Showing 75001 words to 78000 words out of 150681 words

Chapter 26 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9074

a yanayi na haukansa bai taba jin motsin gaske a cikin kwakwalwa da barqonsa ba sai ayau,

Zarewa kansa yayi gabaki daya hakama tinani da hankalinsa gabaki daya gushewa sukeyi Yana rasa kansa tsananin sonta da abinda yake samu da ji a tattare da ita a matsayinta na macen data fara saninsa ya Santa suka kunto juyewan kansa gabaki daya ya ringa nuna mata karfin gaske da Yana buga Kansa da wani irin karfin gaske da hannu daya sbd jin kaman ana bikin mahaukatan Aljanu a cikinsa...

Kuka takeyi sosai na fitan rai da neman sauki da sassauci Amma babu sauki ko sassauci tako ina sbd tako ina tamkar ba AZIZ LIMBA bane.

A daidai lokacinda yake sake rasa kansa wani hayaqi yaji tamkar Yana fita kunnuwansa da suka dauke jin komai na duniya dip sai wani mahaukacin numfashinsa dayake sauka a kunnenta hawaye na bin gefen idanuwanta bata iya motsawa...Wani irin abin da yake kokarin rabasa da ransa yaji ya taso masa tin daga tsakiyar bayansa zuwa mararsa daya sakasa daga hannu ya sakarwa glass door din balcony dinsa dayake har gurin jikin gadonsa a daidai kuma inda suke wani mahaukacin dukan daya saka glass din wata irin qara me karfin gaske da gabaki daya gidan ya dauka Yana watsewa waje.

Ya saki wani irin kuka me hade da ihu Yana mata wata irin qanqamar data kusan rabata biyu ta qarasa macewa a jikinsa numfashinta na sarkewa.

Dukkanin Wanda yake gidan sautin qarar fashewan kofar ya samesa wasu a cikin bacci wainda basu iya bacci ba kuma a kunnuwansu Amma babu wnda ya fito sbd a yanzu kowa ya fara koyan saurarawa da kyau tukuna.

Ammar ne daya kasa bacci a cikin Daren zaune yake Daram kirjinsa na masa wani irin matsanancin ciwon da yakejin ayau tsananin kewan mahaifiyarsa da Mimi,

Ciwon dayake ji a kirjinsa ciwo ne dayake jin numfashinsa na toshewa idanuwansa sukai jajir ya kasa rintsawa ko kadan.

Garba daya kasa bacci sbd halinda Ammar din yake a ciki a bayyane yake sbd yanda idanuwansa sukai jajir.

Tashi yayi jin qarar ya nufi kofa ya fito Ammar din na bin bayansa da kallo idanuwansa na cikowa da wasu zafafan hawaye masu dacin gaske suka gangaro daga idanuwansa yanajin a Karo na farko kewan tasa mahaifiyar yasa Yana jin inama ya bita a yanzu ya huta da radadin dayake ji yana nauyaya kirjinsa...

Kuka ne Mai karfin gaske da wani irin sauti me ban tsoro suka taho masa ya cusa kansa cikin kafafunsa jikinsa na wata irin sanyi Yana yi Yana qanqame jikinsa dumin jikin Uwarsa data barsa a duniyar da baida asalin ubansa daya yafesa bai taba nemansa ko buqtaan son ganinsa ba tana cike kirjinsa da ciwo me tsananin gaske.


Jin Yana neman rasa numfashinsa ya miqe yana hada hanya ya fito Shima yana fita harabar gidan gabaki daya batareda duba da Daren daya tsala ba.

Garba ne ya isa da sauri gurinsa yana tarosa jikinsa sbd yanda Ammar din ya zube akan gwiwansa yana dafe kirjinsa.


******Tsawon mintina ya dauka a jikinta qanqame da ita kafin ya fara kakkarwan sanyin dayaji Yana ratsa har cikin qashinsa.

Bude idanuwansa da suka bude dakyar yayi ya zubawa fuskanta datai jajir har lokacin hawaye ne ke gangarowa gefen idanuwanta dake rufe sun kumbura sosai.

Numfashinta dake fita ahankali ya Shaqa cikin hancinsa Yana lumshe ido karfin jikinsa na dan dawowa ahankali.

Cigaba yayi da shaqar numfashinta da ba karfin komai a cikinsa har tsawon mintina shiru a jikin juna kafin ya saketa ya miqe zaune ahankali Yana ziro kafafunsa qasa.

Bathroom ya nufa kafafunsa a sanyaye Shima jin yake baida karfi kwata kwata.

