Showing 63001 words to 66000 words out of 150681 words

Chapter 22 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9076

a yanzu da AZIZ yayi tafiya duk rintsi duk balai bazata bari ya dawo ya tadda Zaadens a gidan ba bare Fatima.

Nicky a asibiti sai yamma lis ta samu kanta ta wartsake sosai sedai ba karfin jiki dan haka suna baro asibiti gurin cin abinci me tsada suka tafi sukaci suka koshi ta sake samun karfi kadan sbd batason duk rintsi kowa ya fahimci akwai halinda take ciki.

Sai kusan dare suka dawo gidan a gajiye dukkaninsu.

Wanka tayi ta sake gasa jikinta ta sake samun yanda takeso Tasha magani take baccin wahala ya sake dauketa.

Garba ma wuni akai dashi babu lafiya sosai dashi dan Ummah Wadda tinda ta farfado bata iya cewa komaiba ido kawai take binsu dashi.

Ansamu Garba yaji sauki bayan kwana daya ana fama amma kwata kwata Ummah ta dena magana bata taba cewa komaiba tinda aka sameta a sume har yanzu,

Hakan shine abu mafi tashin hankali daya samesu me girma hakama ta dena son zama da kowannensu Kebe kanta takeyi tana tinani me tsananin tsayin gaske.

Dad gabaki daya neman rasa nutsuwansa yakeyi dan haka suka fara tinanin guduwa kawai subar 4&4 dan tafiya neman lafiyarta da abinda suka Tara me kauri a yanzu.

Wannan shawarar itace kowa ya yadda da ita hadda Jannah da hankalinta ya rabu gida biyu sbd a yanzu ta tabbatarda bazata iya rayuwa ba AZIZ LIMBA ba,

Batajin zuciyarta zata sake moruwa idan ta rabu da AZIZ a daidai lokacinda suke tsananin so da buqtaan junansu,

Tayaya zata tafi tabarsa ya shiga mummunan halinda zai rasa kansa gabaki daya?

Gabaki daya sanyi tayi itama kunci da damuwa na dawowa rayuwarta sbd a yanda ahalinta ke tsananta so da shiri AZIZ LIMBA bazai taba dawowa ya tadda su ba duk tsanani.

Ta bangaren su Dad ma damuwar tayi nauyin da kowa yake cikin kunci da nauyin zuciya dan haka kowa rayuwar tayi masa duhu da daci,

Garba ma a cikin tsananin damuwa da qunci yake ta yanda babu abinda yakeso shima kaman son barin 4&4 sbd zuciyarsa dake cikin Dana Sani da baqin cikin halinda ya samu Kansa a ciki na aikata zina da matar da zata kasance Matar me gidan.

Fatma gabaki daya itama kuncin dayake cikeda rayuwar kowa Musamman Jannah da Garba ya sakata sanyi da damuwa rayuwar kawai sukeyi.
#MAMUH

07019691719

*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 36

*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

********
****Nicky ta warware sosai ta dawo daidai cikakkiyar lafiyanta ta dawo bayan jinyar kwanaki datai fama da ita wadda ta hana kowa kira mata likita bare zuwa asibiti,

Mama tayi jinyarta da kulawa da ita sosai tareda fiddausi harta warke ta dawo kan kafafunta.

Abu daya ne ya kasa warkewa a zuciyarta kuma bazai taba warkewaba har abada idan ba ganin bayan Jannah da Zaadens tayi ba tareda shi garban kansa dan Sai ta tabbatarda garba baya duniya kwata kwata ta yanda bazai taba qarar da labarin abinda ya faru tsakaninsuba.

Da wani irin sabon baqin cikin zuciya me karfi da kudirin daukan fansar abinda ya sameta ta warke dan haka kai tsaye bayan warkewanta ta kalli Mama tace

"Mama Zaadens sun yiwa rayuwata illan da bazan taba iya yafe musu ba,
Mama wallahi wannan Karan sai Zaadens sun biya abinda sukayi?
Sai na tabbatarda Zaadens ko da kafafunsu koda gawarsu sai sun bar rayuwar gidan nan kafin dawowan AZIZ sbd zan rasa kaina idan na sake ganin Zaadens da AZIZ,
Mama ki....

