Showing 9001 words to 12000 words out of 150681 words
lokacinda batada sauran hope
So su modibbo sune mutanen da har abada bazata ciresu a wainda suka sake kafa sunan Zaadens dasuba.
Su kansu su modibbo Jannah itace sukafi kauna fiyeda shi Kansa Dad a cikin Zaadens sbd tafi kowannensu shiga rai da sanyin hali dan haka su kawu kudi suka ciro tareda galan biyu na madarar shanu me kyau suka bata kyauta tareda saka mata albarka suna cewa har abada ita din tasu ce ko basu taho ziyara sbd kowaba zasu ringa zuwa sbd ita Musamman idan ta samu mijin aure.
Murmushi tayi zuciyarta na cika da kewansu da jin kaunar da suke mata har cikin ranta.
Dad tareda su modibbo yaci abincin Daren ranar shima Ammar fita yayi da Garba zuwa ganin sauran abokan garban da sukaita dawainiya dashi yai musu godia yanajin sabon da sukai Yana taba zuciyarsa sbd sun kula dashi da zuciya daya batareda sun damu da basu taba saninsaba sunyi hidima dashi dan har wani kauye suke zuwa dashi me nisa akan jaki ko Keke sbd yasha ruwan famfo me kyau da sukaga baya wani iya shan ruwansu sosai.
Ayau ya sake jin ciwo da radadin mummunan talaucin dayake ciki sbd yaso yayi musu kyautar da zata sauya rayuwarsu gabaki daya,
Da a baya ne agogonsa daya kadai idan ya basu suka siyar sungama tsiya da xaman kyau bare idan ya dora hannunsa akan cheque ko Dollars idan zai basu baisan iya adadin dama zai iya basu ba sbd rama alkhairinsu gareshi amma duk da hakan ya musu alkawarin duk yanda rayuwa tayi dashi bazai manta dasu ba zasu sake dawowa garesu.
A cikin Daren su modibbo basu rabu da Dad ba sai dare sosai bayan sun yanke shawarar da Garba da Fatma zaa tafi aikin sbd duk aikin wahala ko karfin da basu saba dashi ba su garban suyi Wanda Jannah yafi karfinta kuma Fatma tayi.
Girgiza kai Dad yayi yace
"Indai zaa tafi dasu to zasuyi nasu aikin ne duka mu karbi halak din mu
Muma zamuyi namu aikin da karfin da muke dashi muci halak dinmu"
Da wannan shawarar aka kwana idan Allah yasa an dauki su Fatman a cikinsu Zaadens din shikenan suma sun samu Tara dukiyar da iyayensu zasu dangwali arziki.
A cikin Daren garba ya sake komawa yayi sabon bankwana da abokansa hakama shi da Fatma suka hau shiri.
Washe gari asubar fari dukkanin jamaar gidan suka tashi bayan sallar asuba babu Wanda ya sake komawa bacci.
Sabuwar madara aka dumama musu dukansu suka sha kafin suka fito ana jimamin rabuwa da juna suka hau mashin mashin aka wuce hadda su kawu da suka rakasu har kauyen da ake shiga mota suka wuce.
Hadda modibbo aka tafi sbd shine zai rakasu yaga har inda suke kuma ya kaisu gurin Alh Siddeq da Zai gabatar dasu ga kamfanin.
Shiru kowa yayi a tafiyar sbd kowa a yanzu jikinsa yayi sanyi sbd basusan rayuwar da zasu tararba kuma Wadda basusan wace iri bace datake saka zuciyoyinsu wani irin rashin sukuni da tsoro harma da fargaba.
Wuni Guda suna tafiya kafin suka iso a gajiye.
Kai tsaye gidan da dakinsu yake inda suke sauka suka nufa.
Kayansu suka ajiye suka fice sallah aka bar su Jannah a daki suma sukai sallolin dake kansu suka zauna suna kallan dakin shiru babu me magana.
Bread da kosai da shinkafa da wake Maheer yazo ya basu da ruwan pure water tareda maganin mosquito da ashana yace su rufe dakin dakyau idan zasu kwanta sukace to.
Abincin sukaci suka koshi Jannah tasha madaran shanu suka kwanta tareda rufe dakin dakyau.
Su Dad kuwa a masallaci suka kwana su dukansu saida sassafe suka dawo dakin suka karya gabaki dayansu a tare kafin kowa ya shirya suka fice zuwa office din Alh Siddeq din Wanda tin jiya suka sanar dashi zuwansu.