Ruwan sanyi ya sakarwa Kansa Yana lumshe idanuwa Yana sauke numfashi masu sanyi da samun nutsuwa a jere.

Ya dade a ciki kafin ya fito.

Ko daya fito yunqurin Amai takeyi Amma batada karfi ko kadan na yunqurin dan haka da sauri ya iso ya tallafota jikinsa Yana kunna hasken dakin me yawa idanuwansa suka sauka akan inda take kwance yaga jini.

Sarawa yaji kansa yayi da karfin gaske zuciyarsa na nauyi,

Da sauri ya dauketa cak ya nufi toilet Yana isa ya kunna ruwan zafi a bathtub ya sakata sbd bazata iya tsayuwa a shower ba.

Wani numfashi me karfi na azaba ta sake ruwan na ratsata ta qanqame hannunsa da dan karamin karfinta tana kasa bude idanuwanta.

Fitowa yayi zuciyarsa gabaki daya tana daukan zafi da halin daya sakata dan haka wayarsa ya nufa ya dauka ya saka Kiran Sayd.

Kiran farko Sayd ya dauka sbd ya farka tinda yaji qarar.

"Ina buqatan Doctors kaman biyu xuwa uku yanzu nan"

Tashi zaune Sayd yayi Yana sake kallan time kafin ya sauko gadonsa Yana cewa

"Ok Maza ko mata?

"Mata duka a yanzu nake buqatansu"

Kashe wayar yayi yana komawa toilet din gurinta yana isa ya bai damu da yanda ruwan datake cikin suka sauya ba ya shiga ruwan ahankali Yana rungumota jikinsa Yana ambatar sunanta cikeda tsananin kulawa Amma bata iya amsawa.

Ganin hakan da yanda take sake sakewa ya saka hankalinsa sake tashi ya fito yana sake daura towel ya dauki wayarsa ya kira Sayd Wanda tini ya fito tareda tada mota dace motar securities din gidan ta biyosa da wasu daga cikinsu.

Daukan wayar yayi cikin matsuwa AZIZ din yace

"Sayd am loosing my mind here me suke jira haryanxu ne??

Cikin sake qarawa motarsa gudu Sayd yace

"Ina hanyar dauko sun sbd zuwansu zai dauki time Amma kafin su iso ko akwai taimakon da fiddausi zata iya bayarwa?"

Da sauri AZIZ din yace yes.

Sayd da sauri ya kira fiddausi wadda take bacci tana ganin Kiran ta tashi zaune tana daukan wayar cikin mamaki.

Bai tsaya cewa komaiba cikin sauri yace

"Fi kije Jannah na buqatanki yanzu"

Kashe wayar yayi Yana sake bankawa motarsa wuta.

Fiddausi take bacci ya saketa ta miqe tana saka hijab akan riga da wandon baccinta masu santsi da tsada ta nufi kofa ta fito dakin ta sauka qasa tana nufar palon da zai kaita saman AZIZ.

Ko data isa harya bude kofar palon Yana zaune palon idanuwansa jajir.

Kasa kallansa fiddausi tayi kaman yanda bai kalletaba yace tayi saurin taimaka mata.

Ko data shiga ya sauya beddings duk da bai wani iya sakawa yanda ya kamata ba ya dai sauya hakama ya sakawa Jannah shirt mara nauyi.

Toilet fiddausi ta shiga ta isa gurin Jannah din da sauri tana kallanta yanda koina jikinta da fuskanta yayi jajir bata iya ko zaunawa tana cikin ruwa kwance.

Ruwa fiddausi ta sauya mata masu zafin gaske tana sake zaunar da ita cikinsu Jannah ta fasa kuka mara sauti amma duk da hakan ya shiga kunnensa dan haka ya dawo toilet din da taimakonsa yana riqe da hannuwanta cikin kulawa kaman zai zare ransa ya bata aka sake sauya mata ruwa yabi duk ya rufe ruwan da towels kusan Guda uku sbd kada ko cinyoyinta fiddausi ta gani.

A haka ya fahimci ruwan zafin Jannan ke buqata dan haka ya sallami fiddausin ya dinga sauya mata ruwa kamar zararre Yana sakata har saida Sayd ya iso da likitoci mata biyu Wanda suka hawo har sama suka dubata da kyau yanda ya kamata babu buqtaan stitches kawai dai girman da yayi mata da karfin daya bata tareda gurzuwa datai ne ya saka ta goge sosai ta dan jin rauni Amma ba dinki.

Magani da allura sukai mata take ta samu wani wahalallen bacci.

