Showing 99001 words to 102000 words out of 150681 words

Chapter 34 - Kalbim Book 2 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

9054

yana xuwar mata a karo na farko dataji tana tsananin kewa da neman mahaifiya a rayuwarta sbd batasan wace irin kaddara ce wannan ba,
Batasan yaya zatai ba,
Batasan me zatai da Kanta da cikin ba,
Batama riqe sunan Wanda kaddara ta sakata samun cikin nasa ba,

Batasan ma Yaya ake cirewa ko renan ciki ba tayaya zata wayi gari da wannan girmammiyar kaddarar batada Wanda zata gurinsa ta fada Masa ya rarrasheta.

Kuka takeyi sosai duka jikinta yana rawa tanajin kadaici da wani irin kewan Dan uwanta da shi kadai gareta Kuma shi kadai zai karbeta da kaddararta suna ciketa duk da tasan bazai ji dadin Abinda tayi din ba.

Kasa tashi tayi sbd yanda kukan nata yake ratsa zuciyarta da dukkanin lafiyarta Dan ayau kwata kwata ko tashi ciwonta beyiba sbd emotional lamarin da bai taba samunta bane akan a sameta a lokacinda take neman ko Wanda Bata saniba bane ya kalleta ya rarrasheta ko zata samu sanyi da sassauci amma babu.

Batasan iya tsawon lokacinda ta dauka a gurinba zaune tana cikin kuka da quncin rayuwa gabaki daya gata da wani irin tsananin tsoro da son rayuwarta da bazata iya tinanin cire cikin ba sbd kawarta daya a duniya Kuma ta rasa ranta ne gurin terminating ciki Dan haka ita bazata iya ba batason rasa ranta tsoro takeji.

Kaman daga sama cikin kunnuwanta ta juyo muryan Jannah wadda ta bude baki cikin tsananin tashin hankalin da itama ta samu Kanta me firgitanwa muryanta na rawar kuka tace

"Fatma Dad da Maheer kasheni zasuyi ida suka San da cikin nan,
Ammar mutuwa zeyi idan ya San da cikin wani a jikina,
Daga dawowa kauyen da suke tinanin sun turamu su samu ciki a jikina wlh Maheer zai iya rataye ni Dad Kuma yafeni zeyi......


Kuka ta fasa mara qara me tsananin ratsa zuciya tana zamewa a darare ta zauna a kujeran dake gurin jikinta na rawa sosai kukanta na sake ratsa Fatma da itama kukan takeyi me tsananin gaske sbd hukuncin da itama zata karba kodai na komawa kauye Kuma tana komawa zaa mata auren dole sbd tayi hankali Dan haka itama zaunawa tayi gefen Jannah din tana fasa sabon kuka.

Nicky datake cikin nata kukan Jin abinda suke ciki Wani irin shock da tsantsar mamaki me girma tashiga Jin Jannah da ciki ta samo daga kauye kenan?

Gangaro mata hawaye sukai tana sake juya musu baya sbd kada su ganta tana Jin Dan sanyi a ranta sbd masifar datake tinanin tana ciki ita kadai ashe tanada yar uwa sbd itama Jannah wani qaramin kauyen ne yayi mata ciki kenan?
Duka kauyen su Garba kenan haka suke ko me?

AZIZ dayake zarewa bayaji baya gani akan Jannah din idan yaji cikin shege ne a jikinta Yaya zaiyi?
Zaici gaba da Sonta ne ko me?

Koma yayane tabbas ita zata sanar dashi Dan fara ganin yanda zai karbi lamarin cikin shege a Jannah,

Idan ya Aminta da aurenta da cikin shegen kokuma Yaya reaction dinsa akan cikin shege a gidansa zai kasance to itama kenan zai iya amsarta da nata cikin,

Koma dai yayane tanason fara ganin yanda zaiyi idan yaji barnar sbd tafara gani Dan itama tasan yanda zaa fuskanci nata koba komai zata samu sauki da sassaucin zaa ce ba itace tafara ba Jannah ce ta fara idan nata ya biyo daga baya.

Wayarta ta fidda ahankali batareda sanin su ba ta dauki hotonsu tareda recording wasu daga maganganunsu akan cikin kafin ta samu dakyar tayi zooming result din hannun Fatma data Kafe da ido tana kuka inda sunan Jannah Zad ya fito baro baro da tabbacin cikin jikinta Sati Bakwai.

Miqewa tayi ya fice batareda sun ganta ma sbd su halinda suke ciki ya ishesu.