Koda suka isa shima kai tsaye su yake jira dan haka a bus din office aka daukesu zuwa wani lafiyayyan kamfanin da ya saka hankalin modibbo da Garba tashi harma da Fatma,
Su kuwa su Dad ganin tsarin kamfanin tin anan sukasan duk Wanda zaa kaisu gidansa da gasken tsayayyen Kansa ne tinda a gidansa baa wani jin hausa ace masu aiki ma sai masu degree da Masters akeso.
Gurin jira aka kaisu suka zauna Alh Siddeq kawai ya wuce ciki.
Bai wani jima ba dayake ya riga ya shigar da sunayensu d matakin karatunsu ya fito aka fara shiga dasu daya bayan daya dan interview.
Dad aka fara yiwa Wanda iliminsa kadai ya kashe baqon da aka dauko daga Lagos da tantance maaikatan kamfanin na daukan masu aiki ga manyan qasa kawai da Wanda kudinsa yakai.
Baa qasar yake ba tsawon 2years shiyasa bai wani San labarin Zaadens ba da abinda yafaru dasu dan haka take Yana yiwa Dad da Maheer da Ammar da Jannah ya saka hannu ya daukesu duka familyn batareda ma yayiwa garba da Fatma da Alh Siddeq ya tayasu rufa rufa aka shigar da sunayensu tareda approving na daukansu aka ce gobe zasu tattaro su dawo inda aka tanadar musu na zaa koya musu aiki na sati biyu kafin a miqa su 4&4 MANSION.
suna dawowa gida shiri sukai washe gari tinda safe suka isa kamfani aka daukesu da mota aka kaisu wani lafiyayyan gida me tsari da jin dadi daidai gwargwado kowa aka basa dakinsa Banda Ummah da aka baro gida tareda modibbo da wata da zasu barwa dakin idan sun tashi ta ringa kulawa da Ummah kafin su fito.
Da farko tsoro fatma ta ringa ji Jannah na taimaka mata hakama Garba dole Ammar ne ya ringa wayar masa da kai.
A cikin sati biyu an sauya musu suturar sakawa sbd bazasu da tsumma ba mansion din kamar yanda akace,
An koyar dasu ayyuka da dama hakama su Dad an koyar dasu nasu suna cika sati biyu cif harsun fara canjawa sbd sauyin guri me kyau aka daukoso zuwa mansion sedai saida aka biya dasu aka dauko Ummah Wadda Dad ya riga ya shigar da sunan matarsa ankuma bSa damar shiga da ita sbd idan aka rasasu bazaa taba samun candidates kamarsuba da iliminsu yakai.
4&4 MANSION shine sunan da suka gani baro baro a rubuce jikin qaton mansion dinda yaci uban nasu a lokacinda suna Zaadens dinsu.
Wani irin tsoro ne ya rufe Garba da Fatma Musamman ganin wasu irin samudawan securities na jamian tsoro zagaye da gate din.
Jannah kuwa 4&4 din ta zubawa ido ranar daurin aurenta n dawo mata sbd 4th April wato 4 ga watan 4 shine date da bazata taba mantawa ba rayuwarta.
Dauke idanuwanta tayi daga kan sunan tana lumshe idanuwanta tareda hadiye radadin daya tasowa zuciyarta sbd radadine datai alkawarin hadiyewa tabinne abinda yake kawosa har abada.
Ammar ma kalmomin ne suka tsaya suka soki zuciyarsa sbd sune numbers da bazai taba mantawaba.
Bude musu mahaukacin gate din akwai bayan angama duba takardun da aka kawusu dasu daga kamfanin.
Gate na biyu aka isa dasu Wanda daga shi suna shiga to shikenan sun shiga ba fita saida izini ko babban dalili.
Suna gani aka rufe gate na biyu rufe sunajin jikinsu na mutuwa sbd ta tabbata daga yanzu su Yan aiki ne dake karkashin me gidan nan da iyalansa.
