita"

Shiru yayi yana kokarin juyawa ta bude Baki tace

"Yaya Maheer nima dan Allah zan bisu saimu dawo tare da Ummah"

Dakatawa yayi sbd Jin zancen wani iri da Kuma muryan datai amfani da ita gurin zancen.

Juyowa yayi ya kureta da kallo me sanyi kafin ya miqa hannunsa ahankali ya kama nata ya janyota gabansa sosai har kirjinsu na haduwa yace

"Ita Jannah gidan aurenta ta tafi,
Ita ummah mijinta ne yakai mata sirikarta ya daukota ita Kuma ke Kuma me zaace kinje yi?

Kin manta kinada aure ne yanzu?

Gyada kai tayi cikin wauta da Kuma fadan gaskiyanta tace eh ta manta.

Da mamaki ya sake Kafeta da ido yana auna shekarunta Dana Jannah wadda ya kusa haihuwa.

Ajiyan xuciya ya sauke yana Dan rankwafowa ya dauketa cak gabaki dayanta yana nufar dakinsa da ita sbd Bata matsayin da zai hanata manta auren dayake Kanta daga yau din.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 80

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa da ita yana shiga da kafarsa ya tura kofar dakin yana rufewa tareda saka key.

Tsakiyar dakin ya ajiyeta yana Dora idanuwansa akanta tayi Dan baya ahankali tana kasa dagowa ta kallesa kirjinta na Dan bugawa da karfi ta bude Baki Jin Shiru a sanyaye tace

"Ba nufina na manta ba,ina nufin zanje ne....

Shiru tayi tana kasa qarawa sbd yanda ya matsota sosai ahankali qamshinta na shigar hancinsa direct hakama tana Jin saukan numfashinsa me dumi a fuskanta.

Sake ja baya tayi kadan tana Dan dagowa ahankali ta kallesa da idanuwanta da suke cikeda hawayen datake tin a wajen.

Idanuwansa akanta suke bai dauke ba yana qare mata wani nutsatsen kallo sbd bai taba tsayawa ya Kafeta da ido ya Kare Mata Kallo ba sai yau din.

Kayan baccin dake jikinta ya kalla riga da wando masu tsantsi har qasa sai qaramar hula dake Kanta wadda bata rife gashinta dayake a tsaf gyare duka ba.

Wuyanta dayake bayyane yafara Kai hannunsa ya shafa ahankali tareda yanjota ta fado jikinsa ya sake shaqar qamshinta daya fara kashe Masa jiki yace

"Fatmah" cikin wata murya Mai cikeda kasala sbd rabonsa da koma a mafarki shaawansa ta mace ta motsa tin bayan rabuwansa da Anny Dan haka ya sauke ajiyan xuciya data fidda numfashi Mai dumi a fuskanta again take ta rintse idanuwanta tana Dan qanqame jikinta tana kokarin janyewa baya ya mannota jikinsa gabaki daya yana hadesu kirjinta yayi kyakkyawan sauka a kirjinsa yana Jin wani irin taushinsu da tudunsu a lokaci daya suna tada tsikar jikinsa gabaki daya.

Fargaba taji tafara shigarta hannuwanta suka Dan fara rawa ta kasa dagowa ta kallesa ta bude Baki tace

"Kayi hakuri to Yaya Maheer bazan sake ba nafasa zuwan zan zauna gida"

Tana fadar Hakan tana Dan kokarin zame jikinta amma ba damar Hakan sbd harga Allah gabaki daya haduwan jikinsu ya gama tada Masa komai musamman Kamshin datake fitarwa me tsananin dadi a hancinsa da kwakwalwansa.

Cikin wata murya me sautin daya sakata kallansa ahankali tana sake shiga fargaba yakai fuskansa ya hade da tata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login