A cikin duhun Daren ana gap da Kiran asuba Sayd ya sake maida doctors din fiddausi kuma taje itama a cikin Daren ta sake dafo madara me zafi da zuma ta sako a gurinda zai aje zafin ta kawo palon ta ajiye ta koma dakinta.

Rufe Jannah din yayi a da abin rufa Yana rage mata ac ya miqe ya nufi toilet sai alokacin yayi wankan tsafta da tsarki da ruwan zafi sosai ya fito ya saka dogon wandan kayan bacci kawai da jallabiya yayi sallar asuba da akai yana idarwa yayi adduoinsa na godia ga Allah daya basa mutane biyu dayafi so akan tasa rayuwar wato mahaifiyarsa da Jannah da ayau ta zama cikakkiyar macensa.

Yana gamawa zare jallabiyarsa yayi ya hau gadon ya shige jikinta ya kwanta Yana shakar kamshin dayake fita a jikinta na rigarsa dake jikinta daya hadu da qamshin jikinta.

Baccin ne ya daukesa a jikinta Shima sedai bai dade sosai Yana baccin ba dumin numfashinta dake sauka a kirjinsa yana tada tsikar jikinsa tareda laushin jikinta da fatarsu dake ta sake mannuwa da juna babu kayan kirji ya saka hankalinsa gabaki daya ya tashi yaji Yana shiga wani dumin jiki da sabuwar buqatarta me karfi da zafi.

Bude idanuwansa yayi Yana zuba mata tana bacci cikin nutsuwa da rashin karfi,

Lips dinta ya zubawa idanuwa Yana kallan yanda sukai ja ya hadiyi wasu yawu masu dumi Yana saka fuskansa wuyanta Yana sauke mata numfashinsa me dumi daya sake dumama jikinta cikin bacci ta motsa ahankali tana dan sake shigewa jikinsa numfashinta ya sake sauka da dan karfi akan fatar tsakiyar kirjinsa take ya zagoyota da hannuwansa Yana mannata sosai da jikinsa Yana Shafa wuyanta zuwa kirjinta ahankali kafin ya gangara zuwa cikinta da Mararta Yana kasa riqe Kansa sbd jin kaman ya hadiyeta gabaki dayanta.

Yanda yake shafarta ne ya sakata bude idanuwanta jajir ahankali cikin sanyi da rashin kuzari ko karfi ko kadan ta kallesa da idanuwanta da sukai wani irin laushi....

Cikin wata irin kasala da zarewan da yaji notikan hakuri da control dinsa na yi ya bude baki da kyar ya iya cewa

"Da kin Sani baki bude idanuwanki akaina ba sbd your eyes sun....kasa qarasawa ma yayi Ya Dora bakinsa kan lips dinta da suka bushe jajir Yana tsotsansu ahankali Yana sake shigewa jikinta Yana zare rigar jikinta kai tsaye.
#MAMUH
#LIMZAD
#BEST LOVE
#ROMANCE
#NICKY
#GARBA

07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 44
07019691719


Rawa jikinta ya dauka cikin rashin karfi ta fara girgiza kai tana ambatar sunanta can qasan maqoshinta daqyar sedai kwata kwata ba alamar zata samu ya saurara sbd hakuri kawai yake bata Yana cigaba da dumama jikinta da zafafan romance kafin ya rabata da komai yana shiga tsakiyanta tareda bude kafufunta a natse ya fara fama mata raunikan da batama San yaushe zata warkesu ba.

Azabar data sake sha ce ta saka ta jin tsoro na kamata ta ringa kuka mara sauti ahankali jikinta na tsananta zafi sosai tana rungume a jikinsa Yana jera mata kalman sorry da I love you a kunnenta cikin sanyi da tsananin tausayinta.

Yana jin gamsuwa iya gamsuwa a tattare dashi,

Madaran da fiddausi ta kawo mata yaje ya dauko mata ya kawo mata ya bata Tasha daqyar jikinta zazzabi sosai.

Dr ya sake kira tace ba komai bane idan ta samu isashen bacci da hutu tareda abinci me kyau zata warware Amma ya daga mata kafa.

Kashe wayar yayi ya kira fiddausi kai tsaye yace ta hadawa Jannah breakfast dinta daban a kawo mata.

Sake taimaka mata yayi ta shiga ruwa sosai tayi wanka ta fito da taimakonsa tayi sallah kafin ya kwantar da ita ya shige toilet Shima.

Yana shigewa ta sauko gadon tana dafa bango sbd jiri tana tafiya ahankali ta dauki hijabinta ta saka ta fice bata gani sosai.