#MAMUH
#BEST LOVE
#HOT LOVE
#HOT ROMANCE
#AY LIMBA
#ZAADENS
#CRAXYLOVE
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899
*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 7
Wata sabuwar duniyar da suka manta yanda take ne suka samu kansu ayau cikinta Wadda koda sun farfado basu taba saka ran zasu shigo cikinta ba a shekarun kusa kusa ba sbd gabaki daya 4&4 mansion turai ce kawai zasuce me zaman kanta a Nigeria dan kuwa tinda suka shigo gate din farko suka San sun shigo wata duniyar ce kawai ana rufe second gate kuma sukasan sun bar qasarsu a yanzu duniyar Familyn 4&4 suke ciki tsundum wadda babu komai a cikinta tukuna sai daular duniya da wata irin shiru da nutsuwa tareda kwanciyar hankali me sanyi da tsafta da suka ji suna samu.
Garba da Fatma da tinda Allah ya halicce su basu taba gani ko jin labarin irin wannan gidan ba da kusan komai nasa kashe musu ido yake hankalinsu mummunan tashi yayi sedai tsoron securities dake zagaye da gidan da bindigogi ya sakasu hadiye tsoronsa a cikinsu Wanda hakan ya ringa juya musu ciki.
Jannah da jikinta har lokacin yake a mace da sunan mansion din daya tinatar da ita rana mafi girma da muni rayuwarta itama hadiye radadin zuciyarta tayi tana jin wani irin ciwo a zuciya da kirjinta.
Ammar da bayan Jannah shi kadai ne ya riqe date din aurenta da LIMBA fes a cikin Kansa sbd shima bayan ranar rasuwar mahaifiyarsa ranar itace rana mafi muni da girman da bazai taba mantawaba a rayuwarsa sbd a wannan date dinne Jannah ta auri waninsa wanda a ranar zuciyarsa ta mutu a kirjinsa mutuwar da har yau bata farfado ba har sai ranar daya auri Jannah ta zama mallakinsa sbd baisan wane irin girman so yakewa Jannah Zad ba.
Dad da Maheer kuwa ajiyan zuciya suka sauke atare cikeda samun nutsuwan zuciya da ruhi sbd sunzo inda zasuyi aiki da karfi da lafiyarsu sbd Jannah da Ummah su samu rayuwar jin dadi da kwanciyar hankali sbd anan tsaro da kariyar da Jannah da Ummah zasu samu ko a nasu mansion dinne iyakacinsa kenan sbd ko qara da hayaniyar waje ko kadan baka jiyowa duk da wata irin anguwa ce da kusan tsaro da tsari tareda rashin hayaniyarta zai tabbatar maka da sai Wanda yakai iya kaiwa yake zaune a cikinta.
Hannun Ummah dayake hannun Dad ya sake riqeta da kyau Yana kallanta cikin kulawa zaiyi magana Chief ta maaikatan gidan ta fito babbar mace da ita Amma ba sosai ba hakama da gani batada sakin fuska ko sakewa ta qaraso tana kallansu daya bayan daya ta tsayar da idanuwanta akan Jannah Wadda take tinanin kamar ta taba ganinta sedai kuma ta kasa tinano inane dan haka ta gyara tsayuwa tareda bude baki ta amsa gaisuwarsu ta ciro wayarta daga aljihun kayan jikinta ta bude sakon da tin jiya aka turo mata na ayyukan da aka riga aka rabawa kowannensu tana sake karantawa tana fadawa kowa gurin aikinsa tana rakasu gurin daya bayan daya har aka kammala kafin ta sake kallansu tace
"Familyn gidan gabaki daya basa qasar amma suna gap da dawowa dan haka kafin dawowansu kuyi iya kokarin tabbatarda Kun sabu da aikinku babu matsalar komai sbd kwata kwata a tsarin ahalin gidan basason matsala ko hayaniyar matsalar,
Akwai me gidan kwata kwata Wanda bama lallai zaku taba ganinsa ba so ba amfanin ku sansa sbd baya lokacin kowa a duniya idan Yana gida bayan na 'yarsa Guda daya tak Wadda itace kusan zuciyar gidan sai ku kiyaye,
Sai mahaifiyarsa da qaninsa sai kuma matar da zai aura inshallah itama kuna buqatan kiyayewa sosai sbd kwata kwata bata son kuskure koman qanqantarsa hakama kusan itace take juya iko a kaf maaikatan gidan sai kuma Yar uwar mahaifiyar matarsa wadda itace tamkar uwa kokuma ace yaya ga 'yarsa dan haka ina sake fada muku da murya me kauri akan ku kula sosai kusan abinda ya kawoku,
Baa fita koina 24/7 kuna cikin 4&4 hakama duk me magana ko wani abin daban ya dameni da zancen.