Sun jima cikin kuka da jimami kafin suka yanke shawarar qin barin kowa ya sani kafin su samu mafita musamman AZIZ din da yana Jin cikin zai iya bayyanawa kowa ba ruwansa da duk Wanda ciwon zuciya zata kama.


Fitowa sukai bayan sun karba tsadaddun maganin da aka rubuta mata suka wanke fuskansu suna kokarin komawa daidai.

Suna barin asibitin gurin cin abinci Fatma tace akaisu sbd Jannah din tasamu taci Dan ana komawa gida ba iya ci zataiba sbd tana ganin su Dad zata iya shiga sabon tsoro.

Wani babban lafiyayyan Eatery suka tafi sukaci abinci sosai me Kyau da tsada suka koshi suka fito.

Basu tafi gida Kai tsaye ba Saida sukai Dan zagaye dukkaninsu suka sake sakewa tukuna suka iso gida.

Gabaki daya Zaune suke a palo sunata jiran dawowansu,

Ummah na zaune gefen Dad Wanda yake kwantar mata da hankalin lafiya kalau inshallah,

Maheer sai Kiran wayar Fatma yakeyi Bata shiga Ammar Kuwa Shiru yake a dayan gefen Ummah ya kasa cewa komai haka kawai yakejin jikinsa yayi sanyi fatarsa kawai ciwon Jannah ba wani serious ciwon bane da yamafi tinanin maleria ce ta sauron kauye ko Kuma yanayin ruwa da cimar kauyen ta taba ta tinda tayi fiyeda shekara koma fiye Bata ci ba.

Suna shigowa Fatma ta Dan sake fuskanta tana kallansu itama Jannah din daurewa tayi tana sakewa suka qaraso suna zaunawa Maheer ya Kalli Fatma yace

"Meyasa wayarki ayita kira ne bata shiga?

Dan marairaicewa tayi sbd sake basar da yanayin tace

"Tace wlh Yaya Maheer nima bansaniba kila network ne"

Maida kallansu kowa yayi akan Jannah suna mata sannu ta amsa tana murmushi a sake tace

"Nafa ji sauki since malaria ce da yanayin sauyin cima kawai amma sun bamu magani tin acan ma naji na fara samu sauki"

Ummah data riqe hannunta cikin nata sauke ajiyan xuciya tayi tana Hana su Maheer da Dad magana tace

"Buqatanmu lafiyarta da Kuma fatan ba wani babban ciwon bane Dan Haka mu godewa Allah"

Shima Dad sanyi da nutsuwa yaji ya qara mata sannu yana cewa taje tai wanka taci abinci ta kwanta ta huta.

Maheer binsu yayi da ido itada Fatma din da suka miqe take suna nufar daki kaman munafukai.

Ammar daya kasa cewa komai maganin yaso karba ya gani amma yanda Fatma ta riqe ledan maganin kaman rai da yanda tafin hannuwan Jannah sukai wani irin hasken daya sakasa kafesu da ido ya saka har suka shige bai samu cewa komaiba.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 58


Suna shiga daki Fatma ta isa gaban dresser ta janyo drawer ta saka ledan maganin ta rife ta nuf toilet da sauri sbd fitsarin tsoron kar a ganosu kaman zai zubo mata.

Jannah ma zama tayi bakin gadon tana sauke ajiyan xuciya tanajin ma kaman da gaske ciwon ya fara tafiya,

Falaq ce ta shigo da fiddausi dauke da tray na snacks da paper meat me dadi da sukai garnishing dasu cabbage and potatoes da mayonnaise.

Fiddausi ce ta hada mata ita Kuma Falaq ta hado smoothie Dan gasar yi mata girkin akai.

Murmushi tai tana kallan yanda suka ajiye mata komai akan table ta taso daga bakin gado tana dawowa kan couch ta zauna tana kallan samosa data balain shiga ranta tace

"Aikuwa duka zan cinye"

Miqewa tayi ta nufi bathroom da Fatma ta fito tayo wanka da alwala daga can daure da qaton towel daure a jikinta ta fito.

Fadawa tayi itama tayo wanka tareda alwalan tana fitowa sallah tafara yi kafin ta shirya cikin freesize riga da wando ta zauna gaban kayan tafara ci tana Jin Wani dadin papper meat din na ratsata tana Sha da smoothie da juice duka.

Fatma data dawo daga Palo dauko ruwa a fridge itama zaunawa tayi tana saka hannu suka fara ci kaman basa cikin damuwa komai.