Cikin gajiya da nata baqin cikin dayake cin ranta da rayuwar da gabaki daya ta juye ta koma batada nutsuwa duk ta haukace akan Zaadens da AZIZ dan haka itama ta gaji amma kuma tafi gajiya da masifun da koyaushe tsarin Nicky yake janyo musu dan ta kusa rasa sashen jikinta akan Nicky tace

"Aisha na gaji da tsarinki da haryanzu babu abinda yake bani sai ciwon zuciya da neman rasa kaina a gaban AZIZ,
Tin yaushe zamu zauna ace mutanen Nan sun gagaremu?
Ni na gaji,abu daya na sani ko a rayen ko a macen nidai su bar gidan nan kafin dawowan AZIZ,

Idan zaki iya mun hakan ta kowace hanya na Miki alkawarin wlh Yana dawowa bazai kwana ba sai an daura aurenki dashi koda a cikin dare ne.

Da sauri Nicky ta juyo idanuwanta jajir sbd kanta dake wata irin rawa tanajin wuta na ci a cikinsa tace

"Mama wlh tallahi sai sun bar duniyama gabaki daya ba 4&4 ba"

Mama da idonta ya rufe tace

"Indai zasu bar AZIZ koma lahirar ne su tafi."

Nicky da maganar aurenta da AZIZ ta birkitata gabaki daya ficewa tayi tana buga kanta da juyasa sbd yanda yake wani Kara Yana mata motsi.

Numfashi me zafi Mama ta sauke tana bin bayan Nicky din da jajayen idanuwanta sbd Nicky zata kawar mata da matsalar rayuwarta a yanzu datafi komai zamar mata babbar masifar rayuwa wato Haduwan AZIZ da Fatima.

*****Falaq ako yaushe yanzu tana gurin Jannah bacci ne kadai se wani abin ke maidata ita da fiddausi sun tare acan duk da basa samun fuska ko kadan a gurin Zaadens sbd tsanar da kiyyyar a bayyane take sosai.

Itama Falaq bata damu dasu din ba Jannah kawai takeso a cikinsu dan haka ita kadai tadamu da ita.

Ammar neman zarewa yakeyi sbd dawowan Falaq rayuwar Jannah zai iya lalata masa komai kamar a baya dan haka ya tsananta fidda tsanar LIMBAs a fili wadda ta qar bayyanarda tsanar da kowa kewa juna a tsakaninsu.

Ayau tin safe kowannensu ke parking a bisa umarnin Dad dan haka zaune take a dakinsu ta kasa hada kayanta data fidda gabaki daya daga wardrobe.

Fatma bata dakin ita kadaice shiru zuciyarta tayi wani irin nauyi da sanyi.

Ummah ce ta shigo dakin ahankali cikin tsananin sanyi itama ta qaraso gurin Jannah din ta zaune gefenta a sanyaye idanuwanta jajir.

Qurawa Jannah idanuwa tayi tsawon mintina kafin ta ciro hannuwanta dake tsananin rawa zata dafa Jannah din sai kuma ta fasa ta rintse idanuwanta ta bude ahankali ta bude baki da wani sautin daya saka Jannah kallanta da nata jajayen idanuwan.

"ABDULAZIZ AYOUBA LIMBA?

Rintse idanuwa Jannah tayi ta budesu akan Umman cikin tsananin mamaki da shock din cikakken sunansa a bakinta sedai tinanin komai baizo kanta sbd mutuwar da jikinta yayi da tsananin ciwon abinda ake shirin aikatawa na rabasa da abinda yakeso idan aka tafi da ita.

Hawayene suka ciko idanuwan Umman ya sake maimaita sunan Wanda ya saka Jannah rungumeta tana gangaro da hawaye masu tsananin zafi da wani irin raunin zuciya tace

"Ummah AZIZ LIMBA shine rayuwata,
Bazan iya rayuwa babu sa ba,
Bazan iya dena sonsa ba har abada,
Zan dena numfashi idan na rasasa,
Zuciyar Ummitah zata mutu kaman yanda ta Jannah ta mutu da dadewa idan aka rabata da AZIZ,

AZIZ yana tsananin buqata,
Baida kowa,
Ya rasa mahaifiyarsa Fatima tin yana qaraminsa shi da Ummitah,

AZIZ yana cikin quncin rayuwar da warakarsa mahaifiyarsa ce,

Babu mahaifiyarsa babu Ummitah tayaya zan barsa nima?