Tafiya tayi suka bita zuwa can bayan mansion din Wanda acan akai bangaren masu aiki anyi tazara tsakaninsu da bangaren masu gidan hakama bangaren masu aikin me girma da tsari sosai wanda shi kansa bangaren masu aikin kamar qaton gidan wani me kudin sosai sbd hatta ac dasu fridge akwai da lafiyayyun dakuna da gadaje da beddings da komai me tsari da daula.
Ajiyan zuciya Ammar ya ringa jerowa Yana hamdala a cikin ransa sbd Allah ya kaddari ya dawo cikin rayuwar jin dadin dasuka rasa hakama a yanzu zai samu nutsuwa da kwanciyar hankalin aikin wahalar ma kowane irine.
Bangaren maza daban hakama na mata amma akwai kofar baya data hadesu dan haka hankalinsu ya sake kwanciya hakama gurin cin abincinsu daya dan haka sai ya zamana kamar palo ne da dakuna tamkar dai sun kama selfcon.
Dakin Jannah da Fatma da Ummah daya da gadajen kwanciyar mutum daddaya Guda uku sai kowa nasa daban sai rug carpet me tsananin laushi da kyau da haske sai mirror da AC da wardrobe itama kowa tasa daban da toilet dinsu a cikin dakin dashima yake irin na masu hali sosai.
Suma dakin su Maheer hakanne sedai su gado uku ne dan haka aka bawa Dad daki daban shi kadai shima komai aciki dan haka dukkaninsu suka samu nutsuwar da suka dade basu samu ba daga nan Madam Sisi ta juya tabarsu zuwa nata dakin dayake daga baya babban daki ne ita kadai dayafi nasu duka tsari.
Kayansu suka ajiye kowannensu ya zauna Yana sauke numfashi kafin Jannah ta kama hannun Ummah zuwa toilet ta nuna mata yanda zatai amfani da komai kafin ta barota tayi abinda zatai tayo alwala ta fito.
Fatma ce ta shiga bayan fitowan Umman itama Jannah ta sa fahimtar da ita komai tayo alwala ta fito kafin Jannah din ta shiga karshe.
Sallah sukai dukkaninsu suna idarwa wayar dake dakin ta hau ringing Jannah ta miqe ahankali ta isa ta miqa hannu ta dauka a natse tace
"Yes ma'am?"
Madam Sisi ce kai tsaye tace su fito su tafi kitchen.
Cikin sanyi da nutsuwa Jannah din tace "ok"
Ajiye wayar tayi jikinta na mutuwa dan batasan ta yanda zasu ringa aiki a karkashin mutanen da batasan yanda zasu ringa treating nata da familynta ba.
Gurin Dad Jannah takai Ummah har dakinsa kafin ita da Fatma suka wuce zuwa lafiyayyan kitchen din da acan ne zasu ringa aiki kafin masu gidan su dawo su koma aiki acan na cikin mansion din na masu gidan.
Koda suka isa akwai wata me aikin da suka gani dazu tanata aikin abinci dan haka kai tsaye suka saka hannu tana sake musu bayanin aikin suna yi.
Duk da aikin gas ne kuma a tsararren kitchen amma sbd abincin mutane da yawa ne hakanan sukaji sun aikatu sbd ana gama na rana aka Dora na dare ba bata lokaci kuma lafiyayyan abinci akeyi Wanda yake cikeda lafiyayyun kayan abinci.
Sai bayan ishai suka baro kitchen din sbd duka kayan abincin da akai aiki dasu saida aka wanke aka maida kitchen din kamar baayi aikin komaiba.
Jannah bata iya cin abincinta na dareba sbd cikinta daya cunkushe da yanayin kamshin abincin da kuma na rana da bai gama narke mata ba datake ji.
Suna isowa daki wanka tayi da sabulun dove da shine aka raba musu kowa anbasa set na kayan wanka da sabulu isashen da zai karshen wata hakama toothbrushes da toothpaste masu kyau da tsada duka an raba musu da body oils masu kyau da body sprays da qarin kaya kala bibbiyu sbd baa bari kazo da wasu tarkacen kaya.
Tana fitowa wankan sallah tayi ko Mai bata iya Shafawaba ta zame ta kwanta.