Hadda fiddausi da Falaq din suke ci gabaki dayansu suna fira hankali kwance a sake.

Bayan suna gama magani Jannah Tasha daga nan ta Dan miqe kwance tana Jin jikinta da cikinta suna mata dadi ta ringa lumshe ido suna fira tana jinsu.

Falaq data ga yanda takeyi ta fara massaging mata kafarta cikin kauna da kulawa.

Har ishai suna dakin Saida Ummah ta shigo da Kanta ta kirasu suka fito anan dining din palonsu zaadens sukaci dinner gabaki dayansu harda Ummah dasu Falaq da fiddausi masu aiki suna serving nasu.

Suna gamawa anan akaita fira har dare sosai tukuna fiddausi ta kama Falaq suka koma samansu.

Jannah ma duk yanda Ammar yaso samun daman fira da ita sbd kewanta da yayi bai samu damar ba sbd baccin dayake cike da idanuwanta.

Shigewa tayi itada Fatma Maheer daman yana daki yanata process din nema musu aiki mekyau daya duqufa kwanakin a laptop.

Garba ma yana daki ya shiga wanka yana fitowa yayi shirin bacci da saka turare me kamshi da sanyi Wanda a yanzu Shima ya riga ya saba da wata irin tsafta da qamshi tareda sanin darajar Kai sbd zama cikin zaadens musamman Ammar dayake kokarin sauyasa sbd yanason duk inda zasu su tafi dashi Dan ingantasa ya maidasa tsayayyen namijin daya San kansa.

Ammar ma miqewa yayi bayan shigewan Jannah ya yiwa ummansa Saida safe ta amsa cikeda kulawa tana Masa addua kafin ya yiwa Dad ya nufi daki.

Dad da umman ne kadai suka rage a palon Dan haka Ummah taje fridge ta daukowa Dad din ruwan dayace yana buqata ta doro a tray me kyau da cup ta dawo ta ajiye gabansa tana Daukan roban ruwan ta bude ta zuba Masa ta miqa masa ya karba yana kallanta a natse cikeda kulawa.

Ruwan yasha a natse yana riqe hannunta cikin nasa yace

"Thank you Allah Miki albarka"

"Amin" tace tana murmushi ta Dan kallesa tana son janye hannunta ya sake riqewa cikin nasa yana cewa

"No Fatima"

"Hanya ta kalla tana murmushi tace

"Yara fa zasu iya sake fitowa"

Baice komaiba ya miqe yana riqe da hannunta suka nufi hanyar bedroom dinsa yana cewa

"Koyaushe zancenki Yara,
Kulawanki ma yanzu duka akan Yara ne Fatima"

Shigewa dakin sukai tana kasa basa amsa sbd zame hannunta datai ta nufi bathroom sbd alwalan sallan ishai da bataiba se yanzu.


Mama da tin tafiyar AZIZ tayi tafiya kauye washe gari sai gata ta dawo bayan fiddausi da Falaq da sukai murna da dawowanta babu Wanda yabi ta Kanta tinda daman dai Zaadens ba Shiri sukeyiba hakama Nicky tinda ta dawo asibiti take cikin damuwa da kunci madam Sisi ce kawai take kulawa da ita sai fiddausi dake kokarin ganin koyaushe ta fito taci abinci sbd kusan kulawan duk ahalin LIMBA kaman a hannun fiddausin take yanzu.

Tsaraban kayan ciye ciyen kauyen da mama ta saba ita ta kawo musu su fiddausi sukaita murna Jannah ma da suka shiga ranta sosai da ita aka cinye tas da Fatma.

Se dare Jannah ta Taho har sama har dakin Maman itada Fatma suka gaidata cikeda girmamawa tareda mata barka da dawowa.

Zubawa Jannah idanuwa Mama tayi bayan ta amsa gaisuwan tana kallanta gabaki daya tana ganin sauyi me yawa a tattare da ita.

Bata kawo tinanin komaiba itama sbd sanin ko aure Jannah din batada shi bare ma wani yayi mata tinanin ciki indai ba andaura mata aure da Ammar bane bayan Bata nan har aka samu cikin.

Ficewa sukai suna fitowa Ummah na isowa kofar dakin Maman wadda haryanzu basu fuskanci juna ba sbd AZIZ na tafiya Mama tayi tafiyarta se yanzu.