Da bin bango da durqusawa take saukowa stairs jikinta na rawa sosai sbd karfin da zazzabinta yake qarawa.

Bata hadu da kowa ba sai Fatma Wadda take gyare palon da sauri ta kalleta tana jefarta mopper ta iso gurinta ta kamata zatai magana take ta fahimci meya samu Jannah din da tashin hankalin gaske ta kalleta tana qasa da muryan tace

"Su Dad kaman sun tashi suna palo fa?"

Duk da halin da Jannah ke ciki gabanta mummunan faduwa yayi ta qanqame Fatma hannuwanta n rawa ta kasa magana.

Kamata Fatma tayi itama tsoron cikeda cikinta jikinta har rawa yakeyi sbd tsoron kada wanda ya fahimci wani abu.

Cikin saa koda suka isa palon babu kowa dan haka da sauri Fatma ta Isa da ita daki ta kwantar da sauri tareda rifeta da bargo tana rage ac sbd yanda jikin Jannah din ke rawar ciwo sosai.

Tana kwantawa babu jimawa baccin azaba ya dauketa me karfi.

Sai a lokacin fatma ta sake ajiyan zuciya me karfi har lokacin tsoronta bai sauka ba sbd balain dazai iya biyowa baya idan su Dad suka San akwai auren AZIZ da Jannah din bare kuma ace suna cikin gidan suna bacci AZIZ LIMBA ya maida Jannah macensa da suke jin gwara ta samu ciki da Ammar ba aure dadai wani abu ya shiga tsakaninta da AZIZ LIMBA.
To yanzu ko ita data Sani mummunan hukunci zata karba a hannun su Dad bare kila jannar,

Ita yanzu gabaki daya jin tayi tana son tafiya kauyen su bar nan din sbd gudun bacin rana.

AZIZ na fitowa bai ganta ba kai tsaye yasan abinda yasa ta koma cikin karfin hali dan haka bazai tirsasa ta Musamman yanzu da batada Lfy dan haka yana gama shiryawa sake Kiran likita yayi yace zuwa 10 na safe su sake zuwa dubata.

Fiddausi ma 10 din nayi takai abinci dakinsu Jannah din lafiyayyu ta jere.

Angama musu komai na shirin tafiya akace Fatma ta kira Jannah din sai alokacin fatma da zuciyarta ke tsinkewa ta sanar dasu Jannah ba lafiya sosai sosai ko bacci basuyi ba Daren gabaki daya.

Cikin mamaki da tashin hankali suka dunguma zuwa dakin.

A yanda suka ganta gabaki daya tayi fayau idanuwanta a kumbure alaman kuka da azabar ciwo ya saka jikinsu sanyi tareda shiga damuwa.

Ammar ne dayake likita ya dubata yaji ba ciwon zuciyarta bane dan haka bai tinani ko nazarin Komaiba saiga likita taxo tareda fiddausi da Falaq wadda duk ta daga hankalinta jin Jannah na rashin lafiya sosai.

Ganin fiddausi da Falaq ne suka kawo likita ya saka basu damu ba sbd sunsan Falaq ko zasu kasheta saita je gurin Jannah din dan haka suka fice.

Dr kadai ce ta shiga ta dubata ta bawa fatma sabbin magani da yanda Jannah din zata kula da kanta ta fice.

Fatma boye maganin tayi sbd Ammar zai iya Sanin na menene idan ya gani kila.

Mai gidan bai sauko ba sai karfe 11 na rana kuma kuma kai tsaye gurin Jannah din ya fara zuwa ya dubata har lokacin bacci takeyi dan haka kai tsaye ya sake wucewa gurin Ummah Wadda yana shiga dakin ya taddata Zaune Daram akan gadon datake idanuwanta jajir alaman kuka me tsananin gaske tasha.

Mutuwar tsaye yayi daga bakin kofar Yana kallanta jikinsa na mutuwa gabaki daya idanuwansa kafe akanta suna sauyawa.

Dagowa tayi itama ta kafesa da idanuwanta jajir a kyaftawa hannuwanta na rawa ahankali tana kasa bude baki tayi magana.

Dad dasu Maheer ne suka iso dakin ganinsa tsaye bakin kofar dakin ya sakasu isowa da sauri cikin tsinkewan zuciya.

Ganinta zaune ya saka dukkaninsu tsayawa cak kaman AZIZ LIMBA zuciyarsu na harbawa da matsanancin tashin hankalin wa zata tina ko ambata a cikin su ko AZIZ LIMBA.