Ummah dataga yanda gajiya take bayyane qarara a tattare da ita zaunawa tayi kusa da ita tana cewa
"Ummijan kin gaji ko?
Gyada kai Jannah tayi tana matsowa ta kwanta jikin Umman tana cewa
"Ummah koina ciwo yake mun"
Mai Umman ta miqa hannu ta dauko tana budewa tace
"Gobe zan tayaki sbd kada ki gaji irin haka,
Banason kina gajiya ke kadai kinji"
Man ta fara Shafa mata a kafafu tana Danna mata kafafun ahankali cikeda kulawa.
Lumshe idanuwa Jannah tayi tana jin dadin yanda Umman ke mata tausan tace
"Ummahna bazaki iyaba kuma nima banason kiyi aikin ki gaji irin hakan ki bari duk ranar dana gaji zance ki tayani kinji"
Shiru Umman tayi sbd bata yadda da hakan ba.
Fatma ma wanka tayi Tai sallah Amma sanin batada me bata irin wannan kulawan ya saka tana gama sallah ta hau gadonta ta kwanta take baccin samun lafiyayyar katifa da AC ya dauketa hadda wani irin gurnanin bacci kamar ba maceba.
Jannah ma a jikin Umman tayi bacci hakama itama Umman data kasa tadata a gurin bacci ya dauketa se dare sosai Jannah na farkowa ta tashi ta tada Umman suka hau gado ta rufe Umman kafin ta koma nata gadon ta kwanta take bacci me nauyi ya sake dauketa.
Washe gari Ammar da wuri ya tashi yayi sallah ya ringa yiwa Allah godia sbd rabonsa da baccin nutsuwa da kwanciyar hankali irin na yau tin ranar da AZIZ LIMBA ya bayyana rayuwarsu dan haka yau da wani irin nutsuwa da sanyin zuciya ya tashi ya kwana a cikin lafiyayyan guri da AC da bargo me kyau yayi wanka da ruwa me tsafta da dumi a cikin toilet mafi nutsuwa hakama da soap me kyau duk da kwata kwata ko kusa bai kai Wanda yake wanka dashi a baya ba sbd sabulun wankansa a baya kadai zai ciyar da wasu da yawa Amma dai a yanda rayuwa tayi dasu yanzu wannan dinma ai babban cigabansu ne wanka dashi dan haka wankan tsafta yayi yai brush da lallausan brush yana sake godewa Allah kafin ya fito aikinsa.
Kusan hakanne ya faru da kowannensu dan kuwa sunyi tashin nutsuwa yau kowa fuskansa bayyane da kwanciyar hankali suka fito ayyukansu.
Dad da Maheer ne securities din second gate dan haka uniform dinsu suka saka suka isa bakin aiki.
Garba kuma wankin bangunan gidan dana motoci da sharan harabar gidan tin daga first gate har second shakuwa Ammar duk wata flower da grass dayake gidan shine me kulawa dasu tareda harkar ruwa shima tin daga gate din farko harna biyun.
Breakfast aka kaiwa kowa wanda su Jannah ne sukai aikin Fatma ce tayi kaiwa kowa harfa securities na can babban gate.
Ummah baya yadda ba saida ta biyosu kitchen dan haka aikin yankan su albasa da bude Maggi ne kawai suke bata.
A kitchen suka wuni se yamma suka kammala komai aka kaiwa kowa nasa sukai wanka da sallah suka zauna hutawa.
Da dare gabaki dayansu sukaci abinci a tare a palon dayake nasu hankali kwance suna firarsu kowa na fadar yanda yafara ji akan aikinsa suna dariyan juna sbd sun ringa sun karbi wannan sabuwar rayuwar kuma.
#MAMUH
#LOVE
#4&4BEST LOVE
#AY LIMBA
#HOT LOVE
#BOSS GOING CRAZY FOR.......
#JANNAH ZAD
#FALAQ LIMBA
#ZAADENS
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 7
Wata sabuwar duniyar da suka manta yanda take ne suka samu kansu ayau cikinta Wadda koda sun farfado basu taba saka ran zasu shigo cikinta ba a shekarun kusa kusa ba sbd gabaki daya 4&4 mansion turai ce kawai zasuce me zaman kanta a Nigeria dan kuwa tinda suka shigo gate din farko suka San sun shigo wata duniyar ce