Ajiyan xuciya Ummah ta sauke a hankali tana sake Jin dukkanin damuwa da Wani dattin tinani akan Sakina yana sake wanke mata sbd duk laifin da Sakina da kuskuren datai kauna da irin riqo da sadaukanwa da uwa data zama ga AZIZ da Ummitah ya take duka laifin da kuskuren Dan har ita har AZIZ har Ummitah babu abinda zasu iya biyanta dashi har abada,

Kuskuren datai shedan ne Dan zuciya sukaci galaba akanta sbd irin kaunar datake wa AZIZ da kishin uwa akan danta daya shigeta Wanda babu Wanda ya wuce Hakan ta faru dashi a cikin uwaye da dama,

Hakama duka kafin wannan ita kanta bazata manta wacece Sakina a rayuwarta ba sbd itace ta zama gatanta Dana AZIZ tin Bata haifi Ummitah ba bayan rasuwar mijinta.

Ita a gurinta komai ya wanke ya wuce tinda shi kansa AZIZ din baiyi fushi da itaba duk girman laifin ya barshi tinda dai uwarsa ce ba yanda zaiyi da ita dole sai hakurin Dan a gurinsa idan har zai iya dagawa Ummah murya to zai dagawa Mama idan Kuma bazai iyaba to har abada bazai iya dagawa Maman ba Dan dagawa Mama murya kaman dagawa Ummah ne shiyasa ma kawai ya hadiye bacin ran da fushin ya kaurace mata sai bayan da ya gama digesting abin Kuma ya sameta da kansa.

Hannu Ummah ta miqa a natse ta buga kofar dakin Maman tana Dan dakatawa.

Mama data gama waya da AZIZ din Wanda yayi mata barka da sauka lfy ajiye wayar tayi tana cewa

"Yes waye ne?ya shigo"

Bude kofan Ummah tayi a natse tana shigowa fuskanta a natse babu fushi babu matsewa babu komai.

Kallanta Mama takeyi cikeda mamaki da wata irin kunya da damuwa kafin ta dauke Kanta tana kasa kallanta a sanyaye tace

"Bismillah zauna"

Zaunawa Ummah tayi a kan lallausan sofan dake dakin tana kallan Maman tareda kokarin kawar da Jin nauyin junansu tace

"Barka da dawowa,ya hanya?ya mutan gidan?

Batareda mama ta kalleta ba nauyinta na qaruwa tace

"Lfy kalau alhmdllh,mutan gida ma duk lfy suna can"

Shiru sukai babu Wanda ya sake cewa komai sbd Mama Bata sa ta inda zata fara ba Dan kunya da baqin cikin duk abinda ya faru datake ji.

Umman ce ta sake motsawa tana Dan sake murmushi me sanyin sauti tace

"Sakina kiyi hkr da duka abinda ya faru Wanda ya faru ne bana cikakkiyar hankalina,

Kuma yanzu Dana dawo daidai din nayita son magana dake amma ban samu damar ba sai gashi kinyi tafiya"

Mama da jikinta ya dauki dumin sanyi da kunyar duniya gabaki daya dagowa tayi bakinta na nauyi tace

"Fatima kina bani hakuri ne sbd ki ragemun girman kunya da abin kunyar dana aikata ne,

Girman kunyar danake ji ai bazai ragu ba sbd nayi kuskuren daya kusan batar Dani gabaki daya amma ki sani wallahi tallahi Fatima banyi komai Dan wata boyayyar manufa danake da ita ba sai akan tsoro da fargaban rasa AZIZ Wanda nake Jin tsananin kishinsa a matsayin Dana bana kaunar duk Wanda zai rabani dashi ko nesantani dashi shine kawai abinda ya rife zuciyata, tinanina da Imani na amma bayan wannan walhi Fatima ban taba binki da Wani sharrin ko manufarba ke da yayanki.......

Katse Ummah tai da girgiza kai tana cewa

"Sakina ban taba zargin da wani abin ba nima bayan wannan Kuma tinda Allah ya kawo saukin abin ai shikenan,

Sannan babbar maganar da nakeson fada Miki itace ki sani ABDULAZIZ danki ne wlh duniyar nan har lahira,

Ban dawo da rabaki dashi ba sbd kece kika fini saninsa a yanzu Dan kece kikai rayuwar datafi tsayi dashi akan ni,
Duniya ma batasan kowace uwar AZIZ din ba bayan ke,
Kece uwarsa a baya Kuma kece uwarsa a yanzu,
Bazan iya rabaku ba sbd akwai shaquwa da kauna tareda girmamawa a tsakaninku,

Ni ina da wasu Yayan a yanzu da zan zame musu uwa har karshen rayuwata Dan haka kema bazan rabaki da naki ba,

Dawowana rayuwarku babu abinda zai sauya Miki keda AZIZ sbd shi kansa bazai yadda wai ya juya ko sauya Miki ba Dan Kuwa shi din Dan halak ne Dan haka ina fatan basai munyi janye janye ba komai ya wuce zamu yafi juna"

Ajiyan xuciya da numfashi Mama ta sauke hawaye na gangaro mata sbd AZIZ da mahaifiyarsa sun nuna mata kyakkyawan zuciyar data Fi tata tsafta.