Zamewa tayi ta kwanta jikin Umman ciwon kirjinta na tsananta da quncin dayake ciketa ta rintse idanuwanta hawaye masu dumi suna sake gangarowa muryanta tayi sanyi tace

"Ummah kaddara ta saka ahalina da AZIZ LIMBA zama maqiyan juna tin kafin mu hadu sbd kaddarar zuciyar Ummitah dake cikin nawa kirjin,

Rasuwar Ummitah ta sauya duniyar AZIZ LIMBA da Zaadens gabaki dayanmu sbd haryanxu muna cikin tsananin Dana Sani da baqin cikin abinda ya faru,

Bantaba Sanin an daukan ran wani dan rayani ba dana dade da karban kaddarata na zabi mutuwata da AZIZ bai shiga qunci da ciwon rasa Ummitansa ba,

Da ayau bamu shiga quncin daukan ran da ahalina sukai ba,

Sun tuba sun nema yafiyar,sunata qara tubarwa Allah,
Ran mahaifiyata ya tafi a gurin girban abinda ya faru,
Ran daddy Mahmoud ma ya tafi,
Mun rasa Saleem,
Mun rasa Anny,
Mun rasa mummy duka akan wannan mummunan kaddarar data hadamu Amma haryanxu gabar tana qin qarewa,

Ummah inason AZIZ LIMBA inason Ahalina dan haka bansan yaya zanyiba..

Kuka takeson fasawa yaqi zuwa sbd ciwon komai dayake dawo mata ta ringa fayyace komai da irin rayuwar datai a hannun AZIZ da rayuwar da suka fada da ahalinta tareda halinda suka shiga na tozarci da rasa komai hatta suna da mutuncinsu ayau sun qare a zero Amma quncin ya kasa qarewa.


Ummah da jikinta ke wata irin jijjiga idanuwanta jajir wani irin gunjin kukan daya girgiza Jannah ta fasa me karfin gaske tana dafe kirjinta dayake mata wani ciwon data ke jin kaman ranta zai fita sbd azabar radadi.

Tashi Jannah tayi jikinta da sauri tareda kallanta Amma ganin yanda jikinta ke tsananin rawa tana kukan Wanda yake daga ja na ciwon rashi ne da baqin cikin.

Rungumeta Jannah tayi da sauri tana fasa kukan tausayinta da kaunarta tana cewa

"Ummah ki dena kuka irin wannan bazamu iya ganinki a wannan halin ba shiyasa zamu tafi dan neman lafiyarki,
Nima Ummah na zabi tafiya nabar AZIZ din sbd neman lafiyarki indai zaki dena jin quncin dayake tokare da kirjinki...

Kuka takeyi sosai wanda Umman ma kukan takeyi.

Fatma ce data shigo taga mugun halinda suke ciki taje ta sanar dasu Dad.

Su Dad na zuwa kowannensu idanuwansa sukai jajir Dad ya kamo Umman tareda rungumeta a jikinsa Yana kasa cewa komai sedai tsananin damuwarsa da dacin dayake ransa a bayyane yake.

Shiru sukai dukkaninsu cikin dacin zuciya suna sauraron kukan Umman wanda ta jima tana yinsa kafin ta dena ta kasa dagowa ta kalli kowannensu.

Jannah ce takaita toilet tayo wanka Maheer ya bata magani Ammar ya bata ruwa tasha ta kwanta Dad ya rufeta kafin dukkaninsu suka fice.

Wunin sukuku sukai cikeda damuwa da dacin zuciya sbd yanayin Umman wadda duk ta kasa cewa komai sedai binsu da ido a duk hidimar da sukeyi da ita.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 37

*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.


**********
Washe gari Dad ya samu Mama yayi magana da ita akan koma yayane suna son tafiya subar gidan.

Da farin cikin zancen ta kallesa tace su shirya tayi alkawarin komai tsurin tsaron AZIZ zasu tafi a gobe sa sassafe kafin kowa ya tashi.

Koda ya taho kai tsaye ya sanar da kowa dan haka suka qarasa shiryawa.

Mama shugaban securities na gidan gabaki daya ta kira da daddare har palon qasa ta sauko tareda kallansa bata son batawa kanta lokaci ta kallesa ta sanar dashi Zaadens kawai takeso ya bari su tafiyarsu kafin dawowan AZIZ,idan ya dawo ztsan abinda zata fada masa Wanda bazaiga laifinsa ba.

Kudi ta ciro bundle goma na Yan 1k ta ajiye masa tana kallansa.

numfashi ya sauke me nauyi shima bai tsaya bata lokaci ba yace gate zai zama a bude goben idan suka tashi tafiya.


Murmushi da ajiyan zuciya me karfi Mama ta sake tana cewa ya tafi zataji da sauran.