Mama ma a daidai lokacin ta iso sbd tin ranar d abin ya faru bata sake saka AZIZ a idanuwanta ba hakama batasan yaya Fatiman ba ta tashi kuma waye ta tina a tsakanin AZIZ ko Zaadens.

Itama tsayawa tayi cak a kofar dukkaninsu kallanta sukeyi kowa zuciyarsa na tsinkewa.

Sayd dake bayan AZIZ Shima zufa ne ya tsinke masa Yana fatan baqin ciki da quncin uban gidansa ya qare daga yau har abada idan har mahaifiyarsa ta Tina sa.

Ummah tsurawa kowannensu idanuwanta tayi babu Wanda tinnainsa ko memorynsa ya fita daga kanta ko daya idanuwanta suka sake cikowa da hawaye masu zafin gaske suna saukowa kan fuskanta ta bude baki ahankali da muryan da babu wnada ya Santa da ita sbd sanyi da nutsuwanta tareda wani irin kewan da har abada bazata cike daga zuciyarta ba Musamman yanzu da babu Ummitah tace

"ABDULAZIZZZ" Cikin wani irin sauti me sanyin daya saka kafafunsa sarewa Yana zubewa qasa a bakin kofar wani irin kuka me karfin gaske Yana kubuce masa ya kai goshinsa qasa Yana sujjada cikin kukan daya tada tsikar jikin Sayd dasu Fatma dake palo duka a tsaye suna sauraron komai.

Yana dagowa daga sujjadan ya isa gurinta da wani irin karfin gaske ya fixgota jikinsa ya rungume da tsananin karfi Yana wata irin tsima zuciyarsa na neman fashewa da farin cikin duniya gabaki dayanta.

Baya mama tafara yi kafafunta na kakkarwa idanuwanta na cikowa da hawayen baqin cikin duniya gabaki daya tana jin rabin jikinta na neman shenyewa sbd riqewan dayake.

Zaadens ma kusan mutuwar tsayen sukai idanuwansu duka akan Umman wadda take qanqame jikin danta idanuwanta kafe akan Dzad da Shima nasa ke kafe akanta.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 45

Sayd ma baisan lokacinda ya zube qasa yayi sujjada ba Yana jin wani nauyi na sauka daga kirjinsa sbd ciwon dake danne da rayuwar AZIZ na rashin mahaifiyarsa na shekaru shima jinsa yakeyi sbd yafi kowa Sanin irin hali da quncin da zuciyarsa ke lullube cikinsa,

Falaq ma da sauri ta qaraso tana rungume daddyn nata ta baya tana tayasa murna sbd ita farin cikinta akan daddynta y samu abinda yakeso ne tinda ba Sani datai Daddynta nada wata asalin uwar ba bayan Mama se yanzu da abubuwa suka bayyana.

Cikin wani irin farin cikin da bai taba shiga ba a rayuwarsa tin rasuwar mahaifinsa Yana qanqani ya dago Yana kallan fuskan Umman ya kama hannuwanta duka biyun yayi kissing nasu ya rungumesu a kirjinsa Yana rufe idanuwansa kirjinsa kaman zai fashe da farin ciki.

Falaq dake bayansa ya janyo ya rungumeta yana jin itama kaman zai maidata ciki ya dagota yana kallan Umman ya Dora hannun Falaq akan nata ya hada ya riqe a cikin hannunsa ya bude baki yace

"Ummah ga wata Fatimanki,
Little Ummitanki ce,
Jinin Ummitah c..... Kasa qarasawa yayi sbd wani irin sanyi da jikinsa yayi Yana kallan yanda hawaye ke gangarowa daga idanuwan Umman ta zubawa Falaq ido Yana kallan kamanninta da bata Sani ba na Ummitah sbd tin daga ranar data haihu ta tasa hankalinta hakama ko data rabu da yayanta suna Yara Ummitah na qanqanuwa sosai.

Falaq zubawa Umman ido tayi itama tana kallan matar data haifi mahaifiyarta sbd daman can Mama a matsayin mahaifiyar daddynta take kallanta mantawa takeyi Sam da itace uwar tata mahaifiyar sai a yanzu ne take jin ta hadu da mahaifiyar data haifi mahaifiyarta.

Ahankali Umman ta sake dago idanuwanta ta sauke akansu Dad dake tsaye jiki a tsananin mace Musamman Ammar daya iso yana ganin halinda ake ciki idanuwansa da suke jajir a kumbure suka ciko da wasu irin hawaye masu tsananin zafin gaske sbd a Karo na uku ya sake rasa Uwa dayake tsananin buqata a rayuwarsa dan mummunan rayuwarsa dake cikin tsananin duhu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login