Ummah ganin hakan ta qara Bata hakuri tana Dan kokarin Jan Maman da firar baya sbd son su sake kaman yanda suke tin farkonsu.

Kuka sosai Mama ta fasa a gaban umman tana Bata Wani irin hakuri harta saka Umman kuka sukai abinsu suka Shirya daga nan suka koma Tina baya Dan shine zai dawo musu da cikakkiyar kaunar da sukewa juna me karfi da tsafta.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 59


Har dare Ummah na tareda Mama Dan haka ma ko dinner tare sukai gabaki dayansu anan bangaren Bata je gurinsu Dad ba.

Jannah ma a cikinsu tayi dinner tareda su Falaq Maman nata kallan Jannah tanajin zuciyarta Bata nutsu ba da sauyin dayake tattare da ita sbd AZIZ dinta daya gama mutuwa akan Jannah din gashi kaman da akwai matsala.

Ita dai Jannah Bata wani riqe Maman a rai ba sbd haryanzu ita takewa kallan mahaifiyar AZIZ dinta Ummah Kuma ummanta ce kawai.

Sun gama dinner a dakin ummah tayi kwanciyarta karshe ma anan ta kwana da zazzabin dare batareda ta bari Umman ta sani ba.

Washe gari gabaki dayansu suka fita su Biyar Ita, fiddausi,Falaq, Ummah da Fatma fiddausi ce tajasu a mota suka tafi gyaran Kai sbd kowannensu yana buqata.

A wani tsadaddan spa sukai branching Wanda Already fiddausi da Falaq nada Vip card a gurin already Jannah ma tanada shi itada Anny tintini amma yanzu ta rasa card din amma kusan dayake akwai sauran maaikatan baya a gurin suna zuwa suka ganeta tareda tarbanta cikin tsananin girmamawa da rawar jiki.

Bangaren Manyan clients nasu aka kaisu sukai booking gurin gabaki daya sbd Ummah da fatma da ta Dan iya zuwa irin guraren yanzu itama sbd ko Lagos kusan so uku suna zuwa irin guraren.

A gurin suka wuni sai yamma suka baro suka dawo kowannensu fuskansu na daukan ido hakama skins nasu sai qamshi sukeyi me dadi.

Tinda suka dawo Ammar yake bin Jannah da Kallo me sanyi sbd ta sake zama kaman wata tauraruwan rayuwansa amma hakanan yakejin jikinsa na sanyi akan Jannah din da kansa.

Fatma ma garba dayake ganin shi gabaki daya ta sauya Masa tayi wani irin haske da ja ta sauya kaman ba ita ba yauma ganin yayi ta qarasa sauya Masa sai tsokanarta yakeyi da Fatma ce wannan ko baturiyar Fulani.

Dad take fadawa yace ta kyalesa neman magana yake.

Maheer dai Shima magana ne kawai baiyiba amma Fatman ta sauya gabaki daya a idanuwansa dayake tinanin ko shi kadai ya sauyawa Ashe ba shi kadai bane amma gudun ace Shima tsokanarta yayi tinda girmamasa takeyi sosai sai yayi Shiru abinda.

A gajiye suka dawo Dan haka babu wata hayaniya a gidan dukansu kowa yayi daki yai wanka basu fitoba har washe gari.

Kwana biyu Jannah ta samu karfin jikinta duk da kowane dare da qananun zazzabi take kwana amma babu Wanda ta bari ya sani daga ita sai Fatma suketa nuku nukunsu da neman mafitan yanda zasuyi gashi kaman kada su San dashi sai taga cikinta yana kokarin fara Dan kumbura tinda an sake daukan kwanaki da sanin.

AZIZ kowane dare suna wayansu a Wayan Fatma Bata fada Masa ba Kuma tanata tsoron tinanin terminating cikin amma Shima Hakan tana tsoro.

A bangaren Nicky ta rame tayi fayau ta zama kalar tausayi sbd babu me kulawa ta Kanta,
Mama ce take kulawa da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login