Yana fita Nicky dake labe tanajinsu ta sauke numfashi zuciyarta na tafarfasa sbd bata dauka Mama zata bata Mata shiri ba,
Ita Sam batason Zaadens su tafi dan su rayu sbd Jannah zata iya dawowa rayuwar AZIZ hakama Garba har abada zaici gaba da Tina yanda ya sameta dan haka ita sam batada niyar subar gidan a raye dan haka bama kowa ze kai gobenba bare kai labari.

Da daddare karfe 9 na dare Mama ta iso bangaren Zaadens din gabaki dayansu suna zaune.

Abinci Dad ke kokarin ganin ummah taci ko kadan ne Amma kwata kwata ta kasa zazzabi ne sosai a tattare da ita kuma har lokacin taqi cewa komai.

Ammar dake gefen Umman daya Yana mata fita ahankali ko dagowa beyiba ya kalli Maman sabanin kowa daya dago ya kalleta hadda ummah data dago jajayen idanuwanta ahankali ta kafeta dasu.


Mama bata batawa kanta lokaci ba ta jefa musu kudin dayake hannunta a gabansu ta kalli Fatima cikin idanuwa kafin tace

"Gobe karfe 7 na safe kubar 4&4 zaa bude muku gate wannan kudin kuma ku tabbatarda kunyi nisan da AZIZ bazai taba ganinku ba har abada"

Tana fadar hakan ta juya tabar gurin babu Wanda ya kalli kudinta bare tankawa

Harta bace ummah bata iya dauke idanuwanta akanta ba kafin ta rufe tana sunkuyar da kanta.

Har karfe 10 suna waje kafin suka tattara kowa ya shige.

Ummah Dad ne ya kama hannunta har dakinsa suka shige.

Itama Jannah suna shigewa wanka ta fada tayi da brush tana fitowa ta zauna ta shafa turare kadan kafin ya saka doguwar rigar bacci me tsantsi ta nufi gadonta ta hau.

Cikin bacci taji fatma na tada ita batareda tayi nisa sosai a baccin ba.

Bude idanuwanta tayi ahankali ta kalli Fatman.

Janyewa Fatma tayi tana kasa cewa komai dan Jannah taga waye a bakin kofar shigowa dakin daga waje.

Kaman a mafarki ta gansa tsaye sanye da ash Armanis da waya da jacket a hannunsa da alamar daga mota nan ya wuto direct.

Farin cikin daya cike zuciyarta ne ya sakata saukowa gadon da sauri ta nufesa da wani irin gudu tana isa ya dauketa sama Yana rungumeta itama tana qanqamesa farin ciki fal zuciyarta.

Fatma ma farin cikine ya ciketa ta sunkuyar da kai.

Kallan fatma yayi batareda ya sauke Jannan ba ya furta "thank you" ahankali cikin kasala yana juyawa da ita ko takarmi ko wani abin rufe jikin babu a tareda ita.

Suna barin gurin baifi da minta biyar ba Ummah ta dawo dakin ta kwanta a gadon Jannah tana duqunqunewa.

Suna isa bai ajiyeta ba sai tsakiyar bedroom dinsa Yana kallan fuskanta ya kama bakinta ya sakar mata wani zafafan kiss kafin ya rungumeta yana cewa

"Alhmdlh ya Allah"

Murmushi takeyi tana sake qanqamesa itama kafin ta dago ta kallesa tace

"Daman yau zaka dawo?
Amma kowa besan yau zaka dawo ba?

Fuskansa ya saka a wuyanta ya shaqi qamshinta yana gangarowa har kirjinta Yana shakarta kafin ya bude baki yace

"Yes sedai sa safe su ganni bayan kin gama Dani"

Murmushi tayi tana kokarin janyewa sbd yanda shinshinarsa ke kashe mata jiki hannuwansa na yawo jikinta kaman cakulkuli ta bude baki cikin son kwacewa da dariya tace

"AZIZ"

Tana rufe baki ya sake maida bakinsa cikin nata ya tsotseta da kyau kafin ya saketa Yana binta da kallo idanuwansa a kasalance.

Daqyar ya saketa ya wuce toilet ita kuma ta sauka kaman barauniya taje kitchen ta hado masa tea me karfi da short bread biscuits na shan tea tareda fruits ta dawo.

Taba barin kitchen karfe daya tana bugawa daidai lokacin Nicky ita kuma ta fito dauke da abinda yake hannunta tabi ta kitchen din ta fice zuwa bangarensu.

Motarta ta nufa ta bude ta dauko qaton galon na diesel da ashana ta rufe motar ta nufi bangaren Zaadens.

Ita kuma Jannah tana dawowan ya fito wanka kenan.

Ajiye tray din hannunta tayi kafin ta motsa yayi Sama da ita tace

"AZI....bata qarasa ba suka fada gadon taba jikinsa ya zagayeta da hannuwansa sbd shine a qasa itace a samansa.

Zubawa juna ido sukai Yana zagaye bayanta da hannuwansa Yana Shafa lafiyayyun cinyoyinta da suka bayyana dan rigarta data janye.

Ahankali ta bude baki zata kira sunansa cikin kasala yace

"Pls don't,youre killing me slowly da yanda kika fadan"

Murmushi tayi tana yin qasa da kanta ya dago fuskanta da hannunsa daya yai kissing hancinta Yana sake shakar qamshinta kafin ya saka kansa wuyanta yai kissing fatar wuyan.

Saukan lips dinsa a fatar wuyan nata ya sakata sake numfashi me dumi ya sauka akan fuskansa ya lumshe idanuwansa tsigar jikinsa na tashi gabaki daya.

Ayau sosai yake jinta ta yanda bazai iya tsallake yau bai mallekta gabaki dayanta ta zama cikakkiyar macen AZIZ LIMBA dan haka juyar da ita yayi ta dawo qasan ya koma samanta Yana zare rigar jikinta gabaki daya daga jikinta Yana zubawa farar lafiyayyan fatar cikinta ido zuwa kirjinta.


A daidai wannan lokacin ne karfe daya da hamshi da biyar ta buga,

Sama sama kunnuwan Jannah suka fara jiyo mata ihun Madam Sisi da hayaniyar iska kaman na hadari.

Dakatar dashi tayi tana ambatar sunansa ahankali cikin mutuwar jikin halin da suke ciki.

Idanuwansa ne suka sauka akan hasken dayake tashi saka ta balcony dinsa kaman na wuta.

Da mamaki ya miqe Yana saukowa gadon kafin ya isa window wutar tayi wani irin karfin gaske.

Hayaniyar mutanen dake gidan da securities ne yake tashi ahankali wanda sakasa qarasawa balcony din idanuwansa suka sauka akan wuta dake cin Bangaren masu aiki sosai.

Jannah wani irin mummunan mutuwar tsaye tayi idanuwanta na neman makancewa

Shikuwa da sauri ya saka kaya jikinsa ya dauko kayansa ya saka mata suka fito bata ko ganin gabanta wani irin gudun tashin hankali takeyi tana ambatar sunan Dad dinta da Ummah.

Ko da suka isa Dad dasu Maheer na fitowa cikin wutar a tsananin hali suna tarin azaba.

Kowa ya fito hankali tashe da tsoro,

Mama Nicky ta kalla wadda kai tsaye ta gane itace tayi aikin

Bata damuba kawai dai fatarta aikin kada ya zama na banza a garesu,

Falaq da fiddausi ma saurin taresu Sayd yayi duka masu aiki kowa ya fito hankali tashe.

Cikin tsananin hali Dad ya kalli Jannah dake tsananin rawar jiki yace

"Ina ummanku?

Shi ta kalla da sauri tana girgiza kai a rikice,

Maheer daya shiga firgici cikin daga mury yace

"Ina Umman take?

Ammar ne yahau ture kowa da sauri Yana dubata bai ganta a wajen ba baisan lokacinda yayi cikin wutar ba da karfi Yana kwala Kiran sunan Umman.

Securities ne sukai saurin riqesa

Jannah ta miqe da gudu tana dosar dakinsu tana kwala sunan Umman cikin tsananin kukan gaske da tashin hankali.

Riqeta AZIZ yayi yana cewa a riqe Maheer da Dad da sukai cikin wutar suma.

Damben gaske aka ringa yi dasu suna kwacewa amma anki sakinsu

Mama kuwa jin takeyi kaman ta qarawa wutar karfi da gudu takeji kowama ya huta.

Ammar ne ya sakarwa security daya mugun noshi ya kwace ya fada cikin wutar Dad na bin bayansa.

Nan Jannah ta sake haukacewa tana Kiran sunan Dad dinta da Umman kaman ranta zai fita.

Buga kofar su Dad suka hau yi da karfi Wadda ta bude da qyar bayan duk sun kona hannuwansu.

Suna shiga ummah da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login